ZAFIN SO Page 21 to 30 (The end)




Baki d'aya ta rasa sukunin ta, har Skul d'in ma ta daina zuwa sai fama take da ciwo duk tabi ta rame, tun abun baya damun Mom har ya fara damunta, ta samu Dad da maganar, har sabbatun da tajita tanayi sai data fad'a mashi, tare suka nufi tinkarar ta a d'akinta tana kwance.
     "Yauwa Mom 'kwara da kika shigo, Mom gashi nan kullun yana zo mun a mafarki, wallahi Mom ina 'kaunarshi, bazan iya airen kowa ba sai shi, Dad ka taimaka ka nemo mun shi duk inda yake, indai da gaske kuna sona tou dole ku nemo mun shi saboda shine farin cikin rayuwata".

       Cikin tausayi Dad yace "Safna me kike fad'a ne wai? Waye shi a ina yake?",
        "Dad ban sanshi ba ban san inda yake ba, dan Allah ku nemo mun shi",
          "Ki kwantar da hankalinki Safna, kiyi min bayanin komai cikin natsuwa mana",
          Share hawaye tayi tace "Dad so d'aya kawai na ganshi a bakin wani layi, tunda na ganshi naji na kamu da sonshi, kullun idan na dawo Skul sai nabi ta hanyar amma bana ganinshi, shine kullun yake zo mun a mafarki, yana nufo inda nake, da zarar ya na nufo shi sai ya 'bace, Dad kullun haka nake".

      Sosai suka tausaya ma 'yar tasu, Mom ta matsa Inda take tace "kiyi ha'kuri kinji auta ta? Yau saura kwana biyar 'yar uwarki ta dawo, ki kwantar da hankalinki insha Allahu idan ta dawo za'a san yanda za'ayi".

    Cikin shagwa'ba tace "tou Dad zaku nemo mun shi idan ta dawo?",
       "Insha Allahu kuwa" ya bata ansa tare da goge guntun hawayen daua rage a fuskarta.

               Bayan kwana uku.
Shirye shiryen taryar Baby kawai sukeyi, hankalin Safna ya d'am kwanta saboda al'kawarin da Dad yayi mata. Sukam ma'aikatan gidan mu rna kawai sukeyi saboda sunji dad'in dawowar da Baby zatayi, dama kuma tunda Safna ta kamu da son Dream guy ta raga masu, sam babu ruwanta da kowa, hakan ba 'karamin dad'I yayi masu ba.

       Nawwaf da Hamza ne suka shirya suka nufi gidan Malan Shazali kamar yanda sukayi al'kawari. Sallamah sukayi ya fito dama ya shirya su kawai yake jira. Tafiya sukayi suka hau keke Napep har UMYU ta sauke su.
     Office d'inshi suka direct amma suka samu baya nan, har sun jiya zasu tafi wani Labourer yace "kaine Nawwaf Sani?",
      "Ehh nine" Nawwaf ya bashi ansa.
        Labourer'n yace "tou yalla'bai yace wai ince maku ku same shi a gida, wai kuyi amfani da wannan katin zaku gane address d'in" ya mi'ka mashi wani d'an card 'karami.

       Kar'ba sukayi suka samu wata napep d'in, kallo d'aya yayi wa card d'in yace "ai nama san gidan wannan, koba shi bane wannan mai kud'in? Wanda da yake aiki a Inland revenue daga baya ya samu d'aukaka?",
       Nawwaf yace "indai ka gane shi tou shine, bana son yawan magana".
       

A daidai 'kofar gidan mai napep d'in yayi parking. Alhaji Shazali da kanshi ya biya kud'in sannan suka nufi 'kofar shiga gidan.
      Direct suka shiga kasantuwar babu gate man tun tafiyar baba tsoho. Wani mai bama flowers ruwa suka gani Nawwaf yace "Dan Allah malan muna da tambaya",
      "Allah yasa na sani" ya fad'a yana 'ko'karin matsowa inda suke.
        "Nan ne gidan Alhaji Sani kuwa? Mun so tambaya tun a waje sai bamuga kowa ba har bakin 'kofar",
          "Ehh ai nan ne, Alhaji mai son mutane kenan, mara wula'kanci, sai dai kuma baya nan wallahi yanzu suka fita su duka gidan wai zasu taro babbar 'yar shi data dawo daga 'kasar waje",
        Yana cikin maganar sai ga Mati driver yace "ko kune wanda yace zakuzo? NAWWAF ko?",
        Saurin d'aga kai Nawwaf yayi yace "ehh mune",
         Mati yace "tou yace in kaiku d'akin ba'ki idan kunzo wai bazasu dad'e ba".

