HARAMTACCEN AURE PART 6




Da safe tana kunna wayarta kiranshi ne ya fara shigowa, ba tare data duba bama ta ɗauka,
   "Assalamu Alaiki" ya faɗa da daddaɗar muryarshi cikin nutsuwa,
   "Wa'alaikas salam," ta amsa mishi,
   "Hajja Majeeda ina fatan kin tashi lafiya" mamaki ne ya kamata sosae yanda har yasan sunanta,
   "Yi hak'uri don Allah ban gane mai magana ba"
   "wanda kike tsammanin kiranshi ne, ko kuma nace wanda kike tunani a halin yanzu"
   "Banfa gane mai magana ba"
  "kina neman k'arin bayani dai, anma daɗewarmu a jiya, bai kamata ki sauri mantawa dani haka ba, kamar yanda nima na kasa daina ganin kyakkyawar fuskarki"
     "Shine kuma akace dole sai nayi tunaninka? Don Allah malam na faɗa maka fa ni matar aurece" ta faɗa da alama ya fara ɓata mata rai
   "Ajiyan fa kamar naa yarda, kafin in gano gaskia, don Allah majeeda mu duka ba k'ananun yara bane, ki bani dama in faɗa miki abinda ke tafe dani" shiru ta mishi, hakan ya bashi damar ci gaba da magana,
   "Sunana Shaheed, anma family namu sunfi kirana da sarki"
   "sarki?" ta maimaita, ba tare da taa sani bama,
  Yayi er dariya "da ina yaro kuka ne dani, shine mama na ta samun sarkin kuka"
   Dariya ya bata, ta rik'a abinta ciki-ciki tana saurarenshi,

   "ina rik'e da kamfanin mahaifina ne a halin yanzu, bana aikin gomnati, naayi karatun gaba da secondry har zuwa master's, sannan kuma kamar yanda na faɗa miki ina da Mata shekararmu biyar kenan da aure, Allah bai bamu haihuwa ba, ban taɓa tunanin auren MATA BIYU ba, sai jiya da na ganki, kallo ɗaya kika kwanta min a rai, Allah ya jarabceni da soyayyarki, don Allah Majeeda ki bani dama, ki shigo rayuwarmu nida iyalina, ina matuk'ar k'aunarki,

   Shiru tayi kamar mai nazari, hakanan taji hawaye nason zubo mata,
   "Don Allah kice wani abu Majeed, kice kin yarda, a shirye nake dana miye miki gurbin tsohon mijinki, na zame ma Abdallah tamkar mahaifinshi, ki amince dani, ni masoyinki ne na gaskia"
    Kasa rik'e kukanta tayi, ta kashe wayar kawai ta jefar da ita, taci gaba da kukanta da ita kanta bata san dalilinshi ba, sai da tayi mai isarta, sannan ta shiga toilet ta wanke fuskarta, ta fita daga ɗakin tana jinshi yana sake kira ko kallon wayar batayi ba,

   Kamar mai tsoron wayar ta kasa komawa ɗakin duk da taa gama abinda take, ta nemi wuri a falo ta fara kallon dole har marece yayi, sannan ta koma ɗakin,
   Miss calls ɗinshi 99, ta kashe ta gaba ɗaya ta tura ta jikka ta ajje, wani irin nauyinshi takeji, don yaa wuce saurayi tunda harda Mata, zai kai irin 35 haka, wani irin yanayi takeji a kanshi, anma ta rasa ta yanda zata fassara yanayin, bata ɗauka bayan Majeed ba akwai namijin dazai iya tsaya mata a rai haka, ita tayaya ma zata fara soyayya,
       Kwananta biyu bata kunna wayar ba, sai ana uku, gobe kenan lokacin da Daddy ya bata zai cika, tana gyara ma Abdallah kayanshi ya shigo da gudu,
    "Auntie, Momie na kiya" ya koma da gudu yana faɗa mata, tana tambayarshi 'ina Momien' ko tsayawa baiyi ba,
  Tana zuwa momie ta faɗa mata bak'one tayi, ta koma ta sako mayafi sannan ta fita,

