ZAFIN SO Page 11 to 20
Sani bai dawi Nigeria ba sai da yayi Ph. D ya zama professional Doctor. Ranar da zai dawi Futha ta had'a mashi abubuwan jin dad'I, tayi gayu sosai na dawowar d'an uwanta.
A Airport suka d'auko shi ya 'kara kyau sosai dan dama indai wurin kyau ne to baza'a barshi ba.
Wata d'aya da dawowar shi ya samu aiki a FEDERAL INLAND REVENUE branch d'in Katsina, Dr. Nasir yace "to Sani kaga dai ka samu aiki mai kyau, yanzu abunda ya rage maka kawai aure, bana so ka fara zuwa Office ba tare da aure ba, me kace?".
Susar 'keya ya fara sannan yace "Dady dama....." sai kuma yayi shiru.
"Dama what? Talk Sani",
"Dady ina son ka nema mun wadda zan aura, saboda banda budurwa" ya du'kar da kanshi cikin kunya.
Dad yayi murmushi irin nasu na manya sannan yace "dama haka nake son yi, na dad'e dayi maka mata, kuma matar ma wadda kuka sha'ku sosai da ita",
Kanshi ya d'ago yace "to Dad godiya nake, Allah yasa ta zama abokiyar zaman alkhairi".
Dad yace "Ameen".
Sani bai ko tsaya jin wacece za'a aura mashi ba, da mamaki ya tafi dan yasan a iya sanin shi babu wata mace wadda ya sha'ku da Ita, a iya sanin shi Futha ce kawai, to ai kuma Futha blood sister na ce. Ni kuma Amrah nace "ba wani blood sis, kaine dai kake tunanin haka amma ba haka bane" mudai je zuwa zaka san ko wacece zaka aura.
Sun samu Dad yana karatun jarida, jin alamun su yasa ya ajiye yace "kun shirya kenan?", kai kawai suka d'aga yace "kuje ku kira Khairat da momy'n ku, na riga da na kira Zarah tana kan hanya ma".
Cikin 'kan'kanin lokaci duka suka hallara har da Zarah dake da tsohon ciki. Cikin dattako ya fara da "naaan duk kan ku zakuyi mamaki abunda zai fito daga baki na, to ba abun mamaki bane kuma ya zama fole na fad'e shi, bana so wani ya bani wata fassara haka kuma bana so inji wata magana daga baya", nan ya hau basu labari tun farko har 'karshe, duk abunda ya faru sai daya fad'a har da labarin Malan Sani da akaiwa d'aurin rai da rai a gidan yari, da kuma Marwan daya 'bata tun shekaru 29 da suka wuce. Sunsha koke koke, Sani ma yayi kuka tare da yin godiya ga Dr. Nasir saboda irin ri'kin da yayi mashi, bai ta'ba nuna bashi ya haife shi ba, baya nuna banbanci tsakanin shi da Shahid yaron daya haifa, har ma yafi nuna kulawa a gareshi saboda Shahid shaye shaye yake babu abunda baya sha, shi yasa ma baI wani damu dashi ba. Saude tayi masifar har ta gaji.
Cikin mako uku aka gama hidimar biki, Futha ta tare a katafaren gidan da Dad ya mallakawa Sani.
Wata uku da auren su ta fara laulayin ciki, tasha wahala sosai dan ko 'kanshin gidan ta bata so, a dole Sani ya mayar da ita gida. Satin ta biyu ta warware ta koma gida. Zo kuga kula wurin Sani, ko tsinke baya so dmta d'auke, hutu ma ya d'auko a wurin aiki musamman dan ya baiwa matar shi kula. Ga arzi'kinshi kullun 'kara ha'baka yake, business yake sosai duk fad'in Nigeria babu wanda bai san SS ba, idan ma baka san shi ha to zaka san sunan shi, babu inda baya da branch a Nigeria, tun daga saida motoci, plaza, gidajen mai da sauransu. Gashi da taimakon al'ummah, babu wanda baya alfahari da SS sai dai wanda bai san shi ba.
