AUREN BAZATA PART 1



Ma dai daichin gida ne wanda ya tsaru iya tsaruwa, masu hidimar gidan sai kaiwa da komowa suke.                     
Gabaki dayansu suna zaune a dinning table suna breakfast ba wanda ke cewa komai har suka kammala
  Ammii ce ta kwashe kwanukan takai kitchen tahau wanke wa.


     30mints later
Daddy ne ya fito cikin shirin sa na zuwa daurin auren dan kaninsa wanda xa ayi a garin Karaye
"To Ammii zan wuce to daddy Allah ya kiyaye hanya "
" Ameen ameen sai na dawo.

Tafe yake akan hanyar sa ta zuwa Karaye gudu yake ta tsulawa kamar dan shi akayi titin  kasan cewar titin ba cunkoson abin hawa.
       Sai da yaxo dai dai inda ze shiga garin gwarzo ya taka kusa aiko tayar sa ta fashe.

  INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJU UN shine abinda daddy yake maimai tawa, waye zai tai makeshi da sanyin safiyar nn  gashi bashida spare tier balle ya canja.
      Daddy yana tsaye jikin motarsa yana neman mafita tunani yake kodai ya bar motar ne yatafi gurin daurin auren?  To in ya tafi wa zai bar wa motar sa, yasan komai zai iya faruwa idan ya tafi.
   "To ynx ya zanyi yace afili.


Sauri yake tayi kasan cewar yau daurin auren amininsa ya zama dole ya halarchi wnn daurin auren.
 Tundaga nesa ya hango shi kuma tabbas yaga alamar yana cikin yanayi na neman taimako kasa ya farayi da motarsa yayi parking dan gaba da daddy sannan ya fito.

 Sannu Alhaji
Yawwa sannu yaro
"wani abu yasami motar ne? 
" Ehhh taya ce ta fashe gashi banida spare.  
   "subahanallahi" Aikuwa inada spare a bayan motata  nn ya xagaya ya dauko masa tayar.
  Bari naje nn gaba kadan akwai masu gyara sai suzo su saka maka
   To madallah inji daddy yana mai fadada fara 'arsa. Daga nn safeer yy gaba shikuma daddy ya tsaya.
 Befi 20mints sai gashi da Mutum biyu sun dawo nn suka shiga daura taya suka gama.

   Nagode sosai yaro
"Bakomai wlh ae yiwa kaine "
Ina kanufa daddy ya tambaya.
   Karaye zani daurin auren abokina,  Ae nima nn na nufa
 Daga nn kowannen su ya shiga motarsa suka kama hanya wanda cikin lokaci kadan suka isa kuma aka daura auren dasu.

  Sai bayan da aka daura auren ne Alh. Al 'ameen sarakee Ya samu kebewa da safeer inda ya bashi complementary card dinsa
  "Ga wnn card dina ne don Allah gobe ka sameni a office"
  To nagode kuma insha Allah xaka ganni....


  ASSALAMU ALAIKUM wa alaikumussalam sannu da zuwa Alhaji
"yawwa Ammii ya gidan?  "
" lafiya kalau Ammii tace tana binka bayan Alhaji zuwa daki.


   3 hours later
Shukra kixo inji daddyn ki yana son magana dake
    To Ammii shukra tace tana mikewa daga kwancen da take

  Da sallama ta shigo cikin dakin cike da biyayya ta gaida mahaifinta  ya answer da fara 'arsa.
  Zuwa chan daddy yayi gyaran murya ya fara magana kamar hk
  "shukra inaso ki bude kunnenki ki saurare da kyau kuma ki dauka cewa maganar da xan fada miki umarnine ba shawara ba.
    Gaban shukra ne yashiga bugawa da sauri sauri to me daddy xe gaya mata ne wae
 " Kina jina ya katse mata tunanin da take "
 " Ehhh Kawai ta iya cewa tana sauraronshi
Nayi miki miji kuma nn ba da dade waba sai zo ku fahimci juna
"  miji kuma shukra tace tana xaro idonta

   Alhaji miji fa kace
"Ehhh   miji mana menene "?
 Ae naji ka fadi abinda baxe yiwu bane

 Ae kuwa dae sai ya yiwu kuma ki zuwa ido ki gani yana gama fadar hk yafice daga gidan ma gaba daya.




KO WANENE MIJIN DA ALH SARAKEE YA XABA WA YARSA?
  SHIN XASU AMINCE DA AUREN KO KUWA A A?  




Knocking yake a kofar office din Alh sarakee
  " yes come in inji sarakee,
 Kai tsaye safeer ya shiga cikin office din har kasa ya durkusa yana gaida Alh sarakee
Abun ba karamin dadi yama sarakee ya answer fuskarsa a sake
 " Have a sit
"Thank you sir
Safeer nasan xakayi mamakin abinda yasa na nemeka kuma ni anawa ganin ba abun mamaki bane,  Alfarma nake so kayimin dan Allah
  "  Alh wace Alfarma kakeso nayi maka
Inaso dan Allah duk abinda nace kayi min kayi
  "indai be sabawa addiniba me zai hana nayi maka
  "  be saba bama cewar Alh sarakee cikin sauri

    " gyara xama yayi yafara dacewa
A gaskiya na yaba da hnklin ka shine nakeso na hada ka da yata dan Allah ka aure ta
    Maganar ta xowa safeer a BAZATA baxe iya cewa a a ba amma shi har ga Allah bashida burin Aure a wnn lokacin
   " Dan Allah karka ce a a inaso kasani yata batada wani aibu ba kuma dan tarasa mijin aure ne na bakaba  a a kawai dai dan na yaba da hankalin kane nakuma ji dadi da ka temaka min a lokacin da nake tsananin bukatar temako
 " To Alhj madallah nagode
  " nine da godiya safeer  ynx sai ka bani number wayar ka kuma in kuma in ka samu lokaci sai kazo ku sasanta kanku ko
  To insha Allah xanxo.

