AUREN BAZATA PART 3
"Sun dade sosai sunayin sallar, sunawa kansu addu 'ar samun zaman lafiya, Bayan sun idar ne Safeer ya fuskanci Shukra ya fara mata Tambayoyi akan Addinin ta kuma Alhamdulillahi yaji Abinda yake sonji, kasan cewar Shukra Ma' abociyar Addini ce "
" Tashi ki kwanta kinji Shukra "
" To tace sannan ta cire Hijab dinta ta hau gadon ta kwanta "
" Sai da Safeer ya karayin Sallah raka 'a Biyu ya kara rokon Allah kan ya basu zaman lafiya sannan ya musu Addu' ar samun zuri'a dayyiba"
"Daf da Shukra ya kwanta har tana iya jin numfashin sa akan fuskarta, Hakan ne yasa ta Runtse idonta sosai "
" Shafa kan Shukra yake A hankali har zuwa jikinta, Sannan yasa bakinsa akan nata yana tsotsa a hankali "
" Wani nishadi Shukra taji tanaji bata masan cewar ta iya kiss ba sai yau Kawai jitayi ta fara mayar masa da martani "
" Ganin da nayi Safeer na kokarin zame rigar jikin Shukra ne yasa na jawo musu kofar na dawo palour na zauna "
" 4:00Am inata gyangyadi nafara jin kukan Shukra nace barin leka ko za a nemi taimako na "
" A zaune Safeer yake yayinda Shukra ke rungume a jikansa yana aikin lallashi "
" Sannan Shukra kinji kwanta bari na hada miki ruwan wanka "Ya fada yana kwantar da ita"
"Toilet ya nufa ya hadawa Shukra ruwa me zafin Gaske yasa Dettol a ciki sannan ta fito"
"Cak ya daga Shukra be direta ko inaba sai cikin ruwan zafin, Ae Shukra najin ta A ruwan zafi ta Kankame Safeer sosai hade da Sakar masa kuka sosai "
" Hankali tashe shima ya kara Kankame ta yana mata sannu "
" Kiyi hakuri kinji Shukra in kika shiga ruwan zafin nn zaki dena jin zafin kinji "
" A hankali ta gyada masa kai hade da runtse idonta "
" Sai da Safeer ya gama Gasa Shukra sannan ya hada mata ruwa ta tsarkake kana, ya dauke ya maidata kan gado wanda dama ya changer bed shirt din tun tana wanka"
"Toilet din ya koma shima yayi wanka sannan ya fito ya kwanta a kan gado ya jawo Shukra jikinsa yana lallashinta yana kuma gaya mata How sweeter she is "
" A haka dai bacci ya kwashe su dukansu, Sai Asuba sannan suka farka "
" Daga ta yayi Cak kamar dazu ya kaita toilet ya zaunar sannan ya zuba mata ruwa tayi Alwala "
" Jiransa tai yayi Alwalar shima sannan suka fito tare, Shine ya shimfida musu abin Sallah ya daukowa Shukra Hijab tasaka sannan ya tada Ikama "
" Sai da su kayi Nafila raka 'a 2 sannan sukayi Sallar Asuba, kafin suka koma gado suka kwanta rungume da juna "
Shukra ce ta fara yin bacci ta barshi yanata tunanin Daren jiya, Yayi matukar farin ciki da ya samu shukra virgin, Dama yasan Shukra kamila ce ya kuma sa ran samun budurcinta"
Sai gurin 11:15Am suka farka Shukra ce ta mike tana takawa a hankali kamar wata me koyan tafiya tayi hanyar kofa "
" Riko hannunta yayi yana tambayar ta inda zata "
" Zanje kitchen ne ta fada masa kanta a kasa don wani kunyarsa taji tanaji, Batajinma zata iya hada 👀dashi "
" No kibarshi kawai ki koma ki kwanta zansa Aysher tayi mana breakfast din ko Miemie sai ta kawo mana"
"A a ba sai ka basu wahala ba zanyi da kaina"
"Sai yaji ta burgeshi sosai ya kuma kara mata matsayi a zuciyarsa "
" Haba Shukra kinfa gaji taya zakiyi wani girki, Tunda nace zansa Aysher tayi ki hakura kawai "
" Gani tayi bazata iya cigaba da musu dashi ba saboda wani zazzabi daya ke neman rufe ta sai kawae ta cire hannunta a nasa ta koma kan gadon ta kwanta "
" Parlour ya fito ya zauna sannan ya kira Aysher ya fada mata tayi musu breakfast ta aiko miemie dashi Shukra batajin dadi"
"Bayan kamar minti Arba'in Shukra ta fito daga wanka kenan sukaji ana knocking a kofar parlour "
" Safeer ne ya mike daga kwancen da yake ya fita ya bude kofar, Miemie ya gani tsaya a bakin kofa rike da basket "
" Karban Basket din yayi sannan yace 'ki gaida Mamah yana kokarin rufe kofar "
" Shammatar sa tayi a shige parlour' n tana masa dariya, Ae da sauri yayi kanta yana cewa'Zo ki fita malama "
" Da gudunta ta kara sa dakin Shukra ta sameta kwance a kan bed ta lumshe idonta kamar me bacci "
" Aunty wai bakida? Ko dai haihuwa zakiyi ne ta fada tana shafa cikin Shukra tana neman baby"
"Mikewa Shukra tayi zaune ta cire hannun Miemie dake kan cikinta "
" Miemie ina Mamah?
"Tana Gida tace na gaisheki "
" Ina Answer wa "
" Miemie Harda kara matsowa kusada Shukra tana tambayarta
'Aunty wae inji Anty Aysher wae bakida lafiya?
'Aunty ciki ne da k..... "
"Shigowar Safeer ne ya katse wa Miemie surutun ta"
"Har gaban Miemie yazo yaja kunnenta har sai da tayi kara yace
"Wae me yasa bakya jin magana ne, Ba ce miki nayi ki tafi gida ba shine harda fakar ido na ki shigo da gudu kina min dariya ko"
"Yi hakuri yaya dan Allah Sakar min kunne da zafi fa ta fada tana goge kwallar data zubo mata, Dan sosai take jin zafin rikon da yayi mata "
" Bazan sake ki ba sai kin fada min me kike cewa kika ganni kikayi shiru"
"Shukra ce ta janyo miemie tana goge mata hawayen fuskarta"
"Kai ya Safeer yanzu kan tazo muna hirar mu shine zaka sa ta kuka fisabilillahi Shukra ta fada kanta a kasa hk kuma murya can ciki don sosai take jin zazzabi da ciwon kai "
" Ni Gulman tane banaso shiyasa ya fada yana fita daga dakin"
"Tare sukayi breakfast din harda Miemie dan dama batayi ba ta tawo "
" Zazzabin daya rufe Safeer ne yasa shi yin bacci, sai bayan la 'asar sannan ya farka yayi sallah ya koma bacci"
Ganin duk suna bacci ne yasa miemie tayi musu Tuwon semovita miyan agushi tasha busashshen kifi da ganda😋, A flask tasa tajera a dinning sannan ta koma dakin Shukra ta samu bata tashi a bacci ba "
" Kayan jikinta ta cire tashiga toilet tayi wanka, Ta fito ta shirya sannan ta koma parlour ta zauna tana jiran Safeer ya tashi ya maidata gida"
"Sai bayan magrib dukansu suka farka inda Safeer ya jasu sallah dan bayajin ze iya zuwa masallaci "
" Sai da sukayi Dinner ne Safeer yace Miemie ta taso ya maidata gida dan yasan inya barta zata iya cewa zata kwana"
"Dukansu suka fito harabar gidan, Inda Shukra ta shiga gaba Miemie kuma baya suka kama hanyar gidan Mamah.............
"Cikin lokacin da be wuce minti Arba 'in ba suka karasa gidan Mamah "
" A tare suka shiga cikin gidan dukansu inda suka tararda da Aysher kadai a parlour tana karatun wani hand out "
" Mikewa tayi da fara' ar ta ta riko hannun shukra suka zauna sannan ta shiga gaida ta cike da ladabi "
" Sama taje ta kira Mamah sannan ta dawo suka cigaba da hirar su, Bayan kamar minti 3 sai ga Mamah Da Abbah sun sauko a tare "
" Shukra ce ta sauko daga kujerar da take suka shiga gaisawa da surikanta Kanta na akasa, Sannan Safeer ma ya gaisa da iyayen sa "
" Shukra ya jikin "Mamah ta tambaya
" Jiki Alhamdulillahi ae naji sauki "
" To Allah ya kara lafiya "
" Ameen suka ce dukansu kafin Aysher ta tashi ta kawo wa Shukra ruwa da lemo "
" Da kinbarshi ma Aysher muda zamu tafi yanzu ta fada kasa _ kasa kuma a kunyace"
"Lah bakomai Wallahi Aunty "
" Bayan kamar minti goma Safeer ya mike. Yana duba agogon hannun sa
"Tashi mu tafi Shukra dare nayi fa"
" a a kabarta Anan mana tadan kwana biyu tunda bata jin dadi "Inji Mamah"
"Jiyayi zuciyarsa tabada wani Dum, Aiko ya hade rai A a Mamah dan Allah ki bari mu tafi ae taji Sauki ya fada yana Riko hannun Shukra "
" To marar ta 👀 cewa akayi ra 'a rike tane wae kake wani cin Magani "
" Ba hk bane Mamah nima fa banida lpy ina bukatar kulawar ta nima dan Allah kiyi hakuri "
" Miemie! Miemie dauko min key din dadin Safeer kizo ki bude masa "
" Mamah tace sannan ta juya tana kallonsa "kai ma sai ka zauna a nn din a kula daku gaba daya tunda bakada lafiya"
"Komawa yayi ya zauna hade da dafe kansa yana magana da zuciyarsa
"Mamah BAZATA gane irin son danakewa yarinyarnan bane tayama zan iya barinta ae inma yazama dole ta zauna nima ko zama zanyi"
"Abbah ne ya kalleshi sannan ya dawo da kallon sa gun Mamah.