Bayan wata bakwai cif Futha ta haifi kyakkyawar yarinya son kowa 'kin wanda ya rasa. Dad da Mom kuwa ba 'karamin dad'I suka ji ba, saboda Zarah bata haihuwa, shekarar ta uku kenan da aure amma shiru ko 'batan wata bata yi ba. Tun a asibiti Dad yace "idan zaka bani dama zanyi wa yarinyar hud'uba", Sani yace "na baka dama Dad".
Dad yayi mata hud'uba da RABI'ATU, bayan ya gama ya fito yace "na mata hud'uba da sunan mahaifiyarka marigayi ya, sai a ringa kiranta da BABY". Sosai Sani yaji dad'I. A ranar aka sallame su daga asibiti.
Shekarar Baby uku aka 'kara yi mata 'kanwa, anan Dad ya bash izinin yayi mata hud'uba da duk sunan da yake so, shine yayi mata da SAFNA.
Some years later.
Baby ce ta tafi Bangladesh karatu, Safna kuma wannan shekarar ce ta kammala Secondary School. Akwai banbancin hali sosai tsakanin Baby da Safna, domin kuwa Safna bata ragama kowa, komai tsufan mutun sai ta zage shi, tana amfani da damar data samu ta dukiya take wula'kanta duk na 'kasa da ita, Baby kuma tsakanin ta da mutane sai giramamawa, Safna ta samu goyon baya ne daga mamanta, dan kuwa bata son laifinta ko kad'an.
CI GABAN LABARI...
Haka Nawwaf ya kasance kullun yana sayar da ruwan shi kuma yana samun nasarah. Sai dai baya rabuwa da takardun shi Na degree. Sosai malan Shazali yana jin dad'in huld'a da Nawwaf saboda yana bakin 'ko'karin shi Na ganin ya cika al'kawarin kawo balance d'in shi na kullun. Tuni ya kama nashi d'akin a gidan da Hamza yake haya, babu Wanda baya jin dad'in shi a gidan.
A 'bangaren Safna kuwa tun ranar data kori baba tsoho take faman mafarkin Wanda bata bata San shi ba, da zarar ta kwanta bacci ya d'auke ta sai tayi mafarkin saurayin. Koda kuwa baccin rana ne. Abun ba 'karamin damun ta yake ba amma ta kasa fad'awa kowa damuwarta. Sai dai kuma duk ta rasa kuzarin ta, ko makaranta take bata da aiki sai tunanin mutumin da data san asalin shi ba.
Mom CE kwance tana tuna irin wula'kancin da Safna tayi wa baba tsoho, saboda tun da abun ya faru hankalin ta bai kwanta ba. Idan tana tuna irin furucin da yayi wa Safna har hawaye take yi.
Kwatsam Mom tazo gittawa ta gaban d'akin Safna taji ta sama sama tana kuka, a hankali ta matsa bakin 'kofar taci gaba da sauraren ta, bata dai shiga ciki ba sai jin ta tayi tana fad'in "I love youh ! Me yasa ka kasa bayyana min kanka? Me yasa kullun kake zo min a mafarki? Bayan kasan Na kamu da 'kaunar ka, I can't live without you, pls ka bayyana min kanka".
Sosai hankalin Mom ya tashi da jin furucin da Safna keyi. Kasa shiga d'akin tayi sai ta nufi nata tana taya 'yar ba'kin cikin soyayya da d'an mafarki.
Alhaji Sani ne tafe cikin motar shi yana driving cikin natsuwa, a hankali motar ke shirin tsayawa har ta tsaya da kanta, sosai ya firgita Dan bai San yanda zayyi ba kuma gashi babu masu gyara a wurin. Fitowa yayi daga motar ya bud'e gabanta yana tunanin yanda zayyi.
Nawwaf ya taho yana turin baron shi data ciko da ruwa. Ganin mutun tsaye alamar yana Neman taimaki ne yasa shi matsawa inda mutumin yake yana fad'in "Alhaji lafiya kuwa?"
