AISHA HUMAIRA Part 6
Wooo ni kuma,
Eh msna kina mamaki ne ?
Uhm'uhm kawai.dai ina nazari ne
Chakulkuli ya soma yi mata shaku ko shakku ko tana dariya tace aa wasa nake yi wasa nake yi dan Allah ka bari wallahi na tuba na daina
Kima kara mana
Su nas na bakin kofa jin dariysr yayi.yawa yasa su leqowa gaba daya suna bakin kofar suka yi gyaran murya
Ehem ehem
Humaira na kokarin kwacewa daga jikin sa ya dsda rike ta hamma ka cika ni suna kallon mu fa dan Allah ka cikani kaji
Kawai kun cika msna kunne kun manta cewa da wasu ma a gidan ba ku kadai bane 😏
To waya kawo ku? Dama ina neman hsnyar korar ku ina tunsnin yi muku kora da hali i think wannan shi ne best way na korar ku
Aa yi hakuri mana gobe xamu tattara mu koma mun gaji da wannan korar da halin da kake mana
Ato ku kuka sani
Wayar humaira ta soma ringing ta dauka taga sunan fatima a jiki da fara'a ta dauka
Hello ya kike?
Lafiya lou ya gida
Alhamdulilahi,kina ina ne?
Ina gida
Haba koda naji dan na hahanga ban ganki ba
Ta dafa goshin ta wai wallahi na manta fatima amma yanzu zan shigo makarantar
Ok sena karaso
Azo lafiya amin.
Kagani ko kasa na manta ina da lectures
Haba dan Allah gaskiya makarantar nsn zata uzura min ta shigar min rayuwata da yawa
Gaskiya kar kije nima kinga saboda ke naki zuwa.
Amma ni ai shhh yasa hannun sa a lips dinta ta nuna masa kofa ka manta su hamma nas na kofa
Kyalle su ganin kwakwaf ya kawo su kuma zan gyara musu zama kawai ki bani hadin kai kawai kin yarda nayi abunda nayi kinji.
Uhm ta fada ta gyada masa kanta.
Bakin sa ya kai kan bakin ta ita ksnta bata san cewa haka zai mata ba
Ihu suka sa daga waje suka yi falo da gudu shi kuma ya saketa yana dariya
Lah'ila hamma dubi me kayi ai shi kenan ka bsni kunya matsa min ta hankada shi ya fada kan gadon yana dariya
Yana tsaye ta canja kaya ta dauko mayafi yace aa mayar ai kin daina yar sa mayafi sede a gida ki min ado
Hamma ! Ba wani hamma da gaske nake miki ina tunanin ma zamu je kasuwa a dinko miki hijjabai kamar guda hamsin haka
👀👀 hamsin kuma?
Yes
Amma why?
Cox am d boss!
Hmm mr.arrogant ni bsn sa hijab fa
To mrs.arrogant sekin sa
Amma bana so
Ni kuma ina so
Ta riko collar din rigarsa cizon sa tayi a kumatunsa zan sa amma yau kawai.
Uhm 🤔 zan yi tunani
Murmushi tayi kai mr.arrogant ka fiya kishi
Matar tawa ce se ina kishin ta ya fada yana jan hancin ta muje na kai ki daga nan zan wuce aiki tunda ba kya nan
Wai mr.arrogant yaushe ka zamo mr.romantic
Sanda na fara son ki hannun ta ya riko muje kar ki makara
Ina zaku lovers?
In da kuka aike mu
Oh humsira kin yarda masdook ya maida ke marar kunysr karfi da yaji ko ?
Aa hamma makaranta zanje shi kuma seje aiki
To mu fa?
Kuyi gadin gidan inji hamma
To me mata se kun dawo to Allah sa ku msna girki fa
Hamma yusuf ya cilla masa fillow marar mutunci zan rama ne
Yo me ka iya kaida amiran taka ai de kasan na fika a komai a fannin lobbaya
Hehe wa yaga farin shiga basaban ba dama shi haka dan kauye yake da samun guri har yafi dan birni ma
Daga baya kenan
Se anjima kar kusa na makarar da.my love
To se kun dawo
Amira ta shigo.kitchen din kuma dama ta dadde jikin kofar da hamma zai fita seta buya a bsyan kofar tsugunawq tayi a kasa kusa da humaira
Humaira rungume ta tayi tana kuka
Humaira naji komai amma abin yayi yawa ki daina wahalar da kan ki bayan kinsan komai kinsan cewa bszaki iya rayuwa ba tare da hamma ba then mesa kike wahalar da kan ki hamma da baya son ki amma yanzu ya dawo yana sonki seki sauko ku zauna lafiya
Hmm amira kenan me kike nufi?
