HARAMTACCEN AURE PART 5
Wani wahalallen miyau ne ta haɗe da k'yar, tayi tsuru-tsuru da ita kamar wadda aka dasa, buɗe baki tayi zatai magana ta kasa ta bar bakin buɗe tana kallon Aunty Zainabu,
Jikinta bai tashi kyarma ba saida Aunty Zainabu ta doso inda suke, tana tafiya tana kallonsu fuskarta babu annuri, bata ankara ba sai dai taji ta fara jik'ewa da zufa ta ko ina,
"Aunty wallahi zan miki bayani, don Allah ki dakata, abinda kikaji ba haka bane"
Bata tankata ba harta k'araso inda take, tuni taa gama sandarewa, sai dai taga ta duk'a inda take, ta ɗaga filo ta zaro wayarta, sannan ta juya tabar ɗakin, ba tare data tanka musu ba
Wata munafukar ajiyar zuciyah ta saki sannan ta juyo inda hafsatul kiram take itama duk taa haɗa zufa, tama fita ruɗewa, (wanda suka karanta littafin hafsatul kiram sun santa da saurin ruɗewa, abu kaɗan ke sakata kuka), tuni hawaye suka wanke mata fuska, harta so ba Majeeda dariya,
"Akwai matsala fa" inji Majeeda,
"Matsalan me kina ga batace komi ba, da alama bataji mu ba"
"Zanyi fatan hakan hafsat, anma nifa hankalina bai kwanta ba da irin kallon da take mana" duk sukai shiru kowa ya rasa abun cewa,
Sun daɗe a haka babu wanda ya iya cewa komi, k'arar shigowar text ne ya katsesu a wayar Majeeda, duk saida suka firgita, sannan ta daure ta duba, kamar wata marar lafiya,
"I don't say it enough, but wanted to let you know that I love you."
"luv uh too i swear, ina ka shige?"
"cikin zuciyarki...lol ina hanya hope kowa dai ya gama tafiya, ina kewar matata da yawa"
Ta sauke ajiyar zuciyah, addu'ah ta shiga yi Allah ya kawoshi gidan da wuri, tare da Addu'an Allah yasa Aunty Zainabu bataji su ba.
Firarma kasawa sukai ita da hafsat, da gudu ta tafi toilet ta zazzagar da fitsarin data kusan saki shigowar Aunty, tana dawowa ta zari jikkarta,
"Tohh Aminiyah, nidai zan tafi"
ta tashi da sauri tana gyara ɗaurin zane, "ina kuma zaki tafi ki barni cikin wannan bala'i?"
"Haba, ki kwantar da hankalinki mana komai zai dai-daita insha Allah, zamuyi waya Ya Umar yana waje"
"kema fa hankalinki tashe yake taya zan kwantar da nawa?" dafa kafaɗarta hafsat tayi, suka fito tana kwantar mata da hankali,
Sai dai me? Falonta wayam babu furnitures nata, komai an kwashe kamar sabon gini, duk suka saki baki suna kallo har Aunty Zainabu tazo ta bangajesu ta wuce bedroom ɗin nata tana sauri,
Kayan sawarta ta dinga kwashesa tana juye mata a akwatunanta, hafsat na ganin haka ta mata sallama ta tafi, bata samu maa ta amsa mata ba,
Tafiya tayi da sauri inda Aunty take ta rik'e mata hannu,
"Aunty ina za'a kaimin kayan kike kwasarsu?"