"Mamah ki barsu su tafi mana tunda ta samu sauki ko, Kuma shima yace bayajin dadi yana bukatar kulawar tafa "
" Aiko ko zasu tafi sai dai suje da Miemie ko shara da wanke wanke ta dinga tayasu tunda basuda lafiya "Inji Mamah"
"Safeer ne yayi saurin dawowa kusa da Mamah 'Dan Allah Mamah ki barta baseta jeba, (Shi harga Allah bayason zuwan yarinyarnan gidan sa)
"Sai fa taje, In ko BAZATA jeba sai dai kabar Shukra anan, Dan ba ta yarda za a bar me yaron ciki tana wahalar da kanta "
" A zuciyarsa yace kowa yace mata Shukra cikin da ita, A fili kuma yace To naji Mamah amma dan Allah ki bamu Aysher wannan yarinyar ba abinda zatayi mana wallahi "
" Bawani nn kaidai kawae baka so najene amma naga yau ni nayi muku dinner akaci ana santi Miemie tace tana hararansa "
" Pillown kujera ya jefa mata sannan yafara magana yana huci (wai shi ransa ya baci) "
" Yaushe nafara wasa dake wae miemie, wallahi zan gyara miki zama, mayyata kawae nace bazaki kin dage sai kinje "
" Kome zakace sai dai kace amma saita je Mamah tace sanda tamike tayi hanyar room din su Aysher dan hadawa Miemie kayan tafiya "
" Yi hakuri kaji Safeer addu 'a zakayi mata Allah ya shirye ta inji Abbah "
" Yanzu saboda Allah Abbah yarinyar nan abinda take ya dace shekara goma sha biyu ae ba wasa bane, Ita Aysher sanda tana shekarun Miemie haka tayi wallahi sai na gyara mata zama in tazo gida na "
" Hakuri zakayi Kaji Safeer kidinga yimata fada da nasiha amma banda duka "
" Fitowar Mamah rike da trolley ne miemie na biye da ita yasasu yin shiru, Miemie sai dariya takewa Safeer shi kuma yana watsa mata uwar harara, Aysher da shukra ma dariya suke "
" Mikewa sukayi dukansu suka fito dan yimusu rakiya, sai da motarsu ta fita daga get din gidan sannan su Mamah suka koma "
8:20pm suka karasa gida Safeer ne yafara shiga gidan sannan shukra janye da trolley 'n miemie a bayanta kuma miemie ce sai muxurai take tasan haduwarta da Safeer ba sauki"
"Sai da Shukra takai Miemie dakinta ta sata tayi wanka ta fito ta shirya ta kwanta ta yi mata add' a, ta kashe mata switch din dakin sannan tayi dakin Safeer "
" Sanda ta shiga ta tarar har yayi wanka yayi bacci, Wankan itama tashiga inda bata wani dau lokaci ba ta fito tayi joining Safeer a bed "
" Karfe 3:00dai dai zazzabi ya damu Safeer ya tashi yana ruwan sanyi, Bayan son ya tashi Shukra shiyasa ma ya sauka akan bed din "
" Kamar ance Shukra bude idonki ta farka ga mamakinta bataga safeer akan bed ba sai tayi tunanin ko toilet ya shiga "
" Bayan kamar minti biyar ta mike da niyar zuwa toilet din ta duba shi, can ta hangoshi kwance akan center carpet "
" Da sauri ta karasa gurin shi ta da goshi ae batasan sanda ta sake shi ba saboda wani xafi da taji jikinsa yayi (tsaf za a gasa masara tsabar zafin da jikinsa yayi lols) "
" Sai sannun take jera masa duk tabi ta ruda kanta "
" Shukra ki kwantar da hankalin ki zazzabi nefa kawai "
" Ya Safeer zazzabi ne kawae fa kace "Ta fada tana mikewa ta shige toilet"
"Hannunta rike da wani dan karamin farin towel da kuma wani bowl cikeda ruwa ta fito takaraso wajensa"
"Dago kansa tayi ta dora akan cinyarta sannan ta cire singlet din jikansa ta sa towel din a ruwan ta matse sannan ta fara goge mai jikinsa "
" Haka ta dinga yi masa har sai da taji jikinsa yayi sanyi sannan ta maida bowl da towel din toilet "
" Ko kafin ta fito har Safeer yayi bacci a gurin, Ganin bazata iya maida shi kan bed din ba ne yasata kwanciya a kusa dashi da daura kansa a Hannunta (Yadda akewa yaro in xeyi bacci) Ai bata wani dade ba baccin ya dauketa itama "
" Da asuba safeer ne yafara tashi shi kwanciyar tasu ma dariya ta basa kamar wani danta"
"Sai da yayo alwala sannan ya dawo gurin Shukra, Daga ta yayi a hankali yadda bazata firgitaba "
" A hnkl take bude idonta akan Safeer, Murmushi yake mata itama haka, Addu 'ar tashi daga bacci yashiga karanto mata, Binsa tashiga yi har suka gama sannan ya rakata har bakin toilet din ya dawo yana jiran Fitowar ta "
" Sai da je tashi Miemie tasata yin Alwala sannan suka dawo dakin safeer yasasu Sallar "
" Duk su ukun a gurin suka kwanta sai gurin 9:15 shukra ta tashiga tashiga toilet don yin breakfast "
" Ruwan zafi ta dafa tasa cikin tea flask ta debo kayan tea ta jera su a dinning sannan ta dawo kitchen tafara musu Gireba, wadda zasu hada da tea"
"Bayan ta gama ne taje ta tashi miemie ta hada mata ruwan zafi tasata wanka, Sannan itama tashiga wanka a dakin Safeer "
" Bata fito ba sai da shima ta hada masa ruwan wankan sannan ta fito ta tarar ya tashi a bacci ma "
" Ya safeer ka tashi lafiya "
" lafiya kalau "
" Ya karfin jiki kuma "
" Alhamdulillahi "
" Masha Allah, ka shiga na hada maka ruwan wanka "
" To nagode Shukra Allah yayi miki Albarka "Ya fada yana shiga toilet"
"Wata Ash colour jallabiyya tasa ta daura bakin dankwali tashafa powder da maroon lipstick ta fito parlour tasamu Miemie suka fara hira abinsu "
" Dukansu nagani a kan dinning suna breakfast Miemie nayiwa Shukra labarin Haiydar sunata dariya abinsu "
" wayar Shukra ce ta fara ringing, Duk suka juyo suna kallon wayar sai da Shukra ta fasa ihu sannan ta dauki wayar "
" Hello Neesa luv "
" Bawani Neesa luv munafika kinyi Aure kin manta mutane ko"
"Haba dae Aneesa ni na isa na manta ki ne, kiyi hakuri dan Allah tafada kamar zatayi kuka"
"Ke kika Sani, Dama fada miki zanyi anjima zamuzo sai kimin sending address naki"
"Yanzu ma kuwa shukra tafada cikeda murna, Baki fadamin kedawa zaki zo ba"
"Ni da DR. Sumayya wannan wadda ta tafi sudan din "
" Na ganewa, Dawa kuma?
"Da soofy galadanchi, Da Aysher bichi, da Aunty Ameena kaura, Da Eeshatullah da fancy da Ma sultan da Aunty sis da meela adeel "
" Ihu ta saki ashe yau inada manyan baki a gidan, ME kuke so na girka muku "
" Bamuda zabi mudai inji Neesa "
" Yawwa Neesa naji kamar kince da meela adeel za a zo "
" Eh meye"
"Dan Allah ki rufa min asiri kar tazo tamin snatching Irin yadda taso tayi wa Ruky mama "
" Hhhh ni ban iya rashin mutunci ba bazan iya cewa bazamu zo da ita ba, Kema da kinsan irin rokon da ta dinga min azo da ita da baki ce hk ba "
" jiki a sanya ye SHUKRA tace to Neesa luv sai kunxo, Ta kashe wayar tana bawa Safeer labarin yau sunada Manyan baki a gidan "
" Tare suka shiga Kitchen ita da Miemie, steamed cous - cous da Egg sauce suka farayi sannan sukayi fried rice sukayi Banana, coconut and pineapple Drink suka sa a fridge sannan Shukra tashiga wanka don sun mata waya sun tawo, Tabar Miemie tanayin liver sauce...........
"Bayan kamar minti goma Miemie ta gama liver sauce din ta shige toilet don yin wanka ita ma "
" Shukra da Miemie ne kadai a parlourn suna kallo kuma suna jiran zuwan Manyan bakin su "
" Knocking din dasuka ji a kofa ne yasasu mikewa dukansu suna rige rigen bude kofar, Shukra ce tayi nasarar bude kofar ae ko sa Aunty sis ta fara cin karo, Rungumeta tayi tana murnar ganinta don she really missed her "
" Basu guri tayi suka shigo parlourn suka zauna, Meela se karewa palour kallo ake, Miemie ce ta durkusa har kasa tana gaida su daya bayan daya "
" Shukra ce ta shiga kawo musu drinks da bottle water, Bayan sun gaisa da shukra kuma sai suka tsinke da hirar yaushe gamo"
"Shukra a ina kk aiki ne "Soofy ta tambaya"
"Ke ni bana wani Aiki, Aikin gidan miji na nake "
" Shukra knn meyasa bazaki sa ya nema miki aiki ba ko a nn Maryam clinic ne da kuke kusa "
" Ke nifa Aikin ya fita a raina, Amma dae zan gwada "
" Sai bayan zuhr prayer sannan Miemie ta Fara kawo musu Abinci, Neesa ce tayi service nasu suka fara ci suna santi (Kunsan ni na koya ma Shukra girki dole suji dadin sa) "
" Shigowa Safeer yayi da Sallama a Bakinsa ya durkusa har kasa yana Gaida Aunty sis, Bayan sun gama gaisawa ne kuma su soofy Galadanchi, Neesa luv, DR. Sumayya suka fara gaida shi cike da ladabi, Sosai ya yaba da Hankalin kawayen Shukra "
" Meela dai batasan sanda glass cup din hannunta ya fadi kasa ba gurin kallon Safeer (Snatcher anga HANDSOME guy 🤣) "
" Juyowa sukayi dukansu suna kallon meela da mamaki, Shukra ko hade rai tayi tana kallon Meela kafin ta juya taja Hannun Safeer ta shige Bedroom dinsa dashi "
" Meela wae har ynx kina nn da halinka saboda Allah, ki sa Mutum a gaba da kallo har da fasa cup inji Aneesa Rai a bace "
" Nan dai suka sa Meela a gaba suna ta mata fada, Aunty sis tace suyi shiru duk sukayi kuwa "
" Nasiha tashiga yiwa Meela me ratsa jiki,(Uwar Arziki) Har kuka sai da Meela tayi tana bawa Aunty sis Hakuri tana kuma tabbatar nata ta dena Halinta "
" Hade rai tayi tana watsa wa Safeer harara 'Ya safeer ba seda nace karka dawo gidan ba sai sun tafi, Amma shine ka dawo ko?