Ina nufin ki zauna da hamma lafiys ki manta da abunda ya faru a baya ki sauko ku zauna lfy.
Ohh saboda yayan ki ne shi yasa zaki ce na manta wulakancin da ya min?
Aa ba haka bane kar kiyi misunderstanding dina ba haka nake nufi ba naga kina wahala shi ma yana wahala kin fi kowa sanin hamma ...
Hmm amira nagode amma ban gama yarda cewa hamma ya fara sona ba sena gama yarda tukuna kinsan dai ba wanda ya kain ni son hamma
Na sani kowa ma ya sani
So seki sa ido kiyi kallo kawai
To naji amma dan Allah ki sassauta masa horon yayi yawa 😜.
hmm zaki sani ai muje ni in huta
Kin ma isa muzo ki huta ai hira till down
Haba dea kin san ni dai zan iya barin komai amma banda abu biyu
Na sani mana da bacci da kuma hamma yep muje to
***
Tare suka yi girki su uku yan matan
Suka jera a dinning suka zauna gaba dayan su abinci ne kala kala
Hamma na gefen humaira amma ba abunda yake ci kawai juyawa yayi yana kallon humaira
Nas ya tabo ni"imatullahi da kafa ya masa nuni da bakin sa alamar ya kalli masdook
Shi kuma ya tabo yusuf
Suka fashe da dariya amma duk da haka baya jinsu be masan suna yi ba se humaira ce ta ji abun ya yi yawa ta dan harxuka wai me kuke dariya kamar wasu ...
Amira tace ke kuwa ya ba za ayi dariya ba dubi hamma kamar an kafa shi a gun kin tafi da shi gaba daya in anyi magsna yace baya soyayya.
Juyswa tayi ta kalli hamma masdook kawai se ta ji kunya ta kamata sosaai ta take masa kafa
Ouch!humaira,
Se suka fashe dariya ita kuma ta yi daki da gudu
Keyar sa ya sosa yana jin kunya kawai kun cika mana gida kun sa mana ido
Au masoya mun kusa tafiya mu baku guri ni nasan ka matsu
Wai shin wannan shi ne masdook kuwa wanda baya son humaira?
Ni'ima wallahi Allah ka kiyaye ni ina ruwan ka da bana so amma yanzu ina so se me?
Aa daga tuna maka baya se cibi ya zama 'kari.
Mikewa yayi ya koma dakin sa wanka yayi ya shirys tsaf se zuba kamshi yake yi ya koma kasa dakin humaira ya shiga tana zaune ta sake wanka amira ma na dakin kallon ta yayi ita kuma dariya take masa kasa kasa na tsokana hararta yayi yace out zsn gana da matata bsn san.gulma.
Fita tayi tana tsoksnar sa gaskiya naga sabon hamma and am happy.
Humaira zan wuce aiki
Kallo ta bisa dashi aiki kuma?
Eh wani abu?
Baka gama warkewa bafa ka bari bayan kwana biyu ska koma
Aa na huta da yawa kuma ina zaune ne ina tunani kala kala kwakwalwata zata buga tunda ke din ba kida tausayi so kike kiga na fadi na mutu tukuna seki yafewa gawata so better na fta akwai masu sona tunda humaira ta daina son hamma din ta
Uhm'uhm se ka dawo
Allah yasa amin.
Taya zan nuna maka cewa na yafe maka am.testing you?
Nima sena rama yadda nima ka wahalar da zuciyata
Har ya fita ya dawo ya shigo dakin again yana kallon ta
Kukan me kike yi kuma humaira?
Ba komai
Ya zaki ce min ba komai ? Bayan ga hawaye kina yi ni na dame ki ko
Uhm
To yi shiru bazan kuma kinji yi hakuri share hawayen ki
Hamma
Uhm ina jinki
Ya fada ya na cigaba da taya ta ninke kaysn nata
Hamma ina son ka bani izinin zuwa gida gun dada
Saboda me ?
Kawai akwai.amsoshin tambayoyi da nake nema daga gunta dan na kasa sukuni da hakura da hakan har sena ji ba'asi da kuma abunda kunnena yake son ji
Ko zan iya jin me yake damun ki?
Hmm a baya na kwatanta hakan a da amma ban samu gamsasshiyar tarba daga gurin ka ba
Hmm maganar abban ki ce ko?
Uhm ita ce wadda a gurin ka bata da muhimmanci.
