HARAMTACCEN AURE PART 2
Batayi wani barcin kirki ba saboda yanda ta k'agara gari ya waye, ga uban kukan da tasha da safe duk idanunta sun kunbura. Gari na gama haske ta shirya wurin 11 tace ma Momie taa tafi gidan Aunty Zainab, da yake tasan matsalanta da damuwanta kuma bata da wani abokin shawara kamar Aunty Zainab ɗin shiyasa momie bata hanata taje ta kwantar mata da hankali ba.
Napep ta tara ya kaita gidan Aunty Zainab, tana sauka daga napep ɗin yana fitowa da motarshi daga gidan, ta juyar da kanta gefe kamar bata ganshi ba, yayo kanta da mota kuwa har ya kusan take mata k'afa sannan ya fito daga motar.
Yana nunata da ɗan yatsa yace "ina fatan kinsan abinda ke faruwa, kuma baki amince musu ba" sai data gatsina sannan tace "kaima kasani ai bazan taɓa amince da auran ka ba"
"Yaa miki kyau, don wallahi aka aura min ke gutsun-gutsun ina iya miki in jefar dake, don ko kaɗan baki cikin kalar matan da nake so"
Tsoki kawai taja ta juya ta tafi don batason tsayawa magana dashi ma, wata tsanar shi ce ke k'ara zo mata ta shige gidan Aunty Zainab kawai.
Tun daga ranar kullum cikin damuwa suke, babu wanda bai kwanta rashin lafiya a cikinsu ba, k'iyayya sosai suke nuna ma junansu, anma iyayensu sukai watsi dasu sai dai hidimar biki kawai suke.
Duk yanda suka so a fasa auren sai da aka ɗaura shi su duka babu mai so, a tunaninsu iyayen idan akayi auren daga baya zasu warware ne suci gaba da son junansu, basu sanda babban kuskure ne suka tafka ba (inji rash kardam).
A gurguje dai
Mu koma labari....
Ci gaban labari
A hankali majeed Yace "miye mafita? Nifa tsakanina da Allah bazan iya zama dake a matsayin mata ba" tace "nima haka wallahi, kuma indai zamu zauna a inuwa ɗaya sai munyi faɗa" yace "hakane ya zama dole musan abunyi" tace "tohh me zamuyi?"
Yace "mu rabu kawai kowa yayi sabgarshi, tunda kowa ɓangarenshi daban" ta zaro ido "idan fa suka gano?" yace "tohh waye zai faɗa musu? Kinga saima in samar miki admission kici gaba da makarantarki" tace "hakane tohh sakeni"
Ba wani tunani ko damuwa a fuskarshi Yace "na sakeki saki ɗaya" itama ba da wani abu a ranta ba tace "saki ɗaya ai ana komawa" kafin ta rufe "baki yace "na sakeki saki biyu" tace "ai wallahi saki biyunma ana komawa, ka cikashe kawai" Yace "na sakeki saki uku.
Wani ihun daɗi ta saki saboda tsananin farin ciki, ta tashi tana tsallen murna, harta tafi ta dawo.
"Anma babu ruwan kowa da harkar kowa? Babu aurenka a kaina, babu faɗa a tsakaninmu, ko nuna iko da shisshigi" yaja tsoki yana juyar da fuska
"ke duk wannan ya dama, salon kuma shegen surutunki ya kai ki faɗa ma wani"
"Anma haka zamu zauna ba tare da kowa ya sani ba?
"nafa gaji da ganinki wurinnan malama, babu abinda ke tsakanina dake, ki ɓacemun da gani"
Kamar ta maida mishi da bak'a, ta tuna idan tayi hakan faɗa ne zasu ci gaba, ta taɓe baki kawai ta shige ɗakinta, cikin ɗokin ta kira ibraheem ta faɗa mar.
Kiranshi ta dinga yi anma tak'i shiga har ranta ya soma ɓaci don yanda ta k'agara ta faɗa mishi tasan sai yaa fita murna, cikin haka sai ga kiran hafsatul kiram babbar Aminiyarta kenan.
