AISHA HUMAIRA Part 3




Dakin sa ya shiga ya dauko wayar sa.
  Hello kamal!
Hello hamma an wuni lafiya?.
lafiya lou
     Kun taho ne?
Aa hamma
Se yaushe?
  Wallahi bsn sani ba
Kamar ya?
Aisha din ce taki.hanzartawa nima ita nake jira.
   Bani ita a waya
Tana cikin daka amma bara na kirata sena kira ka.
 Kudin ka ne?
Aa
To kirata ina jin ka.
Cikin dakin ya shiga ya mika matq wayar amsa
  Me?
Ban sani ba
Karba tayi ta sa a kunnen ta
Hello!
  Be tsaya amsa matq ba ya fara magana
""Ki yi maza ki fito ku taho gida ina jiran ki kar ki sake na kuma kiran ku a waya"""
  Zumburo bskin ta tayi cikin masifa.
  Ban ji kin amsa bs ya fada da tsawa tsawa
Ta zabura ta mike
Naji !
Mikqwa kamal.
 Kai kuma ka tabbata kun fito yanzu kun taho
 To hamma yanzu zamu taho.
 Ya kashe wayar.

Kinga me kika jawo mana ko?
Kin san hamma ba kirki gare shi ba yanzu ya ma mutane ihu a waya
 To kayi hakuri mana hamma
Suka yi sallama da amira sannan suka taho gida.

***
A farfajiyar gidan suka same shi gaban ta yw buga dum tsabar fargaba domin kuwa idan shi sun rine sunyi ja dasu.
 Hamma kamal ya yi ciki da mota dan ya parker ta ni kuma kaina na sadda kasa kamar munafuka zan wuce
  Da hannu ya min nuni da na zo
  Jikina na bari na karasa kusa dashi.
 
 Tsugunawa zata yi ya zare mata ido ya mata alamu da ta mike tsaye ya kalleta ta kalle shi
  Humaira!
Na'am hamma dan Allah kayi hakuri wallahi
  Shhhhhhhh!ki min shiru ki min shiru mara kunya kawai uban wa waye yace kiyi waje baki fada min ba haka kike ce min kina sona?
Bayan ban isa ki tambaye ni zaki wani guri ba saboda ni makiyinki ne
  Aa hamma dan Allah kayi hakuri kaji wallahi bansan zaka zo ba kuma ni nayi niyar fita na fadawa dada amma taki bsri na
  Shi ne kiks yi gaban ksn ki
Aa hamma na tambayi mama fa ita tasa hamma kamal ya kaini can katsinan.

Da yamma tayi hankalin ki be baki kiyo gida ba
Shiru ta masa kamar ya mareta haka yayi mata tsawa.
Ta zabura kqmar ta gudu
  Kinyi na farko kin yi na karshe kar ki kuma
To insha Allah bazan kuma ba.
  Anjima ki kawo min shayi da abincin dare ke nake so ki girka min dan *a sanadin ki nazo*
Bambarakwai taji maganar ta kura masa ido
 Kina kallona menene?
Ba komai cikin gida ta koma gun dada.

Wai ina kika je ne?
Katsina naje
Katsina?
Eh me kike ihu kamar baki sani ba
Kin rika aisha
Da na yi me ?
Au tambayata ma kike yi
To matambayi na bata ne?
Mikewa tayi bara na yi wanka nazo na dora masa girkin kar ya samu damar zalintatw kuma
ai gwara ya zane min ke
Dada kenan ko guba ne zan iya sha saboda shi me kums dan ya dakeni ai dadi zanji ma hannun shi a jikina.dada ta kama bakin ta cikin alajabi wannan wane irin so ne humaira kewa masdook.
    *(eternity love)*


Nunata tayi da dan yatsa kar ki sake ki min maganar banza marar kunya kawai ban badawa kizo ki kwata kinji.

Waje tayi dauke da jaka rataye a hannun ta mayafin ma ta dan dosana shi a kafada tayi dakin inono

Salamu alykum
Wa'alaykum salam,
Inono zaji je unguwa kuma banda isssan kudin mota kuma zan yi tsaraba kidan rabani man a jakar ki
  Ina zaki haka?
Gun yar'uwata zani je
Katina din zan barki kije a mota ke daya?
Uhm zan iya ai
To badani ba kin fadawa mijinki?
Wai kowa seya ce na fadawa mijina ni banda ma num shi kum...
  Kinga fita min a daki kin ji ko?
Tayi waje tana kumbure kumbure sai gidan su hamma masdook din ta shiga
 
Mama na daka a tsakar kida ta zauna suka gaisa sossai har da tsokanan ta
  Mama zani gidan amira kuma na kira wayar shi bata shiga kuma su dada sun ki yarda na kira shi banda isassan kudin mota nikam.