Bata tankata ba taci gaba da kwashewa, sai da ta gama kwashe komai, ko k'yalle bata bari ba ta jasu tayi waje dasu, Majeeda ta k'ara shan gabanta,
"Aunty don Allah ki faɗamun ina zaki kaimun kaya?" k'ara shareta tayi taci gaba da jan kayan,
Duk ta ruɗe kuka kawai take kamar wacce ake zare ma rai, ta kwanta nan k'asa kamar k'aramar yarinya tana gunjin kuka,
"Don Allah ki rufamun Asiri Aunty yanda naki ya rufu, ki taimakeni karku rabani da Yaya Majeed, shine rayuwatah, don Allah Aunty ki tausayamun" idan Aunty Zainabu ta tankata ku da kuke karatunnan kun tanka, haka taci gaba da kuka har muryarta ta soma sik'ewa,
Tana ji tana gani suka kwashe komai na ɓangarenta, harta Abdallah goyeshi tayi a bayanta, ta wurga mata mayafi,
"ki tashi mu tafi nace"
Da tafiyar gwiwa ta gangaro inda Aunty take ta rik'e k'afafunta,
"ki kasheni ma kawai Aunty, zaifimun sauk'i da rayuwa babushi, don Allah karki Rabani da Yaya Majeed Aunty, ina sonshi" ta k'ara fashewa da kuka hannuwanta rik'e da k'afafun Aunty Zainabu,
Ji tayi Aunty ta k'yalk'yale da daria,
"lallai Majeeda bansan sanda soyayya ta rufe miki ido ba haka, ranar da za'a kawoki kin cika ma mutane kunne, 'don Allah karku kaini, bazan iya rayuwa dashi ba,' yau kuma kece da cewa bazaki iya rayuwah babushi ba, Sabon gidan da Dadd ya baku zaku koma, ko wani kike ba ajiyar kuɗin da za'a sake miki wasu kayan?"
Wata doguwar ajiyar zuciyah ta saki tana jan numfashi, ta ɗago kanta tana kallon Aunty cikin shakkun maganar data faɗa, murmushi taga tana mata,
"Aunty dgsk sabon gidan zaki kaini?"
"da gaske mana, idan ba can ba ina zan kaiki?" shiru tayi sannan hankalinta ya fara kwanciya,
"da tunanin me kikeyi?"
"ba komi Aunty, mu tafi" tana maida mata murmushinta, suka fito suka tafi, sai jan Aunty take da labari don ta tabbatar ba haushinta takeji ba, ita kuma taci gaba da biye mata,
Bata ankara ba ta gansu hanyar gidansu Majeed, ta ɗago fuskarta cikin wani hargitsin tana kallon Aunty, tun kafin ta mata magana ta rigata,
"Zamu biya ki musu ban kwana ne" sannan ta saki ranta, hankalinta kwance suka shiga gidan, kai tsaye ɗakin Abba suka wuce
Kowah ya haɗu a ɗakin kamar ana wani taro, Daddynta da Momie, Umman Majeed da Abbanshi, harda Zahra ma, Majeed ta hango shima zaune, anma bata ga alaman damuwa a fuskarshi ba don shima ba'a mishi maganar ba, kuma bai taɓa kawowa a ranshi zasu san da maganar ba,
Ganin haka itama bata damu da ganinsu ba, don bataga alamar Aunty taji maganar da tayi ba, suka samu wuri saman carpet ita da Aunty suka zauna, suna satar kallo ita da Majeed,
Abban Majeed ne ya fara magana "bamu zauna nan don ku mana k'arya ba, ko mu saurari wani shirme naku, kun riga da kun gama kaimu k'arshe, ku faɗa mana tsakaninku da Allah wanne irin zama kuke tsakaninku"
Ba wani shakku a ran Majeed yace "irin zaman da kukeso muyi Abba, mun daina faɗa, ina bata duk wani hakk'inta na aure, ka tambayeta kaji" tun kafin a tambayeta ta amshe
"sosae ma kuwa Abba, yana kulawa dani, muna zaman mu lafiya"
Daddy ya jefa musu da tambayar da duk saida ta kusan katse musu en hanji,
"Bayan kun raba auren naku kenan?" duk suka fara muzurai irinna mararsa gaskiya, dak'yar Majeed ya iya k'arfin hali,
"Raba Aure kuma daddy kamar wasu mararsa hankali, mema zaija mana raba aure?"