        Bayan shi sukabi har cikin wani katafaren d'aki mai d'auke da kayan jin dad'I da more rayuwa.
       Umurni yayi masu da su zauna kan wasu luntsumammun kujeru, zama sukayi suna ta f aman kalle kalle.


Bayan Mati ya bar d'akin ne Hamza yace "ohh! Masu kud'I suna jin dad'in su, kuga fa yanda d'akin nan yake dan'kare da abubuwan duniya, ga sanyi ta ko ina yana ratsa fata, 'kanshi kuwa sai ratsa hanci na yake, wannan fa itace aljannar duniya".

        Nawwaf yace "kai fa Hamza matsalata da kai magana gareka wallahi, yanzu miye amfanin hakan? Idan fa maeu gidan suka shigo ko kana so su raina mu ne? Dan nifa bana son raini kuma kafi kowa sani",
      Malan Shazali yace "ayi ha'kuri dai".

        Wata budurwa ce tayi sallamah hannun ta d'auke da serving tray tana turawa, har 'kasa ta du'ka ta gaishe su cikin ladabi sannan tace "ga wannan kuci kafin masu gidan su dawo".

       Godiya suka mata sannan ta tafi ta barsu. Food flasks d'in da aka zuba abincin kanshi abun kallo ne, cikin fasaha Nawwaf ya bud'e ya fara zuba yellow rice, d'ayan ya bud'e yaga vegetable soup da taji hanta da 'koda, zuzzuba masu yayi sannan yace wa maoan Shazali "ga naka", ya mi'kawa Hamza ma nashi sannan suka fara kwasar girki suna santi.

        Bayan sun gama tass ya zuba masu exotic drink a glass cups ya basu, shi kuma ruwan faro ya zuba saboda baya son za'ki sosai.

Murna sosai tayi lokacin data hango 'yar uwarta tna sauka daga jirgi. Da sauri tayi hugging d'in ta daidai isowarta wurin su. Cikin tausayi tace "Safna me ya same ki kika koma haka? Kinga yanda kikayi rama kuwa?",
      Kamar tana jiranta ta fashe da kuka ta rungume ta. Rarrashinta ta fara yi amma sam ta'ki yin shiru. Da 'kyar ta tsagaita da kukan suka nufi inda Dad da Mum suke.

       Sunji dad'in yanda suka ga 'yar su ta 'kara kyau abunta, dama kuma gata jar fata. Shiga motar sukayi suka kama hanyar gida.


              Dad da kanshi ya sauka ya bud'e gate sannan ya dawo motar yace "wallahi ina haushin rashin gate man d'in nan, gashi kuma mutanen yanzu wuyar yarda gare su, tunda Safna ta korar mana da gate man shiknan. Na yarda da mutumin nan sosai ban ta'ba zama da wanda naji lokaci d'aya ya kwanta min ba kamar shi, kawai sai dai na dawo na tarar babu shi, dama kuma ban san garin su ba a masallaci kawai muka had'u dashi".

        Baby tace "Dad wai ashe har yanzu Safna bata daina wannan halin ba? Ai ni nasha ta girma ta daina",
       Dad yace "ina kuwa zata daina? Ai banga ranar ba".

         Safna ta fashe da kuka tace "Dad ai fa tunda Aunty Baby ta dawo nasan bazaka sake sona ba, indai tana gida haka muke da kai". Kuka sosai t akeyi cikin si'kewar murya.
       Mum tace "gaskiya ku 'kyale mun 'yata ta huta, bana son ana mata haka fa".