"Ran Amarya ya daɗe tare dana angonta"
"wacece Amarya? Yanzu duk k'wak'warki dai bazaki kirani da wannan sunan ba" inji majeeda.
Bayan hafsatul kiram tayi dariya tace "Tohh ina angon naki? Na kasa hak'ura ne na kira ki, duk da nasan kunanan tare yana jinya" ta faɗa cikin tsokana don tasan zata k'ular da majeeda.
"banson iskanci fa hafsa, ina auren yake da har zai samu zuwa kusa dani ma?"
"saman kanki mana, da aka ɗaura miki jiya".
"tohh wallahi na saukeshi yanzunnan, karma ki ɓatan rai ina cikin farin ciki?"
"kamarya majeeda?" ta faɗa da mamaki"
Da yake majeeda ta yarda da hafsatul kiram sosai, kuma tasan duk rintsi bazata taɓa faɗama wani sirrinta ba, kuma tana cikin son ta faɗa ma wani, nan take ta kwashe komai ta faɗa mata.
Shiru tayi kamar wacce tayi suman zaune sai da majeeda tace "ko kin kashe wayar ne?"
"kin kashemin bakin magana dai? Yanzu auren naku kuka kashe a washe garin amarcinki? Kuma zaku zauna a gida ɗaya? Haba majeeda kamar dai....."
"kinga rik'e mamakinki da duk maganganunki, da kuma sirrina, kinsan don na yarda dake ne na faɗa miki ko? Babu wani abin dana sanin insha Allah"
"Allah ya yarda, anma duk kin sakemin jiki"
"tohh a warware lafiya, ki gaishe da Ya umar" bata jira me zata ce ba ta kashe wayar.
Layin ibraheem taci gaba da neman, sai sintiri take a tsakar ɗakinta, can taji taa fara ringing, ta samu kujera ta zauna tana jiran ya ɗaga anma har ta katse shiru.
Sai da ta mishi kira biyu ana ukun ne ya ɗaga da alama barci ya tashi.
"na kwanta barci da tunaninki, banyi mafarkin komai ba bayanki, gashi na farka da zazzak'ar muryarki, plz in fara jin sautin lallausan murmushin masoyiyah ta" sai da ta mishi murmushin sabo da yanda kalamanshi suka mata daɗi tace, "ba murmushi na kaɗai zaka farka dashi ba, harda Albishir ɗin da zaiyi maka daɗi sosai"
"faɗamin da sauri masoyiyah, tunda kafin ki faɗa ga tukuicinki" ya sakar mata daddaɗan kiss a kunne
Ta rufe ido ta buɗe cikin nishaɗi, "Yaimin daɗi sosae masoyi, karfa ka sakani mantawa da albishir ɗin"
"sai in k'ara miki wanda zai saka ki tuna"
"banma manta bafa, anma duk da haka naa biyoka bashi, yanzu miye yayi mana katanga da zama mallakin juna?"
"Auren ki da majeed mana" inji ibraheem
"tohh k'ara kwantar da hankalinka, don indai aurena ne yanzu....."
Maganar ta mak'ale mata saboda ganinshi tsaye a k'ofar falonta, yana wurgo mata wani mugun kallo
Shirun da Ibraheem yaji tayi ya saka ya dinga "hello, masoyiyah, kina jina?"
"ina jinka masoyi zan kiraka yanzu," sannan ta katse kiran tana k'ok'arin dai dai ta nutsuwarta.
Ta kalli majeed tana mayar mishi da irin kallon da yake mata "Meya shigo dakai ɓangarena? Ka mantane sharaɗinmu na babu wanda zai shiga harkar wani? Kuma bazaka zo inda nake ba"
"ke har kina da bakin magana? Baki manta da sharaɗinmu ba meyasa kike k'ok'arin faɗa mishi sirrinmu?"
"ni ban faɗa mishi ba ko kaaji naa faɗa?"