"Haba Shukra me yayi zafi wae haka nifa zuwa nai mu gaisa da Aunty sis "
" Bata kara cewa komai ba ta juya ta fice tana huci"
" Shukra ce ta fito tana huci taja Hannun Meela ta turata waje sannan ta nuna ta da dan yatsa 👉🏻kada ki kuskura koda wasa ki kara zuwa gidan Daga hk ta rufe kofar ta ta dawo suka cigaba da hirar su da kawayenta "
" Sai da sukayi sallar La 'asar sannan suka tafi inda Shukra ta cikasu da tsaraba, Suka tafi suna murna, Suna fita Soofy Galadanchi ta dawo tana tanbayar Shukra ta koya mata yadda ake Garnished cous - cous "
" Karki damu Soofy anjima mu hadu online zan koya miki "
" Godiya tayi mata sannan tafice inda ta samu suna jiranta, daga nn suka wuce gida "
" Tunda Shukra ta shiga daki bata fito ba sallar Magrib ma a daki tayi ta har ynx bata gama hucewa ba kan abinda Safeer yayi mata, Tace kar ya dawo saboda tana kishinsa bataso wata mace ta kalleshi, Office ma da dahali da ta hanasa zuwa, Amma sai da ya dawo "
" Da sallamar sa ya shiga dakin Shukra ya hango ta can karshen gado ta kifa kanta jikin pillow da alama kuka take "
" Da sauri ya karasa kan bed din ya dagota ya Rungume tsam a jikinsa yana bubbuga bayanta "
" Batayi wani yunkurin kwa cewa ba sai ma kara kankame shi da tayi don dama hakan take bukata a halin yanzu, So kawai take ya lallasheta ya bata hakuri ko taji sanyi a ranta "
" Yi hakuri kinji Shukra cute, Kidena zubar da hawayenki a banza bayan nace miki Mazaunin mace HUDU kike a gurina, Ba wadda ta isa na kalleta bayan inada ke, Cry no more swthrt kinji "
" Wata nannauyar ajiyar zuciya ta saki batasan sanda murmushi ya kubuce mata ba, Ta wani kara narke masa "
" Nagode Ya safeer "
" Murmushi shima ya sakar mata ya shafa fuskar ta yace 'Ashe kina sona har haka Shukra, irin wannan kishi Haka "
" Harara ta watsa masa irin ta wasan nn sannan tace' waye yace maka ina sonka "
" Kishin da kika nuna da kuma kukan da kike kan wata ta kalleni yasa nagane kina sona "
" Hannayenta Biyu tasa ta rufe idonta cike da kunyar sa, tana dariya kasa kasa "
" Dagata yayi suka sauko daga bed din suka fito parlour hannunsa rike dana Shukra "
" Sai zuwa 10:00pm suka tashi Miemie tayi dakin Shukra sukuma sukayi dakin Safeer don yin Bacci "
" Washe gari Wajen 12:00am bayan sun gama breakfast Shukra tace zata Gidan Ibteesam, Tare suka tafi da Miemie suka bar Safeer kadai a gida yana cigaba da Aikin Construction na company da yasamu "
" Wayarsa dake kan center table ne tashiga ringing, Karasawa yayi ya dauka da Sauri ganin Haiydar ne me kiran "
" Assalamu alaika Haiydar ya kk ya Hajiya "
" Lafiya kalau muke Safeer me kirki cikin kwanta goman da kayi kana hutu baka taba kirana a waya ba koda wasa, Amarya ta mantar da kai mutane ko"
"Eh ta mantar din in kayi zuciya kaima kayi AUREN "
" Karka damu nanda Shekara uku zanyi Aure Miemie nayin Graduation (Candy), "
" Ka wahala wallahi Haiydar lokacin ina nn da dan yaro ma "
" Kai ka Sani nidai AUREN SOYAYYA zanyi ba AUREN BAZATA Haiydar ya fada yana dariya "
" To sai me ae AUREN BAZATA Alheri ne, duk wanda beyi Auren bazata ba ae be ji dadin Aure ba wallahi "
" Hhhhhhhhh a hakan "
" Nidai yanzu ba wnn ba jiya mutumin daya baka Aikin Company a san Francisco yaxo munata kiranka bakayi picking ba, So yace next week yakeso a fara Aikin so saika zama cikin shiri ko"
"Eyya kuyi hakuri kunsan in ana tare da Amarya ba a iya komai amma insha Allah zan kirasa muyi magana "
" Kai ka Sani jibi dai zaka dawo Aikin ae inji Haiydar wanda yana gama fadar hk ya kashe Wayarsa "
" A nn Safeer ya kira mutumin suka gama mgn kan Next week ze tawo san Francisco "
" Sanda su Shukra suka dawo Safeer ya basu labarin komai, Zo kuga tsalle gurin Miemie za aje inda ba 'a taba zuwaba ko a mafarki "
" Ke kuma Ihun me kike hk, To ba inda zani dake Anan kinzo kin shiga rayuwar mu shine kike so ki bimu can a cigaba da samana eyes ko "inji Safeer yana hararan Miemie"
" Fasa masa ihu Miemie tayi ni wallahi sai kunje dani "Shukra dai batace komai ba sai kallonsu take
" Baki sake Safeer yake kallonta, Wani sabon salon iskanci ne wnn kuma Miemie? To wlh zakiyi kuka me dalili kinji ya fada yana murde mata bakinta "
" Shukrah ce ta janye ta tana lallashinta "
" Kai ya Safeer dan Allah kawai kasata kuka ana zaune kalau, In bazaka jeda itaba kace bazani da keba ba saika sata kuka ba "
" komai beceba sai daukan car key dinsa da yayi ya fice daga gidan ya tafi gidan Mamah ya fada mata, Sosai suka tayashi murna tare da yimasa fatan alkhairi "
" Bayan yabar gidan Mamah gidan Ammii ya wuce wanda cikin sa 'a ya tarar da Daddy, Nan suma yayi musu bayanin tafiyar sa sukayi masa Addu' a sannan ya dawo gidansa ........
"Yau ta kama Monday kuma yau Safeer ze koma Aiki saboda hk Shukra tunda tayi sallar Asuba bata koma ba tashiga Kitchen don hada musu breakfast "
" Sweet potato ta soya tayi egg sauce sannan dafa ruwan zafi tasa a tea flask ta jera a dinning sannan ta shiga dakinta donyin wanka "
6:50am Safeer ya turo dakin Shukra cikin shirin sa na fita office, Ita kuma lokacin ta fito a wanka knn tana shafa cream a jikinta"
"Wae har ka shirya ya Safeer ta fada cike da Mamaki "
" Eh mn zokiyi serving dina breakfast na wuce sauri nake yau Ahmad zezo "
" Waye Ahmad kuma "
" Wanda zanyiwa Aikin company a san Francisco mana "
" ok, To jirani insa kaya sai inxo "
" To, miemie bata tashi bane ita "
" Eh itada ba fita xatayi meye nata na tashi da wuri haka, "
To kiyi sauri dae kizo ya fada yana fita daga dakin"
"Bayan Safeer ya gama breakfast sai da Shukra ta rakasa har mota ta jira ya fita a gidan sannan ta dawo ta fara gyaran gidan "
" 12:00pm Ahmad yazo Office din Safeer kuma sun gama mgn kan cewa ran friday zasu tawo san Francisco, Sosai yaji dadi yadda Safeer ya karbi Aikinsa ya kuma yi masa alkawarin zuwa akan lokaci "
" Yau saura kwana 2 tafiyar su Safeer saboda haka yace Shukra ta shirya kayan Miemie su Maidata Gida da daddare "
" Bata rai Miemie tayi wane zatayi kuka, Sai hararar Safeer take kasa kasa, karaf suka hada ido "
" Zo nan Miemie ya fada rai a hade "
" Kukan shagwaba ta saki taje ta makale a jikin Shukra kamar karamar yarinya "Aunty Shukra Kinga yaya ze dakeni ko
" ME kika yi masa Shukra ta tambaya tana kallon Safeer da Fuskar tausayi (Irin kar ya daki Miemie) "
" Harara na tayi ya bata Answer yana dauke kai "
" Shukra ta dawo da kallonta kan Miemie wadda take ta zare ido kamar tayiwa sarki karya, Miemie bakya jin Magana ko kina abun kamar karamar yarinya, Ya Safeer din sa 'ankine da kike hararar sa?
" A a Aunty Shukra yi hakuri bazan kara ba "
" Kima kara, Shukra ta fada tana jan hannun Miemie zuwa daki "
" Koda suka shiga dakin kayan Miemie suka hau hadawa, Sosai Shukra ta yiwa Miemie nasiha kan halayenta, Da alama nasihar ta shige ta don har kuka sai da tayi tana bawa Shukra hakuri "
" Tun 7:00 pm suka tafi gidan Mamah maida Miemie, Mamah tayi mamakin nitsuwar Miemie don yan kwana kin da tayi a gidan Safeer sosai ya ke mata fada, Shukra kuma tayi nasiha "
" Sun dade gidan don se wajen 11:00 su Aysher suka rakasu mota suka tafi gidansu"
"Washe gari Da Safeer zai tafi Office sai da ya sauke Shukra a gidan Ammii sannan ya wuce "
" 4:30pm Safeer ya shiga Office din Haiydar da sallama a bakin sa, Ya samu guri ya zauna yana fuskantar Haiydar "
" Malam wae yaushe zaka fito da mata ne kayi Aure, ko baka gaji da zaman gidan Hajiya ba?
"sai nan da shekara uku meye matsalar ka?