"Wa kake tambaya cikinmu?" inji Abba,
"daman ina hankalin yake? Ban taɓa tunanin zaku iya aikata hakan ba, kun munafunce mu, kuma kun cuci kanku..." Majeed da har yanzu baisan yanda akai ba, yayi saurin cewa
"Abba mufa ba abinda muka aikata, idan ma wani ne yakeso ya haɗamu daku wallahi sharri ne"
"waye zai muku sharrin cikinmu? Koda yake, daman kun daɗe da maidamu shashashai tunda har kuke tunanin bazamu gano zaman da kuke ba" Abba ya mik'a hannu ya ansa wayar Aunty Zainabu data ɗauka kusa dasu, ta kunno recordn ɗin maganar Majeeda da hafsa yanda kowa zaiji,
Majeeda kamar ta zunduma da gudu, tama kasa zama kamar wacce zafi ya kama, hawaye ne kawai ke kwararo mata ta ko ina, tunda take bata taɓa shiga tashin hankali haka a rayuwarta ba, tama kasa ɗaga kai ta kalli kowa, Majeed ma tunda ya ɗukar da kanshi bai k'ara ɗagowa ba, zufa kam rigarshi harta jik'e,
Ɗakin yayi shiru, sai sautin kukan Majeeda dake fita a hankali,
"Shima wannan ɗin sharri ne?" Abba ya tambayesu,
"Anma na rantse Abba babu abinda ya shiga tsakanina dashi..."
Wani irin k'wallo Daddy yayi da ita,
“shi cikin Abdallahn a ruwa kikasha cikinshi? Ko har yawon iskanci kike fita?" tai saurin rik'e bakinta, tana dafe inda daddy ya sa mata k'afa saboda zafin da yake mata, idanunshi sunyi jajir da ɓacin rai,
Sai lokacin takai kallonta ga Momie, ta duk'arda fuskarta tana share hawaye da alama kuka take, wannan wane irin tashin hankali ne yau take gani?
Abban Majeed ma cikin rawar murya da alama dauriya yace,
"kun cucemu, kun karya duk yarda da mukai daku, Alk'awari ne mukai ma mahaifinmu, Anma a sanadiyyarku mun kasa cikawa, Allah ya gani munyi iyakar k'ok'arinmu, anma kun nuna mana baku isa ba, HARAMTACCEN ZAMA?, bansan a ina kuka samo wannan tarbiyyar ba, kuma kunyi kaɗan kuce mune muka baku ita, me kukeso jama'a suce a kanmu? Mun muku auren dolene kuka maida kanku haka? Wlhy k'arya kuke duniya ta zagemu a kanku, bazamu taɓa yafe muku...."
Umma tace "duk meya kawo hakan Alhaji? Yanzu kuma inka musu baki ya kakeso su zama?"
"harna yaushe kuma? ZAMAN DADIRO fa, wallahi zaifimin daɗi ace mutuwa sukai da inga wannan rana" duk k'arfin halin da Abba yake da kuka ya k'arasa maganar,
Can ciki Majeed shima Yace "Ayi hak'uri Abba, kuskure...." wani irin Mazga da Abba yakai mishi a baki har saida yayi jini, cikin tashin hankali ya buɗe bakin sai gashi har hak'ori ya fita,
Hakan baisa Abba ya saurara mishi ba, saima ya tashi ya rufeshi da duka ta ko ina, daddy na rik'eshi anma kamar yana k'ara mishi k'arfi, shiko Majeed ko motsawa baiyi ba, yana zaune yanda yake Abba na jibgarshi, dak'yar daddy ya k'waceshi ya matsa sai huci yake,
"ka k'yaleni in kasheshi in huta da wannan bak'in cikin nashi, ai duk laifinshine, shine babba kuma sakaran banza, inama amfanin haihuwarshi?"