"kina shirin faɗa dai, wannan ba k'aramar magana bace da idan kin faɗa ma wani yaɗuwarta bazai kawo matsala ba, har yaushe kike tare da Ibraheem da kika yarda dashi har zaki faɗa mishi wannan sirrin namu? Ke kin kasa rik'e sirrinki ta yaya kike tunanin wani zai rik'e miki? Wallahi karki kuskura ki faɗa ma wani wannan maganar"
Jikinta yaa riga da yaayi sanyi, taama kasa maida mishi, ya juya ya bar ɗakin, taja tsoki "daman gulmace da sa ido ya shigo dakai kenan" ta harari k'ofan tana murguɗa baki kamar yana ganinta, sannan ta tashi ta shige ɗakinta.
Yinin ranar bak'i ta dingayi masu zuwa ganin gidan Amarya, kowah yazo sai ya zagaya gidan ana lellek'a ɗakunanta, ba k'aramin haɗuwa da tsaruwa gidan yayi ba, ga dukiyar da iyayenta suka zuba mata a ciki.
Ba ita ta zauna ba sai 9 na dare bak'inta suka gama tafiya, duk taa gaji ga yunwa bata samu taa girka komai ba, baba haule dai taa koma gida,
Kwanciyah tayi ta jawo wayarta miss calls ɗin Ibraheem ne babu iyaka, itama ta kirashi bai ɗaga ba, ga yunwar dake yatsina mata y'an hanji, mik'ewa tayi kawai ta nufi kitchen ta ɗaura girki, da yake an haɗa mata komi.
Fried cous-cous ta dafa dai-dai cikinta, sai k'amshi ne ke tashi, tananan tsaye harya gama dahuwa ta sauke ta jawo plate zata zuba kenan ta juyo wayarta na ringing a ɗaki, ta ajiye da sauri ta tafi ta ɗauka wayar.
Ibraheem ne, ta zauna gefen gado sannan da ɗaga kiran.
"Da fatan ma'abociyar kyakkyawan murmushin nan tana cikin nishaɗi"
"sosai tunda ina tare da muryan masoyinah"
"kawai ɗazun ina cikin ɗokin jin albishir daga gareki, saiki yankemin waya, halan angonki ne ya kiraki?"
"shiya shigo dai, anma ai bai isa don ina waya dakai in katse saboda shi ba"
"Hmm, kin manta da mijinki ne? Kina kulawa dai don baniso muna shiga hak'k'ik aure da yawa" sai can ya tuna kuma.
"Yauwah aurenki yanzu ma... me kike cewa?" sai da ta ɗan daburce duk taa rasa me zata ce sannan tace "yanzu ne yake k'ara damuna masoyi, anya bazamu gudu muyi aurenmu?"
"Aure akan aure kenan? Nifa banda matsala da iyayena Masoyiyah jiran fitowarki kawai nake, basai mun gudu ba kinji tawan"
"tohh" kawai tace mishi a zuciyarta tunani take anya bazata faɗa mishi ba? Kuma sai taji tsoran kashedin da Majeed yayi mata haka kawai ta fasa faɗa mishi.
Majeed yana ɗaki shima babu inda yaje, sallah ce kawai take fiddashi, sai juyi yake akan gadonshi saboda yunwar da yakeji tunda rana, daya juya sai yayi tsaki "Yanzu mutum ya tafi restaurant yana haɗuwa da idon sani akama yi mishi surutun ya fara fita cin abinci"
Gani yayi zaman bazai mishi ba, ya tafi kitchen ya duba ko zai samu abinci.
Cikin sa'a kuwa ya hango tukunya saman cooker gas, ita ya fara buɗawa, abinci ya gani kuwa da zafinshi k'amshi sai tashi yake, ya jawo plate ɗin daya gani a wurin ya juyeshi tass sannan ya fito falo ya zauna ya fara ci.
Sai da ta gama wayanta da ibraheem daman yunwa duk taa addabeta, ta fito ta wuce shi a falo ta nufi kitchen ko kallon inda yake batai ba, shima ko sanin taa wuce baiyi ba.
Ta duba inda ta ajiye plate babu, kodai bata ɗauko ba? Ta janyo wani plate ɗin dai ta taho zuba abinci, tana buɗa tukunya wayam babu komi, fiddo idanu tayi waje cikin mamaki ta ɗauka tukunyar tana girgizawa kodai bata gani dai dai bane, anma wayam babu komai.
