HARAMTACCEN AURE PART 1
Kwance take a tsakiyar gado, tasha lullub'i da shiga ta alfarma, k'amshi ne yake tashi ta ko ina a jikinta, an mata irin lullu'bin da ake ma Amare danginta sai shirye-shiryen tafiya suke.
A cikin mayafin nata, wayar tace ri'ke a hannunta tana kan chatn sai murmushi take cikin farin ciki abinta.
Ibraheem ne Yace "Amarya kinsha 'kamshi.
Sai da tayi fari da ido sannan ta fara typin
Majeeda "Haba dear banson haka fa ko ina amsa sunana Amarya ai sai randa na ganni a gidanka"
Yace "hakane fa tawan, shiyasa ba wani kishi nake da wannan auren naki ba"
Majeeda "Ay 'kara ka kwantar da hankalinka kam, don wannan auren nawa dashi da babu duk ɗaya"
Yace "kedai ki kulamin da abinda nake matu'kar so, karki bari ya 'kwacemin a darennan plz"
A zuciyarta kamar ya soka mata wu'ka takeji, anma a zahiri sai tace "menene zan kula maka da?" cikin zolaya tayi maganar hakan ya sanya har sai da tayi dariya a zahiri.
Duk 'yan ɗakin saida suka jita hakan ya sanya wata Abokiyar wasanta tace "ikon Allah! Ni majeeda na tab'a ganin amarya irinki, ranar aurenki anma baki damu ba ko kukannan bazakiyi ba?" wata tace "kema kin faɗa, nima tun d'azu nake gulmarta a zuciyatah, ban ta'ba ganin Amaryar da batayi kuka ba ranar aurenta koda babu hawaye"
"Haba Aunty zaynabu, aure ai abin farin ciki ne ga masoya, ko wanda kika ga suna kukan don rabuwa da iyayensu ne"
Cikin lullub'in nata sai data gatsina sannan tace a ranta "Allah ya tsareni da zama Masoyiya da majeed, wlhy ko kad'an aurennan bai dameni ba tunda ba sonshi nake ba".
Saida kowa ya gama mata bankwana ya tafi, sannan ta yaye mahafin da aka mata lullu'bi dashi daman duk yaa dameta, hafsatul kiram ta zato ido tana kallonta "wai majeeda badai da gaske bakiyi kukan amarcin ba?" tace "ke banson iskanci uwar meye a cikin kukan amarcin? Aishi wlhy bai isa inyi kuka saboda aurenshi ba tunda ya yarda aka aura mishi ni".
Tace "Allah ya huci zuciyarki" majeeda tace "Ameen" tana gyara kwanciya "sai yaushe zaki tafi?" hafsa tace "Yanzu fa don naga ma shirin korata kike" yanayin da tayi maganar ya bama majeeda daria tace "wace ni da korar Hafsatul kiram? Idan ma anan zaki kwana wlhy muyi kwanciyarmu anan"
Hafsat ta ri'ke baki "kinga rufamin asiri, Ya umar har ya iso sai waya yakemin" majeeda tace "yayi masoyan asali" ta rataya jikkarta tace "Tohm Asubah ta gari majeedar majeed" harara takai mata, don ta tsani a haɗa sunanta dana majeed, ko bankwanarta ma bata amsa ba.
Ta duba online har ibraheem ya sauka, ta kashe wayan kawai ta murgina ta kwanta idonta cike da barci ga gajia.
Sai da barci mai daɗi ya fara ɗibanta, kamar daga sama taji an jefo mata wani abu samanta, a firgice ta farka haɗe da tashi zaune tana shirin kurma ihu tayi ido huɗu dashi.
Cikin masifa ta sauko daga kan gadon "Miye haka majeed zaka wani jefo min Abu ina cikin barci na?" galala yake mata kallo sannan Yace "ke kin d'auka barci ne ya kawo ki gidannan?" sannan ya girgiza kai yana ta'be baki "tohh kima ajiye wallahi tunda kika yarda kika aureni, kazar amarci ce aka bani in kawo miki don nasan da kwa'danta kika kwanta".
