AUREN BAZATA PART 4



"Yau tuesday Safeer na zaune a office dinsa da yamma misalin karfe 3:20pm Haiydar ya shigo da sallama a bakinsa, Sai da Safeer ya answer masa kafin ya kariso ya zauna yana facing Dinsa "


" Ajiye Files din hannun sa yayi sannan ya ce

    "Haiydar ya Aikin?

" Alhamdulillahi "
" Dan Allah ka tayani yiwa Hajiya Godiya tana ta hidima wallahi Allah dae ya kara girma "


" Sai da Haiydar yayi murmushi kafin yace ae bakomai Safeer yiwa kaine "

" Duk da haka dae kae mata godiyar "


" To insha Allah zan mata, Daga nan dae suka cigaba da Hirar su wanda mafi akasarin hirar dae akan Miemie ake yinta, Har sai da ran su ya baci dukansu sannan Haiydar ya mike yana bin Safeer da Mugun kallo "
 


   " Ae dama na dade da sanin baka sona da kanwar ka shiyasa kake ta wani kakkaucewa to wallahi duk a binka sai na Auri miemie insha Allah, kuma gobe xanje na samu Abban na masa magana da kaina Haiydar ya fada yana nuna safeer 👉🏻"


"Murmushi Safeer yayi yana mikewa da niyyar fita sannan yace Haiydar kanada Matsala wallahi kullum anyi ta maimata magana daya ne wae, Haba da Allah be a man mana me xakayi da wata miemie yarinya ko gama mallakar hankali batayi ba "


" Naji koma me zakace sai dae kace amma dae sai naje na samu Abbah inyaso kafin naje ka rigani zuwa ka zuga kaji ko "


" Ni na isa na zuga shi Haiydar Allah ya bada sa a kaje wallahi, Kuma Allah ya huci zuciyarka "

Daga nn dukansu suka fito kowa ya shige motar sa ba tare da sunyi sallama ba"


"Sanda Safeer ya isa Gida Shukrah na kitchen tana toasting bread, ta fito da sauri tazo ta kama hannun sa tana masa sannu da zuwa "


" ME ake mana ne Shukrah cute naji gidan kamshi Safeer yace yana rungumo Shukrah jikin sa "


" Bread nake toasting wallahi yau shi nake Sha 'awa shukra tace sanda suka karasa dakin, Shigewa toilet tayi don hada masa ruwan wanka shikuma ya cire kayan jikinsa ya daura towel ya bi bayanta "


" A bakin kofa suka hadu, ta raba zata wuce ta gefensa yay saurin janyota, "Ina zaki kuma?


" Kitchen zan koma ta bashi answer tana kokarin janye jikin ta a nasa "


" Ya kwantar da murya kamar me shirin yin kuka 'Da wanka zaki min Wallahi na gaji yau tunda na zauna ban tashi ba "


" Dariya tayi sannan ta kwace jikinta ta fita da sauri tana masa gwalo, shima dariyar yayi sannan ya fara wankan sa "




" sanda ya fito ya samu shukra a parlour tana cin toasted bread nata nan yayi joining dinta suna ci suna hirar su abin sha, awa, sanda suka kammala Shukrah ta kai bowl din kitchen ta dawo ta sameshi suka cigaba da hirar su har zuwa lokacin sallar magrib sannan Safeer ya fita mosque ita kuma tashiga daki don yin sallah "



" Washe gari Safeer beje office ba a gida ya zauna ya taya Shukrah hada musu trolley sai bayan sallah la 'asar sannan ya tafi gidan Mamah dauko Miemie kamar yadda ya mata alkawari , Sanda ya shiga gidan Miemie ce kadai a parlourn Aysher na kitchen, Mamah kuma na sama, Miemie tasa trolley a gaba ta buga tagumi harda dan hawayenta don ta gama fitar da ran zuwan Safeer, Ae tana ganin ta fasa ihun murna ta nufo shi da gudun ta, Saurin dakatar da ita yayi ta hanyar mata wata gigitcciyar tsawa

    "Kina kara sowa nan sai na kwada miki mari wallahi, shashasha kawai"



"Kuka ta fasa tana kwalawa Mamah kira kamar Safeer yamata wani abun , A tare Mamah da Aysher suka iso parlour'n suna tambayar ta lafiya "

  " Ba yaya Safeer din nan bane bezo da wuri ba kuma yanzu yazo wae ze mare ni, Miemie ta fada cikeda da shawgwaba tana kara fashe wa da kuka "


" Ba Safeer hatta Mamah da Aysher da Abbah da ya shigo yanzu sakin baki sukayi suna mamakin Karfin hali irin na Miemie "


" Kinsa Allah in baki rufe min bakin ki a gurin ba zan fasa shi inyaso kiyi me dalili  Safeer yace rai a bace "


" Ganin da gaske yake yasa Miemie sa hannunta ta rufe bakinta tana sauke ajiyar zuciya, zuwa can ta dawo kusa dashi ta durkusa har kasa sannan tace
     "Ya Safeer Dan Allah kayi hakuri kaje dani wallahi na dena rashin ji"

"Komai beceba sai juyawa da yayi gurin Abbah suka gaisa sannan yayi wa Aysher da Mamah Sallama, ya juyo yana hararar Miemie wadda har ynx take a durku she a gaban sa

     "Kin dau trolley mun tafi ko sai na bigeki tukun, Da sauri Miemie ta dau Trolley tayi gaba abinta ko sallama bata yiwa su Mamah"



"Cikin Mota Ko kallo Miemie bata ishi Safeer ba, ita kuwa sai satar kallon sa take, kula da hakan da yayi ne yasa shi kallon ta tayi Saurin sunkuyar da kai kasa, sai yaji ta basa tausayi, Har ga Allah yana son Miemie fiye da Aysher ma amma halinta ne ke hada su fada, "

" Meye kike kallona ya fada yana maida kallon sa ga titi "


" Bakomai tace tana kallon gefe, shiru ne kuma ya biyo baya har suka karisa gidansa "


" Shukrah najin horn tayi Saurin leko wa, ae MIEMIE na ganinta ta saki trolley hannunta taje da gudu zata rungumeta, Ae Safeer ma sai ya sa gudu ya riga miemie zuwa ya shiga tsakanin su yana wa Miemie wani mugun kallo,

    "Nawa ake biyana a gidanku da zaki barmin trolley a wajen nufinki na dauko. Miki ko, kuma da kika tawo da gudu da me zakiyi"


"jiki a sanya ye Miemie ta koma ta dauko trolley ta zo tashiga gidan "



" Yau ta kama friday kuma yau zasu tafi San Francisco, kasancewar jirgin 8:00am zasu bi yasa suka gama shirin su tun 7:00 suka fito suka tafi daukan Aysher a gidan Mamah don ita zata dawo da motar gida, 7:40 a Airport ta musu, Nan aka zauna hira har sai da aka kira su, sukayi sallama da Aysher suka Shige jirgi"


"Cikin jirgi Shukrah da Miemie duk bacci sukayi tayi har sai da jirgin su yayi landing a San Francisco sannan suka farka, Shukrah ce ta fara fita sannan Safeer, miemie na ziro kai ta shaki iska me sanyi, ae bata san sanda ta saki ihu ba ta ware hannayenta duka biyun ta rufe idonta tace""Wayyo Allah wayaga Miemie a sabuwar duniya, Ni anya ma kuwa zan koma gida "

" Ae Safeer besan sanda ya finciko ta ya matse bakinta cikeda da Bacin rai ba don iya kunyata wa ta kunyata sa.............







"Ahmad Safeer ya kira ya shaida masa sun iso sannan suka koma gefe suka zauna miemie tacika tayi fam kamar zatayi kuka don taji zafin matse mata bakin da safeer yayi, Sai hararan sa takeyi kasa kasa shiko bema san tanayi ba don duk hankalinsa nakan Shukrah da take masa hira sai dariya suke abinsu "


" Zaman kamar minti talatin sukayi wayar Safeer ta fara ringing, yai Saurin cirota a pocket dinsa sunan Ahmad da ya gani ne yasa shi Saurin picking don ya gaji da zaman gurin "

" Mun iso fa kuna wajen ina "Ahmad ne ke masa wannan tambayar?

" Mikewa yayi sai ya hango Ahmad da Azeeza, Gani ina hango kuma bari mu karaso Safeer yace yana yiwa Shukrah da Miemie alamar su taso, Kafin sukayi sallama da Ahmad "


" Sanda suka karasa inda suke Shukrah tayi tsalle ta rungume Azeeza ta ma manta da cikin dake jikin ta

    "Kibi A hankali Shukrah karkije ki bige mana Babyn mu inji Ahmad, sai a nn Shukrah ta tuno da cikin tai Saurin dafe wa sakamakon wani juyawa da taji yana yi ta runtse idonta sosai, Sannu kawae suke mata bama kamar Safeer daya bi ya rude, Azeeza ko ji tayi dama a jikin ta ciwon yake don tana jin Shukrah a ranta ta dauke ta kamar lil sis din ta Zafeera "


" A haka dae suka shiga motar Ahmad yaja su, ko cikin motar Shukrah na dafe da cikinta ta kwanto a jikin Safeer sai Sannu yake mata, Tafiyar kusan minti goma sukayi sannan suka isa gidan Azeeza ta fara fita ta bude kofar parlour sannan Miemie da Ahmad suka fito, Safeer ne karshen shiga gidan rike da Shukrah tanata kukan shagwaba wae ciwo, Niko nace wannan yarinyar ta fiye dangwa lolo 🤣"



"Azeeza taja hannun Miemie ta kaita wani karamin Room tace tayi wanka sannan taje ta dauko mata trolley dinta, Sanda ta dawo har miemie ta shige toilet hakan ne yasa ta fita ta wuce kitchen tana kwaso flask tana kae wa dinning sai da ta gama shirya dinning din sannan ta wuce dakin ta "


" 30 minutes later "

" Dukansu na zaune a dinning suna cin abinci, Miemie na kusa da Azeeza suna hira, Miemie tace Aunty can you do me a favour pls "

" why not! What do you want?

"I want you to take me out just to see your state "

" ok i promise to take you difference places like Zoological garden, Cinema and shopping mall "

" Cike da murna Miemie tace When?

"Next tomorrow insha Allah inji Azeeza "

" Ae MIEMIE bata san sanda ta mike ta fara rawa ba 💃🏻💃🏻, Ahmad da Azeeza sai dariya suke mata don ta shiga ransu sosai a dan zuwan nn nata, Takaichi ya cika Safeer gashi ba kusa dashi take ba balle ya kwada mata mari ko ya huce takaichi, Yayi ta jifanta da harara amma ta share as if to say ba da ita yake ba, "


" Azeeza tace Miemie you are very good in dancing when are you going to teach me?