"Wallahi kuwa kaga ina cikin tafiya he ja fara jin tana tsayawa ban san dalili ba har said da ta tsaya",
Cikin tausayi yace " Allah sarki! Barin duba duk da ba wai na iya gyaran bane"
"To Bismillah" Alhaji Sani ya fad'a fuskar shi d'auke da murmushi.
'Dago kanshi yayi yace "Alhaji ai babu ma ruwa a cikin motar nan, kaga" yayi mashi nuni da ya duba ya gani.
"Kana da gaskiya kuwa, Ashe babu ruwa a ciki, kuma fa wallahi har sai da na cewa Sanusi ya zuba mun ruwa wata 'kila ya manta ne, shi yasa ma banyi tunanin rashin ruwa bane".
Nawwaf ya d'auko jarka d'aya a baron shi yayi amfani da marfin jarkar har ya cika wurin ruwan.
Sosai Alhaji Sani yaji dad'I, ya kalli Nawwaf cikin jin dad'I yace "ya ma kace min sunanka?",
"Sunana Nawwaf" ya bashi ansa,
"Malan Nawwaf ha'ki'ka naji dad'in yanda ka taimake ni, kuma bani da abun biyanka sai dai inyi maka addu'ah, Allah ya saka maka da alkhairi, ga wannan card d'ina ne" ya mi'ka mashi card d'in shi wanda yake d'auke da address d'in gidan shi dana office, sai kuma phone number da occupation d'in shi.
Nawwaf ya kar'ba yace "Alhaji wannan fa?",
"Ka neme ni dan Allah, saboda yanzu zan bar garin ne zuwa Kano yasa bazan tafi da kai ba, amma wannan katin nawa sai ka neme ni insha Allah zan samar maka aiki ko da messenger ne na office d'ina, amma sam wannan aikin bai kamace ka ba",
Nawwaf yayi saurin katse shi da "Alhaji ni fa dan Allah nayi maka ba wai dan ka biya ba, kayi ha'kuri ka kar'bi katin ka",
Alhaji Sani yace "kayi ha'kuri ka kar'ba malan Nawwaf, nima ba wai ina son biyanka bane, kawai dai kayi min hallaci ne shine nima nake son saka maka da shi".
Da 'kyar ya shawo kan Nawwaf ya yarda zai same shi a office ba gida ba. Nan suka rabu cikin farin ciki kamar dama sun san junan su. (Nima marubuciyar sai da suka bani mamaki, ta yanda naga suna yi ma junan su, ko da akwai wata dangantakar oho).
Da komawar Nawwaf gida kuwa ya bama Hamza labarin duk yanda sukayi da Alhaji Sani,
Hamza yace "amma kai banza ne Nawwaf, ai inda ka mayar da katin nan da kayi wa kanka, wai ma ban in 'kara gani". Kar'ba yayi ya 'kara ganin occupation d'in shi sannan yace "kaga fa VICE CHANCELLOR ne na UMYUK, Nawwaf kai da ke neman aiki ka sani ma ko ya nema maka? Degree ne fa gare ka, kuma yanzu naji ance har masu degree d'in ana d'aukan su lecturing sai daga baya su 'karo karatu, ai yanzu yanda za'ayi kawai ka shirya gobe mu tafi dan ban sani ba ko nima in samu ko da labourer ne",
Nawwaf cikin murna yace "ka ga kuwa hakane, inda na biye ma wannan mugun halin nawa shike nan da nayi wa kaina santacciya, kuma nifa ban ma karanta komai na katin ba sai yanzu, ai shikenan kawai sai mu tafi, amma gaskiya gobe ina son zuwa 'Kauyen mu kuma kwana biyu zuwa uku nake son yi, insha Allahu idan na dawo sai muje",
"Tou Allah ya kaimu, kai wannan halin naka na zurfin ciki bai da wani amfani, wai ace ina tare da kai har zakayi tafiya amma bazaka fad'a mun ba sai da labari ya kawo labari, kuma kasan dole akwai sa'kon da zan bayar akai ma su Baba",
Cikin halin ko in kula Nawwaf yace "tou naji ni dai tashi ka raka ni in kaima oga balance, har da baron ma zan kai dan kar in aje a sace ta ko kuma yayi tunanin zan kai mashi balance gobe",
Hamza ya mi'ke yace "nikam a shirye nake, kaine uban tsafta da zakace dole sai kayi wani wankan",
"Haba Hamza yanda ake yin ranar nan mai ZAFI ai dole sai da wanka sau uku a rana",
Hamza yace "nikam wallahi bazan iya ba, wannan sai kai Allah ya d'aura mawa".