Ba haka bane humaira ban san mezan fada miki bane game da mahaifin ki saboda bazan iya fada miki komai ba amma ki shirya gobe se mu tafi tare katsinan kiji daga bakin baffa ko dada saboda na kasance d'aya daga cikin irin mahaifinki
Kallon sa tayi cikin mamaki
Hamma ban gane ba
Eh zaki gane nan gaba ni na kasance mara adalci , mara ksunarki ,mara bada umarni a gare ki amma ina neman afuwa a gareki dan Allah ki samu koda wata yar karamar kwana ce a cikin zuciyar ki na soyayya ki yafe min.
Wallahi tallshi ina sonki wannsn sabon masdook ne wancan masdook din ya mutu na fiso naga kina min kallon soyayya kina min kallon me adalci kina min kallon da kike min a da nayi missing din wannan looks din.
Humaira ya tsuguna a kasa
Ta mike da sauri subahanallahi hamma dan Allah ka mi'ke ka daina tsuguna min dan Allah kar ka sa min zunubi dan Allah ka tashi hamma ka tashi
Bazan tashi ba humaira ni na kasance me laifi a gareki na kuntata miki na bakanta miki na cuce ki na hanaki sakat na wulakanta ki....hannun ta tasa ta kulle masa baki kar ka karasa wallahi hamma tun tuni na manta da komai kawai ina dada tausasa zuciyata ne ina so in yarda da irin son da kake min.
Rungume ta yayi da tsauri nagode humaira nagode da kika yafe min tabbas kin kasance daya daga cikin mata masu yafiya masu hakuri da ladabi ga mazajen su
Humaira ina son ki
Mu yafi juna hamma ka fasa fitar?
Tun yaushe ai ni na samu gurin aiki ina zan iya fita na barki ba
Kai hamma
Allsh kuwa
gaskiya ka zama lazy
Ai laifin ki ne
Ba wani dama can laxy ne
Baysn zuwanki rayuwata na zama lazyn
_bayan kwana biyu_
*katsina(dikko)*
Dada ta rungume ta tayi tsam tana kuka
Ke yar nan me na kuka?
Kewar ki mana dada na yi kewar ki da yawa Allah sarki jikalle nima ina ta tunsnin ki kina csn kina hutawa abunki kin msnta da wata dada can.
Tab di baki san yadda na yi kewar ki ba
To ya gidan ?
Lafiya lou
Amma dai ba damuwa ko?
Eh komai lafiya lou
To masha Allah
Bara naje gun su inono mu gaisa sannan na je gun mama zan dawo ina da magana da ke fa me kyau.
To se kin dawo
Allah sa
Amin!!
Bayan ta gaisa da ko wannen su ta dan dadde
Tana fitowa taji an jawota jikin kofa ya hadeta ya mata katanga da hannayen sa
Ta dora hannun ta a kan kafadar sa tana jan hancin sa da daya hannun nata mr.arrogant ka fiya shakiyanci.
Uhm mrs.arrogant ke kika sani zama shakiyayen ai
Oh really!
Yep yanzu da haka zaki tafi baki neme ni ba kin shigo gidan namu?
To afwan amma dea kasan dalilin zuwan nawa ko?
Nasani amma be zama cewa ki.ki bani time ba ko?
Haka ne amma so nake ayi ta ta kare gaba daya.
Haka ne muje na raka ki!
Uhm'uhm ku gama ganawa da mama tukuna
Aa muje ai mama bata da matsala xata gane cewa masdook yana da bukatar matar sa a kusa.
Kai kam.ka xama mara kunya laifin ki ne matas.
Kasan me?
Aa ya fada yana jawo hannun ta muje ina jinki
Kawai ina mamakin yadda muka zama daya cikin kankanin lokaci
Dama can daya muke kawai ban gane da wuri ba se yanxu kuma ki daina mamaki da ikon Allah komai me faruwa ne
Haka ne tare suka shiga cikin gidan suna hira kasa kasa kawai sede kaji dariyar su ta masoya cikin shaukin juna da son juna kamar wasu *(romeo & juliet.)*
Dada ta
Ba wani nan ja'iri tunda ka dau matar ka kuka bar garin nsn ban kuma ganin ku ba zaka min wani dadin bakin ku na maza
Dariya yayi to ya za ayi tunda nsyi amarya ai dole na bar uwargida tunda ta tsupha
Hehe lallai da me ta fini zamanancin ko barbada kumatu??
Abun dariya ya basu suka sa dariya gaba dayan su harda kuka humaira
Ni na isa nafi uwargida kyau ?
Ato kema ai kin sani shi yasa
Sossai ma dada
Kai hamma ka daina tabo min dada kaji ko
Yasa hannu shi a goshi alamar yana saluting dinta yes ma!
Kinji ko ya daina
Rasa yadda zata yi ta tambayi dada maganar abban ta take saboda bata taba yi mata ba
Dada
Uhm ina jinki
Dada waye abbana?