Yawwa baka gayamin suwaye iyayenka ba da kuma karatunka da inda kake aiki
"sunana safeer muhammad mai lafiya  babana shahararren dan kasuwane, nayi makarantar primary da secondry a garin Abj kasancewar kasuwanchi yakai mahaifina can garin Abj bayan na kammala secondry ne muka dawo garin kano inda na samu Admission a B U K na karanci "Architectural technology"  ynx hk ina aikin gwamnati sannan kuma ina aiki on my own nakanje gari gari indai ai nemeni ina zuwa nayi Aiki.

 To masha Allah, Allah ya taimaka
    " Ameen ameen Alhj nagode
 "  Nine da godiya sai najika

 Daga hk sukayi sallama.



  WASHE GARI
   shukra wai me yake damunki ne ace tunda aka miki maganar auren nn shikenan bakida wani aiki sai kuka
  "Ammii ya xanyi da raina wae ni xa ayi wa auren dole
  To shukra ya xakiyi ae sai hkr kawai
" yanzu Ammii ba abinda xakiyi akai?
   To me xanyi shukra ae a gabanki yace na zuba ido ko?  sbd haka rungumar kaddara ne kawae ya dace dake a halin ynx
   "Bazan iya ba wlh Ammii banason koma wane ne kawai a kyaleni
  To ae sai ki bari inya dawo kije ki gaya masa       (zuwa wannan lokacin Ran Ammii ya soma baci da kalaman shukra)  tana kaiwa nn tafice mata a dakin.

  Wayar shukra ce ta fara ringing kamar BAZATA dauka Ba sai kuma da dauka "Aneesa ce class mate dinta tun a secondry har zuwa ynx da suke karantar" Optometry "  a B U K.
 " Hello Aneesa Y kk
"lfy shukra are you coming today?
"i don't think so
Buh why? 
Am not feeling better
"wishing u quick recovery shukra luv
Thanks
   Aneesa dan Allah inkin gama lectures ki biyo gida kafin ki tafi
    "to insha Allah zaki ganni

    Da sallama Aneesa tashigo cikin gidan Ammii ta samu a falo suka gaisa ann ne ta tambayeka shukra..
     
    Tana ciki tana aikin kuka.
 "  kuka kuma Ammii bari nashiga ciki na sameta to.....




Shukra wae me yake damunki ne Ammiii tace min kina kuka
   Hmmmm Aneesa ba dole inyi kuka ba wae ni xa ayi wa auren dole..
What...come again shukra i didn't get u aure fa kika ce
    "Ehhh aure wae daddy xemin da wani banza wnd ban sanshi ba
    To ynx shukra zuba ido xakiyi ayi auren bawani mataki da zaki dauka.

   Hmmmm banida wani zabi Aneesa abinda dae na sani  shine" Wallahi tallahi daga ranar da aka daura auren nn daga ranar koma wane mijin yayi sallama da kwanciyar hankali da xaman lafiya.... Tunda dae ya zabi aure na tokwa ya xabar wa kansa masifa ne wae ni shukra zai Aura.... Hmmmm!!!


   Hmmmm to nidai ba abinda xance sai dai
Ince Allah ya kyauta
  "Ameen inji shukra"
Nidai Kinga tafiya ta cewar Aneesa tana mikewa
     "ki gaida mamah"
Zataji insha Allah tafada tana ficewa daga dakin.




@Safeer's house

Dukansu na gani zaune a palourn mamah suka kallo
  Safeer ne ya ke ta satar kallon Abba, Abban ne ya lurada shi
    "Safeer ya akayi ne

" Abba wata magana nake so nayi daku sai dai ban san yanda zaku dauki maganar ba,
     Juyowa Dukansu sukayi suna fuskantar shi suna jiran suji me zai ce
  "muna jinka Safeer fadi me kake so kace kaji

  Nan Safeer ya gyara zama ya fara basu labarin tun haduwar sa da Alhj sarakee har zuwa bashi yar shi da yayi
    " Alhamdulillahi "shine abinda daddy yace yana me kara fadada murmushin kan fuskar sa
   " ynx yaushe ne bikin to inji Mamah ta fada da murnar ta.

  Yace baxe dau lokaci ba
  To Allah ya nuna mana
   Ameen Dukansu suka hada baki gurin fada


   Yeyyyyyy!! Miemie ce tasa ihu ynx xan fara kiran kawaye in fada musu bikin yaya na yazo
       Kae ranar akwai buduri wlh xamusha rawa da one leg yeeeeyyyyy ta cigaba da ihu....

Dukansu dariya suke banda Safeer daya hade ransa dama shi ba shiga harkarsu yake ba shi baya son rainin hnkl
    "zan koya miki hnkl wlh meye hk mtwsssssss ya fada yana ficewa daga palourn.

 Allah ya shirye ki miemie inji Aysher (yayar miemie ita take bin Safeer). 



Alh sarakee ya yanke auren Safeer da shukra nn da sati biyu xa a daura aure inyaso ta tare koma yaushe ne.


Yau ta kama ranar da Safeer xexo Ammiii ce ke shirye shiryen ta banda shukra dake kwance a daki kamar kullum tana aikin kuka..............


  Safeer ne ke saukowa daga upstairs cikin shirin sa na zuwa gidan su shukra sanye yake da shadda light brown gezna hannunsa sanye da agogo kirar rolex kansa da hula
    Kai tsaye falon Mamah ya nufa ya shiga ya durkusa kusa da Abba ya shiga gaida iyayensa cike da ladabi
 Da fara arsu suke answer wa
"za a tafi neman auren ne miemie ta fada tana buya a bayan mama
   
   Ai kuwa a xuciye ya taso kamar wanda xe doke ta "yi hkr inji mamah kaifa babba ne
" Mamah yarinyar nn ta raina ni wlh inaji fa dana gaisheku sai da answer
    Dariya daddy yayi yace ayi hkr kaji "tashi ka tafi kar ka makara
    To kawae yace ya fice ransa a bace.....