  Tayi shiru mama ta bita da kallo to ina zuwa dakin ta ta shiga ta dauko wayar ta num kamaludeen ta kira bugu daya biyu ya dauka
   Hello kamal !
Mamana ina wuni
Lafiya lou
Kana ina ne?
Ina bayan layi gidan su zaid
To kazo yanzu ina jiran ka
To mama gani nan zuwa.
Youwa.
 Suna hira suka ji sallamar sa
Msmana gani nan ina labari
  Uhm amshi key dina ka kai min ita gidan amira
  Na shiga three mama kt zani yanzu?
Eh man ko kana da aiki ne?
  Aa mama kawai na gaji ne wallahi kin san fa yadda muka yi zirga zirgar garin nan a kwanakin nan
Toh shi kensn ai se kayi ta hutawa ai
 Yi hakuri mamana bani muje matar hamma amma can zan barki ko ?
Ta dan yamutsa fuska jim kadan tayi magana eh can nake tunanin kwana kawai gobe da yamma  ka dauko ni
  Ya tsaya kallon ta cike da mamaki mamana kina ganin humaira wai ta girma haka
  Dariya ta musu kawai ta ce a dawo lafiya amin.

Suna tafe suna hira haka suka dau hanyar kt .
  Ran ta fes fal ta ma manta bata yi wa dada sallama ba .
 Sede suji a salansa.

Irin wadda ko bayan rai se anyi maganar soyayyarmu wadda ta fi ta *hilal da ilham*
  *(Khairi nace anya kuwa)*?

Wanka tayo ta saka wata atampa kalar dorawa da dison ja a jiki ta fesa turaren *HUGO BOSS*
Ta daura dankwalin ta irin ture kaga tsiyar nan ga kayan yayi mugun kamata iya damewa dai wannsn skit yayi mata ga rigar kamar kirjinta zai faso ya fito waje  ta shafa lipa gloose tayi kitchen ta dauko kaza dan hamma ma'abocin son gaza ne ta sarrafa ta ga yaji da abincin yayi ta yi masa jellof din talliya dan yana son taliya ta juye a kula sannan tayi blending kayan marmari ta sa suger da kankara ta zuba a jug.

Dakin shi ta nufa tana shiga kamahin turaren *philips lumea* ya bugi hancin ta duniya tana son turaren nan saboda mesa turaren har ranta taji kamshin ya shige ta.

Yana zaune kan gadon shi yaji shigowarta juyowa yayi gareta yana kallon ta ba karamin kyau ta masa ba
  Saukowa kasa yayi ya zauna yana tankwashe kafarsa ,
  Russunawa tayi gefen sa ta ajiye kayan abincin zuba masa tayi ta ajiye masa a gaban sa kamshi ya bugi hancin sa
  Ina fata dai babu yaji a abincin nan ?
Tsuru tsuru tayi da ido
Ya kai loma daya bakin sa yaji yaji ya kalleta ya kurbi ruwa sena hukuntaki dan da gayya kika hambada min yajin nan dan na miki fada amma sena hukunta ki .
 Hamma ka bari kar kaci kaji dan Allah sena maka wani abincin mara yaji .
  Kina tsoron hukuncin ne?
Uhm niba hukuncin nake tsoro ba illar da zai maka nake tsoro dan bani son abunda zai illata lafiyar ka ba.

Idanun sa ya lumshe zarazaran gashin idanun sa suka kwanta kan fuskarsa a ransa godewa Allah da yake yi da ya bawa aisha humaira son sa matuka iya makura yayi dacen mata amma a fili yana bude bakin sa keda wuya ya ce
   Ai raba zafin zamu yi nida ke
Cikin tsurewa ta mike zumbur zata fita dan aisha humaira akwai tsoro.

Hannun ta ya kamo fadawa kan sa tayi ya riko ta zageye da hannun sa zuwa cikinta gaba daya ta rude ta dinga rawar mazari dan fargaba.

Bakin sa ya sa cikin nata ya dinga tsotsa kamar wani lollypop ya dinga mata salo irin na daddadan dan duniyar nan ya kasa tsayawa iya nan kawai seda ya zuge zip din rigarta rigar ta fado kasa tayi maza ta sa hannun ta rufe kirjin ta
   Hamma me haka?
Hukunci ne xan miki dole mu raba yajin tare
 Na shiga uku hamma ka bari dan Allah wallahi na tuba
  Da iya karfin ta hankade shi ta yi maza tayi hanyar kofa cikin taku daya ya cadkota ya hadata da kofar kirjin sa na gogar kirjinta

   Ya sa hancin sa yana shinshinar wuyan ta ya na kissing nata ya hada hannun ta da kofar hawaye ke zuba mata a fuska

Rigar ya maida mata ya zuge mata zip din sama sannan ya bude mata kofar da gudu tayi waje tana haki.

