HARAMTACCEN AURE PART 7 ( The end)




   Lokacinda Maryam ta fahimci cikin Majeeda nanan bai fita ba, ba k'aramin kad'uwa tayi ba, ba shiri ta nemo Asiyah har ita suka koma wurin Malam, sai dai sunyi rashin sa'a ya tabbatar musu babu makawa sai an haife cikin, sai dai daga baya zaisan yanda yayi da yaron harma ita Majeedar tabar gidan,
   Bayan wata biyar Majeeda ta haifo santaleliyar yarinyarta Mace, ko ban fad'a ba kunsan ba k'aramin farin ciki iyalannan sukayi ba, har Maryam taji dad'in zuwan yarinyar, tun haihuwarta ita take hidima da ita, wani irin soyayyarta take ji,
    Ranar suna yarinya taci suna Maryam, shawarar Majeeda kenan, ta dage sai anyima Maryam takwara, ansha shagali sosae, tun ranar haihuwarta har washe garin suna, babu wanda bai shaida da haihuwar Maryam ba, harta da Aisha matar Majeed kullum tana gidan, don yanzu sun zama kamar en uwah,
   Kullum Maryam k'arama tana wurin Maryam, tsakaninta da Mamanta sai in tana rigimar yunwa, Shaheed ma acan ya tare b'angarenta wurin d'iyarshi, ita dai Majeeda ta zama er kallo,
    Tun tana da shekara guda suka yayeta, sai dai madara, ganin haka Maryam ta koma wurin Malam, da maganarsu ta baya kar Majeeda ta samu wuri tayita haifa ma Shaheed yara, ita kuma ta zama hoto, shima  abu ya bada da zata zuba mishi a abinsha, tace "shi yafi komai sauk'i malam" sannan tayi godia ta tafi,

    Majeeda na kwance, Shaheed ya shigo d'akin da Marece ne, tayi mamaki sosae don da wuya ya shigo idan ba dare ne ba,
    "Sannu da dawowa" baice komai ba yaci gaba da k'are ma d'akin kallo, duk da daman yanzu yaa daina kulata, sannan ya zura hannu Aljihu ya ciro takarda, ta kalleshi da mamaki,
   "takardar miye?" cikin yanayin da bai tab'a mata magana ba yace "in faɗa miki da baki mana, idan ni yaronki ne, Ansa ki duba" jikinta ba k'wari ta mik'a hannu ta amsa ta buɗa, Saki Uku ne reras, tana ganin haka ta kulle takardar idanunta cike da hawaye, ita kuma k'addarar da Allah ya ɗaura mata kenan,
      "Mena maka shaheed?"
   "kawai na gaji da zama dake, babu laifin da kikamun, ki tattara kawai ki tafi, sannan kuma karma ki sakaran tafiya da Maryam, tuntuni na barma Maryam ita" wani irin takaicine ya taso ma zuciyarta, wani irin kallon tsana take mishi,
     "Sai yanzu ne na fahimceka, lallai yau na yarda ka cika namiji, watau aurena kayi in haifa maka ɗiya ka cimun mutunci? Lallai idan ance maza DUK HAKA SUKE (littafina mai zuwa), bazanyi gardama ba, saika zauna dasu halayensu da baka taɓa tunani ba zasuna bayyana, ka  rusa duk wata yardar dana maka Shaheed, kaci amanatah, bazan taɓa yafe ma cutar dani da kayi ba, kuma Maryam nina haifeta babu inda zan tafi in barta"
    "Da ita kikazo? Zaifi miki ma daki manta da ita, don keda ita har abada, kuma kici gaba da zama har in dawo in sameki" ya fita fuuu yabar ɗakin, anan ta zube k'asa tasha kuka sosae kamar ranta zai fita, da kanta kuma ta rarrashi zuciyarta tayi shiru, jikkarta kawai ta ɗauka tabar gidan,
     Mai napep ya ajeta k'ofar gidansu, ta fito dak'yar take haɗa hanya ta shiga gida,
   Momie da Umma ne a ɗakin tazo gidan, Abdallah ma ya koma gidan babanshi a can ya sakashi makaranta, dak'yar har tana ganin jiri ta faɗa falon, wurin zama a kujera harta kusa faɗuwa, ta jinginar da kanta kawai tana dafe kanta dake mata ciwo sosae, duk suka taso sukayo inda take,
    Kasa basu amsoshin tambayoyinsu tayi, sai dai ta mik'a musu takardar dake hannunta, duk tare suka saki salati, sunyi matuk'ar tausaya mata, Umma kamar karta bar gidan don tausayin Majeeda, babu wanda zaiga halin da take ciki bai tausaya mata ba,

A gurguje dai....