"kai tsaye safeer gidansu shukra ya nufa wanda cikin lokaci kadan ya karasa, parking yayi a inda aka tanada domin parking motochi sannan ya fito
"kai tsaye cikin gidan yanufa xuciyarsa tana harbawa da sauri da sauri ai kuwa sai yaci karo da kaninta
  "yana ganinsa ya taso da fara arsa
" Good afternoon uncle
"Afternoon! How are you
  "Not bad
" good "
Shukra fa? Ya tambaya
" tana ciki tana kuka
"toooooo to ynx xaka iya karamin ita
   "Ehhh ammii tace in kazo ka shigo daga hk yayi gaba shikuma yabishi har guest room ya zauna shi kuma ya fita

   Ammii! Ammii! Ammii
" Na am meye ne kake ta kirana ta fada tana fitowa daga kitchen
   "Ammii mijin Aunty shukra ne yazo
 " ohhh har yazo ince dai ka kaishi guest room ko
  "Ehhh Ammii yana chan yace in kirata
  " to jeka abinka zan turo ta
"To kawae yace ya koma gurin safeer inda suka cigaba da hirar su kamar dama chan sunsan junansu ne.

    "sanda Afeer ya fita Ammii kai tsaye dakin shukra ta shiga 'shukra tashi ki shirya ga safeer chan yaxo yana jiranki'     tana gama fadar hk tafice ba tare da ta jira me Zata ceba"

Koda Ammii ta fita shukra xamanta tayi batada niyyar tashi har sai da takai 40mints a zaune
    "Ammii ce ta leko 'ynx shukra har ynx kina nn a zaune kinbar yaro yanata jiranki shima fa yana da abinyi amma ya vari yatawo gurinki amma kika barshi a zaune ko?
" A a Ammii ynx xan tafi fa.
     "karma ki tafin mana ynx in kira Daddy in fada masa
  " Dan Allah kiyi hkr Ammii wlh ynx xani ta fada tana mikewa
     Ammii ce ta fara fita sannan itama ta fita

"kai tsaye guest room ta shiga Amma koda ta shiga sai tayi tsaye abinta ta kuma sunkuyar da kanta dan ko kallo ma be isheta ba"


  "Tsahon lokacin suka dauka ba wanda yace da dan uwansa komai
   " safeer ne ya katse shirun ta hanyar mikewa yana cewa toni xan wuce
  "sai na dawo ko
" komai bata ce ba illa matsa masa da tayi ya huce
     Yana fita ita ma ta fice kai kai tsaye dakinta ta shige ta rufe.


   "koda safeer ya koma gida be nuna wa iyayensa hk ne ya faru ba kuma koda Alhj sarakee ya kirashi cemasa yayi to karbe shi hannu biyu - biyu.

 

" To biki fa ya gaba to kamar yadda Alhj sarakee yace xa a daura aure inyaso ta tare daga baya hk kuwa akayi
    " Yau ta kama saturday wanda yaune za a daura AUREN  iyayen sai farin ciki suke banda yayan da suke a cikin tsananin bakin ciki musamman shukra da ba son auren take ba
   'Har gwara na safeer wanda shi daman tunda yaga shukra yaji sonta ya shige shi sai dai yayi wa kansa ALKAWARIN baze taba nuna mataba har sai ya koya mata sonshi

 ( uhmm su safeer manya)
   "To abokan safeer duk sun hallara a gurin daurin auren don taya shi murna".

Sanye yake da farar shadda tasha aiki wanda aka yimusu shida Abbansa iri daya, bakin takalmi da bakar hula yasa sai kuma farin agogo da yasa sai kyalli yake yana ta fara a wadda shi kansa besan na menene ba kawae dai ya tsinchi kansa cikin farinciki ne a yau din   ( Niko nace luv ne).


   To Daurin auren ya samu halartar manya manyan mutane daga ko ina a fadin Nigeria wanda yawanchinsu abokan Abba da daddy ne
   "An daura AUREN akan sadaki naira dubu dari.
    Haka dai daurin aure ya watse kowa na farin ciki ana kuma ta sa albarka.
   To kamar yadda daddy yace shukra BAZATA tare ba hk kuwa akayi bata tare dinba tunda ynx ma final exam dinta xata fara ta kammala university.
   To shukra fa sun fara exams gadan gadan wanda ynx ma sun kusa gamawa shikuma safeer ya cigaba da zuwa Aikin sa kamar da. 


      Shukra ta kammala exams dinta kuma ansa ranar tare war ta nanda sati uku.

    "Duka banga rorin biyu shirye shiryen su suke tunda xa ayi mothers night kafin akai amarya dakinta.

  " yau ta kama saturday wanda yaune xa ayi mothers night shukra taci kwalliya kamar ba gobe "Fancy Makeover" itace ta mata kwalliya kuma tayi shirinta cikin wani material me tsadar gaske kalar peach tasa head orange    (hmmmm abin dai ba a cewa komai readers zanso kuga shukra yau din nn ba karya) takalmi da jaka duka orange tasaka.....
   "Daga nn dai aka dunguma zuwa" Shukra event centre "inda ann ne za ayi mothers night din.

    To anchi ansha Alhamdulillahi guri ya kayatu daga nn ne aka kwashi shoki sannan aka rufe taro da addu a   aka dauki amarya aka wuce da ita gidan ta dake nn Nassarawa G R A................................. 




    ASALIN SU

Alhj AL 'ameen sarakee haifaffen garin adamawa yola ne yayi karatun primary & secondry dinsa a garin Adamawa wanda daga nn yayi exam jinsa wato Jamb ya kuma samu point me kyau
    Ya nemi admission a usman danfodio university sokoto wanda cikin yardar Allah ya samu ya fara karanta 'Geology'.
      To bayan ya kammala karatun sa ne be dade ba yasamu Aiki a wani company a garin kano inda ya tattaro gaba daya ya dawo kano da xama


   "Alhj sarakee ya hadu da matar sa fateema ne (Mahaifiyar shukra) a saudiyya inda yaje aikin hajji
   " itama fateema gabaki daya yan gidan su suka je Aikin hajjin kasancewar mahaifinta me Arzikin gaske shine senator na kano central a wnn lokacin
      "To kasan cewar A lokacin Aikin hajji suka hadu yasa basu wani fahimci junansu ba sundai yi exchanging numbers na niyyar in sun dawo gida sarakee zaije ya sameta.

