AUREN BAZATA PART 2




"Jiki asanyaye shukra ta tura kofar dakin safeer da sallama a bakin ta.
      "zaune yake a bakin gado da laptop dinsa a gabanshi da alama aiki yake, da fara arsa yake answer mata sallamar yayin da take karasawa cikin dakin.

    " zama tayi a kasa daga gefen gadon dai - dai kafarshi, ai kuwa da sauri yace "A a dan Allah karki zauna a kasa in gadon ne bazaki hauba saboda ni vari na sauka na barmiki ya fada yana sauke laptop dinsa kasa.

    " A a wlh kayi zamanka nanma yayi" ta fada cikeda da ladabi.

    "komai be ce ba sai zaman dayayi a gefenta yana me cigaba da abinda yakeyi.

  " shiru ne ya biyo baya yayin da shukra ta shiga karewa dakin kallo cike da sha 'awa, dakin yayi mata kyau komai na dakin coffee & milk ne, iya tsaruwa ya tsaru kamar dakin wata amaryar sai dai dakin a hargitse yake sosai kamar ba a taba gyara waba(Abinka da dakin namiji).



     "Yi hakuri ban kawo miki komai ba ko"
     "Lah bakomai wlh"
"Naga ae kina ta karewa dakin kallo kin ganshi a hargitse ko, abinka da dakin gwauro sai hakuri "

    " Wata kunya ce da takaichi suka hadu suka rufe shukra 'ae ita ya kamata ace tana gyara dakin tun asalin, Amma batayiba har wani cewa yake wae dakin gwauro sai hakuri "

    " karfin hali tayi sannan tace, bawani dakin gwauro insha Allah gobe xan gyara dakin in ka tafi office "

   " komai bace ba sai tunani yake gaskiya shukra ta gyaru, Allah ya kara shirya ta ya fada a ransa "

      " Dama naga bakazo bane shine nace bari nazo naji ko lafiya, ta fada tana kallon sa"


     "Lafiya kalau wlh aiki ne ya rike ni"
   "Aikin me?" ta tambaya tana leka system din "

   " Wallahi wani kwangilan construction na' fly over ' muka samu shine naketa fama "

     " To Allah ya taimaka, Amma fa ta zanu "

    " uhmm wannan dai zolaya ne ni ina na iya wani zane!

   "Bawani zolaya ka iya ne shiyasa na fada"

     "Ae shknn"


"Haka dai suka cigaba da hirar su sama - sama, 10:00pm shukra ta mishi sallama, tayi tunanin zece ta kwana a nn amma ga mamakin ta sai bece ba "


   " washe gari 70:30am safeer ya gama shirinsa na zuwa office ya fito palour rike da briefcase dinsa.

   "sam be kula da shukra dake zaune ba sai da kai bakin kofa yaji tana masa magana.

    " Ya safeer breakfast fa "
    " Hannunka ya daga yana kallon wrist watch dinsa kafin yace 'shukra yanzu in nace zan tsaya gaskiya makara zanyi ki ajiye min inna dawo zanci "


    " Kamar zatayi kuka tace dan Allah ka tsaya kachi ko kadan ne karka tafi da yunwa.

     "karki damu innaje chan zanci.
   " Dan Allah ya safeer ka tsaya kaci bazaka dade ba.


      "yana son chi amma bayason ya sake da ita don ba wani yarda da tuban ta yayi ba har ynx"


     "Bata rai yayi sannan ya dauki hanyar dinning"


     "Da sauri ta karaso wane xata fadi ta jamasa kujera ya zauna sannan tayi serving nashi.


     " Abincin yayi masa dadi sosai yanaso ya yaba amma ya danne xuciyar sa har wani yamutsa fuska yake,ya manta when last yaci abinci me dadin wannan.

     "Ture plate din yayi bayan ya gama sannan ya mike.

    " Shukra ma mikewa tayi ta dauki briefcase dinsa ta rakasa har bakin motar sa, sai da taga fitar motar sannan ta dawo ta cigaba da gyare - gyarenta.


       "coconut rice da eng sauce tayi ta saka a flask sannan tayi fruit salad tasa a friend.

      " Toilet ta shige tayi wanka sannan ta fito ta zauna ta tsara kwalliya (irin wadda ta koya a gurin fancy Makeover).


       6:20pm shukra ta kara gyara makeup dinta sannan ta fito palour ta zauna jiran safeer.


       " sai 07:12 safeer ya shigo cikin gidan shukra ko najin horn dinsa ta nemi nutsuwar ta ta rasa fargaba kawai take karya wulakanta ta tunda tasan ita ta siya wa kanta.

     " baki sake yake kallon ta da mamaki tayi kyau sosai kamar ya dauke ta "

    " sannu da zuwa ya safeer ta fada yayin da take karasowa gurinsa ta karbi briefcase dinsa "

   " Yawwa shukra ya gidan?
     "Alhamdulillahi"
 


"Daga nan ya shige dakinsa itama tabi bayansa, kan gado ta ajiye masa jakarsa kamar ta tsaya ta hada masa ruwan wanka amma tana tunanin kar yace ta fiye shishshigi "

    " To inma kin masa shishshigin meye? Ba mijin kibane wata zuciyar tace mata.

    "Juyawa tayi hanyar toilet din ashe wae har ya shige bata saniba tana tunani.

    " karasawa tayi ta ciro masa kaya ta ajiye a kan bed tana addu'ar Allah yasa ya saka kayan data dauko masa.


       "Kitchen ta koma ta debo flask din abinci ta zo ta jere su a dinning, sannan ta dawo palour ta zauna tana jiran fitowar sa.


    " Daddadan kamshin turaren da taji ne yasata dago wa tana kallon shi, da mamakin sai taga kayan data fitomai yasa.


   "zama yayi hade D daukan remote yana canja changes.


    " Ya safeer taso muchi abinci  "

  " Alhamdulillahi shukra naci abinci a gidan Mamah kafin in shigo.


     "Kukan da batasan dalilin saba ta saki ' a yau ta kara data sanin halayyar ta ada.

   " Arude take tambayar ta menene. "

   " ko nafadi wani abu dabe miki dadi bane? "
    " yi hakuri ki dena kukan to, ko saboda naje gidan Mamah ne kike kuka?


    "Da sauri ta girgiza kanta alamar A a"


   "To menene ya sake tambayar ta?
    " ya safeer dan Allah kayi hakuri ka yafemin abinda nayi maka a baya kachi abincin nan"

     "shiru yayi kamar me tunani kafin yace to naji zanci abincin shikenan.

    " Eh tace da murnar ta ta tashi a debe flasks din takawo palour ta shiga serving dinsa.



       "kingani kin bata makeup din ki garin kuka ko, dazu kinfi kyau wallahi 'ya fada ba tare da ya saniba"

    "fuskarta dauke da murmushin jin dadi tace' Ae na dena kukan ynx.

   " komai bece ba saboda wani haushin kansa yakeji na yaba kwalliyar ta da yayi "

"Kwashe plates din shukra tayi ta kai kitchen bayan sun kammala cin abincin, tare da wankesu ta maida komai mazaunin sa sannan ta fito ta sami safeer a palour kamar yadda ta barshi.

     "sannu da zama ya safeer"
     "Yawwa shukra sannu da kokari kema"
   "Yawwa"

"Ya safeer yaushe zaka kawo min miemie ne?
    "Ke yarinyarnan batada kirki surutun ta yafi aikin ta yawa"

"Tana dariya tace ai dama ni ba aiki zata tayani ba, kawai dai bana jin dadin zaman gidan ne ni kadai in baka nn.
     "To shikenan zan kawota amma sai sun gama exams"
     "To Allah ya kaimu lkc tace sannan suka cigaba da kallon su"

     "10:15pm safeer yayi wa shukra sallama bayan ya kashe TV"

    "Yau ma tayi tunanin xece tazo su kwana a dakinsa amma shiru, ita abin ya soma damunta gashi har lokacin mensis dinta ya kusa zagayowa ita tsoron ta daya Ammii tasan cewa zatayi ita taki alhalin ba haka bane"

    "Wasu zafafan hawaye ne suke shigo zubowa shukra tana kara data sanin rashin rungumar kaddarar da batayi ba a baya, a haka dae ta gama duk abinda ya dace ta kwanta.