"Allah ya kiyayemin, ba ro'karka nayi ba don haka ka kwasheta ka ficemin daga ɗaki, kuma wallahi ka sani kaine kayi kuskuren aurena"
"ke kin isa in shigo da ita kuma in fita da ita? A cikin garar ne aka haɗo miki da ɗaƙinnan da zakice in fice miki daga ɗaki?
"oho dai, kaima kasan nafi 'karfin ɗakinnan ai da duk wani abu daka mallaka"
Bai tanka mata ba ya juya zai fita, ta 'kwala mishi kira "kazo ka ficemin da ledar nan nace" bai ko juyo ba wani haushin ya 'kara zo mata iya wuya, daman abinda tafi tsana kenan a halayyar Abdul majeed koda suna gida, jin kai da miskilanci
A k'yamace ta saka hannu ta ɗan ɗauki ledar kamar wacce ta ri'ke abin k'yama, ta wuceshi ta riga shi fita ta tillar da laidar.
A zafafe ya juyo cikin jin haushi yana kallonta, itama kallonshi take ko ɗar babu a fuskarta tana maida numfashi.
Baiyi wata-wata ba ya nufi inda take ya ɗaga hannu ya kai mata wani wawan mari, cikin zafin nama ta kauce har tanajin hucinshi.
Ta ɗago fuskarta tana kallonshi cikin mamaki da takaici "Yanzu Yaya majeed nice zaka ɗaga hannunka ka mara? Wlhy da kayi kuskuren da zaka daɗe kana dana saninshi" Yace "kuskuren me zanyi?" yana matsowa inda take "ke kin isa inyi dana sani don na mareki? Sai in dakeki na daki banza?" tace "mu daki juna dai, don na rantse banyi kama da macen da zata tsaya namiji ya dake ta ba" kafin ta rufe baki kau ya kai mata mari har saida ta du'ke, ta kai hannu tana taɓa kuncinta da take tunanin ko yaa zurma ciki.
Sosai taji marin da'kyar ta iya daurewa ta ɗago, bata tsaya wani tunani ba itama ta ɗaukeshi da zazzafan mari, shima yayi tangal tangal zai faɗi, sannan ya ɗago kallonta kawai yake yama rasa da bakin da zai mata magana.
Itama tsayawa tayi tana kallonshi sai huci take cikin shirin duk yanda ta kama, har lokacin dafe take da gefen fuskarta yana mata raɗaɗin zafi, baice mata komi ba kamar yanda ta zata, sai dai ya fara dube-dube can ya hango incense burning ɗinta, ya janyoshi ya fuzge wayarshi ya nufo ta gadan-gadan.
Batasan sanda ta runtuma waje da gudu ba, tana waige-waige can cikin sa'a itama ta hango wayar chargern 'yan kawo Amarya ta ciro ta tsaya tana jiran isowarshi, kamar wani zaki ya tafo ya ɗaga wayar wuta itama ta ɗaga ya murɗe hannunta sannan ya tsula mata, ta ri'ke wurin ta fara murzawa.
Ya ɗaga ya 'kara zuba mata wata a tsakiyar baya, taji zafinta sosae ta saki ihu, baba haule mai aikinda aka kawo musu ta jiyo da gudu ta fito inda suke tana sallallami.
Ganin majeed ya juya wurin baba haule ya saka majeeda ɗaga tata wayar ta zabga mishi, ya juya yana kallonta idonshi jajir da ɓacin rai baba haule tace "miye haka majeeda shi ga bari ke bazaki bari ba?" tace "ai wallahi baba haule bazai shani a banza ba biyu fa yaimun".