   " to bayanda suka dawo gida ne Alhj sarakee yaje gidansu fateema kuma ta hada shi da iyayenta..
  Baban fateema ya yaba da hnklin sarakee kwarai shiyasa ma bayan dayayi bincike a kanshi sosai ya nemeshi ya kuma shaida masa ya turo iyayensa.

  " Iyayen Alhj sarakee sun zo sun kuma yi duk abinda ya kamata akasa ranar biki wanda ba a wani dau lokaci ba aka daura auren aka kuma kai fateema gidanta dake unguwar 'Farm center'.

      To zaman fateema da sarakee xama ne abin sha awa domin akwai girmamawa da mutunta juna.

 'Haka zaman su ya cigaba har na tsawon shekara biyar wanda a wnn shekara biyar din fateema ko bari bata taba yiba balle haihuwa abinda yayi matukar daga mata hnkl kenan
    "A bangaren sarakee kuwa sam abin be dameshi ba shine ma kullum yake kwantar mata da hankali yana cewa haihuwa ta Allah ce Kuma lokaci ne beyiba in yayi xa ta haihu
  " To da wannan kalami na sarakee fateema tayi amfani wajen kwantar da hankalin ta.
    Ana cikin haka ne fateema ta sami ciki, zo kaga murna wajen sarakee da fateema kai har ma da iyayansu wanda daman suma rashin haihuwar ya damesu shiru dai kawae sukayi.
    
   "Ciki dai yana samun kulawa yadda ya kamata
   Haka suka cigaba da kulawa da cikunsu har watan haihuwa yayi wanda Alhj sarakee takanas ya tafi 'Egypt' danyin siyayyar kayan baby

   " To ana gobe fateema xata haihu sarakee ya dawo wanda washe gari da asuba fateema ta tashi da ciwon mara da ciwon baya wanda sarakee be bata lokaci ba ya dauki fateema sai asibiti.

    " Cikin lokacin da be wuce awa daya ba fateema ta haifo kyakykyawar yarta me kama da Alhj sarakee sak daga nn akayi discharging dinsu kasan cewar fateema da babyn lafiya kalau suke.

    " Ranar suna yarinya tachi suna 'ZAINAB' wato mahaifiyar Alhj sarakee hakan nema yasa suke kiranta da suna 'SHUKRA'



   " Sai da shukra ta kai shekara 7 sannan fateema ta kara samun wani cikin. To wnn cikin ma anyi farin ciki da samun shi kasancewar sun cire rai ma da kara samun wani cikin.


    ," Haka dai take ta rainoncikin har lokacin haihuwar yaxo inda ta haifi yaron ta namiji.
   "shikuma sunan mahaifin fateema yaci wato Mukhtar suke kiransa da 'AREEF.


   " Tundaga kuma wannan lokacin har zuwa ynx fateema bata kara haihuwa ba.
      "Haka yaran suka taso cikin soyayya da kuma kulawar iyaye sosai yaran suke da tarbiyya ga girma ma manya ga kuma kunya da tsoron Allah.






  CIGABAN LABARI

 " TO koda safeer ya taso daga office gidan mahaifin shi ya wuce kai tsaye inda iyayen nashi suka hadu suna mai nasiha kan ya kula da matar sa domin amana ce a gurin.
  " Godiya safeer yayi musu sannan kuma ya kama hanyar gidansa xuciyar sa cike da sake sake tunani kawae yake wace irin tarba shukra xatayi masa?
     " zata karbi kaddara ne ta zauna dashi a hk ko kuma BAZATA karba ba?
      "To da wnn tunanin ne safeer ya karasa gurin wani suya spot ya siyi kaji da kuma fresh milk xe kaiwa amaryar sa...........

      " Bayan yagama da suya spot kai tsaye gidansa dake nassarawa G R A ya nufa koda ya isa yayi worn a gate, gate man ne Y taso da fara arsa ya bude mishi yana gaida shi da fara arsa.
   " To safeer dinma da fara arsa yake answer wa kafin ya wuce gurin da aka tanada don parking yayi parking motarsa sannan ya nufi cikin gidan kai tsaye..........................





    Ko da SAFEER ya shiga cikin gidan kai tsaye dinning area ya huce ya ajiye kayanda ya shigo dasu sannan ya shige dakinsa.
    "kayan jikin sa ya rage ya fada bathroom don yin wanka.



   " A bangaren shukra kuwa yan kawo amarya na fita ta mike ta rufe kofar ta sannan ta koma tayi wanka tasa sleeping dress nata ta kwanta.

    "Bayan kamar 30 mints da shigar SAFEER toilet ya fito daure da towel a waist nasa da kuma wani a hannun sa yana goge kansa dashi.
   " kai tsaye gaban dressing mirror sa ya wuce ya shafe jikinsa da lotion sannan yasa turare ya wuce kan gabon sa dan sa kaya wanda already dama ya fito dasu.

    Bayan da ya gama shirya ne ya fito ya nufi dinning area ya dauko ledar da yashigo da ita sannan ya wuce dakin shukra.

    "Yana karasawa ya murda handle din kofar amma ga mamakinsa sai yaji kofar a rufe gam.

    Cikin bacci shukra taji ana taba handle tsaki kawae taja tana hararar kofar kamar yana kallonta.
   " A zuciyar ta take cewa munafiki da ajinka xan bar kofar a bude ne" mtwsssssss ta dada jan tsaki sannan ta juya baya ta cigaba da baccin ta.
   


    "Shiko SAFEER juyawa yayi ya nufi dakinsa jin kofar shukra a rufe.



   " Washe gari misalin karfe 12:00 na Rana ko wannen su na dakin sa.
"knocking  din da ake a kofar falo ne yasa SAFEER fitowa ya karasa ya bude kofar.