    
WASHE GARI

" Tun bayan asuba shukra bata koma bacci ba gyaran gidan ta shiga yi sai da tagama sannan ta shiga kitchen "

   " kunu tayi sannan ta soya sweet potato, tayi sauce tazo ta jerasu a dinning ta shige toilet don yin wanka "

    " kusan tare suka fito daga dakunan su suna hada ido suka sakarwa junansu murmushin da basu san sunyi ba"
 

    "Good morning ya safeer"
    "morning, how was your night"
    "Awesome"
"Good "ya fada yana yin hanyar kofa

   " saurin shan gabansa tayi, ya safeer breakfast fa"
    "Zanyi a office shukra"
     "Haba ya safeer dan Allah kayi a nan da auren xaka dinga yin breakfast a office"
    "Shi mamaki ma ta basa sai yanzu tasan yana da auren? Ko da batasan a office din yake ba"
     "ki bari kawai ai daman a chan nake, so karki damu kinji ya fada yana wuceta"

     "kara shan gabansa tayi ta durkusa tana rokonsa yaci abinci a gida"

    "Tashi to naji zanci shknn"
    "Eh tace tana goge hawayen fuskarta, nan ta karasa dinning din taja masa kujera ya zauna sannan tayi serving dinsa"
     "sosai yaji dadin kunun dama shi yana so kawai dai dan Mamah batayi ne"

     "thank you very much shukra Allah ya miki Albarka" ya fada yana mikewa bayan ya gama "

   " Ameen nagode ya safeer Allah ya kiyaye hanya "
   " Ameen "

" Yauma kamar jiya har gaban motar sa ta raka sa tajira ya fita sannan ta dawo cikin gida.


      "Abokina yane yau na ganka cikin nisha di kodai yau ka angonce" inji haiydar

    "Kai dan iska ne wallahi bawani angon cewa kawai dai ina jin dadin yadda shukra ta canja halinta yanzu"
   

    "To Alhamdulillahi ae haka akeso"

" Kaga ni tafiya ma zanyi "

    " Gurin shukra inji haiydar yana dariya kasa - kasa "
   " Ban Sani ba "
" Allah ya baka hakuri "

   " kai ni gidan Mamah zani mu gaisa kwana biyu banje ba "

    " ok bari muje tare nima na kwana biyu banje ba wallahi "

   " To shknn "
" Daga haka suka fito suka kamo hanyar gidan Mamah "

     Shigowarsu yayi dai _ dai da shigowar miemie cikin gidan da gudun ta har tana ture haiydar kiris ya rage be fadi ba"

    "Safeer ne yayi saurin janyota yaja kunnenta da karfi wane ze cire shi"

     "Aiko sai ta fasa kara tana kiran Mamah"

    "zakiyi shiru ko sai na fasa bakin kukan, bakida hankali ko, bakisan kin girma ba kin wani shigo a guje kamar karamar yarinya, kuma kin ture Mutum bakisan ki bashi hakuri bako"

    "Allah ya baka hakuri to tafada tana hararar sa kasa - kasa.

   " Bani zaki bawa hakuri ba shi xaki bawa ya fada yana nuna mata haiydar "

   " Kusada haiydar taje tana hararar sa harda murguda baki Allah ya baka hakuri "

   " ji yayi ta masifan burgeshi "ya wani saki baki yana kallon ta, bemasan cewa safeer baya wajen ba sai da yaji su shida Mamah suna sauko wa daga stairs suna hira"

    "saurin saita kansa yayi sannan ya sauko daga kujera ya gaida Mamah cikeda ladabi"


     "5:20 suka bar gidan, haiydar yaso ta kara ganin miemie amma hakan be yiwu ba"

     "sai da suka shigo unguwan su haiydar sannan haiydar din yafara magana
" Safeer wai yarinyar dana gani kanwar kace?
    "Ba tare da ya kallo shi ba yace Ehh ya akayi?
    " number ta nakeso ya fada yana dauke kansa "

     " Baki sake yake kallon sa da mamaki 'me zakayi da number ta kai kuma kar dai kace da Abdallah zaka hada su (kanin haiydar)
     "wani irin Abdallah kuma, da kaina dai"
    "Bangane ba"
 "sonta nake"
"wani wawan birki safeer ya taka wanda har saida yabige get din gidan su haiydar sannan ya juyo ya kalleshi"
    

    "kace me safeer ya tambaya da mamaki"
     "nace sonta nake haiydar ya fada in an i don't care tone.

   " kaji kunya wallahi toni banida number ta kaje inda ka ganta ka karba "
    " kaga malam karka raina min hankali kan nace kabani number zanje har gidan na karba " yana gama fadar hk yafice mai a mota tare da buga masa murfin motarsa.


   " juyawa safeer yayi ya kama hanyar gidansa yana tunanin wae duk haduwar haiydar ya rasa wa ze so sai miemie"

   "Yau ma kamar jiya shukra ta shirya tsaf kuma ta yiwa safeer kyakykyawar tarba da abincin ta me dadi"



    "Da daddare safeer da shukra na zaune a palour wayarsa ce ta fara ringing, ganin miemie ce me kiran ya sashi kin picking"

   "wayar Mamah ta dauka ta kara kiranshi"
   "shiko ganin mama ce me kiran ya sashi picking da sauri"

   "ya safeer abokin nan naka daga gani sona yake, kaga yadda ya saki baki yana kallo na kuwa,"

   "ke yaushe na fara wasa dake ne wae, ni kike fadawa wannan maganar ko miemie? zanyi maganin ki wallahi...........






Washe gari

 " Ya safeer zan bika ka sauke ni a gidan  Mamah na dade ban ganta ba"

      "To je dauko mayafin ki mu tafi sauri nake"

   "sai da safeer ya sauke shukra a gidan Mamah sannan ya wuce office"

    "Haiydar fa" Safeer ya tambayi Massinger'n sa

    "Be karaso ba"
"ok nagode ya fada yana shigewa office dinsa.
    "sai 5:00 sannan safeer ya tashi a office, kai tsaye office din haiydar ya wuce dan yasan yana fushi dashi ne shiyasa ma yau bezo gurin saba"

     "Da sallama ya karasa ciki kafin ya zauna a kujeran dake facing dinsa"
   "Ciki ciki ya answer sallamar ba tare da ya dago ya kalle saba"

   "Haba haiydar me yayi zafi wae hk"
   "Ban Sani ba"

 "kaga in dai akan number ne kayi hakuri ni gsky bazan iya baka number yarinyarnan ba dan bana son rainin hnkl, ba a wasa da itama ya aka cika balle ana wasa da ita"

    "kaga malam karka samin ciwon kai ka gane, kace bazaka bada number ba nace zanje da kaina na karba ba shknn ba"

    "Shknn kam kaga yanzu gidan zanje sai kazo mu tafi ko"
    "Ba zani ba ai nima ina da motar ka tafi kawai in na gama zani da kaina"

   "Allah ya baka hakuri haiydar naga ka dauki abin da zafi" bari na wuce zanje na maida shukra gida ne, sai ka tawo.