     Can ta hangoshi da Abdallah saman cinya sai surutu yake zuba mishi, hannunshi choculate har babu hannun rik'ewa, yana hango ta ya kasa daina kallonta, har tana harɗewa ta samu dai ta k'arasa, taja kujera ta zauna, sannan ta ɗan zamo ta gaidashi,
    Ya amsa yana ta fara'a, har lokacin idonshi na kanta,
   "ke kuma kalan naki salon horan kenan Majeeda?" ta k'ara k'asa da kanta tana wasa da yatsunta,
  "Anan ɗinma babu amsa? Yau kwana nawa kin kashe waya da sai dai ki jini asibiti, kasa daure wa nayi yau nazo da k'afafuna sauraren Amsa"
   "hhm" tace da alama duk ta takura da zaman, haka amsarta ta kasance, sai kuma "eeh" da "A'ah" shi kaɗai yake zuba surutunshi harya lura da yanayinta,
    "Da alama yau baki cikin yanayin kodai sai a waya zaki bani amsar" da sauri tace, "toh shiknan" sai da ya murmusa, "in kuma naji a kashe gobe ki k'ara ganina" murmushi kawai tayi, ta mik'e ta tafi,
   "ba bankwana?" ta kasa juyowa,
   "Allah ya kiyaye hanya"
       "Ameen" ya faɗa yana sauke Abdallah, bayan ya cika mashi aljihu da kuɗi,

   Ya juya zai shiga motarshi saiga Daddy ya shigo, ya tsaya harya fito sannan yaje ya gaisheshi har k'asa cikin ladabi, ya tashi zai tafi ya tsayar dashi,

A gurguje,,,,,,,,,

    Daddy yace "sai dai ban ganeka bane" cikin ladabi yace,
   "Sunana Shaheed ibraheem imamu Abba, nazo wurin Majeeda"
    "tohhhh, Alhaji ibraheem dai wanda na sani?"
    "eeh Abba"
 "tohh masha Allah, idan ka koma gida saika turo iyayen naka, nan da wani ɗan lokaci sai a...."
    Don tsabar jin daɗi ma baisan sanda ya katse Daddy ba,  "Da gaske Abba" wani irin kallo ya mishi na rashin ganewa sannan ya gane bai kyauta ba, daya saka k'ok'onto a maganar, yaci gaba da washe baki ba kunya Shaheed kema Daddy godia,

   Washe gari lokacin daya ɗibarma Majeeda ya cika, tunda safe data shigo gaisheshi ya tsayar da ita,
    "kina sane da yau ne lokacin dana ɗibar miki ya cika"
    "eeh Abba, bani da wani zaɓi, Insha Allah zanyi biyayya ga duk mijin daka zaɓamun"
    "Tohh tashi kije, Allah ya miki Albarka, daga yau ki fara shirye-shiryen bikinki nan da wani ɗan lokaci" wani irin faɗuwar gaba taji,
    "Ameen Daddy" ta mik'e jiki ba k'wari tabar ɗakin, tohh anma meyasa bata faɗa ma Daddy Shaheed ne zaɓinta ba? Kuma dai gani take kamar yaa fasa don tun bayan tafiyarshi, bai nemeta a waya ba, koba wannan ma yanzu tafiso Daddy ya sake mata wani zaɓin da kanshi, don ta samu ta mishi biyayyar data kasa a baya,

•••   •••   •••
   An kusa bikin Zahra, sai aka saka lokaci ɗaya, Duka bangarorin sai shirye-shiryen biki suke, su Majeed anzo biki, shi yanzu hankalinshi kwance, soyayya da kulawa babu wanda bai samu a wurin Aisha, tuni ya manta da komai ya rungumo matarshi don ba k'aramin so take mishi ba,
   Majeeda ma tunda hidimar bikin ta kama, ta kwantar da hankalinta, bama kamar da taasan Shaheed ne zata aura, ta kasa yarda ne, anma wani ɓangare na zuciyarta faɗa mata yake ta fara kamuwa da soyayyar Shaheed,