"Till you take me out, Then i will teach you different types of dance "

" Am so grateful that you are here you are such a durlin Miemie inji Azeeza tana fara a jitake dama za a bar mata miemie don ba karamin son yarinyar take ba, cus she's very clever "


" Safeer dae da haushi ya ishe sa sai kawae ya mike ya shige dakinsu suko basu kawo komai a ransu ba suka cigaba da cin abincin su suna hirar su "


" Da daddare bayan kowa ya shige dakinsa Safeer ya shigo dakin Miemie lokacin tana tsaye tana shirin kwanciya ya hade rai yana kallon ta

     "Bakida hankali ko Miemie, Ke bazaki nitsu ba a rayuwar ki ko kin fi son kiyita hauka ana miki dariya ko, kin dauka birgewa ce wannan? Shekara goma sha uku amma bakida nitsuwa ko kadan, You have to maintain your dignity or else you will regret your life coming to this world, stupid gal kawae yana gama fadar haka ya fice rai bace "

" Miemie dae ta dade a tsaye tana tunanin rayuwar ta Tanaji a ranta ya kamata ta kama kanta ta dena abinda take ko zasu shirya da Brother 'n ta, haka dae ta kwanta ranta ba dadi har bacci ya kwashe ta "


" Washe gari tare Safeer suka fita da Ahmad, Safeer ya tarar da aiyuka birjik a office saboda haka ne ma koda lokacin tashin Ahmad yayi safeer cewa yayi baze bishi ba sai ya gama aikinsa ya tawo daga baya, hakan kuwa akayi Ahmad yaje yahau commercial car ya bawa Safeer car key dinsa yace ya tawo a ciki "


" Sanda Shukrah ta jiyo Sallamar Ahmad ta yunkura ta mike dakyar don cikinta ba karamin girma yayi ba ta fito parlour taga Azeeza na welcoming Ahmad, sai tayi turus ganin Ahmad kamar shi kadae ya dawo, to shi Safeer din a ina ya tsaya? Kamar Ahmad yasan me Shukrah take tunani yace safeer ko? Na baro shi a office yace in kin ganshi a gidan nn yau to ki tabbatar ya gama ayyukan sa ne "Shukrah dae kamar zatayi kuka ta ce to Allah ya dawo da shi lafiya sannan taja kafarta da kyar ta koma daki tayi kwanciyar ta kan centre carpet bata wani dade ba kuma bacci me nauyi ya kwashe ta"


"Sai ba adi salatul Magrib Safeer ya shigo gidan a gajiye, Azeeza da Miemie ya samu a parlour don Ahmad be dawo mosque ba, Miemie tayi masa sannu da zuwa sannan ta karbi brief case din hannunsa ta kai masa daki, sai da ya gaisa da Azeeza sannan ya wuce dakinsu nan yaga Shukrah a kwance tanata bacci abinta sai yaji ta bashi tausayi tuno war da yayi jiya be barta ta samu baccin kirki ba, nan dae ya cire kayan jikinsa ya daura towel sannan ya shige toilet don yin wanka, "


" Sanda ya fito Strait gurin Shukrah ya wuce ya zauna a gefenta ya dago ta ya rungumeta tsam a jikinsa sannan ya sa hannunsa cikin lallausan gashin kanta yana shafawa a hankali sai a nn Shukrah ta bude idonta ae suna hada ido ta fashe da kuka tana kokarin sauka a jikinsa, kara rike ta yayi sosai sannan cikeda lallashi yace Me kuma nayi ake min kuka, yi hakuri kinji Shukrah cute "

" Lafewa tayi a jikinsa tana sauke ajiyan zuciya sannan tace 'Bakai bane ka tafi kayi zaman ka a office ba "


" Eyya yi hakuri kinji bazan kara ba "


" To kawae tace tana murmushi daga nn kuma suka cigaba da hirar su, Tuni Shukrah ta manta da fushin da take ta ware sai zuba hira suke suna dariya abinsu "


" Washe gari Kamar yadda Azeeza tayi promising Miemie zasu fita hk kuwa akayi 3:20 suka fita su biyu dan Shukrah cewa tayi baxata bisu ba, Azeeza ce tayi driving basu zame ko inaba sai zoological garden, Sosai gurin ya burge Miemie, sundan dade a gurin kafin kuma suka wuce Cinema suka yi kallo daga nn kuma suka wuce wani shopping mall Azeeza tace Miemie tadau duk me take so, Miemie dae bata dau komai ba sai wani Makeup kit data dauka (Dama Miemie mayyar makeup ce) "Daga nn dae suka dawo a gajiye, wanka kawae sukayi suka ci abinci suka kwanta sai bacci.........




"Yau ta kama wednesday kuma yau ce ranar da Miemie bazata taba mantawa ba a rayuwar ta, 12:23pm Miemie na kwance a dakinta taji cikin ta ta juya ta mike ta shiga toilet, Tsugunar da zatayi taga jini ya zuba me zatayi in ba ihu, Don ta tsorata iya tsorata though an fada musu a islamiyya amma abun yazo mata unexpectedly, Mikewa tayi a tsorace taba kuka kamar dan shi aka aikota tana bubbude kafa kamar me koyon tafiya a hk ta fito palour, Bataga kowa a parlour ba saboda hk sai ta wuce dakinsu Shukrah "


" Sanda ta shiga dakin Shukrah na toilet Safeer ne kwance yana duba wayar sa, Motsin da yaji ne yasa shi Saurin dago wa, Miemie ya gani ta wani ware kafar ta tana kuka sosai "

" Ke zonan, Me ya sami kafar safeer yace sanda ya ajiye wayar sa akan bed side drawer "

" Karasa wa tayi still tana kuka, Tana kokarin daga skirt dinta, Safeer ya rike hannunta, meya same kine wae?


"Ba jinayi inajin fitsari ba nashiga toilet ina tsuguna wa naga jini yana fita a nn ba, Ta karashe maganar tana fashe wa da kuka, haka kuma tana nuna masa gurin "


" Dan murmushi Safeer yayi don ya gane gaskiyar abinda ya daga hankalin Miemie, "

" To naji na fahimta Ae ba wani abu Bane dena kukan kizo nan, safeer yace a kokarin sa na kwantar wa da Miemie hankali,

"Karasowa tayi ta tsaya a gefen sa, tana goge hawayenta "


" Ae a islamiyya an fada muku cewa duk jinin daya fito a jikin mace yar shekara tara zuwa sama, jinin haila ne ko? Inji Safeer, Daga masa kai kawae miemie tayi alamar Eh, Good, Shekaranki nawa?

13,"ta Bashi answer "

To Kinga wannan jinin na Haila ne bana ciwo ba so ki kwantar da hankalin ki, An koya muku wankan tsarki?


" Eh an koya mana miemie ta basa answer kasa kasa don wata kunyar sa ne taji ta rufe ta "


" Yawwa to yimin bayanin yadda aka koya miki inji, Fitowar Shukrah a toilet yasa duk suka mayar da hankalin su kanta, ta rike hannun Miemie tajata zuwa Toilet, "

" Cikin kayanki akwai sabon pant Shukrah ta tambayi Miemie?

"Ehhh akwai, Miemie ta bata answer, To ina zuwa yanzu ki cire kayanki kiyi wanka kinji inji Shukrah inda tana gama maganar ta ta fito hade da rufe wa Miemie kofar toilet din"


"Kai tsaye Shukrah dakin Miemie ta wuce ta bude trolley dinta ta dakko sabon pant ta dawo dakin su ta Shirya dan dama a wanka ta fito, Sanda Shukrah ta gama shiryawa toilet taje tana bugawa don ta fuskanci Miemie ta gama wankan kunya ta hanata fito wa"

"Bude min kofa kinji Miemie "

" Kamar bazata bude ba sai kuma ta bude, idonta a kasa don wani nauyin su takeji dukan su, Shukrah tace Miemie dago kiga, Miemie ta dago a hankali, nan Shukrah ta shiga nunawa Miemie yadda ake sa Pad a jikin pant sannan ta mika mata ta fice "


" Bayan kamar minti goma Miemie ta fito don taga tsaiwar bazata kaimata ba, Kanta a kasa tayi hanyar kofa, Safeer yace zonan Miemie, jiki a sanyaye Ta dawo ta zauna a kasa kusa da Shukrah, safeer yace baki min bayanin yadda ake wankan ba "


" Kunya ta kama Miemie tayi kasa da kai tana wasa da danyatsanta, ehen ina jinki Miemie, shi Safeer ma mamaki Miemie take basa yadda take wani kasa dakai"

"Shukrah tace Miemie ko ya Safeer ya fita ni kimin bayani?

Daga mata kai Miemie tayi, hakan yasa Safeer kara mikewa akan gado, ke nake sauraro Miemie karki bata min lokaci don bacci zanyi, Miemie ganin ba sarki sai Allah yasa ta bude baki da kyar ta fara masa bayani kamar hk :

"Da farko zan samu ruwa mai kyau wanda dandanon sa ko kamshin sa ko colourn sa bai changer ba, Idan a budadden abu yake kamar bucket sai na karkata nazuba ruwan na wanke hannuna sau uku, in kuma a rufaffen a bune kamar kettle basai na wanke hannunba tunda ba taba ruwan zanyi ba, tana kaiwa nn ta dago ta kallo shi idonsa a kanta, ya daga mata kai alamar ta cigaba, tayi murmushi ta dora :


"sai nayi alwala dai dai, wasu sunce bazan wanke kafa ba sai an zo karshan wankan wasu malaman kuma sunce za a wanke, Sai na hade hannayena duka biyun na cika su da ruwa na zuba a kaina na tabbatar ko ina ya samu zanyi hakan sau uku, daga nn kuma sai na raba jikina biyu a tsaye na fara wanke side din dama na sannan na hagu........


"Masha Allah Allah ya albarkachi rayuwar ki kinji inji Safeer, Shukrah ta kalli miemie tace kinyi kokari sosai, Maganar Safeer tasasu juyowa dukansu suna kallo sa, To Miemie sai ki nutsu yanzu kisan me ya dace dake banda wasa da Maza, su rike hannun namiji ko hawa cinyarsa, in ba hk ba wallahi zaki samu ciki, kuma kinsan ba kyau ae ko "

" Miemie fa cikinta ya duri ruwa ta gama tsorata sai raba ido take kamar tayi wa sarki karya, haka dae Safeer da Shukrah sukayi tayi wa Miemie nasiha, Miemie harda kukanta bayan sun gama Miemie ta mike jiki ba kwari ta shige dakinta ta kwanta sai bacci...