    "Mtwsssssss haiydar yaja tsaki kamar wani mace ya cigaba da abinda yake"
    "Safeer be kara cewa komai ba sai fitar da yayi ya shiga motar sa ya nufi gidansu"


    "Kan cinyar shukra ya taradda miemie tanata zuba mata zance suna ta kyalkyala dariya abunsu"

     "zama yayi yana kallon su 'ke zo nan ya nuna miemie yana hararar ta"

    "kankame shukra tayi tana cewa Aunty kin ganshi ko ze dakeni dan Allah karki barsa kinji"

    " ME kikayi masa shukra ta tamvaye ta tana dago kanta"

"Raba ido miemie ta shiga yi dan tasan batada gaskiya' nidai Aunty kawai ki bashi hakuri "

    " To tace sannan ta juya tana kallon safeer kafin ta ce
       "Ya safeer dan Allah kayi hakuri BAZATA sake ba"

    "Da kin barni na fasa bakin rashin kunya ae"

  "Daga haka sukayi shiru har ann miemie na jikin shukra kamar wata munafika sai leken safeer takeyi"

    "Mamah ce ke saukowa daga upstairs tana kiran miemie"

    "kasa ya sauko daga kujerar da yake ya durkusa yana gaida Mamah mama cike da ladabi"

   "Ashe ka shigo bakayi magana ba"
   "Yanzu na shigo ae, zuwa nayi na zane autar ki"
   "ME tayi kuma?
" Rashin kunya tamin, daga nn ya kwashe yadda sukayi a waya jiya ya gaya mata "

    " Dariyar shirmen miemie sukeyi dukansu, banda safeer daya hade rai don shi bega abin dariya a ciki ba "

     


   " Se bayan sallar isha sannan su safeer suka koma gidansu. "



  " To haka dai rayuwar su ta cigaba da tafiya cikin girmama juna amma babu abinda ya taba shiga tsakanin su"


     "Yau ta kama friday tun safe shukra kejin ciwon mara tana cijewa sai fargaba take kar ciwon yayi worst"

    7:12pm safeer ya gaji da zaman falon da yake shi kadai, don duk yau bega shukra ba se yakejin ba dadi don ko ba komai sun saba "

   " Dakin ya tura ga mamakinsa sai ya ganta kwance tana juyi da hanzari ya karasa bakin gadon yana jero mata sannu "


    " Ya safeer dan Allah karka gayawa Ammii banida lafiya xata min fada wallahi "

  " Bazan fada mata ba shukra bari mu tafi asibiti "

  " A a bazan iya ba ka siyo min magani kawae mutuwa zanyi wallahi "

   " subahannalli "Bazaki mutu ba shukra bari na kira doctor ya duba ki "

    "wayarsa ya dauko ya kira, DR waheeda yasanta tun a secondry skul"
   "Hello waheeda"
"Na am safeer ya gida "
   " lafiya kalau doctor "
" Dan Allah idan bazaki damuba gidana nakeso kixo madam ba lafiya "

    " subahanallahi "yimin sending address di gidan gani nn zuwa"

  "Ba afi 40mints ba sai ga waheeda ta zo, kai tsaye bedroom din shukra ya kaita ya fito ya basu guri"

   " waheeda tabawa shukra magungunan da suka dace amma tana mamakin yadda matar aure take irin wannan ciwon "

 " Kasa hakura tayi sai da ta fita ta kira safeer ta hada su ta tambaye su "shin wani abu be taba hada su bane ko me?
   " kunya ce ta rufe su dukansu "


   " Itako waheeda masifa tai tayi musu kafin ta dawo nasiha "Haba shukra ya zaki hana mijin ki kanki bayan kinsan hukuncin yin hakan (haramun ne miji ya kiraki shimfidar shi kiki, mala'ikun Allah zasuyita tsine miki ne har ixuwa wayewar gari) ko kinason Allah yayi fushi dake ne? Ko kuma kinason mijin ki ya fara bin matan waje "

  " Da sauri shukra ta girgiza kanta alamar A a kafin ta fara magana a kunyace
"To aini be taba cewa nazo dakinsa mu kwana ba"

    "Tana gama fadar hk tafice daga dakin da saurinta"

    "Hakane safeer" waheeda ta tambayeshi tana hararar sa "


    " Nan safeer ya kwashe duk yadda akayi akai auren da kuma zaman da sukeyi a gidan har i zuwa ynx "

    " sosai waheeda tayi mamaki takuma bashi shawara, kafin ya rakota har falour, nn suka sami shukra a zaune waheeda tayi mata sallama hade da karban number ta da niyyar bata shawarwari

    "Har bakin mota suka rakata sai da motar ta ta fita daga cikin gidan sannan suka dawo cikin gidan cike da kunyar juna...........



"koda safeer ya kwanta tunani yayi tayi a ransa me shukra take nufi da tace "Ae shine be taba cewa muje dakinsa mu kwana ba"

"ke nn hakan na nufin shukra ta shirya ne ko me?
   "indai haka ne to Alhamdulillahi"

"Da tunanin nn bacci barawo ya kwashe shi.

Washe gari bayan safeer ya tafi office, shukra tayi duk ayyukan gida tayi wanka sannan ta dawo palour ta kanta ta dau wayarta ta hau WhatsApp.
"  bakuwar number ta gani tamata sallama sai bata answer, bayan kamar 1mint akayi kara mata sallama sai ann ne ta answer.

"Wa alaikisalam "
  " DR waheeda ce"
"Eyya doctor yi hakuri banida number ki ban ganeki wlh "

   " Bakomai shukra ya jikin "
   " jiki Alhamdulillahi "
" Bayan sun gama gaisawa ne waheeda tashiga yi wa shukra nasiha kamar yadda ta daukar wa kana alkawari "

   " sosai nasihar ta shiga shukra dan sai godiya takewa waheeda ".
  
  " Waheeda ta kuma yi adding shukra a wani Grp na matan aure domin tasan zata karu sosai "

   " Bayan da sukayi sallama shukra kwanciya tayi tana tunanin yadda zata bullowa al amarin daga hk bacci ya kwashe ta

  "Knocking din da ake a kofar palour ne ya tadata daga baccin da take,".
   "A nutse ta karasa bakin kofar ta bude, matashiya ce bazata wuce taba ko a shekaru take mata sallama da fara 'arta.

  " Answer mata sallama tai sannan suka shiga palour suka, shukra ce ta mike ta kawo mata drinks da snacks kala - kala sannan ta dawo ta zauna"


     "Sunana ibtisam, nice makociyar ki"

   "Wow nice to meet you ibtee"

   "nice to meet you too"

    "Ina fatan za a min afuwa ni ya kamata ace nazo ba keba"

  "Bakomai wallahi komai nufin Allah ne ae"
  
   "ni kuma sunana shukra"
  

     " Nice name"
"Thanks shukra ta fada tana daukar yarinyar ibtee, kasancewar shukra tana son yara sosai "
  

    " Hira suka shiga yi dan da alama jinin su ya hadu sosai "

  " Ibtee ce ta mike ta dauki yarinyar ta "

 " To shukra ni na tafi sai kuma kinzo ko"
  "To ibtee nagode sosai insha Allah gobe zaki ganni ta fada lokacin da suka fito waje"

   "Har bakin gate shukra ta raka ibteesam sannan ta dawo gidan donyin girki"



    "Haiydar ne ya shigo gidan su safeer da sallamar ma ya taradda Aysher a palour suna karatu itada miemie, har kasa Aysher ta gaida haiydar amma miemie ko a jikin ta cigaba ma da abinda take tayi"

   "Kusada miemie yaje ya zauna yana tambayar ta ya exams"
  "Sai a nn ta dago ta kalle shi,
 

  " Lah Aunty aysher Kinga wanda zan aura wanda na baki labarin sa rannan, sai ta dawo kan cinyarsa tana mishi surutu shi kuma sai biye mata yake suna kyalkyala dariya "


   " Itadai Aysher bata ce komai ba sai kallon su take yi dae "

   " Sosai yaji miemie na kara shiga ransa kasan cewar miemie me farin jini duk wanda ya ganta sai ya sota kawayenta harda manya masu yaya ma kai har kawayen mamah ma kawayenta ne, takanas suke zuwa gurinta "


   " Sallamar safeer ne ya katsewa miemie surutun ta "

  " Da mamaki safeer kebin haiydar da kallo shiko haiydar ko ajikinsa juyawa ma yayi suka cigaba da hirar su da miemie "


    " Haiydar wae dama nan zaka zo safeer ya tamvaya"
   "Eh ya answer shi a takaice"

    "Amma ae baka fada min ba"
   "To ae yanzu gashi nan mun hadu ko"
  "Buh atleast ae ya kamata ka fadamin ko"

"Kaga malam karka samin ciwan kai dama haka akace duk inda zani sai na nemi ixinin ka kikuwa"

   "Ko dan nazo gidanku shine ka wani tsare ni da tambayo yi hk"

   "Nidai bance ba, Allah ya baka Hakuri amma"

   "Ameen"

"Aysher ina mama me safeer ya tambaye ta "

  " Mamah taje unguwa amma bazata dade ba "

  " Nikam gaskiya sauri nake kya fada mata nazo "
   " Tom insha Allah tace mishi yayinda yake fita "



" sannu da zuwa ya safeer inji shukra da tun dazu take zaune tana jiran shigowar sa, ta miki hannu ta karbi brief case dinsa ta wuce dakinsa shima ybi bayan ta"


  "Yau shukra da kanta ta hadawa safeer ruwan wanka ta kuma fito masa da kaya ta feshe su da perfume sannan ta dawo palour ta zauna"



    "Bayan safeer ya fito ne shukra ta kawo musu abincin nan palour ta shiga serving dinsa"

     "Kai shukra ae da baki wahalar da kanki ba keda baki lafiya"

    "Bakomai ae hakki nane(niko nace da bakisan cewa hakkin ki bane sai yau).