     Ansha shagalin biki, garin Mashi aka kawo mana Zahra😉, Majeeda kuma Aka ajeta Katsina Layout, taci kuka sosai, kamar shine aurenta na farko,
    Da dare ya kirasu ita da uwargida domin musu nasihar zaman lafiya, tana zaune kafin uwar gidan ta fito taa tsura ma wani hotanta dashi ido, sunyi kyau sosae tana tsaye ya rungumota daga baya suna dariya, kyakkyawahce anma bata da haske sosae da ɗan k'aramin jikinta mai kyau,
    Jin tafiyarta ne yasa Majeeda ta daina kallon hotan ta maida kanta k'ansa, ta zauna kujera mai kallon wacce suke sai k'amshi take zubawa, da yake Maryam akwai tsafta,
     Sai da ta ɗago ta kalleta ne, kamar ba itace a hotonnan ba, tayi wata uwar k'iba sosae, irin hajiyoyinnan, cif ta cika kujera mai zaman mutum ɗaya, babbar mace mai halin dattako, bai ɗauki wani lokaci yana musu bayani ba, ya sallamesu kowa ta koma ɗakinta,

    Zaman su da Maryam sosai takejin daɗinshi, tana janta a jiki, har dangin shaheed take janta kasancewarta mace mai zumunci, da fahimta, ɓangaren Shaheed ma bata da wata matsala, yana bata kulawa sosai yakeji da iyalanshi, bata da wata damuwa yanzu,
    Sai dai kewar Abdallah da yanzu yake hannun Umma, kowa yaso a bar mishi shi, sai daga k'arshe suka hak'ura aka barma Umma,

    Watansu Uku da aure Allah ya albarkaceta da juna biyu, ba k'aramin farin ciki Shaheed da Maryam sukayi ba, kusan ma Maryam duk ta fisu Murna, tun daga lokacin ta ɗaukema Majeeda duk wata hidimar gida, ita take kula da ita, sai abinda takeso za'a girka, Maryam mace ta gari ce sosae, kusan tare suke rainon cikin,
   Har mamakin Maryam take, mace mai kawaici da k'ok'arin danne kishi, irinsu kaɗanne a duniyar nan, ko godiya take mata sai dai tace
    "banson haka fa Majeeda, ni ban taɓa kallonki a matsayin kishiya ba sai dai er uwa, abinda muka daɗe muna Addu'ar nema ne da Shaheed, Allah bai bamu ba, kuma yaa nufeki da samu, ina tayashi son duk abunda yakeso, wallahi ji nake duk ɗayane"
     "Gaskiyarki Auntyna, ina yima kowacce mace Addu'ar samun kishiya ta gari kamarki" Maryam tayi daria,
    "da kuma macce ta gari kamar ki ba" sukai dariya gaba ɗaya, kamar ba kishiyoyi ba,


   Cikin Majeeda nada wata hudu, k'awar Maryam tazo ta iskesu suna fira da Majeeda, sai dariya suke bazaka taɓa cewa kishiyoyi bane, ko gaisuwar Majeeda dak'yar ta amsa taja Maryam suka shige ɗakinta, tun kafinsu zauna tayi k'asa da Murya,
    "Me nake faɗa miki Maryam? Ke har yanzu kin kasa gane inda ke miki ciwo"
   "ko kuma kece kika kasa fahimtata Asiya, nifa babu abunda yarinyarnan ta tsaremun"
    "Aikam baki shirya ganin aibun kishiya ba, wallahi karki ga yanzu da cikinnan yana miki kawaici, tana ajje ɗa a cikin gidannan keda babu duk ɗaya, a hakan ma ya aka k'are? Wallahi duk yanda kikeson Shaheed tana haihuwa zata rabaki dashi"
  Anzo wurin, don babu abinda Maryam tafi tsana a rayuwarta kamar ace zata rasa Shaheed, "Tohh anma Asiya, nima fa inason inga yaro a cikin gidannan, shekara nawa bamu samu ba?
   "Zaki ga yaro a cikin gidannan, anma kina da iko dashi? Wata da tazo cikin ɗan lokaci zata rabaki da gidanki, idan kuma so kike sai lokaci yayi ki bani labari tohh in saka miki ido"
    "inaaa zan zauna? Nidai yanzu ya za'ayi?"
   "kuɗi kaɗan zaki bada, yanzu daganan wurin wani malamin zaure zanje a lalata abinda ke cikinta, daganan kema in anso miki maganin haihuwan"