Toh waye zai shigo har gidanta ya kwashe mata girki? Kodai aljanu ne, can ta tuna fa ay ba ita kaɗai bane a cikin gidan, toh shi kuma mezai dameshi da girkinta? Tunani dai ta dinga yi taga bazai mata ba, ta fito daga kitchen ɗin can ta hango shi ya saka plate a gaba yana kwasar girki.
Cikin jin haushi tace, "Anma dai in ba'a kawoni da ɗaki a gara ba an kawo ni da cous-cous ko?"
Baiko ɗago ya kalleta ba Yace "Anma a gidana kike zaune, indai zaki zaunamin a ɗaki, dole ne kimin girki, bayan wannan babu wani abu" ba tace mishi komi ba ta koma kitchen ɗin don yanzu batason magana tayi nisa tsakaninsu yanzu zasu fara faɗa.
Bayan wata biyu...
Majeeda ce sanye cikin doguwar rigar material, ta ɗaure kanta da ɗan kwalin, ta jawo Abayarta har k'asa ta saka, sannan ta ɗaura nik'ab a fuskarta, ta janyo hand bag ɗinta sannan ta fito waje. Driver nanan yana jiranta, ta buɗe sit ɗin baya ta zauna yaja motan sai ALQALAM UNIVERSITY dake cikin garin katsina.
Kullum shigarta kenan tunda ta fara shiga makarantar, kamar wata matar aure shiya saka har yanzu batayi koda k'awa babu ruwanta da kowah.
Sai marece sosae ta koma gidan, bata lura da motanshi ba ta saka kanta cikin falon, maganganu ta fara jiyowa.
"haba Aisha, ba nace karki zomin gida ba? Karki manta fa akwai banbanci tsakanin gidanmu da gidana".
"akwai banbanci, anma kasan ko inane zan iya zuwa don in ganka, tunda kai ba son zuwa gidanmu kake ba"
"naji, anma kincemin inzo banzo ba? Ki k'ara hak'uri mana lokaci kaɗan ya rage a fara maganar aurenmu"
"kullum haka kake cewa, ni dai tunda nazo ka bari ko gaisawa muyi"
Wani abu ne ya tsaya ma majeeda har wuya, kamar ta kama majeeda ta shak'e takeji, a ciki-ciki tayi sallama ta shiga ɗakin duk suka juyo suna kallonta, ta k'urama majeed ido kawai, taa daɗe bata ganshi ba, don tunda ya fara zuwa aiki ya daina zaman gida, girki ma idan taayi a kitchen take bar mishi.
taa rigashi ɗauke idanunta, ba tare da tace komi ba ta shige ɗakinta.
Ibraheem ya faɗo mata a rai, yanzu yaa daina kiranta, ko kiranshi tayi sai yaga daman ɗagawa, koya ɗaukama bazasu wani daɗe ba zai kashe wayan, shiyasa itama ta daina damunshi, yanzu hankalinta akan karatun kawai ta maidashi.
Cikin ɗakinta haushin Aisha ne kawai ya cika mata ciki, daganan tana jiyo maganganunsu tak'i tashi ta tafi duk da maganar da majeed ke mata, tashi tayi ta tafi falon bayan ta cire hijabin jikinta, ta gyara ɗaurin kwallabin sannan ta fito.
Shiru suka k'arayi suna kallonta, ita kam kamar ma batasan dasu ba, ta k'arasa gaban kallo ta kunna, ta rik'o remote ɗin ta zauna kallo.
K'asa-k'asa Aisha taci gaba da mishi magana duk hankalinshi na kan majeeda, ta k'ure k'arar ma yanda bazasu ji ba, duk a takure yake anma Aisha taa kasa ganewa, kawai ya juya zai tafi ɗakinshi itama ta mik'e zata bishi.
Majeeda ce tasha gabanta,
"kinfa fara wuce iyaka malama, don tsabar rashin kunya ki biyo mijina har gidana, kinga ban tanka ba shine zaki bishi har ɗaki, ubanme zaki yo a ciki?"