    "kokarin tureshi take yi xata shiga ciki da basket a hannunta
  " ke bakida hankali ne wae kike ture mutane ya fada a tsawace yana binta da mugun kallo...... Wallahi ki kiyaye miemie inba hk ba hmmmm ya fada yana wuce wa cikin falo.

     "Dan nazo gidan ka shine kake min hk ta fada tana tura baki gaba kamar xatayi kuka.
    " Ammiki din ya fada yana hararar ta (shi sam be so wannan yarinyar tazo ba don surutun ta yafi aikinta yawa).

   "Wae ke me kika zo mn gida da sassafe.

  " Baki ta saka tana kallon shi da mamaki 'ynx ne safiya ya SAFEER?...


"To ynx ma ba wannan ba ina Aunty na.

   Tana ciki ya fada a takaice.
  "Au ita bata rashi ba ikon Allah koda yake ae da gajiya gwara ta huta.
  " Gajiyar me ya fada yana mikewa wane zai daketa.

    "Tana ganin haka ta mike gajiyar biki fa nake nufi.
   God save you ya fada yana koma kan kujera.
   " To ynx yaya haka xan tafi ban ganta ba.
   "Ehhh yace yana nuna mata kofa 'fita Dalla kinzo kin Sani a gaba da surutu
      Fita tayi tana waigensa tana zuwa bakin kofa ta labe shikuma ganin ta fita yasashi komawa daki tunda bashi da abinda xeyi.

   " Aiko miemie na ganin ya shige daki tashigo cikin gidan da saurinta tana waige- waige.
    Kai tsaye dakin shukra ta huce aiko sai ta ganta tsaye jikin dressing mirror tana makeup.

   " Aunty shukra ta fada tana yi mata murmushi.   


    "Murmushi itama shukra take mata haka kawai taji tana son yarinyar.
    " ya sunanki ta fada tana kamo hannunta.
     Sunana miemie.
 "Miemie ya gida ya mamah?
"   lafiya kalau muke.
Aunty wae me yasa yaya ya hanani inzo gurinki ta tambaye ta tana karewa dakin kallo.
  
     "Bakomai miemie inaji saboda sanda ya fita ina bacci shiyasa yayi tunanin ban tashiba (Tayi mata karya).


       Ok na dauka sbd yaga kin gajine bayaso in tashe ki.  

  " Gajiyar me miemie? Ni ban gaji ba ae.
    Uhmm kawae tace tana hayewa gadon.

   " Dariya shukra tayi ta koma ta cigaba da makeup dinta.

       "A takaice dai miemie a gidan ta yini sunata hira da shukra kamar dama sun saba da juna.
       " Sanda miemie xata tafi sai da shukra ta cika katuwar leda da kayan makeup ta bata.
      Godiya sosai tayi mata sannan SAFEER ya dauketa suka tafi.



     " Yau ma da safeer ya dawo dakin shukra ya wuce amma yasame shi a rufe juyawa kawai yayi ya koma dakinsa kasan cewar a gajiye ya dawo (shi dama ba wani abu xe mata ba kawai dai zai duba lafiyar tane kamar yadda mahaifinsa yace amana ce a gurin sa).




      " Yau sati biyu da bikin safeer & shukra amma cikin sati biyun nn safeer be taba sa shukra a idonsa ba.


        Dawowar sa daga masallaci knn amma ga mamakinsa sai yaga kofar shukra a bude ae kuwa sai Y xarce dakin.

    " Shigarsa yy dai dai da fitowar shukra daga toilet daure da towel dinda be karasa rufe mata cinya ba..
   Kallon kallo suka shiga yi kafin shukra ta bude baki ta fara zaggaga mishi masifa.

Wnn wani irin hauka ne xaka shigo dakin Mutum ba excuse ta fada tana hararar sa..

     Hauka ya nanata kalmar a zuciyar sa

   "Allah ya baki hakuri ya fada yana juyawa zai fita.
   " Yana zuwa bakin kofar ya rufe da key sannan ya xare key din ya sa a aljihun wandonsa.
      "Takowa yayi gabanta fuskar sa a daure ba alamar dariya.

   " Iya tsorata shukra ta tsorata nn ta shiga yin baya - baya shi kuma yana binta.

     "Hannu yasa ya jawota yana kokarin kunce towel din jikin ta" Bari ba miki cikin mahaukachi yanda ko waje kika fita kika ga mahaukachi vazakiyi masa goriba tunda kina dashi.

   "Kuka tashiga yi tana turashi yayinda take rike towel dinta da dayan hannun, Amma dake karfin ba daya ba sai da ya kunce towel din sannan ya turata zuwa gadon shima ya hau.

     " Ganin batada wata mafita yasata fara rokonsa 'Dan Allah ya safeer ka bari wlh tsoro nakeji, na tuba bazan sake ba.


   " Gani kawai shukra tayi safeer ya mike ya nufi kofar fita sannan yasa key ya bude ya fece. (shi dama beyi niyar mata komai ba kawae dae barazana ya mata).

 
   " Tun daga wannan rana shukra take masifar tsoron safeer bakuma ta sakachin kin rufe kofar ta.


  " Yau ta kama monday kuma yau safeer zai koma aiki sbd hk ya tashi da wuri ya gama shirin sa na zuwa office ya fito palour rike da briefcase dinsa. Ko dinning be kalla ba tunda yasan shukra ba zatayi masa girki ba.

   " Yasa kai xe fice kawae tasha gabansa hade rai yayi yana kallon ta shi sam be ma kula da ita a palour'n ba,

    ," ya safeer dan Allah xan bika ka kaini gida
   To jeki dauko hijabi mu tafi..

 Ihu murna tasa ta shige daki da gudu




"koda shukra tashiga cikin dakin bata wani dade ba kasan cewar dama a shirye take mayafi kawae ta dauko ta fito ta samu safeer zaune cikin motarsa yana jiranta.