Tace "yau naga abinda ya girmi kakannina ni haulatu tunda nake, wlhy ko a labari ban taɓajin amarya da angon dake faɗa ba ranar aurensu"
Yace "Allah ya sauwa'kemun da amarya da wannan baba haule kima daina faɗa"
"haba yarannan, aurennan fa an riga da an ɗaura, ku sanya ma zuciyoyinku ruwan sanyi mana"
Majeeda tace "Ai wallahi badai a aurena da majeed ba, ai nasha faɗa bani sonshi ya nace sai da aka aura mishi"
Ya taso mata cikin faɗa "toh uban waye yace yana sonki? Ke kinsan na wuce da aurenki wallahi" tace "oho dai kuma saina rama ɗayan bulala na don komai zakai dai-dai nake dakai," tana kaiwa nan ba shiri ta tsula mishi bulala.
Ko gezau baiyi ba, saima ya sha'kota fuskarshi tattare da ɓacin rai tana ta kiciniyar k'wacewa anma ya ri'kota gam, ta fara kai mishi bugu yana kaucewa yana 'ko'karin ri'ke hannuwanta.
Wata sabuwar rigimar ce ta 'kara kaurewa, da baba haule taga bazata iya rabawa ba ta fita da gudu tana 'kwala ma mai gadinsu kira.
Shima hayaniyarsu taa hanashi barci ya taso da sauri yabi bayan baba haule suka shiga gidan shima mamaki fal cikin zuciyarshi, da'kyar suka 'kwace majeeda a hannun majeed, baba haule ta shige ɗaki da ita har lokacin bakinsu baiyi shiru ba suna aika ma juna ba'kaken maganganu.
Shima ta lallab'ashi ya tafi ɗakinshi, sai huci yake irinna sadaukan mazannan.
Kowanne da ɓacin rai tare dajin haushin ɗan uwanshi ya kwanta, don barci yana ɓarawo ne kawai ya sacesu, anma kowanne zuciyarshi kamar zata fasa 'kirji ta fito
Washe gari tunda safe baba haule tana gama haɗa musu break fast ko tsayawa karyawa batayi ba ta fita ta tari napep sai gidansu Abdul majeed.
Har lokacin 'yan biki basu gama tafiya ba anata hada-hadar haɗa musu break, baba haule ta raɓa ta gaishe su sannan ta wuce ɗakin Umman Majeed.
Tana falon d'akinta tana waya cike da kwanciyar hankali da alama mai wayan tana tayata murnar bikinne, sai data gama wayar cikin fara'a suka gaisa da baba laure.
Umma tace "Anma dai baba haule lafiya da sassafennan" kanta a 'kasa tace "Rashinta ne ya tado dani tunda sassafennan, don jiya bamu yi barci da kwanciyar hankali ba" Umma ta 'kara sassauta murya cikin tashin hankali tace "meya faru baba haule?" gyara zama tayi ta faɗa mata duk abinda ya faru.
Ran Umma ya ɓaci sosai ta fara faɗa "lallai yarannan anyi mararsa mutunci, mu zasu bama kunya? Ana tunanin in anyi auren zasu daina faɗa anma suyi biris da maganarmu! Bari inje in samu Alhaji in faɗa mishi"
Baba haule tace "tohh shikenan hajia ni daman gani nake tun wuri gara a raba auren nasu tunda basu so, kar wata rana a wayi gari sun kashe kawunansu ma"
Umma tace "su kashe kansu mana, ya fiye mana dai da ace su ba 'kananan yara ba sun sanyamu karya Alk'awari" baba haule tace "tohh Allah dai ya kyauta".
Koda Umma ta jema Abba da maganar shima faɗa ya dingayi, ya ciro wayarshi ya kira 'kanenshi mahaifin majeeda ya sanar mishi, shima faɗa ya dinga yi suka ce su haɗu gidan, bazasu yarda yara su maidasu k'ananan mutane ba harsu tada Alk'awarin mahaifinsu.
Majeeda ta fito daga wanka, tana shafa mai ta jiyo k'arar motoci, da sauri ta zura doguwar riga ta fito daga bangarenta jin kamar maganar mahaifanta.