"Akan mijin da bai damu dake ba baya sonki kike tada jijiyoyin wuya? Abinda ranki ya baki shi zamu yo"
"k'arya kike wallahi ki shigo har gidana kina faɗamin magana, banza mai k'wak'war namiji har gidanshi, ai naga mugun son da yake miki ne ya saka sai dai ke ki biyoshi"
"laaah, ni kike faɗa ma magana? Kana jinta fa majeed"
Duk suka maida kallonsu ga majeed ɗin, "Da bakizo gidanta ba taa faɗa miki? Kinga muje in maida ke gida"
Majeeda tsayawa tayi tana kallonsu har suka fice, lallaima yaa fifita wannan banzar a kaina kenan, har saida ta jiyo ta mata gwalo, haushi kamar ta fasa ihu.
Lallai don yaga yanzu babu aurenshi a kaina ne harda shigomin da wata a gida, wallahi bazan yarda ba nima sai na rama.
Bai wani daɗe ba ya dawo, anan ya wuce ta inda ya barta, ya wuceta inda take tsaye yana tafiya da kakkausar murya cikin gargaɗi yace, "babu ruwanki da kowacece zatazo wurina, babu ruwan wani da harkar wani" ya wuceta sannan ya k'arasa maganar.
Kwana biyu tayi tana tunanin yanda zata rama abunda Majeed ya mata anma taa gaza samun mafita, gashi kullum sai ya raba dare kafin ya shigo gidan, tunda safe kuma yake fita, ita yaa maida ita er gadin gida duk da baiyi mata shamaki da fita ba.
Yauma da marece sosai ta dawo daga lecture, suna hanya drivern ta ya ɗaukota, da yake hanyar gidansu majeed ne, hakanan taji tanaso taje gaishe dasu, ta cema drivern ya biya da ita.
Ya ajjeta ta fito har zata tafi kuma ta dawo "malam balah zaka iya tafiya, zan ɗan daɗe ne" yace, "tohh hajia" sannan ta shiga gidan da sallamarta.
Zahra taci karo da ita, aikam ta buga uban tsalle da gudu ta taho rungumeta "Oyoyo Matar Yayanmu"
"Aifa sis kamar a bakinki aka raɗa wannan suna, ina umma?"
"tana ciki ki shiga bari inzo"
"tohm naa bari".
Ta yaye labulen ɗakin Umma ta shiga haɗe da sallama, ta ɗago tana amsawa tana ganin Majeeda ce ta k'ara faɗaɗa fara'arta tana mata sannu da zuwa, sai yanzu ne ma wata kunya ta k'ara nannaɗeta, ta duk'a har k'asa tana gaida Umma ta amsa mata.
"Ina majeed ɗin ko ba tare kuke ba?"
"Daga makaranta ne yace Driver ya kawoni, anma zaizo ɗaukana Umma"
"Tohh Allah kawoshi lafiya, kuna dai zaune lafiya ko?"
"Alhmdlh Umma"
"ki faɗamin gaskia dai naaga duk kin rame" wai taa rame fa, tace a ranta, tana tuna randa taje gida momie cewa ta dinga yi taayi k'iba taayi haske, alamar dai tana mata zargin ciki ne da ita, da yake momie ce sai ta ce mata "momie ni kece uwah ta farko da akama ɗiyarta auren dole kuma tazo ganin gida a ce mata tayi k'iba" momie tace "watau ma auren dole aka miki ko? Kina nufin har yanzu baku zaman lafiya da mijin naki?" tace ma momie, "ba haka nake nufi ba momie".
Umma ce ta katse mata tunani "Yadai kikai shiru Majeeda? Indai da matsala ki faɗamun in tsawata mishi"
"ba wani matsala Umma, kawai kwana biyu banji daɗi bane" ta k'ak'alo k'arya.
"tohh Allah ya k'ara lafiya kundai je asibiti ko?"