"Haka rayuwa ta cigaba bayan kwana uku Miemie ta tsarkake kanta ta cigaba da rayuwar ta, "




" Yau watan su daya a San Francisco kuma next week Miemie zata koma school hakan yasa da daddare Mamah, aysher da Abbah suna zaune a parlour suna hira har suka gangaro maganar Safeer, Mamah tace Au bari ma nakira shi ya kawo min yarinyata tunda shi zaman can be ishe shiba, Mamah ta janyo wayarta takira Safeer Ringing biyu yayi picking da sallamar sa, Suka gaisa da Mamah "

" Tunda zaman San Francisco bae ishe kuba kana iya kawo min yarinya ta next week zata koma school "

" Insha Allah Mamah jibi zaki ganta gobe da safe zan mata visa, Amma ni bazan samu zuwa ba wallahi aiki yamin yawa anan "

" Kai dae kasani nidai kawae naga yarinyata ehe inji Mamah "

" Yar dariya Safeer yayi yace insha Allah zaki ganta, my regards to Aysher daga hk sukayi sallama "

" washe gari sanda Safeer zashi office ya tsaya yaywa Miemie visa sannan ya wuce "

" sanda ya tashi a office ma beje gidan ba sai da ya tsaya a market yayi wa Miemie siyayya sosai sannan ya wuce gidan "



" Washe gari Miemie jirgin 12:00 zatabi, 11:30 dukansu suka shiga mota Ahmad yaja su sai Airport, Azeeza ta siyawa miemie wani Makeup kit, Miemie sai godiya take mata suna haka har 12:00 tayi aka kira Miemie sanda zata wuce Ahmad ya bata wata lada, taja trolley ta wuce tana masa godiya "

" Da daddare Safeer ya kira Mamah ya tabbatar Miemie ta sauka lafiya suka taba hira da Aysher kafin sukayi sallama, Nan ya kira Abbah suka gaisa sannan ya kira Daddy 'n Shukrah suka gaisa.........





*Nigeria*


"Aysher kwance a kan gado tana duba wani handout yayin da Miemie take gefen ta zaune tana duba kayan da ta dawo dasu Daga San Francisco, poly thene din da Ahmad ya bata ta dago  da sauri dan taji kamar kwali ne a ciki, budewa tayi me zata gani inba waya ba  IPhone 6s+  ta bude idon ta sosai tanaso ta gasgata abin da idon nata ke fada mata, iPhone din dae ta gani, ta fasa ihun murna, Aysher ta juyo da Sauri tana binta da harara don ita har ga Allah tayi tunanin wani abu ya same ta Amma ta ganta a zaune kuma har a lokacin ihun take "

" Meye hk Dalla malama ina bacci zaki dinga min ihu, inji Aysher ta fadi ranta a bace "

" Aunty Aysher ki tashi Uncle Ahmad abokin ya Safeer ne ya sai mun IPhone 6s+, Miemie tace tana janyo Hannun Aysher zata tayar da ita "

" Da sauri Aysher ta tashi tana zare ido ganin da gaske IPhone din ce a gaban ta, kin nuna wa Mamah ne,? Aysher ta tambayi miemie "


" Nima fa ban saniba kawae dae ya bani polythene ne Dazan tawo so ban bude ba sai ynx nake gani Miemie ta bata Answer sanda take saukowa akan bed ta fice ta shiga dakin Mamah, Abbah zaune a gefen bed yana duba wasu papers yayinda Mamah take kwance akan bed din da Alama ta fara bacci"

"Ihun Miemie ne ya sa suka dago dukansu da sauri suna kallon ta, ta karaso cikin dakin da gudun ta tana mikawa Abbah Wayar hannunta "

" Abbah kagani Uncle Ahmad ne ya bani ita "

" Murmushi Abban yayi sanda ya karbi wayar yana kallonta kafin ya dago yace
      "Miemie ae wannan wayar ta miki girma kinsan ma fa ni banason rike waya da wuri saboda batawa yaro brain yake, haka kuma yana bata tarbiyya"


"Wallahi kam, ae kawae karike mata wannan sai tayi graduation (Candy) sai ka bata, in wayar take so sai ka siya mata baby nokia ta dinga communicating da friends nata, Mamah dake kwance har a lokacin ta fada ba tare da ta dago kanta ta kalli Miemie ba "

" Miemie ta bata rai kamar zatayi kuka tana kallon Abbah daya maida kansa jikin papers dinsa yana cigaba da dubawa, Abbah Please karka ji Mamah ka bani wayana kaji "

" Ae kinji me na fada miki bazan bayar ba, zan siya miki karama wannan sai kin gama skul zan baki Abbah yace sanda ya mike ya shige toilet "


" Kuka kawae Miemie tasa ta juya ta shiga dakinsu inda ta tarar Har Aysher tayi bacci, nan ta kwanta tana kuka a hk har bacci ya dauke ta "



" To Rayuwa ta cigaba da tafiya, ynx Aysher ta kai level three (3)a B. U. K inda take karantar nursing, so ynx haka madai anyi posting su Aysher hospitals daban daban don yin practicals inda Aka kai aysher Malam Aminu kano teaching hospital, so Aysher bata wani shan wahala kasancewar ta mai kokarin gaske, sosai Doctors din keji da ita kasan dae itace over roller, "

" Aysher da kawayenta Maryam da Nuriyya tsaye a var render 'n S. O P. D da wani handout a hannunsu suna duba wa, gabaki daya hankalin su nakan abinda suke, Sallamar da sukaji anyi musu ne yasasu Saurin juyo wa suna kallonsa "

" Black jeans ne ajikinsa da white t~shirt yayinda ya dora white lab ~coat akai yayi un buttoning lab coat din, kafarsa sanye da wani black shoe hannunsa daure da white watch, Answer sallamar sukayi cikeda ladabi don shine doctor'n da aka hada su da yanada sakin fuska sosai shiyasa suka saba dashi sosai "
" Cikeda fara a ya answer gaisuwan su sannan ya kalli Aysher wadda gaba daya hankalin ta nakan handout, Aysher in kin gama ki sameni a office yace kafin ya juya ya koma office dinsa "

" Mikawa Nuriyya handout din tayi sannan tabi bayansa, Be dade da zuwa office dinba ta shiga itama, kara gaisawa sukayi kafin kuma sukayi shiru tsawon minti goma, zuwa can yace
   "Aysher wata magana zamuyi dake to amma kuma naga kamar Karatu kike so kibani number ki inyaso sai muyi magana a waya ko zuwa anjima ne"

"Badan Aysher taso ba sai dan kawae ganin girman sa da take ne yasa ta karbi wayansa da yake miko mata ta sa masa number ta ta mika masa, Hannu ya miko mata alamar ta basa wayarta aiko ba musu ta miko masa nan dae yayi mata saving number sa as Mahmoud sannan ya bata, ta masa sallama ta fice "


" Bayan kamar kwana 2 da faruwar Hakan Mahmoud ya kira Aysher suka gaisa, Aysher batayi wani mamakin jin cewa Mahmoud yana sonta ba don dama ta dade da ganin alama, Mahmoud dae be kyale Aysher ba har sai da ya tabbatar ya samu shiga "





*San Francisco*


" Shukrah da Azeeza zaune a parlour suna hirar haihuwar Shukrah don yanzu cikin nata nada wata takwas kenan, inda Azeeza ke cewa ita tafi son a haifi Namiji ita kuma Shukrah wae tafi son Mace suna cikin wannan musun ne Ahmad da Safeer suka shigo da kaya masu uban yawa daga gani dae daga kasuwa suke, Azeeza ta mike ta karbi kayan ta shige dasu wani dan karamin daki inda anan ne suka ware don tara kayan Baby, Shukrah dae daga zaunen da take ta musu welcome don baxata iya tashiba saboda swelling da legs nata sukayi, Safeer ne ya karaso inda take ya durkusa gaban ta ya fara massaging mata legs din har sai da ya tabbatar swelling din ya ragu sosai sannan ya taimaka mata ta mike suka shige dakinsu, a tare sukayi wanka bayan sun shirya suka dawo parlour inda Safeer da Ahmad suka fice Azeeza kuma ta shige kitchen "

" White spaghetti ta musu bayan ta gama ta daura soup kan gas, bata wani dau lokaci ba ta gama ta dauko flask set din ta jera a dining sannan ta dawo parlour tayi joining Shukrah suka cigaba da hirar su har lokacin magrib yayi suka tashi sukayi "


" Ba *Ahmad*  da *Safeer*  suka dawo ba sai ba'adi salatul Isha, abinci sukaci a tare suka danyi kallo sannan sukayi wa junansu sallama Suka shige dakinsu, *Shukrah*  ce kawae ta sake wanka don cikin nn yana sa mata jin zafi sosai,Sanda ta fito har Safeer yayi bacci saboda haka itama ta kwanta gefen shi sai bacci "


" To rayuwa tanata tafiya don ynx cikin *Shukrah*  ya shiga watan haihuwa saboda haka *safeer*  da *Ahmad*  sukayi handling company 'n su gurin wani yaron Ahmad *Ammar* don Ammar yanada Amana da hankali sosai, zaman gida kawae su *Safeer*  suke, Da zarar *Shukrah*  tayi wani motsi na nuna alamar jin ciwo zasuyo kanta suna jero mata sannu "


" To ana cikin haka har E D D' n Shukrah ya cika, tun safe Azeeza ta shirya musu trolley, Shukrah dae ta dage bazata hospital ba wae ita batajin ciwo saboda hk a gida zata haihu "


" Haka suka yini lafiya cikin gidan, sai zuwa yamma sannan Mara da bayan Shukrah suka fara mata ciwo nan fa hankalin kowa ya tashi ba kamar Safeer da hankalin ya gama tashi, wani karfi yaji yazo mishi bemasan sanda ya daga Shukrah ba sai mota, nan Ahmad ya biyo shi, nan Azeeza ma ta fito da trolley sai hospital.........






"Sun isa asibitin cikin sa a aka karbi *Shukrah*    aka wuce labour room da ita, Shukrah tafi karfin awa daya acikin labour room amma ta kasa haihuwa hakan ne ya bawa likitocin damar bata inducing drug tasha amma ta kasa haihuwar, Anan kuma suka fara tunanin yimata C. S ".