Hangosu tayi kuwa kowannensu fuskarshi babu walwala, gabanta ya faɗi tabbas akwai matsala, a sanyaye ta fito daga ɗakinta kamar marar gaskia, ta samu wuri ta rakuɓe tana gaishesu.
Umma kawai ta amsa mata, sai ga majeed ya fito da shirin fita, shima saida gabanshi ya faɗi ganinsu su duka a falon, a sanyaye kamar ita shima ya koma gefe ya zauna 'kasa, shi baima samu kowa ya amsa mishi gaisuwan ba.
Shiru ɗakin yayi na 'yan mintuna sannan Abba Yace "sannunku kunji, sannunku da abinda kuka aikata" duk suka k'ara sunnar da kawunansu kamar mararsa gaskiya.
Abba Yace "Tohh wlhy ku buɗe kunnuwanku kuji, ku baki isa ku maidamu k'ananan yara ba, mune nan mu muka haifeku, Alk'awari muka ɗaukar ma mahaifinmu kuma akanku bazamu karyashi ba wallahi"
Daddyn majeeda Yace "in banda shirme da shiririta irin nasu ai idan ana shiga kabari a fito tohh za'a aurennan a kwance"
Abba Yace "bawai kunga daman muna ɗaga muku k'afa ba, tohh wallahi kuka kuskura kuka raba aurennan sai dai ku nemi wasu iyayen badai mu ba" duk suka ɗago a tare suna kallon Abba.
Daddy Yace "wallahi nima ba a gidana ba, kuma zan tsine miki ne duk ranar da kika k'ara faɗa da mijinki"
Umma tace "ita kaɗaice mai laifin? Baza'a ɗaurama ɗiyata laifi ba a barshi ga k'wareta, nima kau ina shirin tsine mishi duk ranar daya k'ara dukanta"
Gaba ɗaya komi ya kwance musu, sauraren iyayensu kawai suke har suka gama faɗansu suka tafi babu mai wani kuzarin magana duk sun kasa motsawa daga inda suke, har iyayen nasu suka tafi.
Sunfi rabin awa babu wanda ya motsa daga inda yake, babu wanda ya cema kowa wani abu, duk wani kuzarin dake jikinsu ya saki.
A hankali majeed Yace "miye mafita? Nifa tsakanina da Allah bazan iya zama dake a matsayin mata ba" tace "nima haka wallahi, kuma indai zamu zauna a inuwa ɗaya sai munyi faɗa" yace "hakane ya zama dole musan abunyi" tace "tohh me zamuyi?"
Yace "mu rabu kawai kowa yayi sabgarshi, tunda kowa ɓangarenshi daban" ta zaro ido "idan fa suka gano?" yace "tohh waye zai faɗa musu? Kinga saima in samar miki admission kici gaba da makarantarki" tace "hakane tohh sakeni"
Ba wani tunani ko damuwa a fuskarshi Yace "na sakeki saki ɗaya" itama ba da wani abu a ranta ba tace "saki ɗaya ai ana komawa" kafin ta rufe "baki yace "na sakeki saki biyu" tace "ai wallahi saki biyunma ana komawa, ka cikashe kawai" Yace "na sakeki saki uku.
Nikam mamaki ne ya kamani da wannan ɗanyen hukunci da suka yanke a tsakaninsu, anya kuwa zaman nasu zai yiwu a haka?
Kafinnan waye Abdul majeed? Wacece majeeda? Menene tarihin auren nasu? Idan kuka biyoni a sannu zan warware muku
WANI LOKACI KAFIN AURANSU...
Alhaji Sani da Alhaji salisu, y'an uwane dake matu'kar son junansu da son zumunci, kaka Abdul hameed shine mahaifinsu mahaifiyarsu khadija taa rasu da daɗewa, shi kaɗai ya rage musu shiyasa suke matu'kar ji dashi.
Alhaji sani wanda suke kira da Abba, kuma mijin Umma, yana da yara biyu, Abdul majeed wanda aka saka ma sunan kaka, da kuma 'kanwarshi zahra.