      Da wannan maganar suka 'karasa cikin gidan fuskar Sagma duk hawaye ya bushe mata.

Duka ma'aikatan gidan suka fara du'kawa har 'kasa suna gaishe da Baby, saboda sunfi sonta Miy da kowa dake gidan. Fuskarta d'auke da murmushi take ansa gaisuwar. Mati driver yace "yalla'bai bakin ka fa sunzo tun d'azu kai suke jira",
      Dad yace "ok ka shiga kace masu ina zuwa".

        Abinciccika kala kala suka tayar kan dinning Zarah ta jera. Sallah kawai sukayi sannan suka fara kwasar girkin Zarah. Dady yace "gaskiya ina alfahari da yarinyar nan Zarah indai wurin girki ne, duk irin ba'kin da zanyi bana haufin ta".

       Mum tayi saurin 'bata fuska tace "tou ashe shi yasa nake barinka da ita tana dafa maka, tun da kai baka son girki na kullun sai dai na Zarah".
      Caraf Safna ta kar'ba tace "kema dai Mum tun yaushe nake ce maki ki bari in kori yarinyar amma kin 'ki bari, indai baki barni na koreta ba har hawan jini sai ta saka miki".

      Baby tace "haba Safna! Wai ke yaushe zakiyi hankali ki daina wula'kanta mutane? Safna kiji tsoron Allah! Duk wanda zaki gani a duniya tou yana da tashi darajar, kuma mutun da kike gani ba abun wula'kantawa bane, idan kuma baki daina ba tou wallahi dole akwai ranar dana sani".

       Mum tace "Allah ya rabata da dana sani, insha Allahu bazata ta'ba yin dana sani ba a rayiwarta.
     Murmushi Dad yayi yace "duk laifi na ne dana tado maganar ai, yanzu dai ba wannan ba, ina da ba'ki suna can suna jirana".

Mum tace "su waye?",
      "Wannan mai saida ruwan dana baki labari mana, Nawwaf",
       "Au! Wanda kace ya taimake ka ko?",
        "Ehh shi fa, nayi masu al'kawarin zamu had'u a office ne yau, so kuma sai ga batun dawowar Rabi'atu, shine na bada sa'ko idan sunje ace su same ni a gida".

       Mum tace "ok".
  Tashi Dad yayi yace "idan na shiga sai kuzo ku gashe su kuma". Bai tsaya jin amasar su ba ya tafi.

       Sallamah yayi suka amsa yace "afwan fa ma barku",
      "Babu komai" Nawwaf ya fad'a. Sai a lokacin Dad ya kula da malan Shazali, wata irin fad'uwar gaba yaji, kawai ya samu kanshi da son mutumin da bai ta'ba gani ba sai yau.
      Bayan sun gaisa su Mum suka shigo, itace gaba sai Baby da Safna bayanta. Wurin zama suka samu Baby ta gaishe su cikin girmamawa. Safna kuwa ko kallon arzi'ki baeu ishe taba. Sun d'auki kimanin minti biyar zuwa shida ta mi'ke tace "Mun na tafi sai kun shigo" fuskarta yatsine kamar mai tsohon ciki.
     Har ta tafi kuma ta waigo, had'a idon da zatayi kawai taga dream man d'inta. Idonta ta murza sosai sannan cikin tsoro tace "bawan Allah kayi ha'kuri ka tafi, kullun gizon da kake mun kenan, ka hanani duk wani jin dad'in rayuwa ta" ta juya ta kalli Dad tace "Dad kayi min al'kawarin duk inda yake zaka gano min shi amma ka'ki, Dad wallahi bazan iya rayuwa ba tare dashi ba".


Duka wurin kowa kallon ta yake yanda ta koma oamar mahaukaciya lokaci d'aya. Musamman ma Nawwaf da yaga tana nuni dashi alamar duk maganganun da take fad'I dashi take.

       Mum tace "wai Safna meke damun ki ne? Waye dream man d'in naki?",
       "Mum gashi nan a zaune, wallahi mum shine kullun yake zo min a mafarki, son shi ya zame min ciwo wanda bazan iya maganin shiba matu'kar ban aure shi ba" ta fad'a cikin kuka da 'karfi.