"  *Safeer*  ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kewaye yake ya rasa inda zaisa kansa, duk da Air condition din dake gurin amma gumi sai zuba yake a jikinsa kafafunsa sai rawa suke jiyake kamar ya cire ciwon ya dawo kansa, *Azeeza*  da  *Ahmad*  sai kokarin bashi baki suke amma sam yaki jinsu, ya zauna ma yaki zama *Shukrah*  kam sai ihun ta take tana kiran *Ammii, Mamah, Aysher, Miemie kai har meela ma sai da Shukrah ta kira, yana cikin wannan halin daya daga cikin Doctors din da suka karbi *Shukrah*  ya fito Sukayi Saurin mikewa suka nufeshi, *Safeer* bakinsa sai rawa yake ya kasa ma yimasa magana, doctor ne ya dafa kafadar *Safeer*  yana bashi baki kafin ya miki masa wani paper wa yayi signing ayiwa *Shukrah* C. S "

" Duk jarumta irin ta *Safeer* besan sanda ya fashe da kuka ba, da kyar ya karbi pen a hannun Doctor din ya dora kan paper, maganar da Wata Nurse ta fito tana yiwa doctor be kan yazo *Shukrah* ta haihu ta samu baby Boy  ne yasa *Safeer* wulli da pen & paper hannunsa ya bi bayan Doctor cikin dakin, nan *Azeeza*  da *Ahmad*  ma suka rufa musu baya sai dakin, Sanda suka shiga dakin har Nurse ta dauki Babyn ta fice dashi"

" *safeer*  ya kara da gudu da niyyar rungume *Shukrah*  Amma sai yayi Saurin dakatar da kansa don ganin tayi wani mugun nushin sai ga baby Girl ta fito, Zaro ido sukayi cike da mamaki da kuma farin ciki, *Safeer* ya rungume *Shukrah*  tsam a jikinsa yasa kukan farinciki, besan da bakin da zeyiwa *Shukrah*  godiya ba don ta bashi farin cikin sa Twins, *Shukrah* tayi karfin hali tasa hannunta tana goge wa *safeer* hawayen idonsa, Don tafi kowa sanin irin son da *safeer*  yakewa yara, Doctor ne yayi gyaran murya *Safeer* yayi Saurin daga *Shukrah* yana goge hawayen daya gangaro masa "


" Nan dae Nurses su 2 suka shigo da babies *Safeer* yayi Saurin karasawa ya karbi Baby girl din shikuma *Ahmad*  ya karbi boy din, anan kuma Nurse ta shiga da *Shukrah*  toilet don ta gyara jikinta "


" Nan safeer ya shiga snapping babies yayi marking duk contact nasa na WhatsApp yayi musu sending, nan fa aka fara kiransa ana masa murna, Aysher ma ta kirasa sanda yace takai wa *Mamah*  wayar kin karba tayi, tadai ce Allah ya raya *Twins*  "


" washe gari akayi discharging nasu, Abokan aikin su *Ahmad*  sai zuwa suke, kayan Babies kuwa kamar zasuyi magana don yawa, sai zuwa dare sannan *safeer*  ya samu damar kebewa da *Shukrah*  ya zuba mata ido tana rike da Baby girl dinta, tsawon minti Arba 'in suna hk, Har sai da *Shukrah* ta gaji da da kallon nasa tayi magana"



"Your look is so intense, it makes me nervous, what do you want?  *Shukrah*  ta tambayi *Safeer*  sanda ta dauke kanta "



"  *safeer* ma dauke kansa yayi sannan yace ALL what i want is your love, can you do me a favour and give me that much? I promise to live with you for ever, Indeed you are a blessing, kinbani farin ciki a rayuwa ta, i have never expected dis, being a Daddy of twins at this very tym"


"Why not? I will give you my luv for the joy you brought into my life, for understanding my needs, for allowing me to be part of you at the same time for turning back to the face of all my mistakes  *Shukrah* tace harda dan hawayenta "


" Rungume *Shukrah* ,  *safeer*  yayi itada Babies dinsu ya musu selfie.......








" *SAFEER*  ya kurawa twins dinsa ido fuskarsa dauke da murmushi, yanaji a ransa yanzu bashida wata matsala tunda Allah ya masa babbar kyauta wadda ba kowa yake waba, a fili yace 'Alhamdulillahi'
   
   " *SHUKRAH*  ta juyo ta kalleshi ya mata murmushi yace
   'Baki tambayeni wani suna nayi wa yara khudubah (Huduba)  dashi ba'

" tayi murmushi sannan tace abinda nake taso in tambaya kenan wallahi, wani suna aka sa musu?

"Murmushi Ya fadada sannan ya dauki Baby boy dinsa ya rungume yace
   'Saboda karamci, da mutunci, da Alfarma da kuma babbar kyauta da *ALHAJI*  *SARAKEE*  Yamin yasa nayiwa dana huduba da suna *AMEENULLAH*  Alkunyar sa kuma shine *LABEEB*  Inaso a ringa kiransa haka don suna ne me kyau sosai, Ya ajiye shi gefe sannan ya dauki Baby girl din, itadai  *SHUKRAH* sakin baki tayi bawae batayi sammanin haka ba, a a kawae dae abin yazo mata a *BAZATA* ne, Ta zame daga kan bed din ta durkusa akan kafafunta zatayi magana *SAFEER*  Shima ya zame yayi Saurin sa hannunsa daya ya rufe mata baki sannan yace, ita kuma nasa mata sunan Mamana wato Khadeeja za a dinga kiranta da suna *LABEEBA*  "

" Hawayen farin ciki ne yazubo mata tayi Saurin goge wa tana murmushi tana kara jin son *SAFEER*  Na ratsa jinin jikinta don ya mata komai a rayuwa yayi wa *DADDY* ' *NTA*Takwara, tasa hannu ta zame nasa hannun sannan tace
 ' Hakika banida bakin yimaka godiya don kayiwa mahaifi na abinda ba a taba yimasa, yayi Saurin dakatar da ita ta hanyar cewa
  'Nima Yamin abinda ba a taba min ba a rayuwa ta inajinsa kamar *ABBANA* , banajin a kawae abinda zan masa nabiya sa abinda yamin saboda hk karki ce zaki min godiya kinji "

" Wayarsa ce ta fara ringing yayi Saurin mikewa ya dauko akan bed *MAMAH*  Yagani ajikin screen din yayi Saurin dagawa yamata sallama "

" Idan kai bazaka dawo ba to ka kawo min *SHUKRAH*  kaji ko bakaji ba tace rai a bace "

" Dakyar ya iya bude baki yace *MAMAH*  naji kuma insha Allah cikin satin nan zamu dawo "

" Gobe nake so ku dawo na fada maka... Tana gama fadar haka ta kashe wayarta "

"  *SAFEER* YA juyo ya kalleta yace *MAMAH*  Tace gobe take so mukoma so ynx zan fita nayi mana Booking flight, Da sauri *SHUKRAH* tace to don itama zaman garin ya isheta musamman ma ynx data haihu tana bukatar ganinta kusada *AMMI*' *NTA*
, tare suka fito *AZEEZA* Kadai ce a a parlour don *AHMAD*  Bayanan,  *SHUKRAH* ta mika mata babyn hannunta sannan ta karbi na hannun *SAFEER* , "

" shiko yana fita ya nemi commercial car yace driver ya kaishi ' *AL* *HARAMAIN*  *TRAVEL* *AND* *TOURS* *LIMITED* , be dauki wani lokaciba ya gama komai, sai da ya shiga wani shopping complex yayi shopping sosai sannan ya wuce gidan, Sanda ya isa ana kiraye~kirayen sallar magrib nan yayi alwalla suka fice mosque tare da *AHMAD*,  sai da su kayi sallah isha sannan suka kamo hanyar gida, a hanyar dawowar sune *SAFEER*  Yakewa *AHMAD* Bayanin tafiyar su gobe, sosai *AHMAD* Yanuna rashin jin dadin tafiyar su koba komai sun saba, kuma yana jin tausayin *Azeeza* sosai don tasa *LABEEB*& *LABEEBA* Sosai azuciyarta, besan yadda zasuyi goben ba, Saurin goge Hawayen dasuka taru a idon sa yayi dai dai sanda suke shigowa parlourn gidan, a tare *Ahmad*  &  *Safeer* sukaci abinci don tuni su *SHUKRAH* sukaci nasu "

" Sanda suka gama cin abincin sukayi sallama, lokacin da *Safeer* yashiga dakin tararwa yayi *SHUKRAH* na hada musu trolley yakarasa kan bed ya dauko *LABEEBA* Yamata kiss a kanta yace Babyna ki tashi ga *PAPA* YA dawo, Baby kice you are welcome *Papa*"

" *SHUKRAH*tasa dariya tace kai *ya* *safeer*  karfa son baby yamaka illa, yarinyar da kwanan ta 3 kawae a duniya kake expecting tayi welcoming naka  "

" Hade rai *safeer* yayi yana hararar ta toke ina ruwan ki, Ni banason irin hk ehe, Dariyar ta cigaba da yi har sai da ta k'ularda Safeer yaja tsaki sannan ya kwantarda *Labeeba* ya musu addu a sannan ya kwanta"


"Sanda *SHUKRAH* ta gama hada trolley toilet ta shige tayi wanka, koda ta fito kitchen ta wuce tahada tea tasha sannan ta dawo dakin tasaka wata doguwar sleeping dress ta kwanta a bayan *Safeer* "


" Ya Safeer kayi hakuri dani naga kamar kayi fushi, Shiru yayi mata alhalin yana jinta, nan ta cigaba da masa magiya amma yaki kulawa, zuwa can dabara ta fado mata tasa harshen ta a fuskarsa tafara yawo dashi, nan *safeer* ya juyo ya rungume ta....