"Bude motar tayi ta shiga bata cemasa ba shima bece mata ba haka suka kama hanyar gidan su shukra kowa na sake sakensa cikin ranka.


     "cikin lokacin da be wuce 40 mints ba suka karasa gidan su shukra, kasancewar safeer nada aiki sosai a office yasa ko da shukra ta fita be bita cikin gidan ba.


   " Ango kasha kamshi abokinsa yace masa yana dariya irinta tsokana.

   "Koma bece ba yakaro yana mika masa hannu suka gaisa sama - sama kasan cewar sun kusan makara.


" sanda shukra tashigo cikin gidan bata samu kowa a palour ba hakan nema yasa ta shigewa dakin Ammii kai tsaye.

    "zaune ta samesu ita da Areef suna kallon wani serious.
 "  Da mamaki suke kallon ta kafin Ammii tayi karfin halin mata magana

      "ke kuma lafiya kika xomana gida da sassafe, ina safeer din yake ta fada taba kallon kofa kamar me neman shi.

   " Ya wuce office in ya tashi zai shigo ae ta fada tana wucewa kan gadon Ammii.

    "Aunty shukra yaushe ya safeer xe dawo inji Areef.
 

  " Ban Saniba ta fada tana juya masa baya.

  "To Aunty ki kirasa ki tambaye sa mn.

  " Karka dameni Dalla malam.

  " Bekara cewa komai ba illa ma fitan da yayi daga dakin.

   " Duk abinda suke Ammii na jinsu sai da Areef ya fita ne ta juyo tana kallon shukra

     "shukra anya ko kuna zaman lafiya da yaron nn

    " Ammii wace irin magana kikeyi ne wae, waya gaya miki bama zaman lafiya.

    "Halinka nasani ae shukra.
" To Ammii ki kirasa mn ki tambayesa.

      "Bazan kirasa ba sai dai in bari shawara kan kiji tsoron Allah kada ki tauye wa yaron nn hakkin sa karki ganshi shiru - shiru ki zaluncesa, idan mu bama ganinki Allah na ganin ki.

     " Kai Ammii dan Allah wae waya fada miki bama zaman lafiya me ma ya kawo maganar xalunta da wani tauye hakki.

   " kedai kika Sani inji Ammii tana ficewa daga dakin.



    "shiru shukra tayi tana tunanin mgnr da Ammii ta gaya mata, tanason daukar maganar Ammii amma shedan yana mata huduba.






      4:00 pm


" Daddy ne ya shigo cikin gidan daga office shukra yasamu a palour, da mamaki yake binta da kallo.

    "Daddy sannu da zuwa ta fada kafin Ta durkusa har kasa ta gaida shi.

    " Ba yabo ba fallasa ya answer sannan ya shige dakinsa, Ammii ma ta fito daga kitchen tabi bayan daddy.

       4:40 daddy ya fito palour yace Ammii ta kira masa shukra.

"Bayan Ammii sun fito tare da shukra dukansu suka zauna a kasa suna jiran me xance.


    "shukra lafiya na ganki a gida kuma.


       Ita abinma mamaki ya bata exactly tambayan da Ammii tamata irinta daddy ya mata.
  " Lafiya kalau daddy kasan yau ya koma office shine yace bari ya kawoni gida inya dawo xexo mu tafi.


      "Ajiyar zuciya daddy ya sauke yace to madallah Allah ya dawo dashi lafiya.

       Ameen sukace dukkansu kafin kuma shiru ya ratsa palour ' n.

       " Shukra ce ta katse shirun ta hanyar cewa daddy daman inason magana da kai.

     "Dawo da kallon sa yayi kanta sannan yace ina jinki.

    " Daddy so nake asamomin Aiki in dinga zuwa da xaman gida, kaga duk kawayena damuka gama service aiki suka samu.

      "sbd kawayenki na aiki shine kema xakiyi Ammii ta tamabeyata.

   " A a Ammii gani nayi da zaman gidan ai gwara na dinga zuwa aiki ko.


     "To shukra ae alhakin aikinki ba a hannu na yake ba mijin ki keda ikon samo miki aiki baniba.

      " To daddy kamishi magana dan Allah ta fada kamar zatayi kuka.

       "In banda abinki shukra ae kin fini kusa da safeer ke yakamata ki tamvayeshi, kuma bama wannan ba yana iya yiwuwa in tamabyeshi kuma bayaso amma ya amince sbd ni na tamvaya baxe iya cewa a a ba kuma Kinga ae na shiga hakkin sa ko, Amma idan ke kika tamabyeshi tunda ba tsoronki yake ba xe gaya miki gaskiya in yana so ko baya so.



       "To tace tana goge kwallar data cika mata idonta.


        Shiko daddy yana gama maganar sa ya tashi ya shige dakinsa.
     Ammii ce ma ta tsaya tana bata baki kantayi hkr ta tambayi mijinta inya bari to, in be bari bq kuma sai ta hkr.




       6:00 pm safeer ya tashi daga aiki yana cikin tattara files din dake gabansa abokinsa ya shigo.


          "Gaisawa suka shiga yi kafin Abokinsa ya zauna,
     " safeer wae ya naganka haka ne so silent inji haiydar.

      "Bakomai safeer yace yana dauke kansa daga kallon haiydar.

    " Da komai safeer sai dai in baxaka fadamin ba, amma a gani na be kamata ka boye min komai a yadda muke da kai Amma bakomai in bakason fadamin bazan matsa mk ba.

       "ka gane haiydar wallahi kwata kwata banida kwanciyar hankali tunda akayi auren nn, na dauka bayan auren komai xe dai - daita ashe tashin hnkl ma yana gaba.

      " Haba safeer ynx akan wnn ka tayar da hankalin, maxa fa gwagwarmaya aka sansu dashi, ae kai da kanka xaka jata a jikin ka ka mantar da ita cewa AUREN BAZATA aka yimata ka koya mata sonka bawae ka tsaya zuba ido ba.