   "da gaske nima zan samu haihuwan?"
  "indai kinyi yanda akace, kuma saikin yarda da malamin sannan zaki ga aiki",
   "gaskia wannan ba k'aramin Albishir bane, anma don Allah kar ayma Majeeda wani mugun abu" tsoki Asiyah taja,
   "hajia idan kinason aiki, ki tashi ki ɗauko yanzu in dawo miki da magani, da zafi-zafi ake dukan k'arfe"
   "inaso mana, yanzu kuwa"
Ta tashi ta lalubo mata kuɗi ta bata, har bakin gate ta raka ta sannan ta dawo,

   Ranar Majeeda keda Shaheed, Anma Maryam ita tayi komai kamar yanda ta saba, babu wani canji a tare da ita, bayan sunyi dinner yaja matarshi suka wuce ɗaki,
    Ta fito daga wanka tana ɗaure da towel, ta isa gaban mirrow ta zauna zata fara shafe-shafe, suka haɗa ido ta cikin madubin yana kwance ya k'ura mata ido, suka sakar ma juna murmushi,
   "banson kallo fa"
   "laifine don mutum ya kalla matarshi? kawai tunani nake"
   "tunanin me kuma?"
  "Da wanne irin farin ciki zan kasance a ciki? Idan ya kasance dake na fara rayuwa"
  "hhm zaka fara ko"
  "wallahi da gaske nake Majeeda, ban taɓa farin ciki ba kamar ranar dana fara ganinki, kowanne dak'ik'a ɗaya da nayi tare dake, ina alfahri dasu, ji nake kamar donke kaɗai akayi zuciyatah, kece farin cikina"
    "nima ina farin ciki dakai sosae, inajin daɗin kasancewa dakai, ina sonka fiye da kowacce halitta dake doron k'asa" ita kanta batasan sanda maganar ta fito mata ba, anma tasan tabbas k'aryane ta faɗa,bata da kamar Majeed a zuciyarta,
  Cikin farin ciki ya tashi ya tare ta zata saka kaya,
    "da gaske kike kina sona fiye da kowa" cikin son subar maganar tace "da gaske mana, har kana k'ok'onton soyayyar da nake maka?"
   "A'ah wlhy, kina nufin har daddyn Abdallah kenan?"
    "wake Maganar daddyn Abdallah kuma yanzu?"
   "nidai inason sani plz, nasan kinso Majeed sosae Majeeda, kina nufin son da kikemun yanzu yafi nashi?"

   Rasa yanda zatayi tayi, duk ya tsareta da tambaya, gashi batason ɓata mishi rai,
     "Soyayyar Majeed daban take a zuciyatah, ban taɓa tunanin zan iya koda kallon wani namiji a matsayin namiji ba bayanshi, anma a yanzu da nake tare dakai, banama tunawa dashi, nikam soyayyar da kake nunamin ma ta isa, ban buk'atar sanin tsakanin Ni da Aunty Maryam wakafi so, wannan sirrin zuciyarka ne"
   "ke ta dabance Majeeda, kalamanki suna matuk'ar tasiri a zuciyatah, kece wannan sirrin na zuciyatah, kinason sanin wa nafi so?....."

Girgiza mishi kai tayi, ba magana, ya jawota ya haɗa da jikinshi, ya fara aika mata da sak'onni cikin wani irin yanayi, m sai da aka turo k'ofa sannan sukai sauri suka saki juna,
   Maryam ce saida ta shigo tsakiyar ɗakin sannan ta fahimci halin da suke ciki, sai da ranta ya sosu, anma ta kanne kawai,
   "kuyi hak'uri na shigo muku kawai, bansan oga na ciki ba"
   "haba, Aunty keda ɗakinki kuma"
   "uhm, maganinki na kawo miki, nasanki da wasa dasha"
  Ta mik'a mata ruwa a cup da maganin, ko kaɗan bata kula da yanayin canjawar ruwanba, sai da ta kwankwaɗeshi tass, sannan ta mik'a mata cup ɗin,
    "nagode sosae Aunty"
  Ta ɓata rai "banson haka fa, sai da safenku" ta fita ta rufo musu k'ofa
Ta juyo wurin Majeed tana mishi murmushi,
    "Auntynah tana ji dani sosai"
     "gaskia ne, nayi sa'a sosai da samun mata na gari"
   "Muma munyi sa'a da samun miji na gari, da kowacce mace zatayi alfahrin samu"
  Ya jawota bayan ta gama saka rigar barcinta,
   "hajia nifa na gaji da wannan jan lokacin" ya kashe musu fitila, saboda yau cikin tsananin buk'atarta yake,