*washe* *gari*

"Dukansu a airport, *Azeeza*  rungume da *labeeba*  tanata kuka kamar shi aka aikota, ita tunaninta daya yadda zatayi rayuwa bau tare da Shukrah ba gakuma twins da tasa su a zuciyarta,j *Ahmad* ganin kukan *Azeeza* bame karewabane yasashi   mata alkawarin kaita Nigeria before or after naming ceremony, saida sukaga tashin jirginsu sannan suka koma gida


~~~~~~~~~~~~~~~

*HAIYDAR* zaune gaban Hajiyarsa da alama fada take masa
  "Haiydar wai kai yaushe zaka nutsu kayi Aure ne, akan idonka Safeer yayi Aure gashi har matar ta haihu amma kai kaki kafitarda matar ko"

"Ba hk bane Hajiya yarinyar da nakeso yanzu tayi junior waec dinta, so jira nake tayi grads sai a fara maganar auren "

" Kana hauka ne Haiydar, nace hauka kake Haiydar, ajinka zan cigaba da zama da kai har nanda shekara 3 to inma bacci kake ka farka, Nabaka two weeks kakawo min mata ko in zabo maka da kaina hajiya ta fada rai bace daga hk tafice ta barshi yana tunanin wae shi za a samowa mata yarasa me zai kira wannan auren da Hajiya take shirin yimasa (Niko nace *AUREN* *BAZATA* Xatayi maka), Ringing din dawayarsa yake ne yasa shi daukan car key dinsa ya fice daga gidan, tafiyar minti talatin ce ta kai shi Airport, nan ya kwashe su sai gidan Mamah, A hanya ne yake fadawa Safeer Hajiya zatamai AUREN BAZATA, me Safeer zeyi inba dariya ba. . . Dakyar ya tsayar da dariyar sa yace karka damu Haiydar *AUREN*  *BAZATA* *ALHERI* *NE*. . .





"Sanda suka karasa gidan Mamah cike suka shame shi da mutane as if to say ranar sunan ne, *MIEMIE*  Tazo da gudu ta rungume *SHUKRAH*  tana murna da ganinta nan dae aka fara gaishe gaishe, daga nan *Safeer*  ya fadawa *Mamah*  ze tafi gidan su *Haiydar*don nan akwai hayaniya sosai, To kawae yace sannan suka fice "

" Saida *SHUKRAH*tayi wanka taci abinci Sannan ta kira *Amminta*, *Ammii*  naganin kiran amma taki picking don ita dama me alkunya ce, Text *SHUKRAH*  ta mata tace sun sauka lafiya, Bayan kusan awa daya ta mata reply tace sannun ku to"


*MIEMIE*  sai nan nan takeda twins taki yarda kowa ya dauke su, wae 'ya' yanta ne


Washe gari *Ibteesam* tazo ta kawo wa babies kaya masu yawa, Hajiyar Haiydar ma tazo nan take yiwa Mamah bayani cewa tabawa Haiydar two weeks ya kawo mata kuma taga kamar be dau maganar T serious ba amma dae ta shirya bashi mamaki, don dama akwai wata yar yayarta *Zafeera*  zatayi wa yayar tata magana sai a hadasu don zafeera yarinya ce mai hankali da nutsuwa sosai, dama tun farko tayi wa Haiydar sha awarta amma da taga kamar zafeera bata gabansa yasa takyale amma tunda dae yanzu yaki kawo matar toko zata hadasu, sosai Mamah ta goyawa Hajiya baya acewarta ae Haiydar ya girma, kuma ma ae shirme me zai sashi cewa wae sai ya jira Miemie, nan dae suka gama magana Hajiya tayiwa Mamah alkawarin duk me ake ciki zata fada mata, Sanda zata tafi ta ajiye wa twins Rapper na 100 sannan ta fice, Mamah ta bita tana mata godiya "

" Duk wannan shirin da hajiya takeyi Haiydar be Sani ba don shi tunda tamishi magana bata kuma yimasa ba, saboda hk yace ko dama wasa take masa shiyasa ma yasake ya cigaba da harkokinsa"



"Gobe ne suna amma har yau *Ammii* taki zuwa taga su *labeeb* ,, *Mamah* ta kirata yafi a Kirga amma kullum cewa take gata nan da taga abin bame karewa bane yasa takashe wayarta, Gidan *Ammii*  ya cika da yan uwa da abokan arziki amma ba *SHUKRAH*  koda sukayi wa *Ammii*  maganar sunason akawo ta gidan ayi sunan anan cewa tayi ita ba ruwanta haka sukayi ta surutansu suka gaji"



"Da yamma Alh Sarakee ya duro Nigeria don dama ya dade a Senegal bayanan ma akayi haihuwar amma *SHUKRAH* ta mishi albishir din *Safeer*  ya mishi takwara, Sanda ya iso ana kiran sallar la asar saboda haka saida ya tsaya yayi sallah sannan ya karaso gida, *Ammii*  ta mishi girki kala kala amma saboda zumudin ganin *Labeeb*& *labeeba*  Yasa koda yayi wanka be tsaya cin abinci ba ya dauki babbar trolley daya shigo da ita ya fice, Sanda yake tada mota *Ammii* ta same shi
   "Yanzu Daddy fisabilillah gidan mutane xakaje ba  kara ba alkunya, koni fa har yau banje ba"

"Daddy dariya yayi sannan yace to Ammii ni na hanaki zuwa ne? Akwai bukatar naga grand child's dina shiyasa kikaga ma nadawo don bayau zan dawo ba ka ida sai next week zan dawo amma na tattara komai na ajiye nazo sannan kice zaki hanamin zuwa ganin su, yana kaiwa nan yayi reversed ya fice daga gidan, jiki ba kwari Ammii ta koma cikin gidan azuciyarta tana mamakin Daddy don gaba daya yariga ya saba da turawa komai nasa irin nasu yake "

" Cikin Sa a Daddy ya samu Safeer da abbah a guest room da alama suna tattatuna abu me mahimmanci ne, Da fara 'a Abbah ya tare shi yayi da Safeer ya durkusa har kasa ya gaida shi cikeda ladabi "

" Ashe kuma an samu karuwa? *DADDY* Yace yana maida kallon sa gun *ABBAH*

"wallahi kam an samu Alh. *sarakee* D Hajiya *Khadija*  Abban yace fuskarsa dauke da murna, Allah dae ya raya mana su bisa tafarkin addinin musulunci "

" Hada baki sukayi dukansu wajen cewa Ameen "gyaran murya Daddy yayi sannan yace Madallah Nagode da Girmamawa ko kuma ince da bani wani matsayi da kayi safeer, hakika kai abin alfahari ne kuma ka can can  chi yabo Allah ya maka albarka, Sakamon alkhairin dakamin ka sama yaronka sunana nayi alkawarin daukan nauyin duk wani abu da za'a ci ko sha na kuma dau nauyin gurin da za'a zauna kai hatta ragunan sunanma na hutar da kai insha Allah daga nan zuwa dare za a kawo "

" Abbah yayi Saurin kallon shi yace haba Alhaji ae baza ' ayi haka ba, hidimar tayi yawa ae yau fa ka dawo kasar ma gaba daya, ka barshi wallahi zamuyi komai insha Allah "

" Murrmushin manya Daddy yayi yace bafa ku kuka Sani ba haka kuma badan bazaku iyaba yasa zanyi  A a kawae dae tukwucin Alheri ne, so karku damu kudai kawai kuyi fatan ayi taro lafiya a tashi lafiya "



 Godiya dukansu suka mai kafin safeer yace bari yaje yasa akawo Twins, to Daddy yace sannan suka cigaba da hirar su da Abbah"

"Sanda safeer ya shiga cikin gidan A parlour ya tararda *AYSHER*,  *SHUKRAH* & *MIEMIE*, Shukrah na Rike da Labeeba yayinda miemie ta rike labeeb, hararar miemie yayi sannan yace waye ya baki ixinin daukar min yaro salon kiyar dashi ko, ke daman ba nutsuwa gareki ba, Hade rai Miemie tayi ta ajiye labeeb da karfi kan kujera har sai da yaron ya fasa kuka, Safeer ya zo da gudu zai rike ta tayi dakin Mamah da gudu ya bita, Aysher ce tayi Saurin daga labeeb tana jijjiga shi "

" Jikin Hajiyar Haiydar ta fada, Hajiya Kinga ya Safeer yanamin gori akan 'ya' yansa ko, kuma don na ajiye masa shine zai dakeni, tana kaiwa nan ta fashe da kuka kamar wadda ya daka, Shi safeer ma mamaki ne ya hana masa cewa komai shi a duniya be taba ganin yarinya irin miemie ba, Mamah tace ae sai ka fita tunda burinka ya cika kasata kuka kaji dadi, Miemie ta fakin idon Mamah tamasa gwalo tace cikeda shagwaba Mamah yaushe zaki haifar mana twins muma adena min gori "


" dariya sukayi dukansu sannan safeer ya fice yasa Aysher Da Shukrah su kaiwa Daddy twins"




WASHE GARI


Tun asuba mutane suka fara cika gidan duk da cewa a tourist camp za ayi taron sunan amma kafin7:00 gida ba matsaka tsinke, ba ayi girki a gida ba kasancewar an riga anyi order a can tourist camp din snacks kuma anyi order a me. Biggs, Drink ko Wata Aminiyar Mamah ce Hajiya Maryam Anas ce tadau nauyi "


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

12:00pm na isa tourist camp gurin ya cika sosai da yan uwa da abokan arziki, Bayan bude taro da Addu ' a da wata babbar Malama *safiyya* *yakasai* da tayi ne kuma aka vukaci D. J Yasa sauti nan fa yan *SHUKRAH NOVELS suka zage sai rawa suke ba kamar Safiyya* *Galadanchi* da *Zee* *zee*, sai da komai ya lafa sannan aka fara rabon Mutane sai karba suke, can nagano wasu mutane sun koma gefe sunata dura abinci da lemo a jaka kara matsawa nayi don ganin ko suwaye, wazan gani inba, *MEELA*  *SOFTIE*  *EESHATULLAH* *MAMAH* *SKY* *FEUXER* *MARYAM*& *NURIYYA* ba, suna ganina suka fara raba ido, Haka dae taro ya watse mutane sae sawa twins albarka suke "




" Sai wajen 11:00pm safeer ya samu kubewa da Shukrah, fitowarta a wanka knn tana shiryawa yakarasa ya rungume ta taba ya a tare suka sauke ajiyar zuciya, yace mata a cikin kunnen ta

"Bazan taba gajiya da yimiki godiya ba Shukrah kinmin komai a rayuwa ta, Allah ya miki Albarka kinji, yanzu ki fadamin duk me kike so insha Allah zan miki "


" Shukrah tai Saurin juyowa tana kallon shi sannan tace da gaske ya Safeer "


" Yace Da gaske "



Tace Aiki nake so na fara, yace wannan shine yafi komai sauki, akwai wata kawar Mamah tare sukayi  


" *SHUKRAH* tace karka cemin *AUNTY MARYAM ANAS*, *Safeer* ya kalleta cikeda mamaki sannan yace karki ce kinsan ta?

" *SHUKRAH* ta mishi hararar wasa sannan tace lallai yaza ayi ace bansan taba tare fa sukayi secondry skul da *Ammii* fa kuma tana zuwa gida sosai,  *Safeer* yayi murmushi mai kyau sannan yace Masha Allah ynx inna fita zanyi wa *Mamah* magana insha Allah komai zaizo da sauki don *Mamah* tana bani labarin saukin kan *Mummy Maryam Anas* tun suna uni maid haka take duk da kasancewar ta over roller amma bata da girma kai,  *SHUKRAH* ma murmushi tayi sannan tace Allah sarki Allah dae ya shige mata gaba, kuma nagode sosai da Amincewar dakayi *PAPA'N TWINS*, matsowa *Safeer*yayi ya rungume ta sosai sannan yace kinfi karfin komai a gurina wallahi *SHUKRAH*  Allah dae yayi miki Albarka ya kuma kara miki lafiya ya kare ki daga sharrin masu sharri, sosai *SHUKRAH*taji dadin addu 'ar tasa saboda haka ta manna bakinta akan nashi ta soma kissing dinsa sundau lokaci sosai a hk kafin *LABEEB*ya fasa kuka sukayi Saurin janye wa haka kuma suka nufeshi da sauri,, *SHUKRAH* C tayi nasarar daukan sa Tasan yunwa yakeji don duk basu zo hannunta ba, shiyasa tayi Saurin yaye rigarta tasoma feeding nashi"

"sanda *Safeer* ya fita a dakin gurin *Mamah* yaje yamata bayani yadda sukayi da *SHUKRAH* kuma hakan ya mata dadi at last dae zata taimaki mutane da yawa kuma ta mishi alkawarin zatayi, *Mummy Maryam Anas* maganar a yau ba sai gobe ba, nan  *Safeer* yashiga godiya sannan sukayi sallama da *Mamah*  da kanshi ya kai Hajiyar *Haiydar* gida sannan sukaje ya samu *Haiydar a gida saboda hk suka zauna sunata hira Safeer* sai
Tsokanar *Haiydar* yake wae za ayi masa *AUREN BAZATA* Sai da *Haiydar* ya bata ransa sannan *Safeer* ya kyaleshi sanda ya masa sallama ma ko answer wa ma beyi ba haka *Safeer* ya tafi ya nayiwa *Haiydar* dariyar mugunta"


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°


*Hajiyar Haiydar* T samu yayar ta  *Hajiya Safiya* kan tana son hada *Haiydar* &  *Zafeera* Aure kuma Alhamdulillahi maganar ta tasamu karbuwa a wajen *Hajiya safiya Da Alhaji mai kano* mahaifin *Zafeera* kenan Don Alhajin cewa yayi nanda wata biyu za ayi bikin acewarsa ae su suka haifi yaran kuma sunada hakki akan su haka kuma suna da ikon zaba musu abinda yayi dai~dai da rayuwar su, saboda hk ba bukatar tambayar *Zafeera* ko bata sonsa"



" *ZAFEERA* Itace 'ya mace guda daya tilo a gurin *Hajiya Safiya* shiyasa ta dauki son duniya ta dora mata"

"hajiya kawae dauriya take don sam bata son abinda zai taba *gudaliyar ta*,kuma tana tunanin yadda zasu kwashe da *Zafeera* DUK da dae tanada saukin kai kuma tasan bazata ce A a ba, Amma tana ganin dae kamar an shiga hakkin ta, da kyar ta iya bude baki tace Allah dae ya sa komai yazo da sauki "


" Ameen Hajiyar Haiydar tace "

" Shiko *Alhaji Mai kano* cewa su kashe kansu in anyi AUREN, daga nan dae ya mike ya fice, To itama Hajiyar Haiydar sallama tayi wa Hajiyar Zafeera ta fice "