"Kaga Malam in zaka dawo hayyacinka ka dawo Miemie fa tayi maka kankanta kabarwa Abdallah kawae ka nemi wata "
" Bazan bar masaba yaje shima ya nema mana inji Haiydar ya fada rai a bace "
" To na fahimce ka bakada Budurwa ne shiyasa, Ko kanason Aysher na baka ita "
" Banason ta ni Miemie nake so kuma ko kaine babanta baka isa ka hanani AUREN taba" Haiydar ya fada sanda ya mike yana tattara kan table dinsa "
" ni na isa na hanaka auren Miemie? Allah ya baka Hakuri zo muje gidan Ammii zan dauko Shukra sai ku gaisa ma "
" To kawai yace sannan suka fito a tare kowa ya shiga motar sa suka kama hanyar gidan Ammiii "
" Sanda suka je gidan Ammii ana kiran sallar Magrib saboda haka basu shigaba sai da sukayi sallah a wani masallaci kusada gidan "
" Sai bayan sallar isha sannan suka baro gidan Ammii, Areef harda kukansa (Kukan rabuwa) "
" Washe gari Safeer beje Aiki ba fita yayi yayo musu siyar yar duk wani abu dayasan zasu bukata kuma bazasu samuba acan "
" Da yamma wajen karfe biyar Safeer da Shukra kwance akan gado rungume da junansu suna hirar su ta masoya akayi Knocking a kofar parlour "
" Safeer ne ya mike yasa rigarsa sannan ya fice don duba waye "
" Yana bude kofar yaga wata yarinya kamar Shukra take da yarinya a hannunta, Yarinyar na ganinsa ta fara mika masa hannun alamar ya dauketa tana kiransa da Daddy"
"Hannu yasa ya karbeta sannan suka gaisa da Mamanta, Guri ya bata ta shigo parlourn sannan ya wuce bed room din Shukrah don kiranta "
" Da fara 'a dauke a Fuskar ta ta karaso parlourn "Sannu da zuwa Ibtee, ya Gida ya Amal?
" Lafiya kalau muke, ae Amal fushi take dake tunda kin dena zuwa gurinta "
" Eyya Amal tayi hkr tana raina wlh, Naga ta makale wa ya Safeer kamar ta sanshi "
" Ae da alama mijin kin nn yana son Yara da yawa, Yaushe za haihu ne Ibtee ta fada tana neman daga rigar Shukra "
" Rike Hannun Ibtee Shukrah tayi tana dariya, Ke ni banida ciki fa "
" Zama ki fadi gsky ne "
" Daga nn Shukrah ta mike ta kawo wa Ibtee lemo da ruwa "
" Sai da aka kira sallar magrib sannan Safeer ya kawowa Ibtee Amal yawuce Mosque, itama gidanta ta tafi"
"Zuwan Ibtee ne ya hana Shukrah hada musu kayan su sbd hk bayan sun gama cin abinci sunyi sallar isha shukra ta shiga daki don hada musu kayan "
" A tare suka hada kayan da Safeer sannan sukayi shirin bacci don jirgin karfe bakwai zasu bi "
"Safeer ne ya musu addu ' a ya tofe musu jikinsu sannan suka kwanta rungume da juna"
"Yimin labari me dadi Shukrah, Safeer ya fada mata a kunnenta "
"Ya Safeer ni ban iya lbr ba sai dai kai ka yimin, Shukra ta fada kasa kasa"
"To zan miki wani iri kike so "
" Kowanne ma "
" Nan Safeer ya fara mata labarin cikin kunnenta "
" Sai dariya Shukrah take kyalkyalawa tana kara shigewa jikinsa, a takaice dai sai da Suka raya daren ranar, "
" Tun kafin Asuba Suka farka sukayi wanka sukayi nafila suka jira sallar Asuba, Tea kawae suka sha suka sa kayan su a booth suka tafi gidan Mamah "
" Aysher da Miemie suka dauko sannan suka wuce Airport "
" Jiran minti goma sukayi sannan aka kirasu, Suka wuce suna daga musu hannu, Zo kuga kuka gun Miemie harda birgima a kasa wae kar Shukrah ta tafi ta barta "
" Aysher ce taja motar ta maidasu gida har amotar Miemie kuka take, suna zuwa gida ta kwanta a parlour sai bacci.......
"Cikin jirgi Shukra sai bacci takeyi daga Zaunen da take, Safeer ne ya kwanto da ita jikinsa dan tafi jin dadin baccin"
"Ko da aka kawo musu abinci ma be karba ba don yasan Shukra bazata ciba, kuma dama shi bayajin yunwa, Cigaba da Aikinsa yayi har suka isa San Francisco "
" Jirginsu na landing Shukra ta farka tana raba ido, Mikarda ita safeer yayi suka sauko a tare "
" Wayarsa ya dauko ya shiga dialing number Ahmad, Wanda tana fara ringing ya dauka don dama sunyi waya da safeer ya fada masa sun kusa sauka "
" Mota Ahmad ya dauko yazo ya samesu a zaune kan resting chairs na airport din, safeer na ganinsa ya mike da fara 'arsa sukayi musabaha kafin suka gaida da Shukra "
" Nan ya kwashi trolley dinsu yasa a mota suma suka shiga suka kama hanyar gidan sa "
" sun samu tarba ta musamman gurin matarsa Azeeza, Yar Nigeria ce itama, bayan sun ci abinci ne kuma Safeer da Ahmad suka fita dan ganin inda za a gina Company 'n sukabar Azeeza da Shukra suna hira kamar dama can sun san juna "
" Har dare basu dawo ba, Abinda ya daga hankalin shukra kenan sosai take son ganin mijinta, wayarta ta dauka da niyyar kiransa sai kuma ta tuna batada number sa, Dan karamin tsaki taja kamar zatayi kuka wae batada number mijinta (Abin takaici) "
" Azeeza ganin dare yayi sosai kuma dawowar Ahmad ba yanzu ba yasa ta nunawa SHUKRA dakin da zata kwanta, Ita kuma ta shige nata, Zaman kusan awa biyu Shukra tayi amma shiru Safeer be dawo ba sbd hk ta shige daki kawai ta kwanta "
" Shiru tayi bayan ta kwanta zuciyar ta cike da tunanin Safeer, Batajin zata iya bacci ba a jikin Safeer ba juyi kawai take a kan gadon sam bacci ya ki zuwa, Ahaka dae bacci barawo ya kwashe ta "
" Cikin bacci taji ana shafa ta tai saurin bude ido don dama baccin beyi wani nisa ba "
" Cikeda shagwaba take kallon sa idonta taf da hawaye
"Ya Safeer shine kaje kayi zaman ko, Ka barni inata jiranka" Tafada tana fashewa da kuka
"Jawota yayi jikinsa yana bubbuga bayanta a hankali
"Yi hakuri Shukra cute kinki insha Allah gobe bazan dade ba yau dinma dan farko ne bakiga guraren da mukajeba, Amma wallahi kina raina sai tunanin ki nake"
"Murmushin jin dadi tayi ta kara shigewa jikinsa 'kaci abinci ya Safeer?
"Naci dazu Shukra yanzu wanka zanyi "
" A tare suka mike suka shiga toilet din ya tsaya a gefe ita kuma ta hada masa ruwan wanka "Bitayi jefensa zata wuce yayi saurin rike hannunta"
"Ina zakije kuma ya tambayeta kasa kasa yana kashe mata ido daya "
" Zanje in fito ma da kayane fa ta bashi Answer tana kokarin kwace hannunta "
" Kara damke hannun yayi 'ki bari muyi wankan mana "
" A a ya Safeer nifa nayi tun dazu "
" Ban yarda ba sai kin sake "
" Kasa cigaba da jayayya dashi tayi dan haka kawae sai ta rufo musu kofar toilet din ta dawo ciki "
" Safeer ne ya shiga ciremata kaya, ita ko kunya duk ta hana ta sukuni sai sunkuyar da kanta take, haka dae ya gama cire mata kayanta tsaf shima ya cire nasa ya hau jikata da ruwa "
" Itama jikashi ta fara yi suna dariya abinsu, A hk dae suka soma wanke junansu wanda tun Shukra na nokewa har sai da ta saki jiki "
" Safeer na gani ya fito daga toilet dauke da Shukra a hannunsa kamar wata baby ya nannade ta da towel, Karasawa yayi ya kwantar da ita a tsakiyar gadonsu sannan yaje inda trolley 'nsu ya dauko cream ya dawo kan gadon "
" Kunce towel din jikinta ya shiga yi inda Shukra ta runtse idonta, Shiko ko a jikinsa sai da ya cire mata towel din gaba daya sannan ya soma shafa mata cream din cikin wani salo me wuyar fassaruwa yake shafa mata, Shukra dai jinta tayi kamar ba a duniya wani irin abu ne taji yana yawo a jikinta, batasan lokacin data janyo hannun Safeer ba ya fada jikinta "
" Nan suka shiga kissing junansu cike da kaina wane zasu cinye kansu, Romancing kansu sukayi tayi kamar ba gobe, Niko ganin haka yasa na fito na barsu susha love "
" Washe gari tun 7:00am Safeer da Ahmad suka bar gidan har dare Shukra nata baza ido ba labarin Safeer, Hawaye ne ya cika idonta tanason ganin Safeer tana tsananin bukarsa, Gashi ta manta bata karbi number sa ba "
" Ganin kuka na neman cin karfinta yasata mikewa da sauri tashige daki, Kwantawa tayi kan gado ta rungume pillow tana kuka mara sauti "
" Karar wayarta ne ya katse mata kukanta, kamar bazata dauka dan saida yazama missed call ma sannan ta dago wayar ganin Aneesa ce me kira yasata saurin dialing "
" Ringing biyu Neesa tayi picking
"Hello Neesa luv ta fada can ciki"
"Shukra Y kk, Ya jikin kuma?
"Jikin me kuma Neesa nace miki banda lafiya ne?