        " Ta yaya haiydar? Taya zan koya mata sona, bayan tunda akayi bikin yau sati biyu knn ban taba sata a ido na ba sai yau, beside ma she is arrogant as a dethroned chief, she is feeling herself because she comes from a very influensive family. Thats why she's doing what she want to me, Amma bakomai idan munada rabon farinta ran juna watarana sai mu faranta idan kuma bamuda shi sai Allah ya kawo mana mafita.


     To Allah ya kyauta haiydar ya fada yana mikewa.
      Mikewa shima yayi yana cewa Ameen suka a tare inda safeer ya nufi gidansu shukra kai tsaye bayan ya tsaya a well care ya musu shopping.....




7:30 pm safeer ya isa gidan shukra bayan yayi parking motar sa ya fito ya nufi cikin gidan rike da shopping din daya yi musu.

"Dukkansu a palour ya samesu, durkusawa yy har kasa suka gaisa da daddy sannan Ammii.

     "Bayan kamar 10mints suka fito gabaki daya don musu rakiya, har gaban motar su suka rakasu Ammii na dada yiwa shukra nasiha kan tabi mijinta.

     " uncle zan biku "
" A a Areef gobe akwai skul ka bari ran friday zanzo sai mu tafi"
     To kadai yace ya koma cikin gidan ransa a bace don ba hk yaso ba.


       Minti talatin ne yakai su shukra gida bayan safeer yayi parking ne duka suka fito kowa ya nufi dakinsa.




      "To washe gari safeer gidansu yakai shukra daze tafi office.

   " Da murnar Mamah ta tare ta, bayan ta gabatar mata da abun motsa baki ta kira mata Aysher ta fice ta basu guri
    

    "Hira sosai sukeyi da Aysher anan ta gane Aysher nada kirki aranta tace dukansu suna da kirki da son mutane sosai.

    " Aysher wae ina miemie ne "
  "  miemie taje skul amma ynx xaki ganta ta dawo sbd suna exams ne"

    "To Allah ya dawo da Ita lafiya"
     "Ameen Aysher tace" sannan suka cigaba da hirar su.
 

       "Ko da lokacin girki yayi ma tare sukayi da shukra kasancewar shukra ta iya girki sosai.

     " 12:14miemie ta shigo cikin gidan da gudun ta kamar an jefo ta aiko tana ganin shukra tayi gurin da gudu ta fada kanta tana murnar ganin ta.

     "Itama da murnar ta take tamvayar ta" ya exams "
    " Exams Alhamdulillahi Aunty, ina ya safeer?
     "Yaje office miemie"
"to kawae tace sannan tashiga cikin don yin wanka.

       08:40 safeer yazo ya dauki shukra inda Mamah ta cika shukra da tsaraba suka rakasu har gurin mota.

    "Aunty shukra xan biki miemie ta fada a hnkl yadda bazasuji ba 
   " To jeki debo kayanki mu tafi "
    " Aunty Mamah bazata bari ba sbd skul "
    " To kiyi hkr ran friday zansa ya safeer yazo ya tafi dake kimin week end a chan ko.
     "Ihu murna tasa ta shige cikin gida da gudu.
      




     " Yau ta kama friday kamar yadda safeer yayi Areef alkawari yaje ya dauko shi bayan sun sha Fama da Ammii wae baza shiba ze takura musu.

       Ko da suka shiga cikin gidan shukra da miemie da Aysher suka samu a palour suna hira abinsu.

      Dakinsa ya xarce bayan sun gaisa dasu Aysher don watsa ruwa.

      " mamaki ne ya cika Aysher ganin shukra ko kallon Safeer batayi ba ballan tana ma ta gaida shi.
   " Wai dama har ynx basa zaman lafiya ne? Ta tambaya kanta.


     "Ataikace dai su miemie yini sukayi agidan da daddare safeer ya maida su gida.

     11:00pm shukra, safeer, Areef na zaune a palour suna kallo, safeer ne ya mike yayi wa Areef sai da safe sannan ya wuce da kinsa.

     " Uncle ni a gurinka zan kwana inji Areef ya fada yana bin bayan safeer
" To Areef je Aunty tama wanka kazo mu kwanta.
     "To ya ce sannan ya wuce dakin shukra.

  

     " karfe uku dai - dai shukra ta farka sbd wNi axababben ciwan mara, dama tayi yi ko wani month, kuka take tayi tana juyi tun tanayi ita kadai a daki har ta saki ihu wanda ya sa safeer farkawa a gigi ce.

      " Da sauri ya karaso dakin shukra inda ya sameta tanata juyi a kasa.
    " jikin sa har wani rawa yake yana kokari dakata sai jero mata sannu yakeyi.

     Haka dai ya daga ta ya kaita motar sa sannan ya dawo dakinsa daukan key.

      "Duk wannan abun da akeyi Areef be saniba baccin sa kawai yake hakan ne ma yasa safeer be taba shiba ya dauki key dinsa ya fice da sauri.


         Kai tsaye asibitin Aminu kano ya wuce da ita inda cikin sa a a ka karbeta akayi emergency da ita.


       "kaiwa da komowa kawae yake a bakin emergency gumi duk ya jika shi, sai tunani yake azuciyar sa 'wnn wani irin ciwo ne yarinya sai suma takeyi (Don sau uku tana suma a hanya kafin suxo).


       " yana cikin wannan tunanin ne wata nurse ta fito take gayamasa an bawa shukra gado takuma bashi list na maganin da ake bukata.

      " sai asuba bayan safeer ya dawo daga mosque ne yasamu ganin shukra.
     "koda yashiga cikin dakin idonta biyu tana ganishi ta dauke kai tare D rufe ido kamar me bacci.
     " ya jikin ki ya tambaya yana xaman abakin gadon.

      "Kamar baza tayi magana ba sai kuma chan tace 'Da sauki'.
  "  ALLAH ya kara sauki to"


      "shiru ne ya ratsa dakin kafin safeer ya dauko wa yarsa yayi dialing number'n Aysher.
  " Bayan sun gaisa ne yake fadama ta shukra ba lafiya ynx hk ma suna Asibiti.