Bayan shekara Uku...
Majeeda ta kwantar da hankalinta, Yanzu ta zama lecturer a makarantar Umyu katsina, tsakaninta da Majeed sai dai mutunci kawai na en uwah, gida ma ganin halin da take ciki ya saka ko maganar aure basu mata, kullum dai suka mata Addu'ar zaɓi mafi Alkhairi,
    Aisha ne da Majeed kwance ya juya mata baya, ba barci yake ba, anma kuma yayi shiru kamar mai barcin,
    "Kayi shiru hniee inata magana ni kaɗai, kuma nasan ba barci kake ba" shirun ya k'ara mata,
    "kana jina fa" baice komi ba, ta kamo k'afarshi ta fara mishi susar k'adangaruwa,ba shiri ya fara dariya, ya kamota ya rungume, tureshi tayi suka fuskanci juna,
    "Wai hniee Meyasa kullum nake maka maganar dawo da Majeeda kake shareni? Wlhy na faɗa maka banda Matsala da hakan, kuma kunason junanku, ga Abdallah kullum k'ara girma yake, zaiso ya ganshi a tsakiyar iyayenshi"
   "ke ba mahaifiyarshi bace?"
   "Duk da haka nidai ka dawo da ita don Allah"
    Fuskarta ya jawo ya haɗa da tashi suna shak'ar numfashin juna "Hakan kikeso" ta ɗaga mishi kai,
    "Zanyi komai saboda farin cikinki, Anma nidai ki dainamun maganar zanyi tunani akan hakan"
   "naji anma baza'a ɗauka lokaci ba?" ya gyaɗa mata kai, duk wannan maganar da take k'arfin hali ne kawai, yana rungume da ita, ɗagotan da zaiyi yaga jinine ke fita ta hancinta, ta tafi luuu ta faɗa gefe, cikin tashin hankali ya rink'a jijjigata, ciwon nata nayau yafi na kullum ɗaga mishi rai, doguwar riga kawai ya ɗaura mata saman kayan barcin jikinta, ya ɗauketa a ruɗe ya saka mota, dak'yar ya iya driving zuwa asibiti,
      Har gari ya waye bata dawo hayyacinta ba, likitoci na iyakar k'ok'arinsu a kanta, en uwanta cike a asibitin, wata nurse ta lek'o tace "Waye Majeed?" da sauri ya matsa inda take yana cewa shine, yabi bayanta suka shiga Maryam na kwance ta farka, idanunya tsaye kanshi tana murmushi, ta mik'a mishi hannunta ya rik'e yana hawaye, ta ɗan ɓata rai da wasa,
    "Miye na kuka kuma hniee? Ka kwantar da hankalinka kaci gaba damun addu'a kamar yanda ka saba, wlhy koda mutuwa nayi ina cikin farin ciki sosae, burinah ya cika, na rayu na wani lokaci kuma zan mutu a matsayin matarka, kada ka manta da maganar da mukayi jiya da dare, kada ka manta dani Majeed" k'ara rirrik'e hannunta yayi,
    "bazaki barni ba Aisha, zamu rayu a tare insha Allah"
   Girgiza kai tayi "ban taɓajin ciwon da nakeji ba a yau, ni nasan wannan ciwon shine ajali na" ta k'ara lumshe ido dak'yar take magana, tashi yayi yana k'wala ma likita kira,  tak'i sakin hannunshi, ya juyo yana kallonta, murmushi ta k'ara mishi,
    "kada ka manta da alk'awarinmu na dawo da Majeeda" sannan ta sakeshi, ya tafi duk jikinshi yayi sanyi, suna dawowa da likita har rai yayi halinshi, anan Majeed ya faɗi sumamme, yasha jinya sosae Asibiti kafin ya ɗan samu,