"Muryanki ya fada min bakeba "
" Keni lafiya na kalau "
" uhmm, Yaushe zaki haihu ne Neesa ta tambaya tana dariya kasa kasa "
" Wani irin Haihuwa ana zaune kalau ae ni sainaci amarchi na kamar shekara 2or 3 kafin na fara haihuwa "
" Koba shekara biyu ko uku ba Neesa ta tambaya tana dariya sosai "
" Dariyar me kuma haka Shukra tace wane zatayi kuka "
" Jinayi kince shekara uku Shukra wa yasani ma ko yanzu kinanan da katon cikin ki, Zama da kyar tashi dakyar Aneesa ta bata answer "
" Dogon tsaki kafin ta kashe wayar ta ta kifa kanta jikin pillow ta cigaba da tunanin other half nata "
" Tanaji Neesa nata kiranta amma batabi takai ba ta cigaba da tunaninta tana addu a Allah yasa kar yau ya dade kamar jiya "
" To yau kam Su Safeer sun dawo da wuri dan agida sukayi sallar isha, Bayan sun idar sukaci abinci sannan kowannensu ya shige dakinsa "
" Shukra bako kunya ta tashi tabi bayan Safeer inda ta tarar harya shige toilet, Azeeza ma ganin Shukrah ta mike yasata itama mikewa tabi bayan Ahmad "
" Sai da Safeer ya kira Haiydar sukayi hira sosai, Sanda sukayi sallama ne Haiydar ya fara tambayar Safeer Shukra "
" Safeer ya dawo da kallon shi kan Shukrah dake kwance akasa ta nannade kafafunta da nashi kamar mejin sanyi,Gashin kanta ya rufe mata fuskarta, Hannu yasa ya ture Gashin gefe ya dago kanta, sai anan ya gane ashe ma bacci take, Nan dae ya fada ma Haiydar Shukrah tayi bacci sukayi sallama, sannan yayi wa Shukrah addu a shima yayi "
" Sai da Safeer da Ahmad sukayi kwana 5 basa zaman gida Shukrah har ta fara ramewa "
" Shukrah ce zaune kan abin sallah bayan ta idar da sallah azahar tana yiwa Safeer addu 'ar kariya, Jin datayi a turo kofar dakinsu yasata saurin dagowa "
" Ware ido tayi tana kallon sa da mamaki, Tunda sukazo san Francisco basu taba haduwa da rana ba "
" Fuskarta dauke da Murmushi ta karaso ta rungumeshi "
" Ya Safeer sannu da zuwa Shukrah tace tana riko hannunsa, Ta zaunar da shi a bakin gado ta haye cinyarsa bakinta yaki rufuwa dan dadi "
" Yawwa Shukra na sameki lafiya?
"Lafiya kalau, Ya Aikin?
"Alhamdulillahi, Aiki ma ankusa kammalawa "
" Masha Allah shiyasa yau kadawo da wuri knn"
"Eh mana, Gobe ma bazan fitaba zan kaiki yawo "
" Ihun murna Shukrah ta sa kafin ta mike taje ta hadawa Safeer ruwan wanka, Bayan ya shiga toilet ne ta fito masa da farar t-shirt da three quarter ta fesa musu perfume ta zauna tana jiran fitowarsa "
" Shukrah ce kwance kan jikin Safeer da alama bacci zasuyi "
" Kinsan irin son da nake miki kuwa Shukrah "
" Saurin sa tafin Hannunta na dama tayi ta toshe bakinsa 'Yi shiru Ya Safeer kayi bacci kaji "Shukrah ta fada tana harar sa
" Harshen sa yasa yana tsotsar tafin hannun nata, Bata janyeba haka bata hana saba, sai ma kwantar da kanta datayi a kirjinsa hade da lumshe ido, A haka dae bacci me dadi ya kwashe su............
"Kamar yadda Safeer yayi wa Shukra Alkawari kan cewa ya yau baze fita ba haka kuwa akayi be fitan ba,"
"Bayan Sallar Azahar ne Safeer ke Sanar da Ahmad yana so ya fita da Shukra, Ahmad din kuma ya Amince ze zagaya dasu suga garin kamar yadda Safeer din ya bukata"
"Dukansu na gani a harabar Gidan cikin Shirin su na fita, Ahmad ya zauna a driver sit inda Safeer ya zauna a gaba Shukra da Azeeza kuma Suka zauna a baya "
" Mesium ya fara kaisu, Sannu a hankali yake musu bayan duk abinda suka gani,Bayan sun gama da Mesium ya daukesu ya kaisu San Francisco state University sosai suka zagaya a cikin University kafin suka fito suka tafi wani hadadden Restaurant nan Suka ci abinci suna ta hira abinsu, "
" Bayan sun fito ne Shukra taga wani dan Asibiti karami a gefe tace tanason shiga, Ae kuwa sai da suka shiga aka zagaya dasu, tayi kuma magana da wata likitan ido inda Shukra ke fada mata Optometry ta karanta, Sosai Doctor taji dadin Haduwa Da Shukra har tayi mata tayin Aiki cikin Asibitin, Shukra ta mata bayani kan cewa ita bakuwa ce a San Fancisco Aiki ne ya kawo mijinta, Sun dan taba hira kadan Sukayi Exchanging phone number daga nn sukayi Sallama Suka bar Asibitin "
" Koda Suka bar Asibitin ba gida Suka wuce ba Saida suka ce Bitch suka yi kalle kallensu sannan suka dawo gida da niyyar gobe zasuje San Fancisco state zoological garden "
" Koda Suka dawo Gidan Sallar isha kawae sukayi kasan cewar sunyi Magrib nan cikin Asibiti, Kwanciya Shukra tayi bacci me dadi ya dauketa, Shi kuma Safeer sai da Suka dade da Ahmad a Parlour suna magana kan Company kafin sukayi sallama kowa ya shige dakinsu "
" Bayan Safeer yayi shirin bacci ne ya kwanta kusa da Shukra yana ta binta da kallo kamar me Shirin gano wani abu a tare da ita, Kawai gani yayi ta kara haske tayi wani kyau, Idan har idonsa be masa karya ba ze iya cewa Shukra tayi kiba, To ko weather garin ta karbeta ne "
" Matsawa yayi sosai ya Rungumeta a jikinsa yana shafa ta sai yaji jikinta yayi santsi kamar jikin jariri, Ransa yana basa wani abu sai kawai ya share, Yana addu 'ar Allah yasa hasashensa ya zama gaskiya A haka dae bacci ya kwashe shi "
" Washe gari gurin sha daya bayan sun gama breakfast ne suka shirya sai Zoological Garden, Sosai gurin yayi wa Shukra kyau dan ko kusa bazaka hadasu da na Kano ba don iya shi ta taba zuwa "
" Riko Hannun Safeer Shukra tayi lokacin da Zuwa zo Gurin lion, Yana ganin su ya fara ihu yana tsalle kamar yana son fito, Shukra ta kankame Safeer a jikinta ta fasa masa kuka jikinta har wani rawa yake ta tsorata iya tsorata har bata iya jin abinda Safeer din ke ce mata "
" Sun dau Tsawon lokaci a haka Safeer sai shafa bayanta yake yana bata hakuri a Ransa kuma yana tunanin wannan irin tsoro na Shukra "
" Shukrah ce ta fara dagowa daga jikin Safeer ta kalle shi tana goge hawayen fuskarta
"Ya Safeer mu tafi gida Zazzabi nakeji"
"Sannu Shukra bari su Ahmad su Dawo sun dan za gaya can ne ya fada yana jan hannunta suka zauna "
" Riko shi tayi sosai don har yanzu a tsorace take Shima ganin hakan yasa shi Kwantar da ita kan kirjinsa yana buga bayanta a hankali, A haka su Ahmad suka dawo suka samesu inda Safeer yayi musu bayanin komai, Nan dae suka koma gida"
"Shukrah ce ta fara shiga gidan ta kwanta nan palour ta rufe idonta, A tare suka shigo dukkansu, Ahmad da Azeeza suka shige dakinsu Safeer kuma ya dauki Shukra cak ya kai daki ya kwantar "
" Sai wajen 3:20pm Shukra ta farka duk jikinta ba dadi ga Zazzabi ta rasa inda zatasa kanta taji dadi kawae sai tasaka kuka, Safeer yana toilet yajiyo kukan Shukra ya fito da Saurin sa ya hawo kan gadon inda take "
" Shukrah tayi Saurin fadawa jikinsa ya kankameshi kamar zata shiga cikin sa, Nan yaji jikinta yayi zafi sosai abin ya bashi tsoro, Yayi Saurin kwantar da ita ya fice daga dakin "
" Azeeza kadai ya samu a Parlour yayi mata bayanin komai, Nan ta mike da sauri takira Ahmad suka je inda Shukra, Azeeza jin yadda jikin Shukra yayi zafi yasa ta fashe da kuka, abinda ya daga hankalin Safeer "
" Da Hanzari Ahmad ya dauko car key dinsa Safeer ya dauko Shukra bayan Azeeza ta sa mata Hijab Suka wuce Asibiti "
" Suna zuwa Aka karbe ta, Bayan test test da akayi Doctor tayi musu babban Albishir cewa Shukra nada ciki har na wata Biyu "
" Zo kuga murna gun Safeer kai bama shi kadai ba harda Azeeza da Ahmad tunda su basu taba haihuwa kuma sun dau Safeer da Shukrah tamkar yan uwansu wannan ne yasasu jin kamar su za ayi wa haihuwar "
" Sai ba adi salatul Magrib sannan suka baro hospital kuma Alhamdulillahi jikin Shukra yayi sauki sai dai rashin kwarin jiki kawai "
" Sosai Shukra ke samu gata gun Ahmad, Safeer da Azeeza, Don Azeeza ta hana tayin komai cikin gidan har ruwan wanka ita ke hada mata da kanta "
" Kayan baby kuwa abin ba a cewa komai don kullum Ahmad ya fita sai ya siyo su hakama Safeer don ya zama dan gari "
" Safeer ne ya kira Aysher ya gaya mata Ankoyi sa a ranar Ammii da Areef sun zowa Mamah ziyara, Nan Aysher ta fada musu maganar cikin Shukra, zo kuga murna gun Ammii da Mamah bakin su yaki rufuwa su a dole murnar samun babban jika suke a take Ammii takira Daddy ta fada masa kusan ma Daddy duk ya fisu don cewa yayi inyagama abinda yake a Dubai zai wuce san Fancisco ya gansu "
" Mamah ta kira Shukra tayi mata murna tayi mata addu 'ar samun lafiya, Ita dai Shukrah kunya kamar ta nutse, sai bayan sunyi sallama da Mamah ta juyo kan safeer tana dukansa da hannu biyu tana mai kukan shagwaba "
" Shine kaje ka fada wa su Mamah inada ciki ko? Yanzu da wani ido kake so na kallesu "
" Rike hannayenta yayi ya janyota Jikinsa ya Matse ta har sai da ta saki yar kara sannan ya sassauta rikon "
" Shukrah Ai ko ban fadawa mutane ba zasu gani ae in mun koma "
" Ni bazan koma ba sai na haihu, Ta fada cike da shagwaba "
" Ae baki isa ba nanda 2 weeks zamu tafi don next week za a gama Aikin company kuma office suna nema na "
" Ni bazan tafi ba sai dae kaje ka barni a nan "
" Bazan barki ba Shukrah "
" Nan dae Shukrah ta cigaba da kukanta na shagwaba wae ita bazata je aga cikin taba sai dae a ganta da baby "
" Shiko Safeer shiru yayi yana jinta don yasan inya biye mata rigima zatayi tayi masa don ita cikin nata da tabara, Rigima da shagwaba yazo mata, Ahaka dae bacci ya dauketa ya sauke ta daga jikinsa ya mata addu a shima yayi ya Rungumeta sai bacci...........