   " Haka dae suka kammala cin abinci kowa ya shige dakinsa "



    " Haka dai rayuwa taciga da tafiya har ranar da shukra ta gama mensis"

   "Da daddare suna zaune a palour su biyun bayan sun kammala cin abinci, wayar safeer ce tayi kara aiko da hanzarin sa ya daga"

"Hello babyna ya kike?
"Gaban shukra ne yayi mummunar faduwa jikanta ya hau rawa"

   "Ok kina son gani na? To ganinan zuwa ynx"
    "ME zan tawo miki da?

" To ganinan daga nn ya kashe wayar ya mike ba tare da ya kalli shukra ba ya dau car key dinsa ya fice da sauri"

     "Ae safeer na fita shukra ta fasa ihu, kuka take baji ba gani a nn bacci ya kwashe ta batare da taga dawowar sa ba.................



10:40pm safeer ya shigo cikin gidan, shukra ya gani kwance a palour kamar zai tasheta sai kuma ya fasa ya mata addu 'a ya tofe mata jikinta sannan ya wuce dakinsa "


ASUBA

" Karar bude kofar da Safeer yayi ne ya tashi shukra daga baccin da take, suna hada ido ta wani dauke kai ta shige dakinta, shima tabe baki yayi yayi gaba abinsa kasancewar an fara kiran sallar asuba "


   " 6:50am shukra ta gama shirinta tsaf ta  dauki car key dinta ta fito palour janye da trolley dinta "


" Fitowar shukra yayi dai - dai da fitowar Safeer daga dakinsa, ko kallo be isheta ba ta wuce abinta ta fita daga palour 'n"


"SHUKRA ce ta shigo cikin gidansu a kitchen ta tayadda Ammii tana hada breakfast Kawai sai ta sa mata kuka sosai "


" A rikice Ammii take tambayar ta wani abun aka mata ne? Ko wani abu ya samu Safeer, Amma ko kulata batayi ba saima cigaba da kukan ta da tayi"


"Ammii ma bata ce komai ba ta cigaba da aikin ta, zuwa can kukan shukra ya fara cimata rai, batamasan sanda ta daka mata tsawa ba,


"Dalla malama kin cikamin kunne da kuka kinajina, in kukan kike sha'awa ki fita ki bani guri kije kiyita yi tunda bakida abunyi, tun dazu sai tambayar ki nake me akai miki kinmin shiru "


" Ammii Aure fa zai yi "

" Waye zeyi AUREN wae Ammii ta tambaye ta?


"Ammii ya safeer ne zeyi Aure, jiya a gabana tayi mishi waya wae tana son ganin shi shine ya tafi ya barni, tana kaiwa nn ta sake fashe wa kuka sosai "


" To sai me aini wallahi ya burgeni, haushin ma daya bani baze wuce rashin sakin ki da beyi ba, Ae naso ma sakin ki yayi ya huta tunda ke bakida kirki bakya jin mgn kin raina mu ko "


" Ammii wallahi shine...... "sai kuma tayi shiru ta cigaba da kukan ta

" Shine me Ammii ta tambayeta a fusace"

"Komai bata ce ba sai ma kara sautin kukan ta da tayi "


" Tashi ki fita ki bani guri kafin na kwada miki mari wallahi "

" Tashi tayi ta fita tana cigaba da kukanta, kusan chin karo sukayi da Daddy.

"Ke lafiyar kuwa? "

" Daddy ya Safeer ne zai kara Aure "


" To shine me "? Daddy ya tambaya irin ko ajikinsan nn"


"Ae Wallahi kadan kika gani, badai ke kince ban isaba, Har Safeer yamin biyayya ke ki kasa min ko? Ae duk abinda kike ina sane dake zuba miki ido kawai nai naga iya gudun ruwanki gashi tun ba 'aje ko inaba kin fara kuka da idanunki"



"Shigowar Safeer ne ya katsewa Daddy maganar da yake, ya durkusa har kasa suka gaisa da Daddy Sannan Ammii "


" Yawwa Safeer yanzu nake shirin kiranki ae sai gashi kazo "Inji Daddy


" Eh Daddy naga shukra ta tawo gida ne kuma ni ba wani abu ne ya hada muba, lafiya kalau muka rabu jiya amma yau naga ta dauko Trolley ta tawo "



" Eh wae zuwa tayi dan shashanci tana kuka wae zakayi Aure "Ammii tace tana hararar shukra.


" Wace yarinyar ce zaka aura? Daddy ya tambayi Safeer "

" Sunkuyar da kansa yayi yace a office dinmu take "

" Masha Allah "Ni da kaina zan nema maka aurenta kaji dan Albarka, tashi ka tafi office karka makara kaji"


"To kawae yace sannan Y mike yana satar kallon shukra ita ko sai zabga masa harara take wane idonta zai fado kasa "


" Kuma ki tashi ki dauki kayanki ki koma gidan mijin ki kafin in bata miki rai wallahi, Daddy ya fada a fusace"


Ko motsi shukra batayiba sai kukanta take baji ba gani "

" Zaki tashi ko sai na kwada miki mari "


" Jiki ba kwari ta mike taja trolley ta fice daga palour 'n "


" Kamar kullum yau ma tayi girkin ta bayan ta gama ne tayi wanka ta tsara kwalliya tanaso taje gidan Ibtee amma kuma bata tambayi Safeer ba gashi batada number shi balle ta kirashi ta tambaye shi"

"Tana nn zaune Safeer ya shigo gidan da sallamar shi "


" Kamar bazata Answer ba sai kuma ta Answer, ta mike da kyar ta karbi briefcase dinsa da ledar daya shigo dashi ta kai komai mu hallinsa, ta dawo ta zauna abinta"


"Yau shukra sai wani share Safeer take yana bata labarin office, shiko sai nunawa yake kamar bema san tanayi ba ya cigaba da bata labarin har zuwa lokacin bacci a nn ne kowa ya tashi ya shige dakinsa"




"Yau kwana 3 kenan Safeer na fita zance, abin na matukar damun shukra, Amma idan ta tuna cewa itace ta bata rawarta da tsalle ta kanyi kuka, in ta zauna ma sai dai tayita istigfari tana rokon Allah ya yafe mata "


" Yau ta kama friday Safeer ne ya fito cikin shirinsa na zuwa office shukra ya tarar a palour idonta duk ya kumbura dan kukan da tayi "

" Ya safeer An tashi lafiya?

"Lafiya kalau shukra "
" Wani abun ya farune naga kina kuka? Ko kin gaji da zama danine?

"Girgiza kai tashiga yi tana goge hawayen da ke gangarowa daga idonta tana kuma kokarin hadiye kukan dake son subuce mata"

"Ko gida kike so ne?
"Eh ka kaini gida gurin Ammii ta fada tana fashewa da kuka "

" To naji zan kaiki amma ki bari sai na dawo daga office "


" Tom " Amma ina so in shiga makota gurin Ibteesam wadda na gaya maka tazo rannan"

"Tom shknn ki gaishe ta "sai na dawo

" Adawo lpy "

" Allah yasa daga nan ya fice daga cikin gidan
"Sallamar shukra ne yasa Ibteesam fitowa daga bedroom ae tana ganin shukra ta fara murna tana mata sannu da zuwa "

" Bayan Ibteesam ta cika shukra da drinks suka fara hira, sosai yarinyar Ibtee ta shiga ran shukra kamar ta kwace ta ta tafi da ita, sai addu 'a take itama Allah ya kawo mata masu Albarka "


" Sai gurin 03:00pm sannan sukayi sallama shukra takoma gidanta "

" Sosai taji dadin zuwanta gidan Ibtee kasancewar ta gaji da zaman gidan ita kadai, shiyasa ta matsu ayiwa su miemie hutu tazo mata"


"To Safeer ya kai shukra gida Amma Ammii bata wani sakar mata fuska ba, sama sama take kulata, sai dare sannan Safeer yazo ya dauketa suka tafi "



" Abin duniya fa ya ishi shukra ganin cewar bikin Safeer ya matso sosai sai wani sabga yake yana wani rawar kai, wani karin abin takaichi ma shine Safeer daya karbo kayanda zai sa ran DAURIN AUREN dakinta ya kawo ya ajiye "




" Yau saura sati biyu bikin Safeer saboda hk ya kawo wa shukra invitation cards ko zata gayyaci kawayenta...............