Sai Alhaji saleesu shima Yara biyu ne dashi duk mata, Aunty zainabu wacce ta girme musu su duka, da Autah khadeeja (majeeda) itama sunan kakarta ne da shiyasa ake ce mata majeeda.
Tun haihuwar majeed, kaka yake matu'kar ji dashi saboda sunanshi da aka saka mishi ga yaron shiru-shiru da saurin shiga rai, babu ruwanshi da hayaniya sai dai baison raini, kusan kullum suna gidan kaka shida Aunty zainabu da ta girme mishi da shekara 3.
Aunty zainabu nada Shekara 10, majeed nada shekara 7, k'anwarshi fatima zahra tana da 2years, aka haifi majeeda, iyayensu sunyi matu'kar murna sosae, bama kamar da tun bayan haihuwar zainabu basu k'ara samun haihuwa ba sai akan majeeda.
Ranar sunah aka saka ma jaririya suna khadija, anma za'ana kiranta da majeeda, kaka yaji daɗi sosai kasancewar sunan matarshi ne aka saka mata, tun a ranar ya k'udurta wani abu a ranshi, tsakanin takwaranshi majeed, ta takwarar matarshi majeeda.
****
Aunty zainab ce ta fito da shirin fita, taci kwalliya da goyon majeeda a bayanta, ta samu momie zaune ɗakinta tana kallo.
Tace "momie zamu tafi" momie tace "tohm a dawo lafiya, a gaida kaka Alhaji" zainab tace "zaiji momie" sannan ta fito har driver ya fito da mota, ta shiga sannan ta kwance goyon majeeda ta rungumeta ya tada mota sai gidan kaka.
Tana shiga da sallamarta, Abdul majeed dake zaune kusa da kaka ya amsa mata yana "oyoyo Aunty zainab" kaka daya cika baki da dambun naman da ƴaƴanshi suka kawo mishi Yace "Allah yasa da matata kikazo mun zainabu" tace "ni baka ma son ganina kenan sai wannan tsohuwar matar taka?" kaka Yace "Ai kinsan dolene naji da deeje, kedai kwantota ki mik'omin itanan mu gaisa" ta mik'a mishi ita majeed duk ya haɗe rai.
Tana hannun kaka sai mutsilniya take irinna jarirai tana ture majeed ta k'afarta, haushi ya kamashi ya rik'o k'afafunnata ya ri'ke, kaka ya lura dashi tun haihuwar majeeda ba wani son ganinta yake kusa dashi ba .
"majeedar zaka ɗauka ne?" saurin girgiza kai yayi.
Kaka Yace "haba takwarah na, ina lura dakai fa tun haihuwar ɗiyarnan ba son zuwa kusa da ita kake ba"
Majeed ya k'ara ɓata rai Yace "Ay nifa babu ruwana da ita kaka, tun haihuwarta ka daina ji dani da taazo sai dai kayita ɗaukanta, ko gidansu mukaje da ummana sai tayita ɗaukanta"
Kaka Yace "kai bakaso ana ɗaukar matar taka ne?" da sauri yace "ni ba matata bace, bani sonta" shiru kaka yayi bai k'ara cewa komi ba.
Kiran sallahn da akayi ne ya saka zainab ta fita ɗauro Alwala, kaka ya mi'ka ma majeed ita yace "ri'keta tohm inyi sallah" kamar bazai amsheta ba, sai da kakanma ya kwantar mishi da ita sannan ya fita alwala.
Kaka na tsakar yin alwala, zainab na shirin shiga ɗakin suka jiyo majeeda ta k'wala wani uban kuka, da gudu zainab ta k'arasa shiga ɗakin ta iske bakin majeed dai-dai k'afarta ya gartsa mata ciwo da sauri ya ɗago.
Ta tsaya tana kallonshi "meka mata majeed?" ya fara kame-kame "wallahi Aunty zainab babu abinda na mata, ita keta kukanta tana halbina da k'afafunta" tace "tohh ka ɗauketa ka rarrasheta mana" badon yaso ba, ya ɗaga ta sama duk da ba wani k'warewa yayi da ɗaukan ba, aykam saitin bakinshi ta dalalo mishi tumbuɗi.