        "Safna wannan shine kike mafarkin?" Mum ta fad'a.
        "Ehh shine Mum, shikenan nasan ciwo na ya warke tun da gani gashi, ai zaka aure ni ko?" Safna ta fad'a tare da matsawa inda Nawwaf yake tana murmushi.

      Kyakkyawan mari Mum ta wanka mata, cikin fushi tace "Safna kina da hankali kuwa? Yanzu ke wannan matsiyacin kike so? 'Kas' kantacce mai tallar ruwa a baro? Baro fa yake turawa da jarkoki manya a ciki, Safna ki kalle ki ki kalle shi, ai wallahi The different is clear, tou tun wuri ma gwamma ki fidda son shi a ranki, saboda kinfi 'karfin wahalalle".
       Cikin tsawa Dad yace "ya isa haka, Hajiya bafa na son wula'kanci, dan me zaki ringa cima bawan Allah fuska a gaban shi?",
         "Ai kuwa cin fuska yanzu na fara matu'kar bai bar gidan nan ba, rufin asirin shi d'aya ne kawai ya tafi kar ya sake dawo wa, wama yasan ko asirce min 'ya yayi? Idan ba haka ba mai zai sa yarinya ta haukace lokaci d'aya akan shi alhali bata san shi ba?"


Nawwaf yayi sairin katse ta da "ke Hajiya ki kama kanki, wallahi kawai ina d'aga miki ne saboda ina ganin kimar mijin ki, amma daba haka ba wallahi ba'ayi wanda zai yi min wannan furucin in 'kyale shi ba, kuma da kike maganar ni wahalalle mai tallar ruwa a baro ai nan halaliyata nake, ni banga wahala anan ba, ki tambayi mijin ki kiji ai har sai da na'ki yarda da yace zai sama min aiki shi ya matsa lallai sai nazo, ki kama kanki wallahi nafi 'karfin ki, Hamza ku tashi mu tafi".

          Baby tayi saurin tashi cikin kuka tace "dan Allah kayi ha'kuri bawan Allah, ni kaina banji dad'in yanda take gaya maka magana ba, amma banda magani ne yasa nayi shiru, and zan ro'ke ka wata alfarma ka taimaka kayi min ita",
      Nawwaf yace "mecece alfarmar?",
        Magana tayi mashi da koni maribuciyar banji me tace ba, kawai dai naga ya koma ya zauna yana ajiyar zuciya.

       Safna tayi d'an guntun murmushi tace "zaka aure ni ko?",
      'Kara murtuke fuska yayi bai bata ansa ba.
       
        Dad yace "ya isa haka dan Allah, yanzu dai abunda nake so dakai Nawwaf ka saurare ni kaji me zan fad'a maka",
      Da 'karfi Mum taja Safna a dole sai sun bar d'akin amma sam Safna ta'ki binta, dole ta tafi ta barta anan.


Dad yayi gyaran murya yace "Nawwaf da farko dai ina mai baka ha'kuri da cin fuskarka da Hajiya tayi, nasan nine naja maka da nace maka ku same ni a gida, inda a office muka had'u da duk haka bata faru ba, sannan kuma ina so ka d'auka abunda tayi maka can tsakanin ku ne bata shafe ni ba, ka d'auka komai bata faru ba kuma zan baka aiki kamar tanda nayi al'kawari",
     Murmushin 'karfin hali yayi yace "babu komai yalla'bai komai ya wuce".

      'Kara matsawa Safna tayi inda yake tace "tou zaka aure ni?",
       Da sauri Dad ya daka mata tsawa yace "ku tashi ku tafi ku bamu wuri".
      Baby taja ta suka nufi 'kofar fita, juyowa safna tayi tace "dan Allah Dad kace kar ya tafi ya barni, wallahi ina cikin tsananin damuwa, nasan dan ya tafi bazai sake dawo wa ba saboda kar Mum ta 'kara yi mashi wani wula'kancin".