" Gajiya Safeer yayi da mikawa shukra invitation cards din ya ajiye mata a bedside drower ya fice daga dakin"


"Kuka kawai ta saki sannan ta private tashi ta dauki envelop din daya kawo mata ta wulla ta bayan gado ta kwanta ta cigaba da kukanta "


" Kukan da shukra tayi ne yasa ta ciwon kai sosai, Safeer ganin duk yau bega Shukra ba yasashi zuwa dakinta duba ta "


" Kwance take a kan bed tana kallon sama yayinda hawaye ke gangarowa daga idanunta "


" Bakin gadon yaje ya zauna tausayin shukra fal zuciyar sa amma ya dake ya fara tambayar ta ko wani abu ne yasameta "


" Kaina kemin ciwo "Tace a takaice


" Sannu Allah ya kara sauki, ko zamuje hospital "


" Ko kallo ma be isheta ba ta juya mai baya saboda wani mugun haushin sa takeji yanzu "


" Gajiya yayi da zama ya mike ya fice, be dade ba kuma ya dawo dauke da leda a hannunsa ya ajiye a bedside drower sannan ya fice ya dauko bottle water da glass cup ya dawo ya zauna a kusa da ita, ita dai bata ko kallo shiba "


" Ruwan ya zuba mata a cup sannan ya balla maganin ya mika mata "

" karbi kisha kinji "

" To tace sannan ta karba ta kora ta koma ta kwanta "


" Shima ficewa yayi a dakin ya wuce dakinsa don yin wanka "



" Kwana uku ne kawai ya rage ayi bikin safeer, Shukra ta rasa yanda zatayi jitake kamar ta kai kanta gurin Safeer amma tasan ko zuwa tayi ma baze kulata ba tunda Aure zeyi "


" Safeer ne ya shigo dakin shukra dauke da trolley, tsaye take tana ninke abin sallah kasan cewar idar da sallahr ta kenan ya shigo "


" Shukra kayan fitar biki na kawo miki "

" Harara ta watsa masa sannan tace banaso ka hadawa Amarya "


" Dariya yayi sannan yace ae Amarya an dade da kai mata nata "

" Kai ya shafa kuma wannan sannan ta juya ta shige bathroom ta barshi nan tsaye "


" A na gobe daurin aure safeer ko shigo gidan beyiba tun fitar da yayi da safe, Shukra kuwa sai kuka take tana data Sani, ko bacci ta kasa sai jira take ya shigo "


" Haka ta hakura da jiransa ta kwanta tana istigfari har bacci barawo ya kwashe ta "




WASHE GARI


" Tun asuba Shukra ke jiran Fitowar Safeer tana zaune a palour ta daura kafa daya kan daya tana wani cika tana batsewa "


" Daga shi sai singlet da short nikker ya fito har ya wuce ta ya dawo yana mata wani shu'umin murmushi "


" Shukra cute sannu da zama, naga kin tashi da wuri ko naki taron zakiyi ne bazakije na Mamah ba"

"Harara ta watsa masa kafin tace Bansaniba "

" Allah ya baki hakuri shukra cute yace yana dariya kasa - kasa "

" Mtwsssssss taja tsaki kafin tace munafiki kawae "



" Tana nn zaune ya fito daga kitchen hannunsa rike da cup ya zauna a kusa da ita yana shan tea hankali kwance "



"SHUKRA yi sauri ki debo min kaya na dana ajiye a dakin ki sauri nake wallahi kinsan da safe za a daura AUREN"


"To ina ruwa na "

" Babu Amma dae debo min kayana wanka kawai zanyi mu tafi, ya fada yana mikewa yayi hanyar dakinsa "

" Dani na ajiye maka kayan, yarda ka ajiye haka zaka zo ka dauka wlh taja tsaki sannan itama ta shige dakinta "


" Fitowar Safeer daga wanka kenan yaga Shukra bata debo mai kayansa ba, ae kuwa kai tsaye dakinta ya nufa "



" Direct wardrobe dinta ya nufa ya shiga cire kayansa, A nn gurin ya shiga sa kayan sannan ya dauki perfume dinta ya feshe jikansa dashi "



" Wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubowa shukra ganin cewa da gaske ne fa bikin Safeer yau "



" Shiko bema kula da ita ba ya fice daga dakin cikin sauri "



" Fitowar Safeer yayi dai - dai da fitowar Shukra tana ganin sa ya fito yana gyara hularsa ta fasa masa kuka "

" Zaro idanu yayi ya karaso gurinta donjin me akayi mata "


" Aiko yana karasowa gabanta ta fada jikinsa ta rungume shi gam - gam kamar wata zata kwace mata shi "



" Cikin kuka sosai ta fara Magana
      "Ya Safeer dan Allah kayi hakuri karka kara Aure na tuba bazan kara ba nayi maka Alkawari yima ladabi da biyayya, Dan Allah ka tausaya min wallahi bazan iya zama da kishiya ba tana kaiwa nan ta kuma fashe wa da kuka ta kara kankameshi a jikanta"


"Hakuri zakiyi Shukra kishiya dai sai anyita kuma maganar yafiya ni na dade da yafe miki, so kiyi hakuri yanzu ki barni na tafi it's Already time Kinga sunata kirana ya fada yana janyeta daga jikinsa"



"Kara fadawa jikinsa tayi tana kuka me tsuma zuciya, shi kansa Safeer sai da ta bashi Tausayi dakewa kawai yayi ya tureta sannan yace


"Bari naje inna dawo zamuyi magana kinji "


" Gani kawai yayi shukra tayi baya jikake tim ta fada kan kujera "

" Cikin hanzari Safeer yayi kan shukra jiki na rawa ya daga ta sai motar sa "




" Gudu kawae yake hankali a tashe sai emergency na" Aminu kano ", cikin hanzari yashiga da ita likitoci suka rufar mata shikuma yayi waje"


"Wayarsa ce ta shiga ringing kamar baze dauka ba sai kuma ya dauka hade dayin sallama "


" Daga daya bangaren akace kana ina ne wae? Kai kadai fa ake jira "


" Kana jina haiydar yanzu haka ina hospital shukra ba lafiya so kuje kawai in daura sai ka fadamin "


" Tom shknn "

" Yawwa Haiydar Nagode saina jika "




" Daga haka ya kashe Wayarsa ya cigaba da kaiwa da komowar dayake a gurin"



"Wata nurse ce ta fito aiko da sauri ya nufeta

"Ya jikin Shukra?
"Meya sameta?
"Ta farko? Ya jero mata wadannan tambayoyin a tare"



"Calm down ok"
Yanzu dai mun bawa Shukra Bed so ya kamata ka kira azo daga gida"


"To Aini baki fadamin abinda ya sameta ba"

"Ka fara kiran gida tukun Doctor ze maka bayani, tana gama fadar hk ta wuceshi"



"Mamah ya fara kira sannan Ammii ya musu bayanin inda suke sannan ya nufi office din Doctor "

Sallama ya masa ya Answer sannan ya nuna masa sit ya zauna"

"Doctor ne yafara masa bayani kamar hk

"Wato jinin matarka ne yau sosai sakamokon firgita da tayi Amma insha Allah komai ze daidaita bari na rubuta maka magunguna kaje ka siya kafin ta tashi "

" Da kyar ya iya cewa nagode Doctor sannan ya karbi card din ya fice da sauri "

" Mamah da Miemie ne suka fara zuwa sannan Ammii da Areef, Alokacin ance za a iya ganin Shukra "

" A tare dukansu suka shiga banda Safeer daya tafi gida debowa Shukra kaya "..............