Gurun ya tsuguna ya fadu ragwaf tsabar kasala ya kulle idan sa cikin sa na murda masa besan mesa ya yinhaka ba besan meya rude shi ya aikata mata haka ba
 Yanzu shi krnan zata raina ni
  Kunya yake ji ma shi.

Dakinta ta fada ta kwanta tana kuka me hamma ke nufi jikina ko ni yake so ?

Inko jikina yake so lallai za ayi wadda za ayi jikina yayi lakwas ya hadani da kasala jikina yana kamshin turaren sa na philips humea.

Hawaye sirara suka zubo mata ina ma ace sona yake dana nuna mishi nima son da nake mishi.

Haka bacci ya dauke ta bata farka ba sai asuba tayi sallah sannan tayi wanka ta koma bacci abunta amma baccin yaki zuwa kawai hamma masdook take hangowa yana rikita mata kwanya gaba daya ta kasa manta jiya balle abun jiyan
Tsaki tayi shi yafi a kirga ta juya kuwa iya juyawa kan gadon ta so ko wahala
Mtsw mutum yayi wa mutum katutu a zuciyar sa ya hana shi sakat ys hana shi yin komai sai aikin tunanin mutum overoll ma mutumin da ba son ka yake ba .
Allah ka yaye min amin.

Masdook dama yau zai koma bakin aikin sa bayan nan kuma za ayi yan gyare gyare a gidan kamin zuwan matar sa.

Gaba daya ta gama rikita shi ya gama kamuwa shi kqm gwara a kawo masa matar sa shi ba walliyi bane yasan bazai sha wuya ba dan kuwa matar shi son shi take babu wani limit why not .......
  Wani murmushi yayi wanda ni kaina ban san me hamma yake nufi ba .


   Wai ni ibrahim tunda mutanen nan suka tfi da yarinyar nan baka taba zuwa kaga halin da take ciki ba ko me take bukata baka tsoron hakkin Allah ya kamakq yarinyar nan diyar ka ce halilinka jininka amma kayi irin shariyar gareta na tabbata ko za a kashe ta a hanya ta ganka kaima ka ganta bazaka ce ga yarka ba balle tace maka baba ko kai ka gane jinin ka ce kai ba abun kunya bane a gareka ?
   Ya kai lomar tuwon bakin sa  ya na juyowa hajiya kenan ai ni banda abun cewa ban san naje su kuma min kallon silar diyarsu a fada min magana ni kaina fa uba ne kuma ina da buri kan yarinyar ammq kin san na kasance mutum mara son hayqniya tun filazal.
  Ni kaina ina son na ganta
Na ga yadda ta koma
Na mata gata irin ta uba na nuna mata zallar kulawa
Sede kash Allah be so hakan ba amma ban fidda rabo ba zata neme ni
 Kai ta gyada masa har kana tunanin zata neme ka?
  Hajiya yar aisha ce fa aisha kuma zuciyatq ce ni kuma yar aisha yata ce jinina ke yawo a jikinta ta ko ina nata tunda ina raye zatq neme ni ko da bayan raina ne amma ni nasan zata nemi baban ta ai da uba ake ado.

   Allah sa hakan amma ibrahim diyarka karka manta a ina ta taso
 Ban manta ba kuma bana ganin laifin su sam sam domin nina jawo nine sila da abunda ya faru be faru ba da hakan bata kasance ba amma ba wanda ya wucewa kaddarar sa babu shi a duniya.
  To Allah karq mana imani amin.


**
Da wani isa yana batsewa ya shiga dakin dada tana shan koko aisha humaira kuma na shan tea da biskit taji zuwan shi ksnta a kasa ta gaida shi bayan ya gaida dada
  Zuba min tea mana!
Hada masa tayi ta ajiye masa a gefe fuskar nan murtuk tsabar fushi ita haushib sa take ji gaba dayan sa
  Wurin ta ta koma ta cigabada karyawa abunta.