      Sosai safna ta bama Dad tausayi, gyad'a kai yayi cikin ranshi yace "insha Allahu zanyi bakin 'ko'karin samo maki soyayyar Nawwaf" a zahiri kuma yace "tou naji jeki".

        Haka ta fita tana waigen Nawwaf har suka bar arean d'akin.

Dad ya juyo yace "barin d'auko maku upper'n",
     "Tou" kawai Nawwaf yace yaci gaba da bin Dad da kallo.

       Da fitar shi malan Shazali yace "Nawwaf a ringa ha'kuri dan Allah, kasan Allah yana tare da mai ha'kuri, kuma indai kana shiga mutane dole ka rage wannan ZAFIN ran naka",
     Hamza yace "gaskiya ne kam, nima dai abunda na gani kenan, dan wallahi furucin da yayi wa matar nan shi yayi amma ni naji kunya, dan ji nayi kamar in fita in bar d'akin".

      Nawwaf dai baice komai ba sai kallo. Suna cikin haka sai ga Dad ya dawo hannun shi d'auke da takardu.
      Zama yayi ya mi'kawa Nawwaf wata takarda guda d'aya, Nawwaf ya kar'ba ya duba sosai yaga Upper ce.
       Dad yace "Nawwaf ka samu junior lecturer kasantuwar karatunka bayyi nisa ba, amma a ko wane lokaci zaka iya 'karo karatu don ka samu 'karin girma",
       Ya kuma mi'kawa Hamza wata yace "kaima ga wannan, zaka ringa share share da goge goge, kuma insha Allahu zaka ringa samun albashi mai 'kwarie".

       Godiya sosai suka yi mashi, ya fad'a masu cewa su fara zuwa aiki daga ranar Monday. Haka suka bar gidan cikin jin dad'I da farin ciki, malan Shazali ma ba 'karamun farin ciki yayi ba.

        A ranar Nawwaf ya shirya ya kama hanyar Bagaruwa dan ya shaida wa mahaifan shi.

Da shigar shi gida ya samu Abbah da Ummah zaune suna hira, yayi sallamah ya zauna inda suke. Ba 'karamin farin ciki sukayi ba da suka ganshi, Abbah yace "Nawwaf lafiya dai kazo yanzu ko?",
         "Lafiya lau Abbah, nazo na baku albishir ne",
        Ummah tayi murmushi tace "wane irin albishir Nawwaf?",
         "Yau dai na samu aiki, na zama malamin jami'ah".

       Sosai sukayi murna da jin haka. Abbah yace "aikuwa tare zamu tafi zanyiwa mutumin godiya, eaboda a wannan lokacin ba lallai bane a samu mutane irin shi",
       Ummah tace "lallai kam, nima dai sai inbi ku ayi dani",
       Nawwaf yace "ehh sai mu bari sai zuwa gobe mu tafi".

         Haka suka shirya washe gari suka kama hanyar Katsina, sai da suka biya ta gidan Malan Shazali dan dama haka yace dashi. Sun samu baya nan, Nawwaf ya bar sa'ko yace "idan ya dawo a fad'a mashi sunzo tare da babanshi, kuma zasu wuce gidan Alhaji Sani sai ya same su acan",
       Sun isa gidan daidai sallar azahar, sun samu Alhaji Sani ja shirin tafiya masallaci, yayi farin ciki sosai daya gansu, ya dai ga Nawwaf tare da wani tsoho da wata dattijuwar mata, yayi masu umurni da su shiga d'akin ba'ki. Ya koma cikin gida yasa Zarah ta kawo masu abinci.

       Suna cikin cin abinci ne malan shazali yazo, daidai shigar shi ne Alhaji Sani shima ya shigo, kawai gaban Safna ya fad'I, jikinta ya bata Nawwaf yana cikin gidan. Da gudi ta nufo d'akin ba'ki, ganin tana gudu ne yasa a rud'e Mum da baby suka biyo bayanta.

Tir 'kashi! Kome wannan had'uwar zata zama? Sai kuci gaba da kasnacewa dani don jin 'karshen labarin.