"Shukra ba ganin su Ammii sun shigo ta fara kokari tashi, Mamah ce ta riketa tana mata sannu "



" Ammii dan Allah ku taimaka min ku bawa ya Safeer hkr karya kara Aure wallahi na chanja hali na, kuma bazan kara rufe masa kofa ba"


"Mamah ce tayi saurin rufe mata baki tana jero mata sannu "


" Yi hakuri kinji Shukra Kinga Doctor yace ki dena damuwa ki kwanta ki huta kinji "



" Kuka kawai shukra tasa don ita tayi tunanin Mamah zata ce an fasa AUREN amma sai taji shiru "



" Da sallama Safeer ya shigo cikin dakin hannunsa rike da trolley wanda ya debo kayan shukra a ciki, bayan sun gaisa da su Ammii ne ya nemi guri ya zauna "



" Kokarin tashi shukra keyi Amma Ammii ta hana hakan, kuka take tayi tana kallon Safeer shima kallon ta yake cike da tausayi "



" Ya Safeer dan Allah ka rufa min Asiri kamar yadda Allah ya rufa maka karka kara AUREN nn wallahi bazan iya zama da kishiya ba bana sonta bana kaunar ta"


"Ammii ce tayi saurin doke bakinta tana hararta"


"Karki so kishiyar to kinsan bakya son kishiyar kike abinda kike "



" Ammii wallahi na dena kuma ki tambaye shi ta fada tana kara fasa wani kukan "



" A a Ammii ba hk ake ba gsky ki dena mata fada Kinga batada lafiya, hawan jini ae ba wasa bane "inji Mamah
" zuwa wannan lokacin kukan shukra ya fara ciwa Safeer rai don Shukra tsakani da Allah take kukan hakan ne yasa Shi saurin tashi ya fita daga dakin "



" Mamah ce ta dawo kusa sa Shukra tana ta lallabata taci Abincin da Aysher ta kawo dazu"



"Mamah bazan iya ci ba mutuwa zanyi wallahi, dan Allah ki bawa Ammii, Daddy da ya Safeer hakuri kinji ta fada tana kara rusa kuka wane shi aka aiko ta"


"Da daddare Mamah cewa tai ita zata Zauna da miemie, Ammii ta tafi gida tana ganin kirki irin na Maman Safeer "


" Washe gari da safe Aysher ta kawo abinci sannan ta wuce School "



9:00am Safeer da Haiydar suka shigo duba Shukra, Gaisawa sukayi da Haiydar sannan ya fita dama Mamah da Miemie sun tafi gida don yin wanka saboda haka dakin ya rage daga Safeer sai Shukra"


"Shiru ne ya ratsa dakin ba wanda ya cewa dan uwansa ci kanka, gajiya Shukra tayi da kallon da Safeer ke mata ta mike ta shige toilet abinta "




" Shima Safeer mikewa yayi yaje ya samu Haiydar a waje suka fice daga Asibitin ma gaba daya "




" Ammii ta riga Mamah zuwa saboda haka ta samu damar yiwa Shukra tatas "



" Sosai Shukra take kuka tanajin inama zata iya cewa Ammii
     "Ni na shirya basa kaina shine be nemeni ba"
Amma bazata iya ba, Hakan ya sata ci gaba da kukanta kamar an aiko ta tanajin inama mutuwa tazo ta dauketa a wannan lokacin ta huta da bakin cikin da take ciki a yanzu "


" Wasa - wasa sai da Shukra tayi one week a Asibiti sannan akayi discharging dinta, Mamah ce ta dage sai ta tafi da Shukra gidanta saboda tana kallon yadda Ammii takewa shukra kamar ba ita ta haifeta ba "



" Haka dai suka tattara suka koma gidan Mamah, sosai Shukra take samun kulawa gurin Mamah da Aysher, Miemie ma ba a barta a baya ba don Sosai take damun Shukra da surutun ta kuma itama Shukran tana jin dadin zama dasu, mutanen kirki yadda suke mata ko safeer basayiwa haka "



" Sosai mutanen Mamah da Ammii suke zuwa duba Shukra, Abokin Safeer ma sunzo, Haiydar ko dama kullum sai yazo kodan yaga sahibarsa (Miemie) "



" Kawayen Miemie duk sunzo dan gida - gida tarinka zuwa tana fada musu azo a duba Auntyn ta batada lafiya, in ba kazo ba kuwa zuwa take ta tawo da kai "


" Sati biyu Shukra tayi a gidan Mamah sannan ta koma gidan Ammii kasancewar next week zata koma gidan Safeer "




" Sosai Safeer ya gyara gidansa har furniture's din Shukra sai da ya changer mata, gida dai ya hadu iya haduwa dan da mukaje nida Miemie cewa nayi bazan tawo ba(lols)


"Ammii ta dage sosai take gyara yarta dan ta fahimci ba abinda ya taba shiga tsakanin su da safeer "


" Yau saura kwana 3 Shukra ta koma ji take gaba daya batasan komawa tunanin taya zata soma zama da kishiya "



" Yau ta kama wednesday kuma tun 7:00pm Safeer yazo tafiya da Shukra kasancewar yau zata koma, Kuka take baji ba gani ko a mota bata kalleshi ba sai kukanta ta take har suka karasa gidan............











"Cike da fargaba Shukra ta fito daga motar Safeer, Bakinta dauke da addu 'a ta nufi cikin gidan "



" Baki ta saki tana kallon yadda gidan ya changer yayi mata kyau wlh sai taji zuciyarta tayi sanyi kamar bawani abu dake damunta, Amma data tuna wae su biyu ne cikin gidan sai taji wani bakin ciki ya mamaye zuciyarta "


" Dakin ta tashige nanma sai da tasha mamaki don ya hadu iya haduwa, sai takejin inama ita kadai ce a gidan da tayi amfani da damarta ta faranta ran mijin ta yadda ya faranta mata "



" Wanka shukra tayi tayi sallah'r isha ta kwanta zuciyar ta cikeda tunane - "tunane tana so ta fito palour tayi kallo dan sam batajin bacci amma kuma tana fargaban haduwa fa Amarya haka dai bacci barawo ya kwashe ta a gurin"




"Asubar fari Shukra ta farka, mikewa tayi bayan tayi Addu 'ar tashi daga bacci ta nufi toilet tayi alwala tazo tayi nafila ta
Zauna tana addu' a kasancewar ba a tada sallah a masallaci ba "


" Koda ta idar da sallah zama tayi tana lazimi tanaso ta fita ta gyara gidan ta daura breakfast amma tana tsoron ganin wata a cikin gidan ta "


" 10:14am tayi shahada ta fito daga dakin ta fitowar ta yayi dai dai da fitowar safeer daga dakinsa, har kasa ta durkusa tana gaidashi tana kuma kokarin mayarda kukan dake son subuce mata "


" Kin tashi lafiya Shukra "

" Lafiya kalau "

" Ya karfin jikin "
Alhamdulillahi na samu sauki ae"


"To masha Allah "

" Har ta wuce sai kuma ta dawo Ya Safeer ina Amaryar?

"Za tazo ku gaisa ae karki damu "

" Durkushewa tayi a gurin tana kuka mai tsuma zuciya "

" Ganin hk safeer yayi saurin zuwa ya daga ta  ya rungume ta tsam a jikansa,

"Yi hakuri Shukra nasan ni Mai lefi ne a gurinki, A sanadiyya ta kika kamu da ciwon hawan jini "


" Kiyi hakuri nayi hakan ne dan na gwadaki naga ko kina sona ko bakya sona, Ashe dai kina sona "


" Amma ba maganar Aure "


" Batasan sanda ta saki ihu ba ta kara kankameshi a jikin ta "

" Ya Safeer dan Allah ka kara gayamin bakayi aure ba, kacemin wasa kake min "



" Shukra wasa nake miki banyi wani Aure ba wallahi "


" Sakinsa tayi taja hannunsa suka zauna akan kujera "

" Ya Safeer bikin wa akayi to "

" Bikin Abokinmu ne Tareeq, a office dinmu yake"

"To invitation cards din fa da kaka kawo min zuwa kayi akayi maka su?