   Tun lokacin daya fara da shasshafa jikinta ta fara jin wani yanayi a jikinta, can cikinta takejin kamar wani abu na motsi anma ba sosae ba yana ɗan tsira, bata ɗauka wani abune daban ba, anma ciwon har tsakiyar kanta take ji, kasa taɓuka komi tayi, wani irin azaba ta dingaji bayan ya tashi ya shiga wanka, kamar tafiyar tsutsotsi haka ta dinga ji a cikinta duk yaa yamutse kamar ana cin kayan cikinta, ga wani irin zafi kamar ana dahuwa a ciki,
   A haka ya dawo ya iske majeeda,
     "wankan fa dear?" shaheed ya tambayeta,
  Dak'yar ta iya buɗa baki tana cije leɓe,
      "zan tashi inyi" baima lura da yanayin da take ciki ba, yaja bargo ya kwanta,

  Haka ta dinga juye-juye, hannuwanta biyu ta dinga sawa tana matse cikin ko zataji sassauci, kamar ruɓaɓɓen abu haka takejin cikin, ta sauko qasa komai ta samu ɗaura ma cikin take ta dinga juye-juye, da taji dai abun bamai k'arewa bane, ko nak'udar Abdallah bataji azaba haka ba, a kwance ta dinga jan jiki har inda Shaheed yake, ta dinga tashinshi, baimasan tanayi ba barcinshi yayi nisa,
    Hawaye ta dinga zubarwa masu zafi, ko ina jikinta ciwo yake kamar ba nata ba, ko hannunta bata son motsawa maganar ma ciwon buɗa baki takeji, haka ta dinga daurewa tana kiranshi, ta saka hannu tana bubbugashi, wani masifaffen ciwon nema idan jikinta ya haɗu da nashi,
   Jinta tayi taa jik'e kamar wacce tayi fitsari, a ruɗe ta saka hannu ta shafa k'asanta, jinine ta gani a malale, ba k'aramin ruɗewa tayi ba, ta fara wani irin kuka,
   "Na shiga Uku, ya Allah ka taimakeni kar in rasa wannan farin cikin na shaheed, don Allah ka tashi shaheed, karmu  rasa abunnan da muke matuk'ar so, ka tashi shaheed karka rasa mu" haka ta dinga kuka, tana sambatun da azabarma bata bari tasan tana yi ba,
    Maryam na jiyota daga inda take laɓe, ta koma ɗaki cikin farin ciki bama kamar da taji Shaheed baisan tanayi ba, anma kuma a yanda take jin tana magana dak'yar tausayinta take ji sosae, da kuma tausayin shaheed idan ya rasa wannan cikin na Majeeda daya k'wallafa rai a kanshi,