"A'ah Yaya, idan har akwai laifinshi tohh nata yafi yawa"
"laifinta data buɗa baki ta sakeshi? Idan har ya daraja maganarmu bai saketa ba zata saki kanta ne? Ko zata ma kanta ciki ne? Shine lalataccen ɗan iskan da yayi sanadin komi, ita tana da raunanniyar zuciya, da kalamai en kaɗan zai iya galaba a kanta" yana gama faɗi ya shige bedroom ɗinshi, Umma ta tashi ta bishi,
Haka su Daddy suma suka fita, Aunty Zainabu taja Hannun Majeeda suka tafi anan kowa ya watse akabar Majeed kamar wani zararre,
Saida Zahra ta dawo ta mishi magana sannan ya mik'e ya tafi yana tangaɗi ko kallon gabanshi baiyi harya shige ɗakinshi
Har sukaje gida Majeeda kuka take, babu wanda yayi k'ok'arin rarrashinta, kamar ranta zai fita haka take wannan kuka,
Suna zuwa Aunty ta rakata tsohon ɗakinta, kayanta komi sunanan, ta kwance mata goyon Abdallah ta ajjeshi sannan ta juya ta barta nan,
Jawoshi tayi ta ɗaura saman jinyarta ta tsura mishi ido, kowanne hali babanshi yake ciki? Shikenan fa kamar k'iftawar ido komai ya gama faruwa, rungumeshi tayi a jikinta taci gaban da kuka,
Bayan kwana biyu,
Majeeda babuci, babusha, saita kama dole, tayi wata uwar rama tayi bak'i sosae, kullum cikin kuka take, daga Momie har daddy babu wanda ya kula da halin da take ciki, Abdallah kanshi yayi ramar dole saboda bai samun isasshen abinci, sai dai da madara ake kaɗa mishi,
Kullum cikin kiran layin Majeed take bai shiga, babbar damuwarta kenan da batasan halin da yake ciki ba, rayuwar gaba ɗaya taa burkice mata da babu Majeed a tare da ita,
Sai a kwana na Uku ne Momie ta fara gajia da halin da take ciki, tunda ta shiga ɗakin bata fito ba, abinci yanda aka kai mata haka za'a ɗaukeshi, ruwa kawai take ɗura ma cikinta,
Tana kwance ta saka waya a gabanta tana kuka, bayan ta gama kiran layin Majeed,
Momie tace "tashi Zaune" babu gardama ta mik'e zaune tana share hawaye, momie ta jawo kwanon Abinci ta ajje mata gabanta,
"banson gardama, ki maza ki cinye abincinnan idan baso kike muci gaba da sanya miki ido ba" kuka ta fashe dashi sosai ta faɗa jikin momie,
"Don Allah momie kuyi hak'uri"
"naji tashi kici abinci nace" ta tallabota, sai da ta tabbatar taci mai yawa sannan ta k'yaleta bayan tasha ruwa, da kanta ta fita da kwanonin sannan ta dawo zauna tana fuskantar Majeeda,
"Damuwar me kike?" tayi shiru ta kasa ɗago kanta, momie ta zare wayarta dake sak'ale a hannunta,
"bamu isa mu rabaki dashi ba Majeeda? Yanzu kiran menene kike mishi?" shiru ba amsa,
"ke ba k'aramar yarinya ba da basai an zauna ana miki faɗa ba, yanzu duk bayan wannan neman wata alak'a kike a tsakaninku? Ki zauna kiyi tunani kanki ne kike cuta, kece mace, daga inda ya samu wata macen zai manta dake, kekau kina nan kullum kina cutar zuciyarki da tunaninshi, kiyi tunani idan har yana sonki me yasa ya sakeki? Da yake kanki rashin hankali ya k'are kika zauna kikaci gaba da zama dashi, kullum kuna cikin saɓon ubangiji, kuna tara ma kanku zunubai, me zakuce da ɗanku idan ya girma ya gano ta hanyar da kuka sameshi? Ki godema Allah da abun ya tsaya a haka, damarkice da zaki zauna kita rok'ar yafiyar ubangiji, ki manta da Majeed da rayuwar da kukayi a baya,"
"Momie wallahi na kasa ne, kullum ina k'ok'arin mantawa dashi, don Allah ki tayani da Addu'ah"
"ki k'ara dagewa kam, don babu wani sauran zama a tsakaninku, babu inda kika taɓajin anyi saki Uku an koma, kema kina tashi kina addu'ah Allah ya yafe miki, ya kuma yaye miki sonshi, namiji ne da ba'asha mishi alwashi, duk yanda yakai da sonki wata rana shida kanshi zai goranta miki,......" nasiha dai sosae Momie ta shiga yi mata, gaba ɗata jikinta yayi sanyi, har momie ta barta tana zubar da hawaye,
"Taya zan fara koyama kaina rayuwa babu Majeed?"