Da wannan suka tashi suka nufi hanyar gidan malan Shazali, a hanya suke fira Hamza yace "nikam Nawwaf ina mamakin yanda mutumin nan yake sakar maka fuska, kaga fa yanda yake da kowa babu mutunci ba fara'a, amma kai har yafe maka kud'I yake yi, gaskiya nikam ina mamaki",
Nawwaf yace "ba kai kad'ai kake mamaki ba, dan wallahi har ni idan na zauna da kaina na mamakin hakan, a dalili na fa kaima har yafe maka kud'I yake yi, kuma gashi kaine ya fara sani kafin ni, hasali ma kai ka kawo ni wurin shi",
Hamza yace "kai share kawai, had'uwar jini ne",
"Hakane kuma" Nawwaf ya fad'a tare da yin sallamah a 'kofar gidan malan Shazali.
Fitowa yayi fuskar nan murtuk, dama haka yake yiwa mutane idan aka zo nemanshi, koda ya had'a Ido da Nawwaf yaga shine nan da nan ya saki fuska yace "Ahh malan Nawwaf ne? Marhaban da kai",
Har 'kasa Nawwaf ya du'ka ya gaishe da shi, Hamza ma ya gaishe shi ya ansa masu da sakin fuska.
"Yalla'bai dama na kawo balance d'ina ne",
Malan Shazali yace "a'a ka barshi na yafe maka Nawwaf"
Nawwaf yace "yalla'bai ai baza'ayi haka ba, ko jiya fa baka kar'ba ba",
Babu yanda bayyi ba amma sam ya'ki kar'ba, daga 'karshe dai ya ha'kura ya mayar da kud'in aljihun shi sannan yace "nagode yalla'bai, dama kuma ina so zanyi tafiya ne gobe zanje garin mu, tou shine naga ya kamata in mayar da baron dan kar in ajiye a d'uke ta",
Malan Shazali yace "tou babu komai Nawwaf, ga wannan ka 'kara kayi ku'in mota, wannan kuma kayi tsaraba dashi".
Sam yace bazai kar'ba ba, amma malan Shazali ya tilasta mashi dole ya kar'ba yayi godiya suka bar wurin.
Washe gari sassafe ya shirya, yayi bankwana ya kama hanyar 'kauyen su Bagaruwa.
Anyi murna sosai da ganin shi, mahaifin shi yashi Mata albarka da ganin guzurin da yayo masa, ya kuma tabbatar mashi da halaliyarsa yake nema. Babu wanda baiji dad'in ganin shi ba, kwanan shi uku ya koma Katsina cike da kewar barin gida da yayi.
Kwana biyu da komawar shi Katsina suka fara tunanin neman address d'in Office d'in Alhaji Sani, basu wani wahala ba suka gane address d'in, kasantuwar sananne ne babu wanda bai san UMARU MUSA YAR ADUWA UNIVERSITY ba, uwa uba kuma idan yace office d'in VC, kowa yasan shi, duk wanda ya fad'a ma yana neman Office d'in VC raina shi suke yi, wasu ma har dariya suke mashi, wasu kuma sai ya wuce suke fad'in "wai ji wancan wawan dashi, 'kazami wai yake neman office d'in VC, barshi yaje a nasan securities ma baza su barshi ya wuce ba". Kowa dai da kalar tsegumin shi har ya samu suka isa.