Bayan shekara ɗaya,
 Da mutuwar Aisha, Abdallah yanada shekara 10, ya zama ɗan saurayi, Maryam nada shekara 4, Majeeda ta zama babbar mace, 'yar gayu da ita, kullum k'ara kyau take, idan ka ganta bazaka ce tayi shekarunta ba, har Gida Maryam ɗin Shaheed tazo neman yafiyarta, Shaheed ma har kuka yayi na zafin rabuwa da ita, bata rik'esu da komai ba ta yafe musu, sannan ta barma Maryam, Maryam k'arama don har lokacin Allah bai bata haihuwa ba,

   Majeeda ce tafe cikin Mota, tana tuk'i cikin natsuwa, duk da saurin da take zuwa gidansu Umman shaheed saboda kiran gaggawar da aka mata, mintoci kaɗan ta isa gidan, mai gadi ya wangale mata gate ta shiga, daga makaranta take duk ta shawo gajia, kai tsaye falon bak'i ta wuce,
   Kamar yanda suka saba idan zasuyi meeting, kowa ya hallara, zahra ce kawai babu, ta gaishesu sannan ta samu wuri ta zauna, kallo ɗaya data ma Majeed ta k'ara hango ramar da yayi sosae,

   Bayan ta samu wuri taa zauna, Abban Majeed yayi gyaran murya ya fara Magana,
      "Wannan karon ba Umarni bane muke baku, shawara ce muka yanke kuma duk saida amincewarku, abinda ya faru mu ɗauka k'addara ne, yanzu kuma dama ce garemu, mu cika Alk'awarin da mukai ma mahaifinmu, muna fatan wannan karan bazaku bamu kunya ba"
   Momie ce ta nisa, tun kafin kowah ya fara magana "Gaskia ni ban yarda da wannan hukuncin ba" su duka suka juyo suna kallonta, taci gaba da magana cikin fahimta,
      "Su duka yanzu ba k'ananun yara bane, kun manta abunda wancan haɗin ya haifar? Shiyasa ni ban cika magana ba, anma gaskia wannan lokacin bazan yarda a k'ara musu dole ba,  su koma halin da suka shiga wancan lokacin ba" Daddy ya katseta
    "Waye yace dole za'a musu? Suna da damar da zasu faɗi ra'ayoyinsu, karki manta da Alk'awari ne muka ma Mahaifinmu, ba don haka ba koda kansu suke so bazamu taɓa k'ara amincewa ba, kuma yanzunma idan har basu so bazamu k'ara tilasta su ba" shiru tayi bata k'ara magana ba,
   Abbah yace "ku muke saurare", Majeeda kanta a k'asa tun tana kuka a hankali harta fara shesshek'a, Majeed ma sai dai tashi yayi ya fita, fuskokin iyayen nasu duk ta nuna rashin jin daɗi, sunyi jugum kowa ya kasa motsawa, message ya shigo wayar Aunty zainabu, ta ciro ta tana ganin daga Majeed ne ta buɗe da sauri, da k'arfi ta karanta yanda kowah zaiji,
    "Ki tayani godia Auntynmu, kunyarsu ta hanani furta komai, sun nuna mana soyayyar da babu abinda zamu biyasu da ita, Allah ya saka musu da mafificin Alkhairi, ya k'ara musu tsawon kwana" kowa a ɗakin saida ya murmusa, sunyi farin ciki sosae, Majeeda ma murmushin jin daɗi take, ta mik'e da gudu ta fita, kunya bata barta ta jira kowah ba, ta shige motarta ta wuce gida,
   Cikin lokaci kaɗan aka fara hidimar biki, shagali sosae akayi wanda ko bikinsu na farko ba'ayi ba, cikin sati biyu aka gama komai aka kai Amarya ɗakinta,