Majeed,
Shima tun daga ranar duk wani farin ciki ya k'aurace mishi, yana raye anma yafi kama da matacce, ko kukan ya kasa yi, idan ya fara kallon wuri ɗaya sai ya daɗe a haka, ko magana baiyi, tunsu Umma na ganin abun wasa harya fara damunsu, ada Zahra ce kawai ke kula dashi,
Umma har sanyashi gaba take taita kukan kodai ya haukacene, gashinan dai har asibiti anje babu wani ci gaba, ko abinci aka ɗura sai anbi da ruwa zai haɗe,
Wata rana Zahra taje take bamasu Momie labarin halin da yake ciki, sai a sannanne majeeda na laɓe ta jiyo, taci kukanta harta gode ma Allah,
Abdallah ne ta goya ta tafi dashi su Umma nata jajenshi, daga can ɗaki ya dinga jiyo kukanshi, takenan duk abubuwan da suka faru suka dunga dawo mishi, baisan sanda ya k'walla k'ara ba, sai a sannanne yayita kuka,
Wani lokacinshi kanshi kukan yana maganin damuwa, sukaita murna jin ya dawo hankalinshi,
Aisha tana yawan zuwa ganinshi, duk da ba wata fira ke shiga tsakaninsu ba, anma tana k'ok'arin debe mishi kewa
A gurguje plz
Bayan shekara ɗaya
Abubuwa da yawa sun faru cikin, ɓangaren Majeeda ta gama makarantarta, hankalinta kwance ta fara mantawa da Majeed duk da abu mai wahala ne ta iya cire tunaninshi a ranta, anma tana k'ok'arin hakan,
Abdallah yayi wayau, yana ɗan jagwalgwala magana, babu inda bai zuwa yawo koda gudu ne, kakanninshi kowanne ɓangare ji suke dashi, duk da ba'a yayeshi ba anma kusan kullum a gidansu Umma yake yini, ba k'aramin tausayin yaron sukeji ba, Aunty zainabu ma ta haifi ɗanta namiji, Abdul k'adir,
***
Anata shirye-shiryen bikin Majeed da Aisha, anyi hidima sosae duk da angon ba wani nutsuwa gareshi ba, mahaifinta ne ma ya matsa akayi saboda yanda ta guji auren kowa ita dai sai Majeed kullum tana gidansu, duk yanda Majeeda taso ta danne zuciyarta ta halarci bikin kasawa tayi, sai dai ta kulle kanta a ɗaki tayi ta kuka,
An ɗaura aure, can kaduna state aka kai mishi amaryar don yanaso yayi nesa da gida,
Dare yayi Amarya na can bedroom ansha lulluɓi ana jiran ango, kamar daren farkonshi da Majeeda shi kaɗai ya shigo da ledar kaji da drinks a hannu, ya tura k'ofar ɗakin zai shiga,
Daren farkonshi da Majeeda ya faɗo mishi, yanda suka dinga faɗa kamar sun cinye junansu, baisan sanda ya saki laidar ba ya dawo da baya, kujera ya samu a falo ya zauna yana sharar hawaye, ba kaɗan ba yake kewar Majeeda,
Shiru-shiru Aisha ba ango, tun tana tunanin yana hanya ya kusan zuwa harta daina ta fara tunanin abinda ya tsaidashi,
Har k'arfe ɗaya babu Ango, hankalinta fa ya tashi ta fara tunanin ko ina ya shige, shawarar kiranshi a wayane tazo mata, ta ɗauko wayarta ta kirashi, can falo ta dinga jiyo ringing ɗin wayar anma ba'a ɗauka ba, haka ta dinga kira tana katsewa, ta fara tsorata, cikin sadaukarwa ta lallaɓa ta fito falon,