Da hanzari baban Nawwaf ya mi'ke tsaye cikin sar'kewar murya ya fara 'kokarin magana amma sam ya kasa, komawa yayi ya zauna ya ri'ke kai yama rasa abunda zayyi, ganin haka ne yasa maman Nawwaf cewa "malan me ya faru ne?",
     Bai bata amsa ba naji muryar Safna cikin kuka tace "Nawwaf ka taimaka ka rufa mun asiri ka aure ni, wallahi I cant live without youh, kai ne jinin jiki na, wallahi tunda nake ban ta'ba jin son wani namiji bayanka ba",
      Sai a lokacin ta kula da baba tsoho,
     Cikin mamaki ta zaro ido tace "baba mai gadi!"
       Shi kuwa Abbah tunda ya du'kar da kanshi babu abunda yake sai tariyo wasu abubuwa da suka faru a baya, so d'aya kawai ya d'ago kai ya 'kara kallon malan shazali da shima shi yake kallo, 'kara sunkuyar da kanshi yayi wasu zafafan hawaye na binshi.


A gaban baba Tsoho ta koma ta risinah tace "ban san da wane irin baki Zan maka magana ba, nasan naci mutuncin ka naci zarafin ka, na maka abunda duk wacce ta aikata shi tou bata cancanci a yafe mata ba, na kira ka da munanan kalamai, kuma tunda na maka haka ban 'kara samun natsuwa ba, tun tafiyar ka nake faman dakon son wanda bai san dani ba, bai san da halitta ta a doron 'kasa ba, na shiga tsantsar tashin hankali mara misaltuwa a dalilin sonshi, sai gashi kuma ashe d'anka ne na cikinka, yau gani a gabanka ina ro'kon alfarma a gareka akan ka taimaka kasa Nawwaf yaso ni, ka sani Baba tabbas Allah ya kar'bi addu'arka, a gabana ka d'aga hannu kace "Allah ya kawo ranar da nima zan ro'ki wata alfarma a gareka",
     Na kiraka da tsohon najadu, yau gani a gabanka na risinah ina mai baka ha'kuri, nayi nadamar munanan halaye na, nayi nadamar hud'ubar da Mum ke bani, nayi nadamar d'aukar kaina da nayi wata high class, nayi nadamar jiji da kai da girman kaina, sai gashi yau basu amfanar min da komai ba sai dana sani, da na sani kuma wanda bashi da wani amfani"

      Sosai Safna ke kuka ta ri'ke 'kafar wandon Baba tsoho da ko saurarenta baya yi.


Kowa idon sa akan Safna da Baba tsoho, sun dad'e a haka kafin Baba tsoho yace:" Duk kan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mad'aukakin sarki! Abunda na dad'e ina fata yau ya tabbata",
       Kowa ya maida kunnuwan shi ga baba tsoho dake bayani kafin yaci gaba da: "kunga wancan da kuke gani" ya nuna malan Shazali,
      "Ehh"suka fad'a su duka.
      Yace "d'ana ne Marwan",
    Bai gama maganar ba naji sallamar Dr. Nasir da matan shi.

       Sai a lokacin Baba tsoho ya 'kara rikicewa, Dr. Nasir da sauri yaxo ya rungumi baba tsoho yana kuka.
       Sun d'auki tsawon lokaci a haka kafin Dr. Nasir yace " Sani! Yau dai abunda muka dad'e muna ro'kon Allah ya tabbata, dama ance addu'ah bata fad'uwa 'kasa banza, yau dai gaka ga mahaifinka wanda ya haifeka",
       Ido bud'e Alhaji Sani yace "what? Dad! Kana nufin baba mai gadi ne mahaifina?",
       "Tabbas kuwa, ashe ma ka sanshi" dr. Nasir ya fad'a,
      "Ehh Dad, dan ma dai baka zuwa gidan nan ne ai da ka sanshi, ya dad'e yana aiki a gida na tun kafin mu dawo sabon nan",
       Dr. Nasir yace "tou shine mahaifinka, wannan wani dogon labari ne wanda bazai yiwu yanzu ba",
        Baba tsoho yayi sujada yace "Nawwaf yau kam Allah ya had'a ka da 'yan uwanka da na dad'e ina baka labarin rabuwata dasu, wancan shine na sani dan yana da shekara takwas muka rabu, shi kuma Sani ban ma sanshi ba, saboda a wurin haihuwar shi ne maman shi ta rasu".