"A a na Tareeq dinne fa na kawo miki, baki ganiba "

" Sai a nan ta tuno hakan ta ta fara dariya kafin tace, Ae kana ajiye wa ka fita na tashi na jefa bayan gado "


" Dariya safeer yake hadda rike ciki yace
"Har na tuno Shukra a gadon Asibiti tana cewa


"Ya safeer dan Allah ka rufa min asiri kamar yadda Allah ya rufa maka karka min kishiya "


" Dukan wasa ta fara kai masa yana dariya yana karewa, Ae ko ta sakar masa kukan shagwaba 'ni wlh ka dena bana so' "

" Janyota yayi zuwa jikansa yana lallashinta "


" Yi hakuri Shukra cute, dena kuka kinji yan mata na, Safeer naki ne ke kadai Shukra "

" Na miki Alkawari baki kulawa, Namiki Alkawari bazan miki kishiya ba, A gurina mazaunin mace "HUDU" kike


"Kara lafewa tayi ajikinsa kafin tafara magana "



" Lokacin da akayi auren nn bada son raina akayi shiba, shiyasa na dinga horaka ta hanyar rufe maka kofa "


" A hankali na gane AUREN BAZATA ALHERI NE"



"Ina kara rokonka da ka yafemin lefina a gareka "


" Baki min lefi ba shukra we only mis understood each other and now we burry da hatchet "


" Haka dai sukayita ga yawa juna su sirrin zukatan su  yan duniya ashe suna son junansu gulma ta hana su bayyanawa) "



" Haka suka yini a gidan basuje ko ina ba suna ta hira kamar dama can suna shiri "



" Safeer sai wani farin ciki yake yau fa shi ango ne "


" Da daddare safeer ya je ya siyo musu kajin amarchi, ya dawo ya samu shukra tana jiran shi "


" Bude mata hannayensa yayi bayan ya ajiye ledar daya shigo da ita, Aiko da saurinta taje ta fada jikinsa suka rungume junansu suna masu jin kaunar junansu"



      "AS YOU START YOUR NEW LIFE TODAY I WISH YOU ALLAH 'S BLESSING, MAY GOD BLESS YOU WITH BEAUTIFUL CHILDS, MAY GOD PROTECT YOU FROM EVERY EVIL DEED"

SHUKRA & SAFEER 👌🏻



  

"Jan Shukra Safeer yayi Ya zaunar da ita a tsakiyar palour sannan ya wuce kitchen ya dauko plate, fork, and knife ya dawo ya ajiye a gaban ta, sannan ya dauko ledar daya shigo da ita ya juye musu kajin"



"Knife yasa ya yanka sannan ya dauka da fork ya kai bakin shukra"


"Cike da jin kunya ta kawar da kanta gefe guda, sannan tasa wani fork din ta dauka ta fara ci "

" Karki ce min kunya na kike ji Shukra "


" Komai bata ce ba sai ma sunkuyar da kanta da tayi, dan duk batajin dadin yadda ya kafe ta da ido"


"Shiru sukayi suka ci gaba da cin abincin su zuciyoyin su cike da nishadi, duk daga idon da shukra zatayi sai sun hada 👀hakan yasata mikewa kawae"


"Karki ce min kin koshi "

" Eh na koshi ta fada tana turo baki gaba "

" Tab ai biki isaba kefa Amarya ce"

"Amarya ko Uwargida 3 month wasa ne "

" Koma dai menene dawo ki kara "Ya fada yana kokarin kawar da waccan maganar"


"Seriously am satisfied ta fada tana bin hanyar dakin ta "


" Shima mikewa yayi ya kai plate din kitchen sannan ya shige dakinsa donyin wanka "


" Fito wa shukra tayi daga wanka ta karasa jikin wardrobe dinta ta fito da sabon sleeping dress ta saka, sannan ta dawo jikin dressing mirror ta shafe jikin ta da lotion ta fesa turare sannan ta hau gado donyin bacci "


" Shima da ya fito jallabiya yasa coffee colour ya shafa cream sannan ya feshe jikansa da turare "


" Zama yayi a gefen bed ya dauko system dinsa ya daura kan bedside drower ya fara aikin sa, construction na company yakeyi, wani balarabe ne ya basa kwangilar company 'n kuma nn bada dadewa ba ze tafi don ayi komai akan idonsa "


" Sai 12:00pm safeer ya kammala construction din nan, kashe system din yayi ya mai data cikin jaka sannan ya mike ya kashe globe din dakinsa ya fice"



"Dakin Shukra ya nufa da sallama ya shiga sai dai ba answer kasancewar Shukran baccinta yayi nisa "


" Globe din dakin daya kunnan ne ya farkar da Shukra tamike tana salati "


" Karasowa yayi ya hau kan bed din sannan ta jawo ta jikin sa "


" Nokewa ta shiga yi dan ita tsoro take ji, fahimtar hakan ne yasashi fara mata magana "

" A a Shukra cute kwantar da hankalin ki ba abinda zan miki kawai dai bazan iya kwana ni daya a dakina bane shine nazo tayaki kwana "


" Jitayi kamar ta daura hannu aka tasa ihu, tana son Safeer tana kuma so ta faranta masa, tanajin zata iya jure duk wani radadi indai hakan ze se sashi farin ciki "


" ME yasa Bazai karbi hakkinsa ba a wuce gurin kawai? Sai taji tana data sanin nokewar da tayi, ita kuma anata ganin ae jan ajine tunda mace dai da jan aji aka santa "


" Ji take inama zata iya cewa ya safeer a shirye nake "Amma BAZATA iyaba"



"Haka dai suka kwanta rungume da juna zuciyar ta na mata zafi, Amma tasan komai lokaci ne in lokacin yazo ko bataso sai anyi "



" Da Asuba Safeer ne ya fara bude ido kasancewar dama sama - sama yayi bacci yau, A hankali ya zare Shukra a jikinsa ya kwantar da ita sannan ya shige toilet don yin alwala "

" Ko da ya fito bata farka ba saboda haka ya karasa kan bed domin tashin ta "


" Hannunta na dama ya kama yasa a bakin sa yana tsotsa a hankali, sun kai kusan 2 mints a haka kafin Shukra ta fara bude idonta a kansa "


" Yana ganin ta bude ido ya mikar da ita zaune yana karanto mata addu 'ar tashi daga baccin "


" Bin addu' ar tashiga yi har suka kammala sannan ta mike ta yi hanyar toilet din "

" Yi sauri Shukra kiyo alwalar kizo muyi jam 'i

"To tace sannan ta shige toilet zuciyarta cike da farin cikin kulawar da Safeer ya soma bata "



" Koda ta fito tarar wa tayi ya fito mata da hijab ya kuma shimfida musu abin sallah "



" Karasawa tayi ta dauki hijab din ta hau abin sallah shi kuma ya soma ikama "


" Koda Su kazo Sujjadar karshe Safeer ya dade yana musu addu 'ar samun kwanciyar hankali da zaman lafiya a sabuwar rayuwar su"




"Bayan sunyi addu' a ne Shukra ta mike zata fita "

" Kamo Hannunta yayi ya jawota ta fada jikinsa ya rungume ta hade da dora kansa akan nata "


" Ina zaki kuma? Ya tamvaye ta murya can ciki "



" Duk sai taji ya kashe mata jiki da kyar ta iya cewa ' breakfast zan hada mana "



" No ki bari sai zuwa 10:00am in mun tashi a bacci kyayi kinji ya fada yana shafa smooth cheek nata "

" Office dinfa ta tambaye shi a kasalance "


" Bazani ba kin manta ni Ango ne "



" Nan ta fara kokarin tashi daga jikinsa, yasake mai data ya kwantar "

" Ina zakije ne wai? Ko toilet zaki "ya rada mata a kunne"


"ji tayi wani abu na yawo a jikanta jin hucin bakinsa a kunnenta "

" Bacci zanyi ta bashi Answer da kyar "


" To kiyi kwanciyarki zansa kiyi bacci kinji "


" Komai bata ceba sai kara lafewa datayi a jikinsa hade da lumshe ido "


" Bayan ta ya shiga bubbugawa a hankali kamar yana son yasa baby bacci, A hankali baccin ya kwasheta "


" Saukar numfashinta daya fara ji a hankali ne ya tabbatar masa tayi bacci, Don haka ya je ya kwantar da ita a tsakiyar bed din shima ya kwanta ya rungume ta sai bacci "


" sai gurin 11:00 suka farka Shukra tayi hanyar kitchen shi kuma ya nufi dakinsa "


" Breakfast me rai da lafiya ta hada musu sannan tayi wanka, Tayi shirin ta cikin wasu English wears riga pink, skirt blue tayi parking gashinta da pink ribbon dama shukra bata son kitso a rayuwar ta "


" Pink din hijab tasa karami tasa blue slippers ta fito palour a gurguje, Suna hada ido ya sakar mata murmushi, murmushin itama ta sakar mai sannan ta wuce dinning ta kwaso breakfast din ta kawo palour...........