    Sai da ta galabaita sosae, harta suma a wuri sannan shaheed ya farka, da sauri ya buɗe idanunshi ganin halin da Majeeda take ciki kwance a gabanshi bata ko motsi, cikin tashin hankali ya shiga girgizata anma ko motsi ba tayi, ga jini malale a jikinta daya qara tayar mishi da hankali,
    Fridge ya ɗauko robar ruwa ya dawo inda take ya fara kwara mata, ta saki wata doguwar ajiyar zuciyar, idanunta sun k'ank'ance saboda azaba ta shiga hawaye,
    "Cikina Shaheed, mutuwa zanyi, mutuwa zamuyi nida babynmu"
   "bazaki mutu ba Majeeda, rayuwatah tana buk'atarki, don Allah kicemun babu abinda ya samu babynmu" girgiza kan zafin ciwo kawai take, tana hawaye, duk ya fita hayyacinshi,
   Ganin yanda take dafe da cikinta, da alama tana cikin azabar ciwo, ya ɗauko robar ruwan ya shiga tofa mata addu'ah, wadda RAZ suka kawo a littafin dodon jatau, da kuma ayatul kursiyyu, suratul ikhlas, falaq da nas, kowanne sau Uku, ya dawo fuskarta ya bata tasha, sannan ya kwantar da ita, ya shafe mata fuskarta da cikin, da hannuwanta da k'afafuwanta, ta kwantar da kanta kawai jikinshi, tayi shiru tanajin ciwon na lafawa kaɗan-kaɗan,
   A haka barci ya ɗauketa jikinshi, ya gyara mata kwanciyar, bai koma barci ba, sai dai ya ɗauko Al-Qur'ani yana karanta mata har aka kira sallah, kallon tausayi kawai yake mata, kamar ya cire ciwon ya maida a jikinshi, rok'on Allah ya shiga yi daya kare mishi abunda ke cikinta, yasa babu abinda ya sameshi,


   Sai da aka kira sallahr asubah ya lallaɓa ya sauketa daga jikinshi, yana tashi itama ta buɗe ido, da k'arfinta ta yunqura zata tashi, ya dawo zai rik'ota
     "ina zakije?"
   "wanka zanyi"
       "tohh kwanta bara in haɗa miki ruwan"
   "Zan iya fa"
  "kedai ki kwanta nace"
     "tohm ranka shi daɗe"
  Ta koma ta kwanta ba don tanajin daɗin kwanciyar ba, don ko ina jikinta a ɓace yake, sai dai jinin ya daina zuba,
    Shiya taimaka mata ya mata wankan, dak'yar ya barta ta gyara wurin duk da tace mishi ta warke, sannan ta koma ta kwanta bayan tayi sallah jinta take kamar bata taɓa ciwo ba,
   "tashi fa zakiyi mu tafi asibiti"
   "Ba buk'atar wani asibiti fa, na warke"
 

 "kinason min wasa da baby ko? Da lafiyanki ma, jini kika zubar fa, na damu da sanin matsayin da babynmu yake ciki plz ki tashi mana" sai kuma yayi shiru muryarshi ta canja damuwa ne fal a ciki,
   "Duk laifinane Majeeda, da nasan zaku cutu jiya duk buk'atar da nake da wlhy dana hak'ura, baki kyautamun ba da baki faɗamun ba tun wuri"
   "Nima fa ban sani ba, anma fa tun kafinnan ne nakejin ciwon, karka zargi kanka shaheed, bara in shirya ɗin"
    "tohm" ya faɗa kawai yayi zurfi cikin tunani, duk damuwah ce a ranshi,

   Tare suka fito bayan sun shirya, karo sukaci da Maryam da kayan abinci a hannunta, ta tare su da murmushi,
    "Yanzu nake shirin kawo muku break fast ashe harkun fito, bara in kai muku dinning" ta juya tana ci gaba da magana, wani irin farin ciki take ciki,
    "inanan ina aiki, anma hankalina na wurinki, ya jikin naki?" sai da Majeeda tayi shiru cikin mamaki sannan ta bata amsa,
    "Yayi sauk'i auntie, Kin tashi lafiya?"
  "lafiya lau Majeeda," sannan ta juya wurin shaheed ta duk'a har k'asa cikin ladabi ta gaisheshi, ya amsa mata kamar shi yayi ciwon ba Majeeda ba, duk ya shiga damuwa,
    Abincinma kaɗan yaci, ya tashi bayan yacema Majeeda ta sameshi a waje, harya juya zai tafi kuma ya dawo da kallonshi kan Maryam, cikin wani yanayin da har saida ta tsorata,
    "Ya akai kikasan Majeeda bata lafiya?" kame-kame ta shiga yi, tama rasa amsar da zata bashi, Majeeda ce tayi murmushi,
    "Ba daɗewa fa ka faɗa mata zamuje asibiti" da sauri Maryam ta ɗago tana yak'e,
   "eeh mana, kaine ka faɗa"
   Har lokacin kallonta yake, don yasan kishi babu abinda bai saka mata, kuma bai manta da maganin data kawo mata ba, don ranar ne kawai ta taɓa bata magani da kanta, shi yamayi tunanin k'wayar maganinne tunda a hannu tazo dashi,
   "tunda muka fito bamui maganar asibiti ba,"