Baisan sanda ya saketa ba saida ta kusan faɗowa zainab ta ri'kota ya fita da gudu yana kakarin amai, sai da suka nutsu suka dinga mishi daria.
Haka rayuwar majeeda da majeed take tun suna k'anana, tun lokacin data fara tafiya data samo abun ɓarna saita nufeshi ta k'wala mishi, shima haka indai daga shi sai ita ne ya dinga mintsininta kenan, kwata-kwata basu zama wuri ɗaya.
Haka rayuwah taci gaba da tafiya, babu jituwa sam tsakanin majeed da majeeda, tana da shekara 6 ko wucewa zatayi sai majeed ya saka mata 'kafa taa faɗi, gata da masifa ita ma ta ɗago suyi tayi dak'yar iyayensu suke rabasu.
Cikin haka kaka ya kwanta ciwon ajali, ya tara 'ya'yan nashi duka ya fara musu wasiyya sannan yace "na sanku da zumunci, da kuma son zumunci, ku k'ara rik'e junanku ko bayan raina, a duk lokacin da naga khadija da Abdul majeed sai wani abu ya zomin a raina, ji nake kamar nine da mahaifiyarku, naso ina da rai inga ranar aurensu, anma kumin al'kawari ko bayan rai na zakuyi musu aure"
Alhaji Sani Yace "Insha Allahu kaka bazaka mutu bama sai kaga auren nasu"
Kaka Yace "inaa Sani, kai dai kawai ku rik'e alk'awari, don ciwonnan nawa jikina yana bani bana tashi bane, ko bayan raina ban yafe ma duk wanda ya saɓa wannan alk'awarin ba a cikinku, majeeda itace matar majeed" tare suka haɗa baki "Insha Allah baba"
Maganar daya faɗa k'arshe kenan, sai dai yayi kalmatus shahada, rai yayi halinsa.
Sunji mutuwar mahaifinsu sosai, sunyi kuka, tare da k'ara jaddada maganarshi ta k'arshe suna k'ara ɗaukarta da muhimmanci.
Sai dai wani Abu, majeeda da majeed suna girma suna k'ara rashin jituwa a tsakaninsu, tun suna ɗaukar abun nasu yarinta ce, har sunkai lokacin da majeeda ta gama secondry school, majeed ma ya gama makarantarshi har ya fara aiki, Aunty zainab kuma anyi mata aure da shekara ɗaya.
Yau gidansu majeed ta shirya ta tafi, zahra nata yi mata tsegumin bata son zumunci sai dai ita tazo, yau dai ta shirya driver ya tafi kaita.
Tayi sallama falon ta shiga, babu kowa, saita wuce ɗakin umma ta gaisheta sannan ta fito ta nufi ɗakin da zahra take.
Hangota tayi ta k'urama t.v kallo da alama a tsorace take, lallab'awa tayi har inda take ko sanin taa shigo ma batayi ba, sannan ta k'wala k'ara saitin kunnanta.
Aikam ta mik'e a firgece daman duk a tsorace take, ko tsayawa kallon majeeda batayi ba ta zunduma waje a guje tama rasa inda zata nufa, itama majeeda tabi bayanta da gudu tana mata dariya sai so take ta rik'ota, anma ina tama k'i tsayawa wuri ɗaya sai dai taji tayi karo da mutum.
Da sauri taja da baya zuciyarta cike da fargaba ta ɗago idonta taga ko waye, suka haɗa ido da majeed yana mata wani irin mugun kallo.
Ganin shine itama taja tsoki kawai ta nufi wurin zahra da tayi tsuru-tsuru tana kallon majeed, tace "muje matsoraciya, kinsan bazaki iya ba kika saka film ɗin horror ke kaɗai a ɗaki kina kalla"
Tace "Tohh yana iya tunda ina son kallo? Film ɗinne yayi kyau" har lokacin zahra satar kallon majeed take daya kasa motsawa daga inda yake har lokacin.