"Ai naaji sauk'i Umma"
Zahra ce ta shigo ta janye ta suka koma can ɗakinta da fira, itama tsokanarta take kodai sun samu rabo,
"nikam sis kamar Abinda kowa ke jira kenan, duka yaushe aka gama hidimar bikin ko hutawa bamu yi ba?"
"Abinda kowa ke jira mana kenan, in hutawa ne kam ai kinyi, anma burinsu Abba kenan kullum ganin en jikokinsu" sai da gabanta ya faɗi, tayi shiru tama rasa abin cewa, tohh ta inama zata samu cikin tunda ba auren garesu ba?.
Haka ta yini cikin gidan duk tayi sukuku kuma, har bayan isha'i taa rasa yanda zata tafi kuma gashi tace ma Umma Majeed ne zaizo su tafi, yanke shawarah tayi kawai ta kira malam balah, shi ɗinma ta dinga kiranshi anma wayanshi a kashe.
Wurin 9 Umma ta lek'o ɗakin Zahra, "wai ina majeed ya tsayane?"
"Umma inajin dai wani abunne ya rik'eshi, anma zan tafi kawai kar dare yayi sosai"
"A'ah ya zaki tafi ke kaɗai? Ki mishi waya dai yayi sauri yazo ku tafi" ita kam ko number wayarshi ma bata da, yama za'ayi yazo ɗaukanta.
Har 10 tayi ta rasa dabarar da zatayi tabar gidan Umma, su duka suna zaune a falo, gabanta sai faɗuwa yake, tun farko ma meya sakata yin k'arya.
Sa'a tayi wayarta ta fara ringing, tayi saurin maida wayan silent sannan tayi kamar taa ɗauka sannan ta ɗan matsa daga inda su Umma suke ta fara magana yanda zasuji.
"hi, lafiya lau ya aiki?" ta ɗanyi shiru sannan tace, "A'ah ya za'ai na tafi kace na jiraka?"
"Ayyah! Tohh a dawo lafia, sai ka dawo gidan" tun kafin ta zauna Zahra tace "Halan ina ya tsaya?"
"wai kinji fa gaisuwar wani baban ɗan wurin aikinsu sukaje Mashi, anma suna hanya kuma motan a cike take, yace inje a napep" Umma tace, "Ayyah!Allah yaji k'an musulmi, sai kiyi sauri dare na k'arayi, tace "tohh shknan Umma"
Zahra ce ta rakata har bakin titi, sun daɗe suna tsaida abin hawa duk da mutane a ciki gashi batason hawan mashin, dak'yar suka samu wani mai napep ta shiga sukayi bankwana da zahra.
Har ya tada zai tafi Yace "hajia ina za'a kaiki?" tace, "G.R.A"
"kiyi hak'uri hajia bazanje can yanzu ba ina ɗan sauri ne" babu yanda ta iya ta fito daga motan gashi dare ya fara nisa 10:3., ta juya ko burbuɗin Zahra babu, ga unguwar babu mutane.
Tsayuwar ta fara gajia da ita ta ciro wayarta tana dubawa, ba don tana da abunyi da ita ba, sai don kawai ta rasa abinyi gashi har lokacin ba wani motan da zata hau.
Wata haɗaɗɗiyar mota ce ja, mai shegen kyau ta wuce inda take, sai kuma akayi reverse da motar aka dawo saitin da take, kaudar da kanta tayi sannan ta matsa gefe. Kusan mintina biyar mai motan bai fito ba kuma shi bai tafi ba ita kamar ma batasan da wani mota a wurinba.
Buɗe motan yayi ya fito da takunshi na k'asaita, "Masha Allah" na faɗa saboda irin kyaun dana hango a tattare dashi, harna kusan jefar da wayata kasancewar darene ina tunanin ko Aljani ne, dai dai inda Majeeda take ya tsaya.