*ni yar waye*?
Kallon ta dada tayi tana mamskin ta humaira mesa kika tambaye ni wannan maganar yau cikin shekarun da suka wuce baki taba tunkarata da wannan maganar ba se yanxu?
Dada wallahi kusan kullum kwana biyu tun bayan komawata kano naji duk duniya ba abunda nake son gani kamar mahaifina dada koda sunan sa ne ki fada min zan iya hakura da ganin fuskar sa ma
Hmm!gaskiya ne humaira ni dama nasan hakan xata faru duk daran daddewa zaki min wannsn tambayar ko ba dadde ko ba jima na san da hakan amma ina tsoron wannan ranar tazo saboda bana son na rasa ki duk da nasan ban yi laifi ba amma bazsn hanaki sanin ainihin mahaifinki ba.
Dada waye mahaifin *aisha humaira**?*
Mahaifin aisha humaira sannan ne a garin gombe
To dada waye shi?
Mutumin kirki ne mutum ne me nagarta mutum ne me hakuri sede kunsan ance mutum baya wuce kaddarar sa duk abunda Allah yaso to seya faru komai kaga bawa yayi to daga Allah ne kuma rubuttace ne.
Haka ne dada
Kar ki rike mahaifin ki humaira dan abunda ya faru illa ki dauke ta a matsayin kaddarar ki kawai abunda ya bata min rai yasa na dauke ki daga hannun su saboda ina tsoron kar a min sanadin ki ksmar yadda yayi sanadin mahaifiyarki saboda sakacin su.
Dada sakaci kuma?
Eh masdook sakaci kuma mugunta da rashin kulawa
To dada muna jinki ki fada mana man.
Ka kirawo min baffan ku da yusuf da ni'ima da dai sauran yan gidan kowa yaji komai mahaifin humaira nada rai .
To dada
Jikin humaira dai yayi sanyi sossea kawai ta kosa taji me ya faru a baya kardai ace *baya da kura*
Kamar yadda dada ta fada haka masdook yayi ya kirawo duk wayanda ta bukata ya kirawo su.
To duk dai kuna nan ko?
Eh dada duk muna nan muna sauraron karin bayani daga wajan ki
To to alhamdulilahi
*ASALIN LABARIN*
*DA*
*KUMA*
*DANGANTAKAR DADA DA IYAYEN MASDOOK*
Malam.mubarak umar dikko mijina kenan ni khadija ibrahim dikko matar sa guda daya jal yana da amini wato mahaifin muhammad (maihaifin masdook).
Aminsa mal.idris kabiru dikko
Sun taso tare tun suna yara har girman su kunsan fulani da yawo gari gari da canjs guri to haka take a gun su mijina da mahaifin muhammad.
Aminai ne na sossai wanda har suka yi ginin wannsn gidan guda biyu iri daya kasancewar idris maraya bashin da kowa iyayen sa su kadai suka zo garin nsn na katsina se Allah ya yi musu rasuwa dalilin wata gobara da akayi a rigar su can wani daji se mahaifin mijna ya rike shi dake shi kadai suke da
Hakan be hana malam rike su ba .
Ba wani.ilimin boko suka yi ba illa sun yi ilimin muhammadiya komai tare ake musu har girman su se ya kasane duk wani sani a harkar gona Allsh ya musu sani a nan basu da matsala
Bayan bikina da mal.da kuma bikin idris da mama ba karamin jindadi iyayen su ka yi ba murna sossea gida daya muke a hade da ni da mama matar idiris
Cikin shekara da rabi muka haihu tare nida mama muka haifo maza na samu idris wanda yaci sunan abokin malam wato(baffa idi kennan)
Ita kuma ta samu muhammad daga nan Allah be kuma bata haihuwa ba saboda cikin ta na biyu ta fdo daga saman bene se ta samu matsala tun daga nan bata kuma samun rabo ba.
Ni kuma bayan idris na samu ibrahim,sadeeq da kuma aisha humaira yar'auta ta
Duk gadon iyayen su suka yo wato noma kensn sede sadeeq da ya nemi yin karatu shi da muhammad aka tura su birni su biyu.
Aisha kuma mafi soyuwa guna da kowa ma saboda fara'ar ta da son mutane ga nutsuwa da ilimi
Sossai ina son aisha
Sadeeq da muhammad cikin shekaru bakwai suka kammala karatun su suka dawo lokacin ko aka yi bikin su gaba daysn su maxan dake mu ba a daddewa ake yi ma maza aure matukar suna da sana'ar su
Se aisha dake cikin shekaru goma sha daya a duniya kanwata marayama tazo daga gombe inda take aure a kumo tazo gaida ni tace na bata aisha.hutu da kyar muka yarda musamman malam da baya son dan shi yayi nisa dashi.