Can ta hangoshi saman kujera yayi tagumi da alama tunani yake, ta daurema zuciyarta ta k'arasa inda yake, sai da ta ɗan taɓoshi sannan yasan da zuwanta,
"Majeeda ko?" ta tambayeshi tana kallonshi da raunanniyar murya,
"bazan miki k'arya ba Aisha, naa kasa mantawa da Majeeda, wlhy komai nake ita nake tunawa" cikin sigar lallashi tace,
"ba abune mai sauk'i haka ba hniee, anma insha Allah nayi maka alk'awarin maye maka gurbinta, zan zame maka mace ta gari, zan maka dun abinda zai faranta maka in guji wanda zai ɓata maka, zan nuna maka soyayya fiye da wacce kake tsammani, ina sonka da yawa hniee"
"ngde Aisha, kiyi hak'uri kinji, insha Allah zanyi k'ok'arin daina tunaninta"
"ba komai fa hniee, taso muje ka kwanta, tunanin ya isa haka," haka taci gaba da lallashinshi da kalamai masu daɗi har sai da ta tabbatar hankalinshi ya kwanta,
A daren ranar Majeeda tayi kukanda bata taɓayi ba tunda tazo duniya, yanzu ne ta k'ara tabbatar ma kanta da taa rasa Majeed, daman Momie ta faɗa mata namiji ba'asha mishi alwashi, shknan har yayi aurenshi,
Ga wani ciwon kai daya matsa mata ko barcin ta kasa, ita kaɗai a ɗaki Abdallah na wurin momie yayi barci tace a barshi tunda ba tashi yake ba, sai faman shafa confo take a kai,
Abubuwa sun mata yawa kamar ita kaɗai damuwa ta k'are mawa, ga faɗan Abba kullum maganarshi ta fiddo miji tayi aure, kamar tana zaune a saman kansu,
Tohh ita wama zata aura? Ita da ba fita take ba ballantana wani yace yana sonta, inma fitar dole ta kama mata da dogon hijabinta da nik'ab take tafiya, ta saɓa Abdallah a kafaɗa kamar matar aure, dole aji shakkar mata magana,
Yanzu haka sauran sati ɗaya lokacin da daddy ya bata ya cika, koya aura mata duk wanda yaga dama, ta riga ta hak'ura da koma wanene, tunda ta rasa Majeed bata da wani sauran zaɓi,
Kwana Uku da bikin Majeed har lokacin bata da wani natsuwa a tare da ita, zata fito dai ta taya Momie en aikace-aikacen da suka kamata, sai Momie tana janta da fira duk don taga hankalinta ya kwanta, anma data koma ɗaki sai wata sabuwar damuwar kuma,
Yauma kamar kullum ta gama duk abinda take, ta shiga da Abdallah toilet ta sake mishi wanka, tun kafin ta shiryashi yaketa son ya fita, tana saka mishi kaya kam yabar ɗakin,
Ta ɗauka ɗakin Momie ya tafi, ta shareshi tayi kwanciyarta har barci ya fara ɗaukarta ta jiyo muryar Momie tana tambayarta "Ina Abdallah" da ta ɗauka cikin barci ne, sai kuma ta tashi firgigit,
"Momie ba wurinku yaje ba?"
"A'ah tunda ya biyoki rabona dashi" ba shiri Majeeda ta sauko daga kan gadon,
"ni wannan hegen yawon na Abdallah, yanzu haka yana can yana ɓarna"
"Aikam k'ara ki nemoshi, don yau yaimun ɓarna kujera zanyi dashi" tana dariya ta zira hijabinta,
"Momie ana zauna mai gida?"