    "Miye haka Shaheed?" majeeda ta tambayeshi, hannu ya ɗaga mata yana kallon Maryam, can dubara tazo mata,
    "Wai Yau nice kake tsarewa da tambaya saboda na nuna kulawa a kan matarka? Jiya kukan data dinga yi tana wayyo cikina waye baiji ba? Ban taɓa tunanin hakan daga gareka ba Shaheed" sauke ajiyar zuciyah yayi sai kuma baiji daɗi ba,
     "Kinsan na yarda dake da yawa Maryam, kiyi hak'uri, na fara tsorone kada ko kishi ya saka kin fara canja halaye, ina tsoran halin Matan yanzu"
   "Duk k'ok'arin da nake akan matarka anma abunda zakamun kenan don yanzu ka samu ɗa? Ni kake zargi Shaheed? Ni....?" ta kasa magana ma saboda kuka,
    "ba haka bane Maryam kiyi hak'uri don Allah" tashi tayi ta ruga da gudu ɗakinta, dak'yar take gudunma saboda kib'a, yabi bayanta, Majeeda ta samu wuri ta zauna duk taa damu itama,
    Sun daɗe yana rarrashinta kafin su fito, tana dariya kamar ba itace ta gama kuka ba,
   "Tohh Majeeda a dawo lafiya"
   "Ameen Auntie, ban gajia kullum da gode miki, inama kowacce mace addu'ar samun kishiya kamarki, kici gaba da hak'uri damu plz"
    "ba komi Majeeda, anma zai addu'arnan taki....,ba kowacce mace keson kishiya ba"
  "indai irinki ce Auntie kowah ma zai so" murmushi Maryam tayi ita kaɗai tasan fassaranshi,
    "Tohh shknan saikun dawo, Allah ya baki lafiya"
   "Ameen"
  Sannan ta koma ciki, su kuma suka tafi asibiti,