A can maryama tasa humaira a makarantar pri ta fara daga farko a gidan da akwai kanin mijin ta dake mijin nata yana aikin asibiti ne a can kumo din.
Wasa wasa har aisha ya zamo tayi sabo da su a can sossai shekarata daya malam ya aika daukota nan fa sunusi ya lallaba su idiris ya musi bayanin dalilin rike aisha su Allah be basu haihuwa ba
To zamu fadawa abba batun ka amma tukuna dai kasan shi me yake so?
Aa
Shi yafi son tayi aure tukuna
Nayi masa alkawari zsn aurar da aisha zan mata gata irin wadda ya kamata ko wane uba yayi wa diyarsa ta cikinsa amma da zarar ta gama makaranta gaba daya dan tayi nisa a karatun ta.
To za kaji daga bakin abban in mun koma
To ke aisha kin zama yar gombe ko inna daga aro kin rike mana kanwa
To ya za ayi ku kuna da yawa gun yaya amma ai ba kamar humaira ba dan kun daukewa dada zuciyarta gaba daya da kyar take sukuni saboda rashin humaira kusa da ita.
Ayya ai zata zo htu
Hhh lallsi.muma ma riketa daga hutu a hsba dai nasan cewa yaya beze hana min rikon humaira ba insha Allah
To Allah ya yarda amin.
Kwansu biyu suka koma masa da bayanin sunusi ya gyada kan sa yace shi kenan baxsn iya hana maryama aisha ba amma zan samu lokaci nida idrisa muje can garin mu gansu na ganta dan ina kewarta sossai
To abba ina jin ma mama da sadeeq zasu je da matar sadeeq
To ai shi kennan wani satin se muje can garin
Allah ya kaimu amin.
Wannan ranar da suka yi tafiys ta kasance bakar rana a garem gaba daya suka shirya suka yi hsnyar gombe a lokacin dada bata da lafiya tana fama da ciwon asthma .
Kwaan su daya abba ya ce ma sunusi ya bashi amanar humaira kuma ya bashi ita har abada ya riketa da kyau tamkar wasiya ya bashi kana da ikon bawa wanda kake so auran humaira amma me addini da tsoron Allah domin aisha humaira rayuwata ce ina mutukar kaunarta domin kuwa ina baka rayuwata ne saboda haka ka riketa da kyau
Insha Allah hamma na rike.
Ke kuma maryama aisha ta zama ysrki ke kike da iko da ita saboda haka gata nan
Humaira ko ba a fada miki ba ki sani wannan sun zama ginshiki a gareki kuma iyayen ki banda rashin kunya bsnda rashin kirki in kin musu tamkar mu kika yiwa ki rike tarbiysr mu kuma kiyi abunda suke so ki kasance me hakuri da juriya a garesu
Insha Allah abba zan yi duk yadda kace
To alhamdulilahi idris kana da abun cewa ne
Aa ai ka gama fadar komai mubarak
To masha Allah muje ko
Hamma sadeeq ga wannan a kaiwa ni'imatullahi
Aa shi kadai?
Kasan shi ne na wurina
Lallai.kinyi kuskure ai masdook ma kinsan yana ji dake kullum aunty
Dariya tayi to a basu dukkan su yaran hudu to humaira mu zamu wuce aa da wuri haka
Ke kuwa kwanan mu biyu fa
Allah ya kiyaye hanya amin.
Kwance take jikin masdook tana zubda hawayen ta yana jin sa ransa a duk a dagule yake jin hawayen humairarsa na xuba gashi bashi da yadda zai yi yasa tayi shiru ko ya hadata da mahaifin ta saboda dada da alkawarin da ta yi ma mahaifiyar ta.
Mikewa tayi da sauri hamma yanzu shi kenan bazan ga dan'uwa na ba wanda muke ciki daya dashi?
Kiyi shiru humaira ki daina kuka dan Allah ki bari kinji nima so kike nayi kukan nima
Aa!hamma kawai ina kukan wahalar da mamana ta sha da rashin yardar da mahaifina ya nuna a gareta yanzu haka maza suke yi.idan suna da mata biyu se daya ta zamo bora daya kuma mowa?
Shhh ba haka bane kinsan kowa da halin sa kuma in kin duba abinda ya faru duk rashin fahimta ne da makirci na mata mahaifin ki bashi da laifi sossai a lokacin ko nine aka fada min cewa kinyi wa mama haka bazan saurari komai ba zan dau hukunci a kan ki dan kuwa uwa ta fi kowa.