Ya daka musu wata uwar tsawa "baku da ido ne da zaku bugi mutum da wasan banzanku na k'ananan yara kuma bazaku bashi hak'uri ba?" zahra tace "kayi hak'uri yaya" tana zungurar majeeda itama ta bashi hak'uri.
Majeeda tace "hak'urin me kike bashi? Shine fa ya shigo ta hanyarmu" ta murguɗa baki sannan ta juya taci gaba da tafiyarta.
Yace "lallai ma yarinyar nan, yauma rashin kunyar zakimun?" waiwayen ɗakin ta kamayi sannan ta ɗago idonta itama ta watsa mishi wani irin kallo sannan tace "babu yarinya anan"
"idan nazo na murɗe wannan shegen masifaffen bakin naki kyamun bayani"
Tace "zan zauna ne kamar sakara ka murɗemin baki? Kaima kasan ba tsoranka nake ba wallahi".
Nan fa faɗa ya kaure, majeed ya kasa wucewa ɗakinshi saboda yanda majeeda ke gasa mishi maganganun, ranshi yayi matuk'ar ɓaci shiyasa yarinyar ko ganinta bai sonyi, masifaffiya ce kuma tayi matuk'ar rainashi.
A zafafe ya nufeta da niyyar kai mata mazga, dai-dai lokacin umma ta fito jin hayaniya, majeeda na tsaye inda take ko gezau ba tayi ba
Umma tace "Aaaaah, majeed mezan gani haka? Abin naku ya wuce faɗa a baki har duka zaka kai mata?" cikin jin zafi yace "Umma zan tsaya k'aramar yarinya kamar wannan ina faɗa tana faɗa ne? Ai wallahi sai ta gane ni ba sa'anta bane".
Tace "ai sai dai in baka faɗa ba wallahi, donni bazan tsaya kana nunamin iko ba"
Umma tace "tohh kuci gaba kunji ko? Tunda a gabana ma bazaku bari ba, kana babba anma bazaka daina shiga harkar k'annan ka ba, zo ka wuce ɗakinka" tana nuna ma majeed hanyar ɗakinshi.
Ya wuce yana aika ma majeeda da harara, itama harararshi take harya wuce ɓangarenshi, sannan taja hannun zahra suka wuce ɗakinta.
Sai dare Driver yazo ɗaukanta, Zahra ta rakota har wurin motar. Zata shiga kenan idonta ya hango mata Majeed babu nisa da inda take, shida wata yarinya da alama zance suke, aikam dariya ta fara harda rik'e ciki. Zahra ta fara dudduba jikinta tasan halin Majeeda da dariyan mugunta tace "wai meya baki dariya haka?" ta buɗa baki zata yi magana ta k'ara kwashewa da dariya. Zahra tace "wai miye haka?" ta soma k'ulewa, shima Majeed yana jiyota hankalinshi duk ya dawo kanta sai aika mata da harara yake ta cikin duhun, dak'yar tana rik'e cikinta tace "Abin da ya bani mamaki na gani, wai mace da zuwa wurin namiji zance".
Zahra ta sassauta murya tace "don Allah ki daina mana, kin san dai halin Yayanmu yanzu ya taso kuyi tayi, itama budurwarnan tashi ce da shegiyar k'wak'wa".
Tun kafin ta gama magana Majeeda tace "barni in faɗa wallahi, an daiji kunya mace da zuwa zance wurin namiji, ko meye ma abun so anan?"
Cikin faɗa ya taso inda take kamar zai shige mata, zahra harta ɓalla da gudu cikin gida, itama shigewarta tayi cikin mota da sauri kafin ya ida isowa tace ma Driver ya tada su tafi. Sannan ta lek'o da kanta da k'arfi tace "kayi kai kaɗai, da wannan marar aikinyin da take biyoka har gida, wlhy k'arama tun wuri ki canja masoyi wannan ba abinso bane" sannan suka wuce nan suka barshi yana cizon yatsa data gama gaggaya mishi maganganu kuma bai mata komi ba.