"ni bani miji da wannan maɓarnacin, na barma Umma dai" dariya kawai tayi ta wuce, kullum cikin bata dariya suke, Momie da Abdallah,
Gidan ta shiga zagayewa, lunguna da sak'o da duk inda take tunanin Abdallah babushi, duk faɗin gidan babu inda bata duba ba, harta fito tsakar gida, inda ake ajje motoci ma taa dudduba babu shi, ta k'arasa tana tambayar mai gadi ko yaa ganshi,
"wallahi hajia da yake na zagaya bayan gida ban lura ba koya fice, kuma saina manta da gidan a buɗe, duk an duba gidan bainan?" bata tsaya bashi amsa ba ta saka k'afa zata fice, kuma saita tuna bata da nik'ab ɗin, da gudu-gudu, sauri-sauri ta koma ciki sannan ta ɗauko ta dawo,
Momie cikin tashin hankali take tambayarta,
"Momie ban ganshi ba bari in duba cikin unguwa"
Abinka da unguwarda babu mutane, yaransu ma basu cika fita ba, sai en tsararun mutanen data gani take tambaya, anma kowa amsar ɗaya ce bai ganshi ba, tsananin tashin hankali harta fara hawaye ta cikin nik'abinta,
Harta yanke shawarar komawa gida ta fasa, tasha kwanar layin bayansu, tana shiga ta hangoshi hannun wani handsome zaune saman bayan mota yana mishi wasa, sai dariya yake abinshi,
Saida ta saukar da ajiyar zuciya, sannan ta k'arasa inda suke,
"Ina wuni" ta gaishe dashi, cikin rashin fahimta yake dudduba kusa dashi, sannan ya dawo da kallonshi gareta ya tsura mata ido cikin nik'abin data rufe fuska dashi, yana son garin fuskar mamallakiyar zazzak'ar muryarnan, shikau Abdallah sai wasanshi yake a jikinshi,
"Yaron dake hannunka nawa ne, ya fito daga gida" majeeda ta faɗa cikin k'osawa da kallon da yake mata,
"ta yaya zan gane ba satarshi zaki ba, kina cikin wannan bak'in Abun"
"na maka kama da mai sata ne? K'ila dai kaike shirin hakan" ta mik'a hannu zata ɗaukoshi aiko ya k'ara mak'alk'ale mutumin,
"Abdallah" ta k'wala mishi kira cikin ɓacin rai,
"Ayam" ya amsa da gwarancinshi,
"Zo muje gida Momie na kira"
"um-um, uncle" ya faɗa yana k'ara rik'e mutumin, takai hannu zata ɗaukeshi da tsiya, ya rirrik'eshi gashi bataso ta haɗa jiki dashi,
"Don Allah ka bani yarona in tafi"
"kingama tsoranki yake, alamar bai sanki ba, ki buɗe fuskarki idan da gaske kin sanshi" ganin tana k'ara ɓata ma kanta lokaci ya sanyata ɗaga nik'ab din, tsaida komi yayi ya tsaya yana kallonta, duk yanda yake hasaso kyawunta a zuciyarshi ta wuce nan,
Abdallah na haɗa ido da ita ya k'ara lafewa jikin mutumin yana daria,
"Auntieee, wannan ne"
"wannan ne me? Kazo muje nace" ta jawoshi ya koma da baya yana dariya,
"Don Allah malam ni Matar aure ce ka bani yarona in tafi"
"Ni naa tambayeki ne? Ai gashinan saiku tafi, nima da kika ganninan mijin aure ne, kawai yaronne bani da, kuma ina matuk'ar son yara da saurin shak'uwa dasu"
"nima duk ban tambayeka wannan ba" sai lokacin yayi dariya sosae harya fara bata haushi,
"wai matar aure, don kuna kama dashi shine zai zama ɗanki? Matar aure ma kama ne da ita"
"tunda kaa gane ina kama dashi, kasan ba satar shi zanba kenan? Ka saukeminshi in ɗauka" ya sauko daga samar motar ya saukeshi anma yaqi sauka,
"gashinan masu ɗa"
Yaro fa yak'i sauka, sai daria yake yana rik'eshi,
"ban juwa, didan"
Duk yanda taso anma yak'i yarda da ita
"hajia ki rok'eni kawai in kai miki yaronki gida" bata saurareshi ba taci gaba da lallashin Abdallah yazo su tafi, anma yak'i yama maida ita kamar k'awar wasanshi,
"Abdallah bazaka je gida ba?", ya tambayeshi, shikau harda saurin ɗaga kai,
"Meyasa?" yayi shiru da yake maganarshi ba k'wari tayi ba,
"mu tafi can muyi wasan ko"
"eeh janje didan"
"Yauwah tohh mu tafi yaron kirki" ya ɗaurashi a kafaɗa sukai gaba don yaga hanyar da Majeeda ta biyo,
"Auntie mu tafi ko? Nima zan wuce gidane yanzu, ko an barmun shi?" batace mishi komi ba dai tabi bayanshi, suka tafi, sai da sukaje dai-dai gidan tace "tohh sauke minshi anan" ana saukeshi kau yayi cikin gidan da gudu,
"na gode" tace mishi kawai, sannan tabi bayan Abdallah, yayi tsaye a k'ofar yana kallonta harta shige,
Mai gadin ya taso rufe k'ofa ya ganshi nan tsaye, ya fasa rufewar bayan ya lek'o da kanshi,
"Barka dai yallaɓai"
"Yauwah baba, sannu da aiki" ya juya zai bar wurin,
"Aiki da godia, wurin Alhaji kazo ne?"