   Bayan en rakiyarta sun gama tafiya, ta shek'a wankanta, tayi kwalliya ta fitar hankali, ko ina jikinta k'anshi yake, ga wata doguwar riga data saka ta daifi babu, irin shigarda tasan Majeed yafiso, sai dai ta ɗaura zani daga sama,
     Yana shigowa tsaye yayi a k'ofa yana kallonta, duk'arda kanta tayi sannan wata irin kunya ta saukar mata, ya ware mata hannuwa alaman tazo ya rungumeta, cikin zolaya tace "yau kuma ina laidan da za'a jefeni da ita?" daria yayi,
    "rufamun asiri zaki jamun ɗauri," itama tayi dariya,
   "nayi alwala fa, kai kawai nake jira"
    "tohm ranki shi daɗe"
  Ya shiga yayo alwala, ya fito, Sallah sukayi raka'a biyu kamar yanda manzon Allah ya koyar damu, ya daɗe yana kwararo musu addu'ar zaman lafiya, sannan sukai godia ga ubangiji,
    Ya rausayar da kanshi yana kallonta, rayuwarsu ta bayace ta dinga dawo mishi, wata irin soyayyarta na k'ara ratsashi, itama kamar hakan takeji, ta hure mishi idanu,
    "ka faɗa mana"
  "na rasa mezan faɗa ne, kullum k'ara kyau kike, bazaki taɓa tsufa ba"
   "kaima hakanne, babu wanda zaice kana da kaman Abdallah"
   "bazan iya bayyana miki farin cikin da nakeji ba da dawowarki gareni, wallahi ban taɓa sanin ina sonki da yawa haka ba saida na rasa ki, HARAMTACCEN ZAMA, ya k'are, Allah ya bamu ikon farantama juna har k'arshen rayuwarmu"
     "Ameen" ta faɗa

GODIYA
   Ta tabbata Ga Allah daya bani ikon kammala littafinnan lafiya, tsira da Aminci su k'ara tabbata ga annabinmu Muhammad (S.A.W), kuraren da suke ciki Allah ya yafe mana, Ameen,

Bani da bakin godia gareku Masoyana nesa da kusa, inajin daɗin yanda kuke nuna soyayyarku ma littafinnan, Allah yabar k'auna, sai kunjini a sabon littafina K'IYAYYA, anma bayan na dawo daga jigawa wurin kishia labarin A HANYAR JIGAWA, yananan tafe ba daɗewa domin nishaɗinku,
   domin gyara ko shawarwari

SADAUKARWA
   wannan littafin sadaukarwa ne ga dukkan jikokin Alhaji sani katibu, duk sunayensu ne a ciki
     Manyan gobe, Allah ya raya mana ku ta farkin addinin musulunci, ya zaɓa muku abokan zama na gari, Ameen

IYAYENA
Allah yaji k'anshi mahaifinmu da rahma ya gafarta mishi, Allah ya k'ara tsawon kwana momienah, Allah ya saka miki da gidan Aljannah, hak'ik'a Uwah ce ta gari, ina sonta fiye da rayuwatah!

   NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
    Ina Alfahri daku, Allah ya k'ara ɗaukaka, ya k'ara mana haɗin kai,

Godiya ta musanman,
   Da taimakonka ne na fara littafinnan harna k'areshi, ILILEE, nama rasa ta yanda zan gode maka, Allah ya k'ara basira, Ameen

AMINAN JUNA
   K'awaye na gari, babu kamarku a zuciyatah, RAZ, k'aunarku dabance a cikin zuciyatah, kalmomi bazasu iya bayyana farin cikin da nakeji kasancewarku cikin rayuwatah ba, Amrah A msh and Zahra bb, Allah ya bar tare.

   Beelybadaru, kina raina a koda yaushe

  En uwanah writer, gaisuwa mai yawa a gareku, Allah ya k'ara basira ya k'ara mana haɗin kai baki ɗaya,

    Duk group ɗin da nake ciki da wanda suke samun littafina, ina mik'a gaisuwa mai yawa gareku, Ma'assalam

Taku har kullum
    Rabiatu sani katibu mashi