"Da alama kina jiran Abin hawa, gashi kuma dare ya fara nisa zai miki wahalan samu" kajimin mutum ko ina ruwanshi dani
"hakane zan samu insha Allah"
"Zai miki wahalan samu fa, kiyi shawara da zuciyarki idan harta amince miki zan kaiki har inda kikeso, babu daɗi kamilalliyar mace kamarki ta tsaya a titi a cikin darennan"
Maganarshi fa hakane, idanma ya tafi ya zata samu wanda zai kaita gida? Kuma da alamar natsuwa a tattare dashi ta san bazai cutar da ita ba, gaba tayi wurin motar kawai ba tace komi ba, ya buɗe mata yaci gaba da karanto addu'ah a ranta.
Har k'ofar gidanta ya kaita "ajjeni nanma yayi" yayi parking ta fito tana mishi godia, murmushi kawai yayi yaja motanshi, dai dai lokacin majeed shima ya sako motanshi kuma yaga lokacinda ta fita daga motan.
Kamar wanda ake hankaɗawa ya shiga gidan tana dai-dai shiga ɗakinta yasha gabanta,
"daga gidan ubanwa kike?" na ɗauka "gidan ubanka zatace"😄 tunda gidansu taje,anma sai tace "gaishe dasu Umma mana, kana da matsala da fitata ne?"
"k'arya kike tun ɗazu Umma tacemun kin taho, wane ɗan iskane ya maidoki?"
"kash!" ta dafe kanta da hannu ɗaya "kaga nama mnta ban tambaya sunanshi ba, ragemin hanya yayi, babu ruwan wani da harkar wani" shiru yayi yana kallonta yama rasa bakin magana, tohh meyasa ma ya tanka mata? Shi ina ruwanshi kowa ma zata kula.
Ta juya ta barshi anan zata shige ɗakinta, k'afarta ta zamo bata ankara ba ta taho zata faɗo da sauri ya tare ta ta faɗa a k'irjinshi ta tallabeta da hannuwanshi, kallonshi take cikin fargaba saboda yanda ta kusa faɗuwa, sai maida numfashi take, shima kallonta yake cikin ido, wani irin yanayi da bai taɓaji ba ya ziyarceshi wannan kallon da suke ma juna.
K'ara matseta yayi a k'irjinshi, tsawon lokaci suna a haka kafinta lumshe kyawawan idanunta ta buɗe, idonshi dai-dai laɓɓanta ta buɗesu a hankali tace "da zafi" yanda ya mata rik'on, sakinta yayi yana dai-daita kanshi, sannan ya juya ya tafi yana waiwayenta, itama kasa motsawa tayi daga inda take ta k'ura mishi ido cikin wani yanayi harya shige ɗakinshi.
Jiki a sanyaye ta shige ɗakinta, ta kasa mantawa da yanayin data motsa fuskar majeed ce ke mata yawo a sanda take a k'irjinshi.
Haka Majeed ma ya kwanta barci da tunanin abinda ya faru, daya rufe idonshi yanayin yake dawo mishi, koda ya buɗe kuwa bazai daina ganinshi da majeeda rungume ba, juyi kawai ya dingayi a lallausar katifarshi yana jiran lokacin da barci zai ɗaukeshi.
Hmm niko nace kome hakan ke nufi??
Da Asuba, ciwon mara ne ya farkar da ita, tun cikin barci ta fara juye-juye harta farka, ta dafe cikinta ko motsi batason yi, tanason ta ɗauko maganinta anma ta kasa tashi saboda yanda ya matsa mata.
Dak'yar ta samu ta mik'e ta jawo jikkarta ta fara laluben maganin sai dai kwalinshi babu ko ɗaya, kamar ta fasa kuka ga wani irin azababben ciwo, haka tana duk'ewa ta samu ta haɗa ruwan zafi a toilet taje tayi wanka anma duk da haka kamar ana k'ara tunzuro ciwon cikin gashi ita kaɗai a ɗaki.
Dak'yar ta iya k'arfin halin kwaso kuɗi a jikkarta ta fito mai gadi ya siyo mata, da yake a ɗan duk'e take tafiya rik'e da cikinta ga azabar ciwo, bata lura dashi yana shigowa falon ba ita kuma zata fita harta kusan kai mishi karo, da sauri ta dawo da baya, kanta a k'asa tabi gefenshi zata wuce, shima gefen da zata wuce yabi suka kusan haɗewa a tare, kuma kowannw ya koma ɗayan gefen, da suka kasa wucewa dai ya saka hannuwanshi biyu saman kafaɗarta, sannan ya juyar da ita ya wuce.