"Misalin karfe daya da rabi Shukra ce da Azeeza a kitchen da Alama Lunch suke hadawa, Azeeza na daga gefe tana dafa white spaghetti Shukra kuma tanayin Beef Goulash "
" Wayan Shukra ne ya shiga ringing ta ajiye spoon din Hannunta ta nufi wayar, Ibteesam ce me kiran shiyasa Shukra tayi saurin picking tana mata sallama
"Shukra Fadamin da bakin ki dan Allah inji Ibteesam da murnar ta"
"ME zan fada miki Shukra ta tambaya "
" Ki fada min SIRRIN BOYE (sabon Novel dina bayan AUREN BAZATA insha Allah) inji Ibtee tana dariya "
" Dariyar itama Shukra tayi don ta gane me take nufi "
" Wata nawa ne?
"Wata Biyu ne "
" kice Amal ta kusa samun kanwa inji Ibtee "
" Ta kusa kam "
" Daga nn dae suka cigaba da Hirar su ta kawaye har sai da Shukra taji Beef Goulash dinta na neman kamawa sannan tayiwa Ibtee sallama ta koma kan girkin ta "
" kamar yadda Daddy yayi Alkawarin zuwa San Francisco ganin Shukrah Haka kuwa akayi ranar wata friday ya kira safeer ya fada Masa gobe ze biyo jirgi yazo ya gansu, Shukrah kamar ta zuba ruwa a kasa tasha don Farin ciki "
" Ranar da Daddy zezo Abinci kala kala Shukrah da Azeeza sukayi, Karfe Uku saura jirgin su Daddy yayi landing a San Francisco, Inda ya kira Safeer a waya Sukaje Shida Ahmad suka tawo Da Daddy "
" Rungume Daddy Shukrah tayi don Murna kafin taja Hannunsa ta Zaunar da shi kan One sitter ita kuma ta zauna a gaban sa tana masa labari sai dariya suke "
" Azeeza ce ta kawo wa Daddy Abinci da Drinks sannan Suka gaisa Nan Safeer da Ahmad ma Suka zo suka kara Gaisawa da Daddy kafin suka tafi suka barshi yaci Abinci "
" Koda Ahmad da Safeer suka fita Hotel room suka kamawa Daddy sannan suka je sukayi masa Siyayya me yawa suka kai Room din sannan suka dawo gida "
" Sanda Suka tafi Mosque ne suka yiwa Daddy bayanin Komai kuma yaji Dadi, Da suka idar Suka kai Daddy Hotel din Sannan suka dawo gida "
" Safeer da Shukra zaune a dakin su Ga abinci a gaban su
"Shukrah yanzu bazaki ci abinci ba, kin taba ganin inda akayi haka? Bafa ke kadai bace ba "
" Ni bazan ci wannan abin ba ta fada tana nuna masa plate din gabansu kamar zatayi kuka "
" To naji me zaki ci "
" Dan wake ta fada tana kwanta wa a jikinsa "
" 😳Dan wake kuma Shukra? Haba da Allah yanzu a ina zan samu dan wake a nn, Kuma naga da ae bakya cin Dan waken "
" Toni yanzu shi nake so ta fada tana fashe da kuka kamar an mata wani abun "
" Rungume ta yayi tsam yana lallashi amma taki jinsa sai kara volume din kukan ma tayi "
" Yi hakuri Shukra dan Allah ki fada min wani abun amma banda wanda bazan samu a nn ba "
" To naji na canja Dan - Malele zanci "
" Safeer kamar zeyi kuka yake ji, Tabarar Shukrah ta soma damunshi, "ynx fisabilillahi Shukrah a ina zan samu wani Dan -Malele a nn"
"Toni shi zanci "
" Shiru yayi mata be kara cewa komai ba ya janyo plate din ya fara cin abincin sa "
" Shukrah ganin ya kyaleta ya sata fasa masa kuka sosai har tana bubbuga kirjinsa, Rike hannayenta yayi da nasa guda daya yana cigaba da cin abincin sa har anan bece mata komai "
" Shiru tayi ta kara lafewa a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya har bacci ya dauketa "
" Sai da ta gama cin abincin sannan ya kwantar da Shukrah a kan gado sannan ya dauki plate din yakai kitchen ya dawo ya kwanta a kusa da Shukrah bayan ya musu addu 'a, Da tunanin rigimar Shukra bacci ya dauke shi "
" Cikin dare yunwa ta damu Shukrah ta mike ta fara bubbuga Pillow' n safeer, Bude idonsa yayi ya sauke su kan Shukrah da tayi kalar tausayi tana kallonsa "
" Ya akayi? Ya tambayeta da muryan bacci "
" yunwa nakeji ta fada tana jan hannunsa "
" Mikewa yayi ya fita, kitchen ya je ya hada mata Tea sannan ya dawo ya samu ta shiga Toilet "
" Tana fitowa ta nufi inda yake da sauri ta karfi cup din hannunsa bata damu da zafin da tea din yake da ba ta kafa kai ta fara sha, Bata ajiye ba sai da ta shanye tsat, Ta zauna bakin gado ta rufe idonta tana maida numfashi, Wani tausayin ta yaji yana shigarsa sosai "
" wani zafi Shukrah taji tana ji sai gumi take, Ganin da yayi tana gumi ne yasashi shiga toilet ya hada mata ruwan wanka, Ya dawo ya daga ta ya cire mata rigar jikanta ya dauketa cak sai toilet, Da kansa yayi mata wanka sannan ya dauko ta ya dawo da Ita ya kwantar kan gado shima ya kwanta sai bacci "
" Sai da Daddy yayi 1week a San Francisco, sosai yayi wa baby siyayya shima sannan Y soma shirin komawa Nigeria, Shukrah yar Rigima wae sai ta bishi,jin safeer be ce mata komai ba yasata yin shiru da maganar "
" Ranar da Daddy ze koma dukansu ne suka rakashi Airport sai da su kaga tashin su sannan suka koma gida suma "
" Yau ake taro bude Company 'n Ahmad, Sosai manyan mutane suka halarci taron kasan cewar Ahmad shahararre kuma fitacce a San Francisco state, Bayan gaishe gaishe, ciye ciye Ahmad ya gabatar da Safeer a matsayin Manager' nsa, sosai abun ya bawa Safeer mamaki don be taba tunani ba kuma koda wasa Ahmad be fada masa ba, "
" Se bayan da aka kammala taron ne Safeer ya samu kebewa da Ahmad inda yayi masa godiyar wannan alherin da yayi masa "
"Safeer ya kira Mamah ya fada mata irin Alherin da Ahmad ya masa, Nan Mamah ta bukaci Safeer ya hada ta da Ahmad din, Ya bashi wayar kuwa inda Mamah tayi masa godiya sosai sannan tayi masa Addu 'a, Sosai Ahmad din yaji dadin yadda Mamah tayi masa "
" Yau saura kwana Biyar su Shukrah su koma Nigeria, Sosai Ahmad da Azeeza suke musu tsaraba wanda yawanci kayan Babe ne, Azeeza ce ma tayi wa Aysher da Miemie tsaraba, inda Ahmad yayi wa Mamah da Ammii tsaraba shi kuma "
" Ana gobe zasu koma cikin gidan ba wanda yayi bacci suna tunanin rabuwa (sabo turken wawa), Jirgin bakwai da rabi zasu bi hakan yasa koda su safeer suka dawo daga mosque wanka ya shiga bayan ya fito ne itama Shukrah tayi "
" 6:40am dukansu suka fito suka shiga mota Sai Airport, Cikin mota Shukra da Azeeza sai kuka suke sun rungume junansu, Suma su Safeer kawae dauriya suke irinta mazaje amma suna jin ba dadi a ransu wannan ne dalilin da yasa basu hana su kukan ba ma "
" 7:30 aka fara kiran sunansu, safeer da kyar ya janye Shukra a jikin Azeeza bayan ya mata alkawari zasu sake dawo wa kafin ta haihu tunda shine manager 'n company' n Ahmad so akwai bukatar zuwansa San Francisco akai akai "
" Sai da Su kaga tashin su sannan Ahmad yaja Azeeza mota wadda har anan kukan take (Sabo da dadi rabuwa ba dadi) "
" A Nigeria Miemie da Aysher ne a kitchen suna ta girki kala kala, Dama Mamah ta nemi alfarmar Ammii kan tazo gidanta su tari su Shukrah gaba daya "
" Ammii bata watsa kasa a idon Mamah don tun 9:00am sukazo ita da Areef "
" To cikin jirgi Shukra sai kukanta take Safeer na Aikin lallashi, Da kyar ya samu tayi bacci sannan hankalinsa ya kwanta "
" 2:00pm Jirgin su yayi landing a Airport na Malam Aminu kano, Suna fita Safeer ya kira Haiydar ya fada masa sun karaso sannan suka koma gefe suna jiran zuwan Haiydar din "
" Bayan kamar minti ashirin sai ga Haiydar ya zo ya fito ya tayasu zuba kayan su a booth ya jasu sai Farm Centre "
" Miemie najin tsayawar mota ta fito da gudu dai dai sanda Shukrah ke fito da ga motar Haiydar, Miemie tayi tsalle ta Rungume shukra cike da murnar Ganinta, ita ma Shukra da murnar ta ta rungume miemie suka shige gidan gaba daya "
" Shukrah na ganin Ammii ta fada kanta ta rungume hade da sakar mata kukan shagwaba "
" Baki Ammii ta saki tana kallon Shukrah da mamaki
"Kukan na meye to Shukrah"
"Na dadi ne Mamah ta bawa Ammii Answer "
" Sai Anan Safeer da Haiydar Suka shigo gidan Nan fa aka shiga gaishe gaishe kowa fuskar sa dauke da fara 'a, Bayan an gama ne Aysher ta shiga kawo musu drinks "
" Ruwa kawai Safeer yasha suka tafi Mosque shida Haiydar, To itama Shukrah Sallah tayi sannan tazo tace Miemie ta bata abinci taci don ita cikin nn harda wani mugun ci yasa mata "
" Coconut rice da Egg sauce Miemie ta zuba mata sai mixed fruit ta ajiye mata a gaban ta, "
" Ae Shukrah na kai Spoon din baki taji zuciyar ta ba tashi ta yarda Spoon din da sauri tana kokarin mikewa, Amma kafin ta mike tuni ta fara Amai a inda take "
" A tare dukansu suka nufeta Aysher ta rike ta tana mata sannu jikinta sai rawa yake
"Aysher ki dauke wannan abincin banason ganinsa Shukra ta fada a wahale"
"Sai da Aysher ta dauke abincin takai kitchen sannan ta dawo ta fara gyara gurin "
" Mamah ko rike Shukrah tayi suka shiga daki ta taimaka mata ta dauraye bakinta ta hada mata ruwan wanka ta shiga sannan ta dawo palour inda Ammii "
" Sanda Safeer ya dawo gidan sai dube dube yake yanason ganin Shukrah Amma bai ganta, Kiran Miemie yayi da hannu ta dawo kusa dashi ta zauna "