          "Dakin Mamah ta shiga ta gaya mata sannan ta wuce kitchen don hada musu breakfast.

     " Kallon sa take tanason masa mgn amma takasa.
     "shine ya fahimci hkn a nn ya tamvayeta.
   " wani abu kike so "
" Ammii nakeso ka kira min"
   "komai bece B yashiga dialing number'n Ammii inda yana shiga yamika mata tare da ficewa a dakin.

   " kusan tare Ammii D mamah suka iso.
    "Bayan sun gaisa ne Mamah ta yiwa shukra ya jiki.
    " Da ladabi ta answer sannan ta gaidasu duka.

      "shukra wae meke damunki ne inji Ammii.
" kamar baxata answer ba chan tace 'ciwon mara'
     Baki sake Ammii take kallon ta da mamaki wae ciwon mara.
    "ita dai tasan in mace na ciwon mara da zaran tayi aure take denawa, likitochi da kansu suke bada shawarar auradda mace mai ciwon mara.

   " to meyasa har yanzu shukra take ciwon mara, kardai har ynx ba abinda ya shiga tsakanin yaran nan?

   Inko hk ne shukra zata gane kurenta.....

SAFEER ne ya shigo cikin dakin hannunsa rike da kaya, a bakin kofa ya ajiye kayan sannan ya karaso ciki ya durkusa kusa da Mamah suna gaisawa da Ammii cike da ladabi.

    "ya me jiki Mamah ta tambaya"
    "Da sauki Mamah"
"Allah ya kara sauki "
     " Ameen suka hada baki dukansu wajen fada.


   "Ammii ina Areef"
"Areef yaje skul "

     To Allah ya dawo dashi lafiya.
   Ameen.
" Safeer bazaka je office bane Ammii ta tambaya?
     "Ehhh Ammii zan zauna Ann!
   

    "  A a baza ayi hk ba tashi xakayi ka tafi inyaso anjima kazo kaji jikin nata inji Mamah.


     AE tama ji sauki inji Ammii Tafada tana hararar shukra, don ita jira take su kebe da shukra ta fada mata dalilin dayasa taki bawa safeer kanta"

     "Tashi kaje gida kayi wanka ka tafi office kaji dan Albarka cewar Ammii."

    "To Ammii Allah ya bata sauki ya fada yana ficewa daga dakin"

     2:40dai - dai safeer suka shigo shida haiydar hakan ne ma yasa bayan sun gaisa da su mamah suka fita suka basu guri"
   

     "Gaisawa haiydar sukayi da shukra cike da girmama juna, sannan haiydar ya ajiye mata bandir na 100 ya mata sallama suka fito tare da safeer.




     " se bayan magrib sannan safeer ya tafi kai maamah da Aysher gida, sai a nn ne Ammii ta samu damar kebewa da shukra.

     " shukra "
" Na'am Ammii ta fada ba tare da ta dago ta kalle taba.

    "HAde rai Ammii tayi sannan tace' dake nake shukra dago idonki ki kalle ni"

     "A sanyaye shukra ta dago tana kallon Ammii zuciyar ta na harbawa da sauri da sauri wane zata fito don tsoro da fargabar.

     " ki fadamin dalilin dayasa kika kika hana safeer kanki shukra "

   " Tambayar tazo mata a BAZATA dan bata taba tunanin Ammii zata gane ba (Yaro yarone).

     "uhmm uhmm Ammii.... Ke ki kiyaye, ki kiyaye ni shukra ni ba sa'ar bace wallahi.

     " kafura ce ke shukra da zaki dinga tauyewa miji hakki?  "Ashe dama baki daukemu da daraja ba shukra?
 " Mu bamu isa dakeba ashe shukra?

     " Wallahi shukra ki bani kunya ban taba tunanin xakiyi haka ba da hankalin ki dakomai, Ace mahaifinki ya isa da safeer Amma be isa dake ba ko" karki manta bafa mu muka haifi safeer ba Amma yamana biyayya amma ke kikasa yimana biyayya shukra.

      "A wnn lokacin shukra kuka take wane dashi aka aikota"

      "To ki Sani wallahi idan mijinki yabi mata alhakin harda ke xa a raba"

      "zakiso ace mijin ki na neman mata shukra?
   " Da sauri shukra ta girgiza kanta alamar bata so "

     To wallahi shukra kiyiwa kanki gata tun baki kaishi bango ba ya sake ki ko ya karo miki aure a banzaba.

   " AUREN BAZATA hauka ne shukra?

     " A a Ammii dan Allah ki yafe min wlh bazan sake ba dan Allah karki gayawa daddy, nayi miki Alkawarin "ZAN GYARA KUSKURE NA".

      "" Karma ki gyara kinji shukra "

    " Ammii dan Allah kar kiyi fushi dani wlh na dena hali na, insha Allah bazan kara halina ba.

    "Daga nn Ammii bata kara cewa komai ba, shukra ko kukanta ta cigaba dayi tana me dana sanin" KUSKUREN DATA TAFKA A RAYUWAR TA "



     " kwanan su shukra uku akayi discharging dinta kuma alhamdulillahi ta samu sauki hakan nema yasa Ammii tace a wuce da ita gidanta.

   "Ammii da kanta tace safeer ya dinga kula da shan maganin shukra sbd shukra batason mgn, kuma yayi mata Alkawarin hakan"


      "To kullum safeer shike bawa shukra maganin sbd tunda ta dawo din nn bata rufe kofa kuma har gaida shi take yi.

     " jiya shukra ta gama shan maganin ta hakan nema yasa safeer beje dakinta ba kamar yadda ya saba duk dare.

    "shukra ganin har yanzu safeer bezo ba yasa taji BAZATA iya hkr ba sai taje ta duba shi saboda yanzu ba lefi ta dan fara sabawa dashi kasancewar har hira yana dan yimata inyaje bata magani.


    " Dakinsa ta nufa kai tsaye gabanta na faduwa dan bata san ya zai dauki xuwan nata ba.......