Wani irin murɗawa cikinta yayi anan ta duk'e-duk'e rik'e da cikinta, ta daɗe a haka kafinta iya mik'ewa tana ɗagowa suka haɗa ido da majeed, duk ta daburce tace, "yadai?" yaɗan saki fuskarshi "ba komi", sannan ta juya ta wuce a wahalce.
Bata iske mai gadi ba, da alama bai gidan gashi duk taa gama jigata, haka ta lallaɓa ta koma ɗakinta, tana faɗawa gado ta saki kukanta marar sauti ga ciwon sai k'aruwa yake, ta dinga murgina saman gado harta sauko k'asa.
"Ga maganin" taji ya ambata, ta ɗaga fuskarta tana kallonshi rik'e da laida a hannu, ya ajje robar faro da cup a kusa da ita, ta mik'a hannu ta ansa maganin, irin wanda takesha ne da pad guda biyu, ta ɓallo guda ɗaya ya mik'a mata cup ɗin ruwa ta haɗiye dak'yar sannan tace "na gode" ta koma ta sulale k'asa tana jiran ciwon ya lafa, a haka barci ya kwasheta duk taa k'udundune wuri ɗaya.
Tausayi ta bashi ganin yanda tayi kwanciyar duk taa takura, lokaci ɗaya har taayi ramar dole, sai lokacin ya tuna ko break fast batayi ba ya bata magani, da sauri ya tafi kitchen ya ɗauko flask da kayan tea ya ajje mata.
Tananan kwance inda ya barta tana barci, anma da alama batajin daɗin barcin ciwon cikin ma bai gama sakinta ba sai rumtse ido take tana rik'e ciki.
Bazai juri ganinta a k'asa ba, ya saka hannu ya tallabota, kamar yaa ɗauka jaririya, ya dire ta saman gado, tun lokacin da yaa ɗaukota ta farka, anma ta kasa buɗa idonta wani irin kunyarshi maa takeji.
Megasa Yaya majeed zaina taɓani koya manta yanzu babu aure tsakaninmu? tunaninta ya katse saboda yanda mararta ta k'ara juyewa, tai wani irin k'ara batasan lokacin data k'ank'ame hannunshi da hannu ɗaya ba, ɗayan hannunta na rik'e a cikinta har lokacin da yake yana tsugune saitinta.
Wani irin tausayi take bashi ganin yanda takeyi, fuskarshi kamar zai tayata kukan, ya kalli hannunta dake sak'ale a nashi, zara-zaran yatsunta masu kyau sosai da taima ado da jan lalle, baisan sanda yaci gaba da murzasu a hankali ba yana kallon kyakkyawar fuskarta, sai runtse ido take, ga ciwon ciki, ga wani irin yanayin da takeji hannunta rik'e a hannun majeed.
Kallonta yaci gaba dayi, sai yanzu ne yake k'are mata kallo, ya saka hannu ya yaye mata yalwataccen gashin kanta mai sulɓi daya rufe mata fuska, fara ce tas, irin farinnan mai kyau, gashin girarta gazar-gazar mai kyau kamar an zana mata shi, gata da manyan idanu masu kyau da ɗaukar hankali, girar idonta bak'a wulik koda a rufe suke idanunta k'ara kyau suke, da dogon hancin ta wanda ya dace da kyakkyawar fuskarta, idanunshi ne suka sauka a kan ɗan 'karamin bakinta (pink lips), ya tuna yanda take motsashi idan tana mishi masifa, sai yaji ta burgeshi ma idan suna faɗa kyau yake mata.
Yanzunma motsashi ta dingashi kamar zata tashi, dimples ɗinta na lotsawa, a hankali yakai ɗayan hannunshi zai shafi gefen fuskarta, kamar ance ta buɗa ido, ya sauka cikin nashi da sauri ya mayar da hannun