" Shukrah fa? Ya tambaye ta kasa kasa "
" Nan miemie ta masa bayanin komai, aiko yayi saurin ture plate din gabansa ya shige dadin Mamah "
" Tana kwance a kasa da alama fitowarta a wanka knn idonta a rufe kamar me bacci ya kara sa kusa da ita ya zauna, Shafa fuskarta da yayi ne yasa ta bude idonta da sukayi ja alamar tana jin jiki sosai "
" Mikewa tayi ta shige jikinsa don ba abinda take bukata a halin yanzu sai shi, Tana so taji dumin jikinsa "
" Kara rungume ta yayi tsam kamar za a kwace masa ita yana shafa gashi kanta har zuwa bayanta, yana mata rada a kunnenta "
" Kara shigewa jikinsa tayi tana lumshe ido, ita kadai tasan abinda takeji a jikinta (Nace wannan ko sun manta a gidan Mamah suke) "
" kokarin kunce towel din jikinta yake aka bude kofa ya juyo da sauri yana kallon kofa, miemi ya gani a tsaye ya watsa mata harara "
" ME ya shigo dake cikin dakin nn? Ya tambayeta rai a bace "
" Ammii ce tace in kira kaci abinci "
" Dalla fita k bani guri ya fada yana nuna mata kofa "
" Fita tayi da sauri dan tana tsoron bacin ransa "
" Wayarsa ya ciro yana snapping fuskan Shukra, Kafin kuma ya shiga kiran Aysher "
" Da Sallama tashigo cikin dakin Amma ganin a yanda suke yasata saurin juyawa "
" Dariya yayi sannan ya ce ta daukowa Shukra kaya tasa "
" Fita tayi bata wani dade ba ta dawo kanta a kasa ta mika masa kayan ta fice da sauri"
"Da kansa ya saka wa Shukra kayan kafin ya soma lallabata kan tazo suci abinci amma tace bata san cin komai, da kyar ta yadda zata sha Tea "
" 4:15 pm Ammii tace itafa gida zata tafi, Safeer ne ya maidata gidan sannan ya dawo "
" Sai bayan Magrib Abbah ya dawo suka gaisa da Safeer ya kara masa murnar zama manager a San Francisco "
" Shukra ma tazo suka gaisa da Abbah inda yayi ta samata albarka yana addu ar Allah ya sauke ta lafiya ya bada nagari "
" Sai da sukayi Sallar isha sannan suka musu rakiya har mota suka tafi gidansu, Gidan tsaf yake don Aysher da Miemie sun zo jiya sun gyara"
"Shukrah ce ta fara wanka tana fitowa ta kwanta sai baccin gajiya, Safeer ma da ya fito daga wankan kwanciya kawae yayi ya musu addu a sai bacci............
SAFIYA TA GARI
"Washe gari Safeer beje ko ina ba a gida ya yini, Sai bayan la 'asar ne Haiydar yazo, Sosai suka yi hira, Shukrah ta fito daga daki da gani a bacci ta tashi, Tana ganin Haiydar ta saki ranta suka shiga gaisawa cikeda girma ma juna, Kallon Safeer tayi taga ita yake kallo "
" Ta bata rai tana harararsa' Zani gidan Ibtee tace tana turo baki "
" Maida kallon sa yayi kan wayarsa yace 'Bazaki ba' "
" Tafi minti biyu tsaye tana kallonsa kafin tasa kukan shagwaba harda bubbuga kafa a kasa kamar karamar yarinya "
" Ganin ko kallonta yaki yi yasa ta zuwa gabansa ta Fisge wayar hannunsa
"Ni wallahi sai ka kula ni"
"Dariya Dukansu kusa sa ba kamar Safeer da yakeyi tsakani da Allah harda Sakkowa daga kujera "
" Abin ya kara bata haushi dama yanzu abin haushi ba wuya yake mata ba, Ta kara fashe wa da kuka tana kallon Haiydar wanda yake kokarin tsayar da dariyar sa "
" Harda kai ko? Nagode "
" yi hakuri Shukra, Ki rabu dashi kinji, yi tafiyar ki gidan Ibtee ki tawo min da Amal in zaki dawo, Safeer ya fada kamar bashi ya gama mata dariya ba yanzu "
" Bazani ba ta fada tana hullar da wayarsa a kasa sannan ta wuce dakinta ta rufe kofa harda key ta fada kan gado tana cigaba da kukanta "
" A parlour Haiydar ya kalli Safeer "wae kae meye hk ne zaka sa yarinya a gaba kana mata dariya"
"Dariyar ya kuma yi kafin yace ae mu biyu mukayi mata dariyar naga "inji Safeer
" Amma ae taka tafi bata mata rai, wae meye ma abin dariya "
" Ni mamaki ta bani Duk fa yau bata kulani ba in nayi mata magana sai tamin Shiru ko kallo ban isheta ba, shine ta bani dariya yanzu ae tazo tana wani bata rai wae zata gidan Ibtee "
" Murmushi me kyau Haiydar yayi sannan yace me kayi mata taki kula ka?
"wallahi ban mata komai ba rigima ce kawai irin tata "
" To Allah ya kyauta Haiydar ya ce tana kallon wayarsa da ta shiga vibrating, Sanda Haiydar ya daga wayar shi kuma Safeer mikewa yayi ya shige Dakin Shukrah "
" Tana zaune tana charting a bakin gado ya karasa kusa da ita ya zauna sannan ya karbe wayar Hannunta "
" ME zaki ci, Ya tambaye ta yana kallonta "
" Murya can ciki tace bakomai "
" kamo hannayenta yai duka biyun yana kallon cikinta daya dan turo kadan dan ita shukra dama cikinta a shafe yake, "Haba Mana Shukrah Cute ya zaki ce ba zaki ci komai ba, ki daure ko tea kisha"
"Ni bazan sha ba ta fada wane zatayi kuka "
" Ni Gidan Ibtee zani tayi min Tuwo "
" To Alhamdulillahi tunda zaki ci tuwon tashi na rakaki gidan Ibtee, Ya fada yana nikam da ita, Hijab ya dauka a kan gado ya sa mata ya rike Hannunta suka fito parlour inda tayiwa Haiydar sallama don ba da wuri zata dawo ba "
" Har bakin gate din su Ibtee yakai Shukra yace ze jira ta ta kawo masa Amal, Tana shiga parlour taga Amal tana wasa ta dauketa takai masa sannan ta koma cikin gidan "
" sanda ta shiga gidan taga Ibtee tana leka bayan kujera, Shukra ta hade rai don batason yin dariya "
" Lafiya Ibtee, Meye a gurin shukra tace tana lekawa itama "
" Ke banga Amal ba kuma fa wallahi yanzu na shiga daki na dawo kuma ban ganta ba Ibtee tace hankali tashe "
" Shukrah ta gimtse dariyar ta ba tare da Ibtee ta gane ba tace to waye ya shigo gidan ya dauketa? dama baki rufe parlour ba? "
" Inafa na rufe, keni zo mu fita Dalla ta fada sanda tasa Hijab dinta "
" Ai kuwa bamuga ta zama ba Shukrah tace sannan tana hannun Ibtee suka fito "
" Fitowarsu tayi dai dai da fitowar Haiydar da Safeer, Amal na hannun safeer ya bata wayarsa tana wasa da ita "
" wata Nannauyar ajiyar zuciya Ibtee ta saki ta kalli Shukra, Shukrah ta tuntsire da Dariya harda rike ciki "
" Ibtee takai mata duka 'bakida kirki Shukrah dama kinsan tana gidanki baki fadamin ba kikasa na tashi hankalina"
"Har anan Shukrah dariya take taja hannun Ibtee ni zo muje kimin Tuwo shi nake so wallahi, "
Kin jawa kanki ae bazan yiba"
"Haba Ibtee Swthrt, matar abu turab, uwar gida sarautar mata daga ke ba kari, Maman Amal Beauty, dan Allah kimin tuwon kinji Shukrah ta fada sanda suka shigo parlourn "
" To naji zanyi shknn Ibtee tace tana karasawa kitchen, ita kuma Shukrah tayi zaman ta a parlour dan in ta shiga kitchen taji kamshin miyar baxata iya ciba "
" Sai ba adi salamu magrib sannan Shukrah ta koma cikin gidanta inda ta dauko Amal ta dawo wa da ibtee ita ta koma ta samu Safeer zaune a palour yana Aiki a system dinsa "
" Ya Safeer zo muci tuwo ta fada tana ajiye flask din hannunta a kusa dashi, Ta wuce kitchen dauko plate da spoons ta zuba musu, Ta mike ta bude fridge ta dauko musu lacasera ta ajiye tana kallon Safeer "
" Sai da ya kammala abinda yake sannan ya switching off system din sannan ya sauko suka soma cin abincin "
" Washe gari gurin 11:00 Safeer yace Shukra ta shirya yakai ta gidan Ammii daga nan su biya su gaida Hajiyar Haiydar, Shukra harda dan tsalle ta shige toilet don yin wanka "
" Safeer ya juya ze fita kenan ya hango wayar Shukra dan dressing mirror, Da sauri ya karasa ya dauka Kai tsaye contact dinta ya fara dubawa cikin sa 'a kuwa yaci karo da wata Number anyi saving as MY NUMBER, Da sauri ya dauko wayarsa ya dau Number yasa yayi dialing, Tana fara ringing yayi saurin Rejecting yayi mata Saving number sa as "HUSBY"
"Sannan yayi saving tata number as "WIFEY"
"Koda Shukrah ta fito da sauri ta shirya ta samu Ya Safeer a parlour suka kama hanyar gidan Ammii"
"sanda suka isa Safeer ne ya dauko wa Shukrah tsarabar su Ammii suka shiga a tare cikin sa a kuwa suka tarar da Daddy na gida "
" Safeer ya dade sosai yana hira da Daddy sannan Y musu sallama ya tafi "
" Misalin karfe hudu da rabi wayar Shukrah dake hannun Areef ta soma ringing, mika mata yayi da sauri
"Baki sake take kallon number ita dai tasan ba ita tayi saving number nn ba, Tana ta mamaki har kiran ya katse wani ya shigo, Sai anan ta dauka da Sallamar ta"
"Jin muryan Safeer yana Answer mata sallama yasata sauke ajiyar zuciya"
"ki fito mu tafi gidansu Haiydar"
"To kawai tace sannan ta shiga dakin Mamah tayi mata sallama ta fito ta samu Safeer a motar sa suka tafi Gidansu Haiydar "
" Sosai Shukrah ta samu karba ta musamman a gurin Hajiyar su Haiydar, Don Hajiyar Haiydar mace ce mai kirki da son mutane duk da kasan ce watar ta mai kudin gaske amma kudinta be sa mata girman kai ba "
" Sai da sukayi sallar isha sannan suka koma gidansu inda Hajiya ta cika Shukrah da tsaraba, sosai Shukrah ta shiga ran Hajiyar don har tana tambayar ta sanda zata sake zuwar Mata.........