Dada na gamawa ta mike zan wuce
Ai se ki bari na gama na raka ki ko ?
Na hutashe ki amma nikam har yau da kwarina
Dada wai ina zaki haka?
Wallahi dan nan gun aminiyata zan je a can makota
  Yyi dariya wai Allah dada har wata aminiya gsre ki
 Ta masa unbola amsa na baka nake ne
Tuba nake a dawo lafiya kiyi yawo kila kashin naki ya sake kullum zama gu daya kamar an dasa ki
  Kai kan akq gwada nafi tsohuwar ka kwarri nifa tsohuwar jini ce ba ta zamani ba
   Yayi dariya sosai sekin dawo dada Allah kiyeye hanya ki tafi mata da tsaraba
   Ficewa tayi abunta ita kam.
Dakin yayi tsit kuma na yan lokuta
Tana gamawa ta mike zata koma daki
Zauna .ya fada ta koma ta zauna tana kumbure kumbure
 Ki kasance cikin shiri ko wanne lokaci daga yanzu za a iya cewa za ayi bikin mu .
Ta dan kalle shi ta kyabe fuska
 Ni in fadama wani abu hamma?
Ina jinki yq fada yana dana wayar sa
  Ni dan Allsh ka sauwaka min wallahi Allah na hakuri ni bani son ka ka sauwaka min na auri me sona bana son wanda baya sona abunda na fada maka a baya duk yarinta ce yanzu na daina ba dole ka soni ba kaji nayi quiting.
  Wannan maganganun da take be dago ya kalleta bama yace kin gama?
Eh
To bazan sake ki ba kiyi duk wadda zakiyi kinji ko tunda kika ce *kina sona*to se mun zauna tare ai dama na fada miki zaki yi dana sanin aurena ba kin ce *ke ni kike so ba ?* to muje zuwa muyi *son* tsabar tsaurin ido irin naki ni zaki cema kina so ki min wannsn bomb din a dangi ai kinga gwara na hukunta ki ko ?
  Hawaye ya zubo mata Allah ya sani tsakani da Allah da zuciya dayq nake sonka amma kai bani kake so ba sha'awata kake yi tayq zan zauna da kai.
   Dariya yayi kasa kasa humaira kenan yo ai na cutu ince ina sonki ke kan ki kinma kan ki karya ko jikin ki nake so ai nawa ne tunda na biys sannsn akq bani
me a ciki abun fa trade by barta ne kina son masdook na yarda na aureki to masdook kuma jikin humaira yake so kuma nq shi ne ba shi kenan ba anyi one one ?
  Tq mike Allah ya kiyaye wallahi bazaka samu ba .
     Haka nake son mace da confidence kin burge ni jiki ai kamar na gama samu ne kawai ki kwantar da hankalin ki zan shayar dake ruwan love yq fada yana mata dariyar mugunta
   Zata yi dakiyace by the way lips dinki akwai dadi fa
da gudu ta koms daki tasa key ta fada gado tana kuka na shiga uku nikam wayyo Allah na najawa kaina.
Insha Allsh bazaks samu nasara ba ksn mugun nufinka!

Tana shiga ya dinga dariys matsoraciya kawai zaki yi mamakina in kika ga new masdook mijin aisha humaira

Cikin shadda hilton milk colour ya fesa turaren sa na philips humea ya sa takalminsa dan paris ya daura agogo ya taje gashin kan sa ya shafa masa mai ya yi waje dakin msma ya nufa suka gaisa yace mata zai tafi shi kam
  Tun yau ?
Uhm
To Allah kiyaye hanya
Kaje gun amira kuwa?
Ya sosa keyar sa mama zan biya in zan wuce a min ahuwa ina kunya ne ni babban wa
Kai baba yaushe zaka rage wannan kunyar kamar mace ya kamata kaje kam ta ji dadi itama ai
 Insha Allah mama zani je ni anjima kafin na wuce
Allah ya bada iko
Amin.