Bare .....hamma yanzu bayan sa zaka bi saboda kaima namiji ne?
No! Ba haka bane ina nuna miki ne
Ni ba abunda xanji ai dama nasan kana son ka karo.aure ko ka auri tsohuwar budurwar ka zainab dan nasan har yanzu tana bibiyar ka bata barka ba kuma....hannun sa yasa kan lebbun ta aisha humaira ki daina min magansr ta domin kuwa zainab past dina ce ke kuma present dina na riga da na msnta da ita bana son zainab tun lokacin da ta ki mutunta dangina da kuma mutunta su tun ranar nayi watsi da ita na shafe babin ta a rayuwata ki dsina tunanin zan auro miki ita sam ba haka bane
Ta mike tayi waje fuu
Kan sa ya ksma yace
*women i tell u*
*Wuyar sha'ani!*.
Dakin mama ta koma ta kwanta a kan gadon ta se hawaye ne suke zuba mata wani irin haushin maza ma take ji gaba daya
Mama humaira ta shigo nsn ne?
Eh tana dakina naga ta shigo tana kuka
Amma baki bita ba mama
Baba humaira nasan tana bukatar tayi kukan a halin da take ciki yanzu
Amma mama?
Hannun ta ta daga masa ya isa baba kaje ka huta ka barta ta huta tayi kukan ko ta ji sanyi a ranta!
Mama ya xan iya barin ta tayi ta kuka
To se ka yi ai kaje din
Zaunawa yayi a kan kujera kusa da ita yana rike da kan sa
Mama wai mesa mata basa da zurfafa tunani kin san ko humaira nima tana min kallon abunda mahaifin ta ya ma aunty nima zsn mata saboda zainab
Ina tunanin zainab dun kun rabu?
Eh mama ni na rabu da ita amma ita har ynzu tana nema na a waya
Kai ka jiyo soko kawai kai ka jiyo
mama nifa bana kulata wallahi ban san yadda akai humaira tasan ta ba
Baba ka tashi kayi wanka ka tafi massalaci kar ka cika min kunne da surutu
Ficewa yayi dakin sa ya koma direct wanka yayi ya fito ya shirya cikin kaftan ya sa turare ya daura agogo sannan ya sa takalmin sa hular sa ya saka a kan sa ya shiga gun mama tana falo har a lokacin amma kallo take
Mama xan wuce
To a dawo lafiya
Amin.
_ni zan wuce massalaci ina fata ki huce kafin na dawo dan in ba haka ba zan shigo har dakin mama na lallaba ki with my own style seki zaba na lallaba ki cikin gidan surukai ko kuwa?_
_MMD_
Yq fice yana murmushi
Tana jin shigowar sakon ta duba ta karanta tana daga kwance lokacin ta karanta tsaki tayi hade da smiling ta tura masa in short
_ni ba ruwana da kai ba ma seka san inda nake ba harda tura masa harara_
_AMD_
Yana mota yusuf ke tukin ya ga sakon murmusawa yayi yana shafa sajen sa
Yadai man?inji nas
Idon matambayi
Maida wukar
_akwai inda ruhina zai shiga na kasa nemo shi ne?mrs.MMD?_
Ta fito daga alwala ta ga sakon dariya ya ba sossai wai ruhin sa
_ruhin ka ai sede zainab me ruwan aisha humaira 😏_
_aisha humaira_
Hmm ya ajiye wayar a aljihun sa saura se hira suke yi a tsakanin su amma gogan ya tafi wata duniyar ta tunanin masoyiyarsa
Wayaga fushin masoyi hutu .
***
Wasa wasa har dare bega humaira ba kuma mama ta hana shi tsallake fallon balle ya shiga dakin nata kan dole ya zauna a falon
_haba my humaira hukuncin ya min tsauri da yawa ki fito koda fuskar ki ce na gani msma ta kafa ta tsare na ganki kema kin bada gudunmowa me kike so nayi ki yarda cewa na rabu da zainab tun kan nasan zan fara soyayya dake ki tausayawa bawan Allahn nan me son ki da gaskiya_
Sallah ta idar taga sakon nasa se kuma tausayn sa ya kamata
Dankwalinta ta daura ta fice falon bakin ta a zumbure
Nesa dashi ta zsuna tana kumbure kumburen fuska
Ya msnta ma a falon msma suke da sauri ya je ya rungumeta tsam ksr ki.kums nesanta kan ki daga gareni humaira *it hurt's*
Hamma me haka mama fa na kallon mu!