" Da daddare har Zafeera ta kwanta Hajiya ta shigo ta kwashe duk yadda sukayi da Hajiyar Haiydar ta fada mata sannan tace
      "kuma Baffanki yasa bikin Nan da wata biyu,"

"Zuciyar Zafeera ta bada wani *Dum Dum Dum* tanason Hajiyar ta, kuma bata jin zata iya watsa kasa a idanun soyayyar da Hajiyar take mata uwa uba kuma tarbiyyar da Hajiyar tamata, Saboda hk tace *TO* Asanyaye "

" Sosai Hajiya taji tausayin 'yar tata amma saboda batason maganar tayi nisa har tasa *Zafeera* kuka yasata mikewa tace kiyi Addu' a *Angel* sai da safe "

" nanma *To*kawai tace mata sannan ta kwanta"


"Duk wannan Abun da ake Haiydar be Sani ba don Hajiyar bata kuma yimasa maganar ba, cikin sati biyu magana ta kankama don har ta isa katsina dangin su Haiydar din kenan, Hajiyar Haiydar da Hajiyar zafeera sun shirya staf zasuje Dubai don hado lefen *Zafeera*, koda *Haiydar* ya tamvayeta inda zata cewa tayi ina ruwansa "

" Sati daya kawae su Hajiya sukayi suka hado kaya masu yawan gaske uwa uba kuma ga kyau da tsada, Sai bayan da suka dawo ne Hajiyar tace wae yazo yaga lefen shi, ko kallon kayan beyiba yayi fice war sa don wani mugun takaichi ne ya durar mishi"


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°


"yau kwanan su *LABEEB DA LABEEBA* 40 A duniya amma *Ammii* bata taba sasu a idanun ta ba sai dae ko a picture shidin ma sau biyu ne, Ranar da *AREEF* Yaje ganin su yayi snapping dinsu ya nuna mata sanda ya dawo sai kuma sanda *SHUKRAH* tayi mata sending a WhatsApp "

" Wannan dalilin ne yasa *Mamah Shukrah Aysher da Miemie* suka shirya mata ziyarar *BAZATA*.. . .



" *AMMII* Na daga cikin daki ta jiyo sallamar su, ta fito da sauri ta tare shu da fara 'arta
   "Sannunku da zuwa, wannan irin zuwa na bazata haka, da kun Sani kun kira ni kun cemin zakuzo ae"


" *Mamah* ta dan harare ta sannan tace to in an kira picking kike, ae ina sane na shirya wannan zuwan bazatan sai da na kira *AREEF* Ma na tambaye shi ko kina nn ya tabbatar min kina nn din sannan muka tawo "


" Murmushi kawae *AMMII* Tayi ta wuce fridge ta kawo musu drinks, *Aysher* ta durkusa kusa da *Mamah* tana gaida *AMMII*, da fara a ta Answer sannan *MIEMIE* MA ta durkusa ta gaida ta,  *SHUKRAH*ma ta gaida ta, ta Answer ba tare da ta kalle taba "

*MAMAH* Ta dawo da kallon ta gun *AMMII* Sannan tace, ae kawo muki twins mukayi tunda kinki zuwa ki gansu, Murmushi *AMMII*Tayi sannan tace ba haka bane ba, abubuwa ne sukayi min yawa, *Mamah* tace to aini gashi nan nazo da kai na"

" *SHUKRAH* ta dan kallo *AMMII* Aiko suka hada ido, Ammii tayi saurin dauke idonta, Shukrah tayi Murmushi sannan ta mike ta do rawa Mata *LABEEB* Kan cinyarta,  *AMMII* Tayi saurin sa hannu ta ture shi saura kadan ya fadi Shukrah ta tare shi tana Murmushi, Mamah tace yanzu dan Allah wae sai ki ture shi haba *Ammii* gaskiya ki rage wannan kawaichin naki yayi yawa wlh ynx zamani ya canja fa, Dariya *Ammii* tayi tace to ae shi kunya, kara da kawaichi a jinin fulani yake, Amma kamar yadda kika ce na rage zan danyi kokari na rage din, yawwa ae haka akeso *Mamah* tace tana do rawa *Ammii* *Labeeba* akan cinyarta, cikeda kunya *Ammii'n* ta daga ta tana Murmushi sannan tace Allah ya raya su yasa masu jin k'ai ne"


"Hada baki sukayi dukansu wajen cewa Ameen"

"Yinin ranar duk sunyi shine a gidan *Ammii* amma *Mamah* ta kula bawata magana data shiga tsakaninsu da *SHUKRAH* a zuciyarta tana mamakin hali irin na *Ammii* kusan wata biyar fa bataga Shukrah 'n ba tun tafiyar su San Francisco gashi ynx tazo amma sai share ta take, Tana wannan tunanin ne taga *Ammii* ta mike ta shige Bed room, *Mamah*ta Dawo da kallon ta gun *SHUKRAH* tace
    *SHUKRAH*  tashi kibi *Ammii' nki* kuyi magana kinji "

 Kamar dama jira take tayi saurin mikewa ta shige dakin da sauri, juyawa Mamah tayi azuciyarta tana dada mamakin *Ammii*, Sanda *Shukrah* ta shiga dakin lokacin ita kuma Ammi zata fito, Shukrah tayi saurin rike hannunta tace *AMMA  NA* ynx kin dena sona ko? Ta fadi haka ne sanda hawaye ke fitowa a idanunta "


"  *Ammii* cikeda tausayin 'yar tata tace ban dena sonki ba *SHUKRAH* ya jikin ki?


"jiki Alhamdulillahi, twins suna fushi dake tunda kinki zuwa ganin su, Dariya kawae *Ammii* tayi sannan tace ae ynx gashi nan kun kawo su ko?

Eh mun kawo su kam, sun danyi hirar yaushe gamo sannan suka fito, sai bayan sallah 'r magrib sannan suka tafi bayan *Ammii* ta cika su da tsaraba "


" washe gari da sassafe *Safeer* ya shigo cikin gidan *Mamah* ya tarar a parlour tana Karanta *Hisnul muslim* ya durkusa kusa da ita yana gaida ta, Bayan sun gama gaisawa kuma shiru ne ya biyo baya don *Mamah* cigaba tayi da karatun ta shi kuma *safeer* zama yayi yana dan Satar kallon ta, lura da hakan da *Mamah* tayi ne yasa ta ajiye littafin hannunta ta ta dawo da kallon ta gurinsa "

" Ya akayi ne *Safeer*?

"kara kasa da kansa yayi kafin yace' *Mamah* dama zuwa nayi mu tafi da *SHUKRAH* &  *TWINS* Tunda sunyi Arba ' in dinko?

"Mamah ta rike ha'ba tana masa kallon mamaki sannan tace to fitsararre mara kunya ni ae nafika sanin sunyi Arba,in din, to barin fada maka baxata koma ba sai nan da two weeks don bamu gama gyaran da muke ba"

*Safeer*ya bata rai kamar zeyi kuka yace wae wannan wane irin gyara ne dan Allah, nidae kawae a barshi haka wannan ma wanda akayi mata ya isa "

" Dalla can rufe min baki mara kunya kawae sai kace bakai ake yiwa gyaran ba, ta nuna masa kofa tashi ka fita ka bani guri, haka *Safeer*din ya fita yana mita
  "Wannan wace irin rayuwa ce, dan anga Mutum me hakurine sai a dinga masa yadda ake so, an cemin 40 days zasuyi na hakura amma ynx an canja magana wae sai nn da two weeks, yaja tsaki sanda ya shige motar sa ya bar gidan"


*SHUKRAH* *SHUKRAH* *SHUKRAH*, Na am *Mamah* Shukrah ta Answer sanda take fitowa daga daki, wuce kije kitchen ki dauko babbar tukunya a dora ruwan wanka, to kawae Shukrah tace sannan ta dauko ta ajiye a gaban Mamah"


"Sassaken bagaruwa Mamah ta zuba sannan ta matse lemon tsami akai tace Aysher tashi kije ki ta fasa, in yayi saiki jiya ki kira Shukrah ta shiga ciki"



"Sanda Shukrah ta fito a wanka Mamah tasa Aysher ta dauko kaskon turaren wuta da bucket na karfe, Mamah tasa Kaskon cikin bucket din tazuba angurya(wanda ake samu a jikin audiga) tazuba bawon (kwanson) citta Shukrah ta zauna akai, Bayan an gama wannan Mamah ta kara zuba wani turare da wata kawar ta ta kawo mata daga Senegal "

" T haka dae rayuwa ta cigaba da tafiya kuma yau Shukrah tayi sati biyun da Mamah ta kara mata, Mamah tasan halin Safeer sarai shiyasa ma bata kirasa ta tuna masa ba, Amma ga mamakin ta har bayan magrib Bai shigoba, abin ya damu Shukrah sosai shiyasa ta faki idon Mamah ta shige dakin ta fara kiran wayarsa, bugu biyu tayi yayi picking "

" Hello *Papan Twins*


"Yap *Mamin Twins* ya kuke?

"Lafiya kalau muke, kai muketa jira dae"

"Murmushi Safeer yayi wanda har Shukrah na iya jiyo sautinsa yace ke bakin biyewa Mamah ba kin share ni, nifa da har na fara tunanin dama akwai wata yarinya teemerh luv tana masifar sona to da har nayi niyyar zuwa gurin Dad nata in nemi AUREN ta nanda two weeks in za ayi bikin Haiydar a hada namu kawai "


" Shukrah ta saki kukan shagwaba tana bubbuga kafa Ni wallahi bazan yarda ba, Ni wallahi kawai kazo mu tafi ko in tawo da kai na "


" Kukan da Shukrah take ne yasa Mamah ta shigo dakin, jin abinda Shukran ke cewa yasa Mamah ta fahimci da wanda suke wayar, saboda haka ta ta koma ta  ta samu Miemie aparlour

 "Miemie je ki kiramin Aysher tazo ku kai Shukrah gidanta, to Miemie tace sannan taje ta kira ta, Mamah da kanta tayi wa Shukrah bayanin Su Aysher zasu rakata, Bayan kamar minti goma sha biyar Shukrah ta shirya tsaf haka ta shirya twins, Aysher da Miemie suka tayata sa kaya a booth, Mamah dae tana tsaye sai da taga fitar su ta koma ciki... . .







"Cikin Mota *SHUKRAH* tayi wa *SAFEER* Text tace masa tana hanya, zo kuga murna gun sa don beyi tunanin *Mamah* zata yarda ta barta ta tawo ba, saboda tsabar zumudi zaman cikin gidan gagarar sa yayi saboda haka ya sa jallabiyya ya fito ya zauna gurin gate man, jefi jefi suke hira, Zaman kamar minti goma sha biyar yayi yajiyo horn a, ko ba a fada ba yasan su *SHUKRAH* ne shiyasa ma yayi Saurin mikewa yaje get din da sauri da nufin bude musu, get man yayi Saurin karaso wa "

" Ranka ya dade, kabari za a bude yace yana kara sawa jikin get din"

"Yi sauri ka bude dae, ba surutu nace kayi min ba *Safeer* yace cikeda kaguwa"

"Nan get man ya bude musu, Aysher ta shigo da motar, yayi Saurin ban bayan motar, Tun kafin Aysher ta gama Parking *SHUKRAH* ta bude ta ziro kafarta, kadan ya rage  *labeeba*  ta fadi a hannunta, Da sauri  *Safeer* ya karaso ya hada ta da *labeeba* ya rungume su cikeda so da kaina, sam ya manta ma dasu *Miemie*(Baki abun magana)  suna tsaye "


" Aysher tayi Saurin dauke kanta, *Miemie* ta tabo Aysher, Aunty Kinga ya *safeer* din nn ko kunyar mu ma beji ba, lallai ", Aysher ta buge mata baki tace kin cika surutu wallahi, bazaki iya dauke idonki ba"

"Duk wannan maganar a kunnen  *SHUKRAH*sukeyinta shiyasa tayi Saurin ture *Safeer* din tace su *miemie* na kallon muda, dariya kawae yayi sannan ya daga kafada irin ko a jikin sa din nn,  *SHUKRAH* ta kallo *Aysher*,  *Aysher* tayi Saurin dauke kai, ita Shukrah dariya ma aysher ta bata tace Bazaku shiga bane kuka tsaya wae, Aysher tayi Saurin kallon ta ta girgiza kai tace baxamu shiga ba Aunty dare ya fara yi kuma ban iya driving din dare ba"


"To Kawai *SHUKRAH* Tace sannan *MIEMIE* ta mikawa *Safeer* *Labeeb* dake hannun ta, *SAFEER* Tsabar mugunta sanda ya karbe shi sai da ya murde hannun *MIEMIE* yace fitsararriya kawai, Allah ya sa dae kina karatu don naga har ynx kanki yana rawa "

" Yar kara *Miemie*ta saki sannan ta kallo shi da fuskar tausayi tace Eyya ya *Safeer* akwai zafi fa, cika mata hannun yayi yace wuce ki bani guri ni, harda dan gudun ta ta wuce ta shiga mota *Aysher* tayi musu sai da safe sannan ta shiga motar tayi reversed T fice a gidan"



10:15 *Safeer* ya samu *SHUKRAH* a dakinta tana shirin kwanciya, ya karaso ya rungume ta ta baya yace mata a kunnen ta kinsan fa yau ke amarya ce, hope you are ready "


*SHUKRAH*ta danyi murmushi tace twins dae suna jinka ni ba ruwa na, Dariya shima yayi ya juya ya kallon su, bacci suke hankali kwance, ya dawo da kallo shi gurinta yace Bawani nn wayo kike son min, ae sun riga sunyi bacci, Dan ture sa *SHUKRAH* tayi sannan ta ja hannunsa suka kwanta suna fuskantar junansu "



"  *safeer* ya kara matsowa jikinta yace mata *i luv u Babe beyond your expectation* "Murmushi *SHUKRAH* tayi tace kayi shiru bacci zamuyi, Matseta *Safeer* ya kuma yi sannan yace tunda nake da ke ban taba jin kince min i luv u ba, kodai har ynx bakya sona  ne"


" *SHUKRAH* tayi Saurin matse hannunsa dake cikin nata haka kuma ta runtse idonta don tana masifar jin nauyin kalmar nan, dakyar ta iya bude baki tace

   *My feelings for you are so strong and deep that i cant convey them in words, because i found no word strong enough to tell you how much i luv u, You are more than amazing, my heart is all yours*~i luv u~"



"tana kaiwa nn ta kifa kanta jikin pillow tana dariya kasa kasa, *Safeer* fa be taba tunanin jin wannan maganar a bakin taba though he's quit sure tana sonsa, tunda dae alamu sun nuna hkn, Saurin dago kanta yayi ya zira harshen sa cikin bakinta ya fara tsotsa cikeda so da kauna da kuma kewarta, kara shigewa jikinsa tayi don tayi missing dinsa sosai 54 days basa tare fa, haka dae suka raya wannan daren"