    Tsadajjen Asibiti sukaje, ba ɓata lokaci sukaga likita, aka mata scanning da duk sauran abubuwa, likita ya tabbatar musu da babu wani abun daya samu cikinta, anma tana k'ara samun hutu sosae, (bed rest) saboda jinin data zubar, sunyi farin ciki sosae, ba kamar Shaheed saida yayi sujjadar godiya ga ubangiji, lallai Addu'ah bata faɗuwa k'asa banza,
    Sun fito tare suna tafiya taji yaro ya rirrik'e mata k'afafuwa,
    "Mamanah" muryar Abdallah taji da mamakinta, ta  juya shiɗin dai ne, ta ɗagoshi dak'yar zata ɗauka, Shaheed ya ansheshi,
   "Yanzunnan fa likita yace ki daina ɗaukar Abu mai nauyi"
     "Uncle"Abdallah ya faɗa, Shaheed ya harareshi da wasa,
   "bana hana Uncle ɗinnan ba" Abdallah yayi dariya,
   "Na daina Daddyna" Majeeda dai kallonshi kawai take baki buɗe,
     "kai dawa kukazo Asibiti?"
  "Nida Umma ne, ni kuma na fito" Majeeda ta kamo kunnenshi zata murɗe,
   "Yanzu yawonnan bazaka daina ba Abdallah?"
   "in zaki mishi faɗa kuma sai kinji mar ciwo? Zo muje kaji Abdallah Umma na can na nemanka" ya juya sukai gaba ta bishi a baya, duk nisan da yayi kau tsaf ya gane inda ya baro Umma, suka shiga batasan ma bainan ba,
   Suka gaisa da Umma, ashe Aisha ce batajin daɗi,
    "Umma Ashe Aisha bata lafiya kuma banji ba"
     "jikinne nata kullum ba daɗi Majeeda, Shiyasa ma bama faɗa"
   "Allah sarki, meke damunta"
  "har yau dai basu faɗa mana ba, anma jikin nata da sauk'i ma" 
     "Allah ya k'aro sauk'i Umma" ta k'ara kallonta, barcinta takesha, ita har manta kamanninta ma take, rabon data ganta tun tana gidan Majeed, hannunta ta duba,
    "Aikam na baro jikkata inda na zauna" Shaheed da keta shan surutu wurin Abdallah yace "bara in ɗauko miki tohh"
    "A'ah yi zamanka bara inje" ta fice da sauri tana tunano inda take ganin ta barota, cikin sa'a ta ganta, tana ɗauka ta juya zata tafi, ta jiyo maganarshi a kunnanta, bazata taɓa mantawa da muryarba, bazata taɓa manta yanayin da takeji idanta saurari muryar ba, shiru tayi ta kasa motsawa daga inda take, ko kallanshi ma batayi ba, wani irin yanayi da bazata iya fassarawa ba ta shiga, ganin haka ya canja akalar zancen,
      "ke haryau baki iya gaisuwa bane?" murmushi tayi jin ya tuno da lokacin da suke faɗa, kafin aurensu kenan,
   "Ayni banga Abinda zan gaisar ba anan"
       "lallaima yarinyar nan, yauma rashin kunyar zakimun?"
   "babu yarinya anan" ta bashi amsa,
   "idan nazo na murɗe wannan masifaffen bakin naki kinmu bayani"
   "Zan zauna ne ka murɗemun baki? Kaima kasan ba tsoranka...." sai kuma tayi shiru tana k'ok'arin maida hawayenta, su duka suka yi daria,
     "Gaskiya da munyi yarinta"  ta faɗa tana juyowa, shima dariyar yake, sai kuma yayi shiru, shima da damuwa a fuskarshi
    "lokacin da muka fara gane gaskiya kuma k'addara tayi halinta" sai yanzu ta ɗago suka haɗa ido, tun bayan rabuwarsu bata k'ara ganinshi ba, shekara kusan Uku, yayi fari ya k'ara kyau sosae, sai dai rama da yayi da alaman bai cikin kwanciyar hankali,
   "Yaya Majeed dukka rame" ita kanta batasan sanda ta faɗa ba,
   "kekam Matatah na kwance Asibiti, kullum ciwo, idan ban rame ba ya za'a gane nine mijin?" ya faɗa da zolaya, sosae ya bata daria,
    "Allah ya bata lafiya"
  "Ameen, kwana da yawa, faɗamun ya rayuwanki?"

 "ba daɗi, tun bayan rabuwar mu, Munyi aure da shaheed, matsalan dangin miji, ga kishiya kullum saita zaneni, miji babu ruwanshi dani, babu ci babu sha, babu wanda zan faɗama matsalana, kaifa?" yaɗan murmusa, irin yanda yake idan taa gama burgeshi,
   "Munyi aure da Aisha, Masifa harta linka taki, safe daban rana daban, ba ruwanta damun girki, kullum tayi ficewarta bata tambayata, ta rainani batajin magana ta kuma..." yayi shiru yana tunani, suka k'arayin daria a tare,
   "ina cikin farin ciki yaya Majeed, bani da matsala da kowah"
   "nima haka Majeeda, Aisha macece ta gari, banda damuwa yanzu saita ciwonta kawai, sai muna tunanin taji sauk'i kuma abun ya dawo"
    "Insha Allahu zata samu lafia"
    "Ameen fa"
   "Yanzu dai mu manta da rayuwarmu ta baya, ko babu komai mu en uwanah ne, kina kallona a matsayin yayanki, komai ya wuce"
   "komai yaa wuce fa," ta faɗa tana share hawayenta cikin dubara, "bara inje yanzu zamu tafi"
     Ta juya ta tafi, shima bai iya ce mata komi ba, soyayyar gaskiya kenan, kowannensu k'ok'arin ɓoye damuwarshi yake da murmushi, anma a zuciyoyinsu sunajin ciwo sosae,
  Tana zuwa sallama sukayi da Umma, bayan ta k'ara duba Aisha, sosae ta bata tausayi,