Barta ta kalle mu seta kuma yarda da yadda nake kaunar ki na ke son ki gobe bazata kuma hanani ganin ki ba gwara tasan aisha ta maida masdook majnoon
Lallai baba to ja matar ka ku tafi can ku ksrats ni dama ina ruwana ai yar kallo ce ni
Kin ji ko korar mu take ya ja hannun ta tana mutsu mutsun kwacewa amma ya mata rikon tsauri haka suka fita daga bangaren mama dakin sa ya nufa da ita ya kullo kofsr dakin kan kujera ya dora ta yw tsuguna shi kuma kallon ta yake yi kswai can tace hamma mesa kake min wannsn kallon?
Kawai ina kallon iko na Allah daya bani ke matsayin mata ta ta sunnah me hankali da nutsuwa ni nasan matata is *brave* kuma ina son ki daina damun ksn ki insha Allah zaki ga mahaifin ki da danuwan ki da nayi.tunanin zuwa cam garin na taho dasu sede dada ta hana amma zan yi tracking nasu se...
Aa kar kayi lets respect dada's emotion zsn hakura har se ya kawo kan sa inda nake ya neme ni ina son amsoshin tambayoyin da suka taru a zuciyata
Uhm as u wish ma lady!
Amma xan miki warning kar ki kuma boye min ksn ki ko ki guje ni in ba haka ba ya ja kunnen ta
Am.sorry my _MMD_
to tell me nine wa?
🤔uhmmm
Ya dunkule hannun sa kamar wanda yake shirin yin dambe seta yi kissing din hannun nasa tace nice
*Aisha humaira matar masdook dikko his only mata my only miji*
Dariya yayi ya rungumeta ita ma ta rungumesa love u suka fada a tare!
Hanyar su ta dawowa birkin su ya lalace kuma ga wata mota na zuwa katuwar mota sunyi kokarin kaucewa amma Allah be nufa ba tayi out da yan motan babu wanda ya shura a cikin su gaba daya yan cikin motar malam,idris,sadeeq,mama,yafindo,du basu yi rai ba haka aka kawo mana gawar su gida ba karamin gigita aisha tayi ba har aka yi arba'in suna garin katsina.
Watan ta biyu garin ta koma saboda makaranta se ya xamana komsi na gidsn ya koma hannun dada ds baffa idi domin kuwa ysnxu sune manya shi da abbi se ibrahim dake binsu.sun tsaya tsayin daka wajan ganin komai na gidan su na tafiya daidai babu wani gargada ko takura sun yi kokari wajan basu tarbiya da kuma basu ilimin islsma babu takura in ksna son boko za a saka in baka so baza a saka ba ya rage naka Allah ya azurta familyn dada da yara maza duk da basu da wani yswa sossai cam.amma alhamdulilahi sun godewa Allah ko wannen su yana girmama na gaba dashi a familyn har sha'awa suke bawa mutane ga harkokin nomam su alhamdulilahi ana samu ba laifi.
Baffa idi yaran shi biyar tun kafin mutuwar malam
Isyaka,yusuf,nasir,fadimatu da rabi'atu.
Baffa iro kuma nada hudu shi kam duk mata se namiji daya
Asiya,firdausi,asma'u da kamal.
Shi dama baffa sadeeq kwansa daya a duniya kamin rasuwar sa shi ds mstar sa ni'imatullahi wanda dada ta raine shi tare da inono wato matar baffa idi.
Se muhammad (abbi)da ke da guda biyu rak
Masdook da kuma zainab (amira)
*gombe*
Humira na gama sakandare kanin mijin sunusi ya aureta amma yana da mata kuma gidan sa ya gina ya dauko mahaifiyar sa da kuma uwargidan sa mardiya wadda bsta kaunar aisha ko kadan shi kuma ahmad ba abunda Allah ya dora masa son sa kamar aisha tun kafin ya auro aisha komai zeyi zece aisha komai zai yi zai ce aisha komai ita hakan ba karamin bakantawa mardiya rai yake ba seta dau wa ksnta alkawrin ba abunda ahmad zai ki nsn gaba kamar aisha .
Farko farko ta nuna tana son aisha dan ta nunawa mijinta its daga gurin ta ba za a samu matsala ba dan ya ysrda da ita haka ma gwagwon sa.
Shi me yawan
tafiye tafiye ne sabida harkar kasuwancin sa ba garin da baya zuwa yana kawo musu kaya komai iri daya
Se kwanan aisha zata fara cutsr.karys aisha bata cewa komai don hakuri gareta
Ran girki kuma abincin ta kamar ta roka haka ake bata shi amma bsta magana ranar da gwagwon ta tayi magana ranar mardiya ta kisisine fuska haba gwagwo me kike nufi ina cutar yarinyar nan?