Dr. Nasir ya sunkuya gaban malan Shazali yace "Marwan ina ka shiga tun shekarun baya? Munyi nemanka har mun gaji amma bamu same ka ba",
       Malan Shazali ya goge hawaye yace "nima dai abunda zan iya tunawa kad'an ne bada yawa ba, na dai san Mum ta aike ni da kud'I suka 'bata, ni kuma sai nayi tunanin zata duke ni idan na koma babu su shine nayita tafiya ba tare da nasan inda zanje ba, a hanya na had'u da wani mutumi ina ta kuka shi ya taimaka ya tafi dani gidan shi, ya saka min suna shazali ne saboda yaron shi mai irin sunan ya rasu, tun daga nan sunan ya bini, a hannun shi na koyi sana'o'in hannu har Allah yayi mashi cikawa lokacin ni kuma ina da 'karfin neman na kaina, nayi aure yanzu yaka ina da yara hud'u, dama tun ranar da Nawwaf ya fara zuwa wuri na nake jin shi a jikina, sai gashi kuwa ashe d'an uwana ne na jini uban mu d'aya dashi".
      AlhajI Sani yace "nima abunda naji knan a jiki na lokacin da Nawwaf ya taimake ni, ashe 'kani na n...",
     Bai gama maganar ba Safna ta mi'ke tsaye tace "kar ku raina min hankali mana, kuna nufin Nawwaf 'kanin babana ne kome? Kenan babu aure a tsakanin mu? Aikuwa bazan ta'ba iya rayuwar aure da wani ba",
     Tsawar da Dad ya daka mata ne yasa tayi shiru tana ajiyar zuciya had'e da kuka.


Baba tsoho yaita bata baki har tayi shiru, sun dad'e suna mayar da labari akan abubuwan daya faru ga kowa, baba tsoho ma ya bada labarin tun tafiyar shi prison har sako shi da akayi kasantuwar an gane ba laifin shi bane.

      Safna tayi nadama sosai dan kuwa har yanzu ji take ina ma ace mafarki ne take, ina ma ace zata auri Nawwaf, sai dai kuma kash! Hakan bazata ta'ba yi wuwa ba.
     Wannan labarin ishara ce ga duka kan masu hali irin na Safna, domin kuwa a kwaisu da dama wanda basa ganin kimar babban mutun. Allah ya shiryi masu irin wannan halin amin.

              Bayan wata uku.
Shirye shiryen biki ake sosai a familyn, duba nakai domin ganewa Ido na wanda akewa biki, can na hango Zarah mai aikin su Safna taci ado cikin alkyabba fara, daga gefenta kuma Nawwaf ne yanata fara'ah.
      A d'ayan gefen kuma Baby ce na hango itama cikin wata jar alkyabba tasha ado, hannunta ri'ke da wani kyakkyawan matashi dogo fari mai tsarin halitta sai fara'ah suke.
       'Kara murza ido na nayi naga Safna daga gaban su ri'ke da selfie stick tana masu selfie. Ita kam Safna anyi cim'bu babu mijin aure, domin kuwa ko wane namiji tsoron tinkarar ta yake.
       A filin da ake kamu ne na hango members na Amrah and Rerbee'art novels suna ta rububin pop corn, kusa dasu kuma na hangi Nafee and Amrah Novellas suma suna ta 'ko'karin su samu souvenirs, members d'in Zarah bb na gani har da dambe suke wai basu samu ba, Extreme Hausa writers kuwa bakin 'karfin su suke don ganin sun shiga filin rawa, sai dai kuma basu samu wuri ba saboda wisdom Hausa writers sun cika wurin.
      Excellent writers kuwa Nafee Ankah ce na gani ta wakilce su tana ta shoki. Mufarka mata kuwa su suka gyara amare domin indai wurin gyaran amare ne tou ba daga baya ba, su kuwa na Amrah's kitchen girke girke suka koyawa amaren biyu.