~~~~~~~~~~~~~~~~~~~




"yau saura kwana biyar bikin *Haiydar* amma bemasan me ake ciki ba, don *hajiya* kobi ta kansa batayi ba, duk wani abu da yakamata da *Safeer*take hatta kayan da zesa suna gidan *safeer* haka ma invitation cards suna gurin sa "


03:25 pm *safeer* ya shigo office din *Haiydar* da sallamarsa ya ajiye envelop kan desk sannan ya zauna yana fuskantar sa, ko kallo *Safeer* be ishi *haiydar*don yana kula da take~takensa, kuma sam zuciyar sa bata aminta da yawan zuwan da *safeer* din yake gidan su "



"  *Haiydar* ga wannan invitation cards din ka ne ko zaka bawa abokanka na gida, don na office na gama basu *Safeer*yace yana nuna masa envelop din daya kawo "



" Murmushin takaichi *haiydar*yayi yana bin *Safeer*da mugun kallo tsawon lokaci sannan ya dauki envelop din ya mika masa yace cikeda takaichi karbi ka fitar min a office kafin ranka ya baci, kuma wallahi ka cire hannunka a maganar nan don gudun bacin rai"

"Dariya Safeer yayi sannan ya mike yace ni bazan karba ba don bana bukatar su, kuma ni bana gudun bacin rai indae akan wannan maganar ne "


" Fita Dalla malam kafin rai na ya gama baci don wallahi komai yana iya faruwa " *Haiydar* yace yana nuna masa kofa, Dariya *Safeer*
Yayi sannan ya fice yana cewa ba lefin ka bane wallahi nanda wani dan lokaci zaka dawo dai dai ae *Auren Bazata Alheri ne*


" Kwanaki sunja kuma gobe za a daura Auren *haydar*amma *Miemie* bata samu labari sai yau din da taji Aysher da Mamah suna maganar, ta zaro ido sannan tazo da sauri ta durkusa kusa da Mamah tace ki kace wae bikin ya Haiydar za ayi da wata banida ta fashe da kuka tace wallahi ina sonsa ina kaunar sa Mamah ku rufa min asiri zan mutu wallahi"



"Aysher ta harare ta tace Dalla can rufe mana baki wae, ina sonsa ina kaunar sa, ke har kinsan wani so "

" Mamah ta janyo miemee jikinta tace yi hakuri kinji Kinga ynx makaranta kike kuma wadda zai aura yar uwar sa ce, kema inkin gama school zai aure ki ae"

"Miemie ta turo baki tace ni wallahi bana son kishiya sai dae ya sake ta ya aure ni, Mamah tace yawwa hk za ayi ke dai ki kwantar da hnkl 'nki kawae, ynx kitashi kije daki ki dauki ankon  ki kan bed ki gwada"


"Mikewa tayi ta nufi dakin tana bubbuga kafa' ni wallahi bazan je bikin kishiya ba... .