Har dare idan ta tuna ita kaɗai sai ta dinga daria, koda suna chatn da Ibraheem sai da Yace mata "wai ya na ganki yau kina cikin farin ciki?" Tace "Ay kullum ma cikin farin ciki nake da annashuwa indai ina tare dakai"
Yace "Hakane Masoyiyatah, anma da alama farin cikin naki na yau yaafi na kullum" tace "hakane fa, wlhy wani abune ya bani daria, anma dai bazaka tambayeni ko miye ba?"
"ko ban tambayeki ba nasan zaki faɗamin ba?😉
"hakane Masoyi, anma ka share kawai"
"na share Masoyiyah, bani labari"
"ba labari sai dai na zuciyatah"
"shi nafiso masoyiyah, bani labarin soyayyatah a cikin zuciyarki"
Anan suka bar maganar, suka ci gaba da firarsu kawai, anma idanta tuna abinda taima Majeed sai ta dinga dariya ita kaɗai, kafin shima ya tashi ramawa.
***
Sun gama fira da Ibraheem yayan k'awarta kuma saurayinta, fito ta rakashi har gaban mota suna fira kamar karsu rabu.
Daddy ne ya shigo ya kallesu Majeeda sai k'yalk'yala daria take, tana ganin haka tayi saurin shanye dariyarta ta dai-daita nutsuwarta, ibraheem ya fita har inda daddy yake ya duk'a ya gaisheshi, sama-sama ya amsa sannan ya wuce cikin gida.
A sanyaye Ibraheem ya koma wurin motarshi ya shiga, ta rik'e k'ofar motar duk taa marairaice fuska ganin canjawar yanayinshi.
Sai ga motar Majeed taa shigo gidan, ta ɗaga kai kawai sannan ta maida hankalinta wurin Ibraheem.
Zuwa yayi har inda suke sannan yayi parking motar ya fito, zai wuce Ibraheem ya mik'a mishi hannu suka gaisa sannan yayi gaba yana cewa...
"yau naaga nacin zance, saurayi na zaune saman seat ɗin mota don tsabar baiji da mace zai barta tsaye tana shan gajia" ya wucewarshi kawai.
Tasan da ita yake, kawai dai bata son ta tanka mishi a gaban Ibraheem ne ya sakata sharewa, ba daɗewa ta sallami Ibraheem sannan ta shige gidan, ɗakinta kawai ta wuce donma karsu k'ara haɗuwa, bata sanma sanda yabar gidan ba.
Da safe taje gaishe da Daddynta, harta taso zata tafi ya tsaida ita, ta koma ta zauna kanta a k'asa gabanta naa faɗuwa.
"ɗazu wanne yaro ne yazo gidannan?" sai da ta ɗanyi shiru sannan tace "Yayan k'awata ne Daddy"
"Yayan k'awarki kuma meya kawoshi gidannan?" shiru ta k'arayi har saida ya k'ara maimaita tambayarshi sannan tace "ba komi fa Daddy".
Yace "ina fatan hakanne, domin kuwa naa riga dana miki miji" da sauri ta ɗago da fuskarta "miji kuma Daddy?"
"k'warai ma kuwa, idan ma bakisan ko wanene ba yanzu zaki sani, domin kuwa tun kina k'aramarki mukayi ma Mahaifinmu Alk'awarin haɗaku aure da Majeed"
Wani irin zabura tayi "Majeed dai Abba? Ni wallahi bazan aureshi ba, na rantse bani sonshi" yace "tohh naji baki sonshi, tashi ficemin daganan, maganar aure tsakaninku dai babu fashi" nan ta k'ara fasa wani kukan, ta tashi ta nufi ɗakinta har tana tuntuɓe a hanya faɗi take ita wallahi bazata taɓa aure Majeed ba.