Note: Ayi ha'kuri da rashin jina kwana biyu, wallahi munyi fama da rashin wita ne, ga kuma Skul. Insha Allahu zakuci gaba da jina a koda yaushe.
A bakin office d'in suka had'u da securities mutun uku, nan suka hana su shiga yayi yayi amma suka 'ki.
Da 'kyar su ka bari ya shiga amma suka hana Hamza shiga. Sallamah yayi a ciki ma ya samu wani security, ya ansa sallamar tare da cewa "Bismillah malan",
Shiga yayi ya samu Alhaji Sani na 'yan rubuce rubuce bai d'ago kai ba, sai daya gama sannan ya mayar da kallon shi ga Nawwaf. Cikin jin dad'i yace "Ahh ashe Nawwaf ne, ina ta tunanin ka kuwa ashe kana kusa",
"Wallahi kuwa yalla'bai, ya aiki?",
"Lafiya 'kalau, ya gida ya aiki?",
"Alhamdulillah yalla'bai, dama nazo ne akan maganar da mukayi",
Da murmushi yace "tou ba damuwa, messenger kake so ko labourer?",
Nawwaf yayi 'kasa da murya yace "yalla'bai ina da takardu anan, sai dai ban san ko za'a d'auke ni dasu ba",
"Kawo su in gani".
Kar'ba yayi ya fara dibawa a hankali tun daga na primary, origine, secondary certificate da sauransu har ya kai ga na degree. 'Dago kanshi yayi ya kalli Nawwaf daya 'kura mashi ido yana kallo yace "kaine NAWWAF SANI?",
"Ehh nine" ya bashi ansa.
"Kana nufin dama harda degree gareka?" Ya washe baki yace "aikam zaka samu aiki mai kyau insha Allahu, ai ban san ma kana da karatu ba".
Nawwaf yace "kusan shekara buyu kenan dana gama amma aiki ya gagara, shine kawai na yanke shawarar zuwa nan birni in kama sana'a saboda mahaifina baya aikin komai".
Da sauri ya d'ago kai yace "baya aikin komai? Kana nufin zaune yake haka kawai?",
"Ehh baya aikin komai, da yana aiki a nan garin sai aka wula'kanta shi, shine ya yanke shawarar ya bar aikin kawai ya koma gida".
Cikin tausayi yace "Allah sarki! Ai mutanen ne na yanzu basu da wani kirki sai wula'kanci, da zarar suka ga sun samu d'aukaka sai su kama wula'kanta mutane, idan ka samu lokaci ko ba yanzu ba sai ka kawo shi idan yana so sai a bashi aiki ko 'karami ne".
"Tou insha Allahu zan kawo shi yalla'bai, mun gode 'kwarai".
Alhaji Sani yace "babu komai Nawwaf, haka kawai nakeji ka kwanta mn a rai, jinka nake tamkar jinin jiki nah, ka dawo nan da kwana uku kafin nan komai ya kankama",
"Tou Allah ya kaimu yalla'bai".
Har waje ya raka shi ya samu Hamza zaune yana kiran fitowar shi.
Alhaji yace "au ashe tare kake da wani?",
"Ehh yalla'bai sun hana shi shiga ne".
Sosai yayi ma securities d'in fad'a saboda shi ba halinshi bane wula'kanci. Yace ma Hamza "kaima kana da karatun ne?",
"A'a ni daga primary na tsaya",
"Tou kana son messenger ko labourer?",
Da sauri ya sosa 'keya yace "ehh ina so indai zan samu".
Ya tambaye shi sunanshi ya fad'a mashi, ya kuma ce dashi su dawo tare da Nawwaf.
Haka suka tafi cikin jin dad'in samun nasarar da sukayi. Ta gidan Malan Shazali suka bi, suka gaishe shi cikun sakun fuska ya ansa, Nawwaf ya shaida mashi duk yanda sukayi da Alhaji Sani, ya taya shi murna sosai ya kuma ce idan zasu koma zaije dan yayi mashi godiya.
Bari mu koma 'bangaren Safna mai Dream guy.