"Cikin plate daya ta zuba musu abincin, haka ma tea a cup daya ta hada musu, Haka sukaci Abincin Safeer ba bawa Shukra Labarin Haiydar da Miemie sai dariya take kyalkyalawa abinta, shiru yayi yana kallon yadda take dariyar bilhakki Sai yaga ta masa kyau, ita ko jin shirun yayi yawa yasa ta dena dariyar tana kallon shi "


" Meye kake kallo na "Ta fada tana murguda masa baki"


"Shi abinma dariya ya basa kamar wata karamar yarinya har da murguda baki "


" Shiru sukayi dukansu har suka kammala cin Abincin, sannan Shukra ta kwashe kayan ta kaisu Kitchen ta fara wanke wa "


" Jin shirun da Safeer yayi ne yasashi bin Shukra kitchen, Tana jikin sink tana wanke wanke abinta, Ya karaso yana tattare hannun rigarsa "


" Kawo in taya ki "


" Jiyowa tayi tana kallonsa "ka tayani me?

" Wanke wanke ya bata answer yana kokarin karban sponge din hannunta "


" A a kabarshi wallahi "


" Bakya so namiki jika -jika ko shiyasa bazaki bani bako "



" A a ba haka bane hutar da kai nayi wanke wanke ae sai mata "


" To ae ni ko a gida ran duty'n Aysher nike mata wanke wanke da shara tayi girki "


" Ah lallai Miemie fa baka tayata "


" Mtwsssssss ni sa 'an tane to "?

" Ni kawai ki bani na tayaki kinji "


" Haka ta bashi yana wanke tana daurayewa sai ta samu kanta cikin nishadi bata san cewa Safeer yanada sauki har haka ba "



" Bayan sun gama gyara kitchen dinne suka fito palour donyin kallo, Shukra ta zauna a One sitter amma Safeer ya dage wae anan yake son zama "



" Mikewa tayi ya zauna, Gashi nan na barma gurin shknn ko "


" A a ya fada yana janta zuwa jikinsa "


" Ae Kema Anan zaki zauna "

" To ae ya mana kadan ka bari na zauna a can ta fada tana nuna masa two sitter dake opposite dinsu "


"  A a kiyi zaman ki a nan ya fada yana kwantar da ita a jikin sa "


" Bata kara masa musu saima lafe da tayi ajikinsa kamar wata marar lafiya (sub-conscious mind) "


Yinin ranar Safeer beje ko ina ba sai da yamma ne yace da Shukra ze tafi gidan Mamah"


"Ko da tace zata bisa kin yarda yayi wae Amarya bata fita ae"


"To shknn zanje gurin Ibteesam kaji "



" To kije amma karki dade "

" Yawwa tnx"


"Har bakin motar sa ta raka sa saida taga fitar sa sannan ta dawo tayi shirin zuwa gidan ibtee "


" Bata wani dade a gidan ibtee  ba ta koma gida don ta naso tayi girkin dare da wuri "


" plantain rings tayi sannan tayi fruit salad tayi ginger drink tasa a fridge, sannan ta shiga wanka "



" Wani coffee and milk material nata ta saka dinkin riga da skirt kayan sunyi dai dai da jikinta ta saka milk din Ear ring tayi parking kanta da Ribbon milk colour, Bata wani yi makeup da yawa ba tadai shafa powder da lipstick sannan ta feshe jikinta da turare ta fito palour "



" Wayarta ta dauka ta hau online tana karanta wani novel na MIEMIE BIE mai suna #Yar gata ce, sai murmushi take ita kadai abinta tana son writern nn tanajin dadin novels dinta"



"Fusge wayar ta da akayine yasata waiwayowa da sauri "


" Kai ya Safeer ni kabani wayana YAR GATA CE fa nake karantawa ta fada a shagwabe "


" Yanzu saboda Allah Shukra bakiji sallamar da DAN GATAN Ki yaketa bugawa ba kin kafawa waya👀kinata murmushi "


" Sannu da ya Safeer wallahi banji ka dawo ba novel din ne ya tafi da Imami na "



" Zan baka amma sai kayi wanka ta fada tana jansa zuwa dakinsa "


" Da kanta ta hada masa ruwan wanka ta kuma rakasa har kofar toilet, sannan ta dawo ta fito masa da kaya ta turare su ta zauna a gefen bed tana jiran fitowar sa "



40minutes ya dauka a toilet din sannan ya fito, straight gaban dressing mirror yaje ya dauko cream dinsa ya dawo kusa da Shukrah ya zauna"



"Shukra cute tayani shafa cream din nan hannuna ciwo yake ya fada wane zeyi kuka "


" Dariya take yi kasa kasa sannan ta karbi cream din tana shafa masa "


" Baki shafamin a baya na ba "


" Cream a baya kuma ya Safeer ta fada tana mika masa kayansa "


" Turo baki yayi gaba kamar wani karamin yaro 'Ni bazansa kayan bama wasu zan dauko tunda bazaki shafamin a baya ba "


" Yi hakuri dan Allah ya Safeer zo in shafa maka to "


" To yace sannan ya juya mata baya ta hau shafa masa, bayan an gama ne ya shirya taja Hannunsa sai dinning "


" Tun da yaji kamshin plantain rings din nan ya kasa sukuni burinsa kawai yaji shi a bakinsa "


" Ae yana fara ci yahau mata santi ita ko sai dariya take masa harda yi masa waigi da serving spoon "




" Bayan sun gama ne Shukra ta kai komai kitchen ta dawo ta sameshi a palour "



" Yana ganin ta fito ya mike ya karaso gurinta hade da rike hannunta "


" Shukrah cute zo muje mu kwanta ni bacci nakeji "


" To kawai tace shikuma ya ja hannunta sai dakinsa"


"A bakin bed ya zaunar da ita sannan ya fita yaje dakin ta ya debo mata wasu sleeping dress iya gwuiwa, sannan ya dauko mata brush dinta ya fito ya sameta kwance akan bed "



" Tashi kiyi wanka kinji shukra ya fada yana mika mata towel dinsa, batayi musu ta karba har sleeping dress da brush nata ta shige toilet "


" Cike da kunya take kallon kanta a mirror, anya zata iya fita a haka kuwa?

"Mutuwar tsaye tayi lokacin da taji safeer na turo kofar hade da kiran sunanta "




" Shukra kiyi sauri ki fito mana nima fa wankan xanyi ya fada sanda ya shigo toilet din"



"Baki sake yake kallon ta tayi masa kyau, Besan sanda ya daga ta sama yana guyi da ita ba kamar wata baby "

" Kinyi kyau ya fada mata cikin kunnenta "


" Nagode tace tana sauka daga jikansa "



" Be wani dade B ya fito yasaka farar jallabiyarsa ya hawo gadon inda shukra take "


" Jikinta ya shige yasa hannunsa cikin gashi kanta yana shafawa a hankali "


" Shukra najinsa ta mishi shiru, shi duk tunanin sa bacci take, saboda da haka ya dunga bin ko ina na jikinta yana shafawa"


"Shukra fa taji kanta cikin wani ya nayi saboda haka ta kara kankame Safeer wane zata shige cikinsa "


" Bakiyi bacci ba Shukrah ya fada yana dago kanta da hannunsa "



" Dakyar ta iya tattaro nitsuwar tace EH "


" Ok tashi muyi Nafilah to ya fada yana mikarda ita zaune "



" A tare suka shiga toilet suka daura alwala suka fito danyin Nafilar Ma'aurata...............