Ke aisha kiji tsoron Allsh kefa kika ce abincin nan ya isheki kuma seki kawo karats gun gwagwo saboda bakin hali ta fashe da kukan karya
Ni aisha bsta fada min komai ba nina lurs da hakan ki dai dinga jin tsoron Allah dan duniyar nawa take?
Gwagwo salamu alaikum
Gwagwo meya faru ?
Aa mardiya lafiya kike kuka?
Ka tambayi gwagwon ka mana duk nan nan da nake da matar ka ina lallabata naga yarinya ce amma gwagwo bata gani ita matar ka munafuka ce seta dunga fadawa gwogwo karya a kaina ita kuma gwagwo seta yarda da haksn kullum in na zuba mata abinci sta ce kadan shi ne xata hadani ds gwagwo
Ke aisha bana son fitina fa kina ji ko ita ba yayarki bace mena ki na fadawa gwogwo salon hada fitina
Budar bakin ta cewa tayi yays kiyi hakuri bazan kuma ba
Shi kenan ni dama kin san ban dauke ki kishiya ba se kanwa ki daina halin ki mu zauna lafiya
To
Ki bani ruwa na sha dan na gaji daga ganin ka ai kam.
Ina ga gwagwo kawsi ko wacce ta dinga girkin ta haksn ma yafi ahmadu haksn yayi
Haba dea a raba girki ki bari zan dinga yi ni ba damuwa ko har yanzu kina ganin ina kwarar ta ne ?
Gwagwo ba komai fa ta dinga yi ba matsala
Kin tabbata aisha eh
To shi kenan ai.
***
Ai kindinga ganin masifa kala kala ba boka ba malam se kisisina mara mutunci kawai ki kwacan miji kina wani simi simi da iyayi kamar munafuka zaki yi bayani .
Cikin wata biyar ta samu juna biyu hankalin mardiya ya tashi lokacin mijin yana umara shi da gwagwo ta dinga hada mata shirme wai magani a haka cikin ya salwanta ya lalace tayi bari
Shekarar ta uku a gidan daga a sace mata kaya ko a dauke wari da wari a bar wani ko a dauke takalmi ko dan kunne ko sarkar ta amma bata taba yin magana ba ko ta nuna hakan
Mardiya kuma ta haifi namiji umar faruk
A lokacin ciki ne da aisha amma ita ma bata sani ba seda ya fito lokacin ba yadda mardiya xatayi ba karamin dadi gwagwo da ahmad suka ji ba da wannan rabon.
Haka ta haifi namiji abu ya tsaya mata a rai bakin ciki kamar me ai seta hada tuggu aisha na wanka kuma yan barka basu fara zuwa ba ta shiga dakin ta kira gwagwo daga dakin wai taje ta huta zata kula da yaron bata kawo komai ba ta koma dakin ta
Ashe allurai ne a hannun ta kusan guda hudu ta bude bakin yaron ta zuba masa su a bakin sa .
Ta koma waje
Aa mardiya ya kuma naga kin fito?
Eh zan duba faruk ne
To bara naje ni
Tana shiga taji ysron nata kuka aisha ta fito kenan sega gwagwo seta ki daukar yaron se gwagwo ta dauke shi rarrashin duniya yaki yin shiru se kuka yake yi ksmar ransa ze fita ke aisha bashi mama muga ko zsi kama?
Uhm
Ungo shi ta amshe shi gwagwo kinga jini ke fitowa daga bakin sa
Jini?
Eh jini
Aa subahanallahi kirawo ahmad a waya yaxo maza maxa a kai shi asibiti a duba shi
Baban faruk ka zo da sauri yaron nan bashi da lafiya
Aah bashi da lafiya meya same shi
Jini ke fits ta bakin sa haksn nan
Innalillahi wa inna illahir rajun gani nsn zuwa
Mardiya ta shigo yana ji yaron nsn na kuka haka ins aisha din ne?
Subahanalahi yana ga haka?
Ta amshe shi zuciyrta fal murna dadi take ji sossea.
Be wani dade ba ya dawo gida asibiti direct ya wuce da yaron likita ya duba shi ya kwantar dashi a kan gado don ya duba shi
Ya gano allurai ne kuma sun huhuda shi a makogwaro gurin ya kumbura sosssi shi yasa jini ke fitowa ya masa allura ya samu ya kwanta
Bayani yayi wa ahmad kan abunda ya gani kokarin kashe yaron aka yi
What!
Allurai a cikin bakin sa garin yaya
To dai gashi nsn aiki za a masa a ciro masa su kuma se an kai shi babban asibiti tukuna likita kafin nan ai yaron ya jigwta ka taimaka kayi masa ni ba surgeon bane wannsn aikin se surgeon amma bani ba