         Bayan Shekara uku.
Dad ne na hanga cikin masallaci bayan an gama sallah ya bayar da hoton Safna yace inda wanda yake sonta ya aura, kowa tsoronta yake saboda duk ansan halinta na wula'kanci, ganin basu da niyyar tanka mashi yasa yace "na bama liman sadakar 'yata safna indai yana sonta, na d'auke mashi komai nata tun daga gida, lefe, kayan d'aki da komai, zai kuma biya sadaki mafi 'karanci wanda shima nine zan bayar, idan liman ya amince gobe za'a d'aura aure insha Allah.

       Take kuwa liman ya fara fara'ah, yaji ance za'ayi mashi komai. "Na amince ko yanzu ma a d'aura" ya fad'a cikin jin dad'I,
      Dad yace "a bari goben dai tukuna".

       Batayi wa Dad musu ba saboda itama mijin take nema, Mum ma taji dad'in hakan. Washe gari aka d'aura auren Safna da limamin masallacin 'kofar gidan su.

    TAMMAT BI HAMDULILLAH

Anan ne zan d'igawa labarin aya, labari ne wanda banyi zaton zayyi tsayin haka ba, sai gashi har ya d'auki wannan lokacin, ina fatan masu karatun sunji dad'in shi kuma sun fad'akartu a cikin shi. Kurakuren dake ciki Allah ya yafe min, inda nayi daidai kuma Allah ya 'karo baseerah mai amfani.

Kunfi kowa a gareni
Iyayena abin alfahari na, ina 'kaunarku kuma ina yaba maku.

Sadaukarwa
Na sadaukar da wannan littafin ga 'yar uwata kuma 'kawata RABIATU SK MASHI, naki ne Zafin so, kina da damar wallafa shi.

Bazan manta daku ba 'kawaye na; Zarah BB, Ummeeter Gidado, sadiya Afka, Kirratul-Ayn, Munayshat, rash Kardam, maman khairat, maman Abideen, mum hairullah, kdeey, nafee anka, ummu abrar, maman usman, kausar luv, mimi B, mrs. Umar, hajar, stylish, teemah luff, zee hrt, meesha lurv, autar hajiya, maryam mukhtar, Nuccee luv, Nana Diso, Futha, Zahra, khadeejah candy, Aunty M. Jabo and Xeenur.
    Bazan manta daku ba Abdul jega, Muhammad abba gana, Raheem jega and Mr. Smiles.
    Naso ace duk sunayen ku su fito amma babu hali, duk wadda ban ambaci sunanta ba tayi ha'kuri tana raina kawai dai babu fili ne saboda mai karatu zai iya gajiya dani.

Tabbas hausawa sunce MAHAKURCHI mawadaci ne, domin kuwa BABU MARAYA sai raggo, ku duba irin YAUDARA data faru tsakanin FADEELAH DA NABEELAH, da kuma RAMUWAR GAYYA da YARIMA SAIFULLAH yayi, wannan wane irin SO DA SHAKUWA ne tsakanin Rabiatu da Imran? Tabbas DAUKAKA DAGA ALLAH take, akwai TSANTSAR ZALINCHI a cikin labarin RADIYAH, sai dai kuma DR. RAFIQ ya magance masu komai, oh! INA ZANGA KDEEY abar alfahari na?, mujiya ce ME BAQIN JINI inji hausawa, soyayyar da KHAULAT tayiwa Tahir ba ta wasa bace har iyayen su na fad'in "wannan wane Irin ZAFIN SO ne suke wa junan su? Ni kuma nace ku rakani wurin HAYDAR DA HAYBAR don ganin wace Irin rayiwa suke ciki.
     Alhamdulillah! Littattafan Marubuciyar kenan, HAYDAR DA HAYBAR na naj zuwa bayan sallah insha Allah, karku bari a baku labari.

Inawa kowa fatan shiga wata mai albarka lafiya, Allah ya sada mu da duk alkhairan sake cikin shi.

Amrah ke  gaishe da duk wani masoyinta na nesa dana kusa.
Luv youh all