Three Months later
"Shukra zaune a dakinta ta sa akwatuna a gaba tana duba wa zallar kayan Babe ne aciki, a zuciyarta tana mamakin irin wannan soyayya da iyayen ta, iyayen Safeer kai harma da Hajiyar Haiydar suke nuna wa babynta, takai one hour tana aikin kayan kafin ta ture kayan ta jingina a jikin gado tana shafa cikin ta dan wata shida wanda ya yayi girma sosai sai kace dan wata tara, Mamaki da tsoron girman cikin ya hana mata nutsuwa a yan kwanakin nan ga nauyi kamar me "
" Tana cikin haka Safeer ya shigo cikin dakin yana Waya da alama da friend dinsa suke wayar, Sai da ya gama ya juyo yana karawa Shukrah kallo wadda gaba daya ma hankakinta baya wajensa, janyota yayi jikinsa yana shafa kanta "
" Shukrah meye matsalar??
"Tsoro nakeji ya Safeer ta bashi Answer kamar zatayi kuka "
" Dago kanta yayi yana mata kallon mamaki kafin yace tsoron me?
"Wannan cikin mana yayi girma da yawa kamar wadda zata haifi guda goma "
" To Shukrah ae lafiya ce, kuma ma ko guda goma kika haifa ai ba matsala bane indai Allah ya baki lafiya ko "
" Kuka kawae tasaka masa wae ita BAZATA haifi guda goma ba "
" Safeer dae yana mamakin Shukrah yanzu ba dama ayi magana sai tasa kuka, ayi mata wasa ta dauka da zafi, lallashinta yashiga yi yana cewa insha Allah daya zata haifa mai kama dashi tunda batason goma "
" o o ni me kama dani zan haifa tace tana turo baki "
" To naji Allah ya sauke ki lafiya shike nan "
" A a "
" Sai me kuma "
" Sai da ta dauke kai kafin tace ni gidan Ammii zaka kaini "
" Kema dae kya ji kunya Shukrah jiya fa har 10:00pm kina gidan Ammii kuma yau ma wae sa rai kike na kaiki "
" Kukan ta ta cigaba wannan karon har tana hadawa da kaimai duka "
" Ganin Abin Shukrah ba me kare bane yasa Safeer saurin ture ta a jikinsa ya mike ya fice, ita ko Kukan ta take tsakani da Allah a haka dae bacci ya kwashe ta a gurin "
" Sai bayan sallah magrib sannan Safeer ya dawo gidan Shukra na zaune a parlour tana cin gireba, suna hada ido ta daure rai ta maida kallon ta jikin TV"
"Yammata na, yanzu kina kallona na shigo cikin gidanki amma ba sannu da zuwa ba komai "
" Ban iya ba tace ba tare da ta kalleshi ba "
" Baki iya gaisuwa ba Shukrah ya fada sanda ya karaso kusa da ita yana binta da kallon mamaki "
" To kaima baka iya dubiya ba ta fada tana murguda masa baki "
" iye Shukrah ya Safeer din kike yiwa haka? Yayi maganar irin abin ya bashi mamakin nan "
" komai ba tace ba sai ma juya masa baya datayi tana cin gireba hankali kwance "
" Ya dade a tsaye yana mata kallon mamaki kafin ya girgiza kansa ya wuce dakinsa a ransa yana cewa
"Shukrah dae ta zama a lallaba"
"Shukrah na nan zaune har 9:00tayi, wayarta ce tayi ringing tayi saurin dauka kamar me jira DR WAHEEDA ta gani jikin screen din sai da tayi murmushi kafin tayi picking, tayi mata Sallama ta answer "
" Bayan yan gaishe gaishe ne, waheeda tace Shukrah bakida kirki wallahi ace kin samu cikin har 6 Months amma baki fada min ba "
" Shukrah wadda kunya ta rufe tayi murmushi batada abinda za tace shiyasa tayi shiru "
" Kinyi Shiru Shukrah ko bakya jina ne? Waheeda ta tambaya "
" Da kyar Shukrah ta ce mata kiyi hakuri ae nayi tunanin ya fada miki "
" Inafa ya fada min, Ae zan gamu dashi ne kedai Allah ya sauke ki lafiya, Badai wata matsalar ko?
"Ba matsala wlh "
" Daga haka dae Shukrah yi sallama Shukrah dae har anan bata dena jin kunya ba, Don sosai take jin nauyin DR Waheeda hakan nema ya hanata sanar mata tun farko "
" To kamar yadda Safeer Yayi wa Shukrah alkawarin zasu sake zuwa San Francisco haka kuwa akayi don yau Safeer Bayan ya tashi daga office Golden season travelling agency ya nufa kai tsaye yayi musu visa shida Shukrah da Miemie "
" Sanda ya shigo gida tarar wa yayi Shukrah tayi baki wasu yan uwansu sune na katsina suka zo, Tsayawa yayi suka gaisa sannan ya wuce, Shukrah kamar bazata tashi ba tayi zamanta ta cigaba da hirar ta sai da wata Auntyn ta Aunty Nabeehart ta harare ta
" Kin tashi kin bi mijin ki ko sai na kwada miki mari tukun na"
"Turo baki Shukrah tayi ta tashi tana cewa Aunty fa banida lpy sannan ta shige dakin Safeer "
" Sanda ta shiga ta samu har ya shige wanka saboda haka sai kawae ta fito mai da kaya tayi kwanciyar ta kana game a wayar sa "
" Sanda ya fito gaban dressing mirror ya nufa ya dauko cream ya dawo kusada Shukrah ya zauna, Tana ganin haka tayi saurin minimizing game din ta ajiye wayar ta mike, sai da ta karbi cream din hannunsa sannan ta kalleshi ta fara magana kasa kasa
"Ya Safeer ka dawo lafiya ya office?
" Alhamdulillahi, Yau na zo miki da albishir "
" Cikeda zumudi tace ya Safeer menene dan Allah "?
" Inna fada miki me zaki bani as a gift "
" Duk me kake so zan baka wallahi "
" Are you sure! Yace in between laughter dan shi kadae yasan tanadin da yayi mata "
" Absolutely sure inji Shukra don bata me yayi ba,
"To shknn zan fada miki koma menene amma ba ynx ba sai dare "
" me yasa sai dare Shukrah ta tambaya cikeda rashin fahimta
"banason tambaya tayi yawa tunda nace sai dare ae saiki hakura ko"
"Shukra bata sake cewa komai ba har dae ta gama shafa masa cream din ta koma wajen bak'in ta "
" Da daddare bayan Safeer ya fito daga masallaci be wuce ko inava sai gidan Mamah inda yayi mata bayanin tafiyar tasu, ya kuma fada mata tare da Miemie zasu tafi "
" Miemie da tunda ya shigo cikin gidan ta rufe idonta kamar me bacci wae don karta gaishesa ta fasa ihu hade da duro wa daga kan kujera "
" Ya Safeer dan Allah dani zaka tafi San Francisco wayyo dadi, Wayaga Miemie a cikin turawa wai! A gaskiya ka gama min komai wallahi God bless your unborn Babe ta karasa harda yar rawar ta "
" Baki sake Safeer ke kallon ta haka kuma rai a hade, azuciyarsa yana daya sanin yi mata visa, Wai dama ba bacci take ba tsabar iskanci ne ya hanata gaida shi ""
"Wata uwar tsawa ya mata wadda ba Miemie ba har Mamah da Aysher da Abbah dake kokarin shigowa parlourn sai da suka tsorata
"Bakida hankali ko, to wallahi ki kama kanki kinsan me yake miki ciwo, in kuma kinki wallahi zan baki mamaki useless kawai"
"Abbah ne ya karaso cikin parlourn ya dafa kan Safeer sannan yace''kayi hakuri babban yaya sai hakuri addu a zaka tayata da ita kaji "
" To kawai yace sannan ya mike yana kallon Mamah yace''ta shirya wednesday zanzo na tafi da ita tunda friday zamu tafi, yana kaiwa nan ya fice daga gidan "
" Tafiyar 40mints ne ya kaishi gidansa, a parlour ya tarar da Shukrah a kwance kamar me bacci, ya kara so kusada ita ya dauke ta cak sai a kan bed bayan ya sauketa ya shige toilet sai anan Shukrah ta bude idonta don kwanciyar bata mata dadi ba "
" Minti goma ya yayi yana shiryawa bayan ya fito a wanka, kan bed yahau ya zauna kusa da Shukrah ya riko hannunta ya akayi ne Shukrah cute?
"Abinda zaka fada min dazu kace na bari sai dare zaka fadamin "
" Me kike ci na baka na zuba ae ynx zan fada miki, kedai ba kince duk me nakeso zaki baniba "
" Saurin daga masa kai tayi don ta matsu taji me zai ce "
" Good gal dama fada miki zanyi Friday zamu tafi San Francisco "
" Ae Shukrah batasan sanda ta fada jikin Safeer ta kankame shiba "
" Shima kankame ta yayi hade da zame rigar jikinta ya zura harshen sa cikin bakinta yana tsotsa as if ya samu sweet ne..............