"Friday 26 october 2015 da karfe hudu na rana daukacin al'ummar musulmai suka shaida daurin auren *ALIYU KABEER DAN KASA* ( *HAYDAR*) Da amaryar sa *KHADEEJA ABDALLAH MAI KANO*( *ZAFEERA*) Kan sadaki naira dubu dari da hamsin, daurin auren da ya samu halartar manya manyan mutane daga fadin Nigeria kai harma da mak'otan Nigeria, "





Da daddare akayi kayatacciyar dinner ta gani ta fada, abokan haiydar duk sun halarchi dinner din haka ma kawayen zafeera guri ya cika har ba masaka tsinke kasan cewar harda yan gayyar sodi ma sun je, haka akaci aka sha aka tashi mutane sai sawa auren albarka suke "
" Washe gari akayi yini da daddare kuma Aka kai amarya dakinta, misalin karfe goma sha daya na dare haiydar yana mike a dakinsa na gidan Hajiya bama shida niyyar fita, a bangaren amarya Zafeera kuwa har ta gaji da jiran ango ta kwanta ta fara bacci kuma generator ya mutu saboda zafi ya dameta, mikewa tayi ta leko palour amma duhu ya gauraye gurin da kyar ta lallaba ta leka dakin dake kusa da nata, wanda take kyautata zaton na Haiydar ne amma ga mamakin sai taga baya ciki, parlour ta dawo ta zauna amma tsoro ya hana mata sukuni sai take ganin kamar Mutum ne ke giftawa ta gefen ta hakan yasa ta mike jikinta na rawa ta shige bedroom dinta ta dau wayar ta, number Safeer ta nemo tayi dialing, Allah ya taimaka mata kuwa ringing biyu tayi yayi picking 


"Hello Safeer "Zafeera tace murya na rawa, ba tare da ta jira yace wani abu ba ta cigaba
   " Safeer dan Allah kazo ka kunna min generator wallahi tsoro nakeji "

" Shi Haiydar din yana ina? Safeer ya tamvayeta cike da mamaki"


"Nina wallahi ban Sani ba, dan Allah kazo, Zafeera ta Bashi answer tana fashewa da kuka, dan har ga Allah tsoro takeji tunda a gidansu bata saba zama cikin duhu ba "


" To shknn gani nan zuwa ki dena kuka, tare ma zamu tawo da haiydar din kinji safeer yace sanda ya mike ya dau car key dinsa, dakin Shukrah ya wuce ya mata bayanin komai, ta mishi Allah ya kiyaye hanya sannan ya fice da sauri "

" Gidan Hajiyar Haiydar ya wuce direct don ya tabbatar Haiydar yana can, Sanda ya karaso gidan dakin Haiydar ya tura, ae ko ya ganshi kwance yana ta bacci abinshi, Safeer yaja tsaki sannan ya karasa ya fara buga mishi pillow 'nda yake kai da karfi, don iya haushi yau haiydar ya bashi "


" Bude ido Haiydar yayi waze gani in ba Safeer, ya hade rai yace lafiya zaka tashe ni ina bacci "

" Ba lafiya ba Haiydar kai kazo nan hankalinka a kwance kana bacci kabar yarinyar mutane a cikin duhu ko, to wallahi ko ka taso mu tafi ko kuma inje in kira hajiya Safeer yace yana hararar Haiydar "


" Haiydar wanda yasan in aka kiramai hajiya tasa ta kare yayi Saurin mikewa yana hararar safeer sannan yace muje cike da kulewa, tabe baki Safeer yayi sannan yayi gaba, shima Haiydar din takalmi kawae Yasa ya bi bayansa, "


" Cikin mota ba wanda yace da dan uwansa ci kanka kowa sai cika yake yana batsewa, Sanda suka karaso gidan ne Safeer ya kalli Haiydar yace
     "Haiydar Zafeera amana ce a gurinka duk wani nauyi nata da hakkin ta a wuyanka ya rataya, kada ka manta zamu mutu zamu koma ga Allah kuma za a tuhume mu kan duk wani aiki namu, kuma kasan Allah baya yafe hakkin wani akan wani, iya abinda kai masa ne kawae in ka rokeshi gafara zai gafarta maka, Wallahi indae k zalunci yarinyar nan sai Allah ya kamaka karka manta yanzu tun a duniya dan adam yake girbar abinda ya shuka, kuma a hakanma sai Allah yasoka da rahma, kaje kayi tunani Haiydar, kada ka yarda ranka ya baci hankalinka ya gushe, nasan anmaka wannan auren ne ba a son ranka ba wannan aurene na baxata, Amma inaso kayi tunani sosai nanda dan wani lokaci zakaji dadi, yana kaiwa nan ya fice ya koma motar sa ba tare da ya jira answer ba, don ya nada tavbacin nasihar sa ta samu shiga tunda yaga jikin Haiydar din yayi sanyi sosai "



" Generator Haiydar ya kunna sannan Y shiga cikin gidan, Sanda ya shiga ya ganta a takure idon ta harya kumbura don kukan da tashi, take yaji wani tausayin ta ya shige shi nasihar safeer ta dawo mishi ya tuna Zafeera fa yar uwarsa ce Kuma yana daya daga cikin wanda zasuji bakin ciki in wani ne ya aure ta ya wulakanta ta, sannan ya tuna *RAYUWAR SAFEER DA SHUKRAH* Ta da data yanzu, yasan hakuri da juriya shine jigon farin cikin su yaji a ransa yana son dan dana rayuwar kwanciyar hankali da zaman lafiya, shiyasa ma yaji duk tsanarta ta goge a cikin zuciyarsa haka wani sonta da tausayin ta suka mamaye zuciyarsa, saboda haka ya karasa gaban ta ya durkusa gab D ita ya riko hannaye ta duka biyun yana mata wani kallo, tsawon wani lokaci kafin ya bude bakinsa dakyar yace

"Zafeera ki dago ki kalleni, Haiydar ne a gaban ki yake magana, nasan zakiji zafin wannan auren haka kuma zakiyi bakin cikin auren wanda bakya so kuma baya sonki, Ni dan uwanki ne bazan ki kiba, matukar dae zaki cire kowa a ranki ki rungumi kaddara, to insha Allah bazaki samu matsala daga bangarena ba"


"Daga mishi kai kawae tayi alamar gamsuwa daga nan dae yaja hannunta suka shiga daki, sunyi alwala a tare suka gabatarda sallar godiya ga ubangiji haka suka kwanta kowa yana sake saken sa, kai a takaice dae a wannan Daren Haiydar ya zama cikakken namiji don ya dan dani zumar da bai taba dan danar taba ya kuma jinjinawa kanwar sa haka kuma ya samata Albarkar rike mutunci ta da tayi"






"kwanaki sun ja sosai Haiydar ya shiga sabuwar rayuwa ya yarda zagin iyaye yafi zabinka ya tabbatar wa kansa wannan itace Kyakykayawar kaddara haka kuma yayi amman na da cewar safeer a kullum wato( *AUREN BAZATA ALKHAIRI NE*)  "



~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ 

Yau watan twins shida a duniya sun girma sunyi wayo sosai haka kuma kyansu ya dada fito kamar ka sace su, kuma yau Shukrah zata fara aiki a *MARYAM CLINIC* Hakan ne yasata tunda ta tashi tayi sallar a suba bata koma B tanata kiciniyar hada breakfast ga twins sai rigima suke ta rasa inda zata sa kanta ta dauki wannan ta goya wannan sukayi shiru abinsu zuwa can ta ajiye su ae tana juyawa suka kuma fasa kuka, zuciya ta cita ta kwada wa *Labeeba* duka a bayanta ae ko akan idon safeer wannan abun ya faru ya kara so ransa a hade kamar be taba dariya ba ita kanta Shukrah ta tsorata, ya daga  *labeeba* yana jijjagata saida tayi shiru sannan ya juya yana kallon Shukrah da fuskarshi datayi ja saboda bacin rai ya nuna da yatsa yace

"wannan ya zama na farko kuma na karshe dazaki sake dukarmin yara in bakya sonsu ni ina son su, wannan ma ae mugunta ne zaki kama yarinya kina duka me ta Sani? Kuma ki hada min kayan su zan kaisu gidan Mamah kafin in auro wadda zata kularmin dasu, yana kaiwa nn yayi ficewarsa ya barta, ae Shukrah bata san sanda ta zube ba a gurin tana kuka kamar ranta zai fita, tayi data sanin dukan labeeba datayi sau ba a dadi, ganin datayi lokaci yana kure mata yasata mikewa taje tayi wanka a gurguje ta shirya tadau labeeb ta fice a gidan, Gidan Ammii ta kaisa sannan ta fice, Sanda ta karasa asibiti office din *DR. MARYAM ANAS* Ta wuce kai tsaye"


"Shukrah bata wani yi mamakin ganin karamci da mutunci da kuma girmamawar da *Maryam Anas* tayi mata ba don tasan labarinta gurin Ammii, Mamah da Safeer ta babbatar zatayi abinda yafi haka"


" *DR. MARYAM* Da kanta takai *SHUKRAH* office dinta, kuma a gaban ta tafara attending patients, sosai ta ya bawa Shukrah kuma bata boye a cikin ta ba saida ta fito ta fadamata"

"Shukrah nayi mamaki sosai yadda kika iya aiki haka "

" Dariya Shukrah tayi sannan tace ai ban manta ba saboda nasa abun a raina kuma ina karanta littattafai sosai dasuka shafi bangaren ido"


"ae haka ake so Shukrah Allah yayi miki Albarka kinji DR. MARYAM Tace sannan ta fice"

1:35pm *SHUKRAH* ta gama komai saboda hk sai da ta jira 2:00tayi sannan taje tayi wa Dr Maryam sallama, gidan Ammii ta fara zuwa tayi sallah taci abinci sannan ta dauki labeeb suka wuce gidan Mamah, basu wani dade ba tadau labeeba suka wuce gidansu"


"4:35 pm safeer ya shigo gidansa yana wani cin magani wae shi a dole fushi yake da Shukrah, Shukrah wadda take cikin kitchen da gudun ta ta rungume shi tana mishi oyoyo, ya tabbatar baze iya yin fushi da Shukrah ba don ta zame mishi jigo a rayuwar sa, matseta yayi sosai a jikin sa yana kissing wuyanka, zuwa can yadago yana kallon ta, Shukrah ya office da Aunty Maryam hope every thing is moving fine "



" Lafiya kalau Shukrah ta bashi answer sannan taja hannunsa zuwa dakinsa, da kanta ta mishi wanka ta tayashi shirya wa sannan suka dawo parlour tadau labeeb ya dauki labeeba, sunacin abinci suna basu haka kuma suna dan taba hirar su, cikin hirar ne Safeer yake fadawa Shukrah  iyayen DR. MAHMOUD Sun kawo kudin auren Aysher kuma ansa ranar biki nanda wata goma "


" To Allah ya sanya alheri ya kuma sa ayi damu Shukrah tace fuskarta dauke da murmushin jin dadi "



" Ameen ameen likitan ido me bawa mutane glasses, nima idona namin ciwo har bana iya gani sosai yaushe zaki min glass Safeer Yace yana dariya sosai"




"Dariya itama Shukrah tayi tace duk sanda ka shirya ka sameni a office zanmaka daga hk tadau plate din da suka ci abinci tawuce kitchen don wankewa........