"A'ah yaron Matar gidan dai na maido"
"matar gidan kuma? Ɗiyar Alhaji dai" harya fara tafiya ya dawo jin haka, baba mai gadi harda gyara tsayuwa zai fara tsegumi,
"Shifa yaron?"
"ɗanta ne, anma yanzu shekara ɗaya kenan da en watanni basu tare da mijin"
Gaskiya mai gadinnan akwai surutu, mutumin ya faɗa a ranshi,
"Allah sarki, nagode sosai baba" ya zaro dubu biyu ya mik'a mishi, ya amsa yana washe baki, don akwaishi da son kuɗi
"ni keda godia yaro," sai kuma ya kasa tafiya, yayi shiru yana so yayi ma baba magana,
"numberta zan baka?" da sauri ya ɗaga kai,
"yauwah baba za'a samu ko"
"eeh yaro, anma ka k'aro dubu biyar", yana kallon tudun Aljihunshi, ikon Allah wannan wanne irin mai gadi ne? Gashi dai tsoho sai tsurku da son gulma, ga shegen son kuɗi,
Ya kwaso duk kuɗin Aljihunshu dubu uku,
"gashi baba, daman su kaɗai suka rage"
"tohh shknan yaro nima rabi zan baka tunda rabi ka bada" baza'ayi haka ba baba ina zuwa,
Ya koma inda ya aje motarshi, ya jawota k'ofar gidan, ya dawo ya mik'a mishi dubu biyar cas sannan yace yana zuwa, ya shiga ɗakin da yake ya ɗauko wayar bala driver daya bari chaji ya kawo mishi,
"Gashinan Alhaji duba, ko hajia Majeeda, ko Majeeda, ko er gatan Alhaji duk yanda kaga an rubuta"
"Sunanta majeeda kenan" ya faɗa yana murmushi, "suna mai daɗi, kuma ya dace da ita,
Ya maida mishi wayar yana godia bayan ya ɗauka number,
Abdallah da gudu ya shige gidan, Majeeda na mishi magana bai tsaya ba saida yaje inda momie take ya faɗa jikinta yana daria, sannan taja ta tsaya tana kallonshi,
"Abdallah ina ka tafine muna ta nemanka?"
"wuyin uncle" ya fara lallaben Aljihunshi ya ciro chocolates yana bata,
"shine ya baka wannan" ya ɗaga mata kai,
"ka daina fita yawo kaji" nanma ɗaga kan yayi, sannan ya sauko kuma ya tafi wurin Majeeda ta ɗaukeshi, suka tafi ɗaki,
Faɗa sosae ta mishi harya fara kuka, ta rungumeshi don batason ɓacin ranshi, ta share hawayen daya zubo mata,
"ka daina rashin ji kaaji yaro nah"
"baran kala fita ba"
"yauwah nima naa daina maka faɗa" taci gaba da lallashinshi har yayi barci,
Da dare harta kwanta, taji wayarta na ringing, ta jawo da duba bata gane number ba ta maida ta aje, mai kiran dai ya nace da kira gashi barci takeson yi, ta ɗauka kawai batayi magana ba,
Ɗayan bangarenma shirun akayi, harta gaji da saurare ta kashe ta maida ta ajje, aka sake kira ta kashe wayar ma gaba ɗaya,