**
Baffa na gama shiryawa zan koma gun aikina
To to Allah ya taimaka ya bada sa'a ya kiyaye ka daga sharrin masharata
Amin baffa
Abbi zan wuce
Allah kiyaye hanya
  Sanda yaje gun dada suyi sallama tana sallah yayi murmushi tsohuwar nan akwai ta da ibada.
  Dakin humaira direct ya shiga tana charting a waya
Sarai taga shigowar shi kuma taji muryarsa kuma over oll taji a jikin ta
  Ta gyara zaman ta tana cigaba da abunda take yi.
 Ya zauna bakin gadon yana mata wani kallo
Wanda se da ta tsargu ga'ba daya ta gaji da yadda yake mata kallon up and down ko ina a jikin ta yake bi da kallo
  Ta ajiye wayar a gefe me kake kallona haka ban san kallo fa
 Da wane idon kika ga ina kallon ki in ba kema kallona kike yi ba ?
Uhm Allah ya sauwake mezan kalla a nan?
Kafarta ya jawo ta zamo kusa dashi abunda kika gsni kika ce kina sona kinga handsome me kyau
Hararsa tayi hade da masa tsaki bata yi aune ba ya matse bakin ta da yatsunsa guda biyu tayi kokarin kwacewa ya rike daya hannun nata da daya hannun ya murda shi baya hawaye suka zubo mata tsabar azaba.
  Kinga kuwa yadda kika yi kyau kuwa?
Ya mata hoto da wayar hannun sa yana dariya kullum sena kalla nayi dariya na hango munin ki.
  Ya sake mata bakin ta yana murmuahi irin murmushin muguntan nan
 Nasan ni kike so bazaki kula kowa ba na sanki da hakan ko ina zan miki wannan shaidar amma duk da haka ki kula min da aurena dake ksn ki bands shigar banza banda yawon banza num shi yasa a wayarta ya kira layin sa
Good na wuce ni sena dawo daukar amaryata ke kenan ki kasance cikin shiri.
  Yayi mata sumba me karfi me tsayi
Sannsn ya wuce abunsa.
Kusan mintin shi uku a soron da zai sada shi da waje yana maida numfashi daga bisani kuma ya shiga motar sa ya koma gun aikin sa.

  
*_bayan sati uku_*

Satin bikin ya matso lokacin kuwa aisha ta samu add a makarantar bayero ta samu medicine a buk se murna sossea ta kamata

Ana saura kwana biyu ayi kamu mutumin ya sauka a garin dikko da lefen shi ya taho nas da ni'imatullahi suka shiga da akwatuna dakin dada akwatinta guda shidda na sa rana guda shidda na lefe ba karanin kaduwa tayi ba da ta ji irin kayqn da masdook ya mata ba sossai tayi mamaki anya kuwa hamma masdook?
Hmm Allah masani
Aka dinga yarinya tayi goshi waye ya mutu waye ya tashi
  A cikin family house dinsu aka yi taron kamu inda mutane suka dinga zuwa autar dada yar gatan dada masoyiyar dada.

Ta sha shiga ta alfarma ta zauna a kasa inda aka mata jere irin na kumbu na yar gatar amarya tace bata son wayanan kyalkyale kyalkyalan na biki.

Ta zauna fuskarta lulube da mayafi me ruwan gwal ta sha adon gwalagwalai.
Masu kamu suka kama amarya inda tasha turaren intemately becham.guri ya dau kamshi.

Washe gari aka yi wuni dama wayarta a kashe take dan bata son damuwa

Shi kuma se kiranta yake yi a waya amma a kashe yake ya kira amira ina humaira ?
Hamma tana cikin mutane
To me kike nufi?
Tayi masa shiru
Ina magana?
Hamma zuwa zan yi na dauko ta na bata waya kasan cewa bazan iya cewa tazo kana kira ba inonono ma magana zata yi anjima zan kawo ma ita amma yanzu kam..
Wallahi ko ki bata ko na shigo gidan
 Hamma ni mezan ce kuma?
Ubanki !
Ta zumburo baki ta shagwabe fuska hamma bara na bata wayar
  Ta kutsa cikin mutane ta mika mata wayar
 Waye?
 Mijinki!

Kina kallo ina cikin mutane taya zan amsa wayar kuma?
Ke kika sani ni bazan iya ba kun sani a tsakiya.

Hamma kaji ai da kyau ta kashe wayar mijinki ya fiya kalula da fi'ili ni kam ku karata harda zagina fa yayi .
Tayi mata dariya kice yau kin samu rabonki


Da daddare akayi mothers eve.
Washe gari akq kuma daura auren masdook da humaira.
 Yan gaban goshin dada bakin tsohuwar yaki ruhuwa dan dadi

Yan matan na zaune a tsakiyar gadon humaira suna ta tsokanarta angwayen suka shigo dakin suna hira a tsakanin su shi ko uban gayyar bakin sa gum yaki tankawq bare ya tofa amma ya bita da kallo shadda ce a jikin ta doguwar riga yasha aikin gana ta yi kyau ta yi daurin nan me hawa hawa gashinta daga baya ya fito
  Amira ta rangada mata kwalliya irin ta zamanin nan tayi mugun kyau mayafinta me tsada ta ajiye shi a gefen ta.
   Kamal yace amarya amarya for the second tym an daura auren ki da mijinki masoyin ki wanda kike so har a zuciya buri ya cika.
Aka sa dariya
Wallahi ban taba ganin me son mutum ba irin aisha humaira yadda take son shi kamar yadda laila take son majnun.
  Gaskiya kam Allah ne ya hada su
Ita dai tsna jinsu bata ce komai ba shima yana jinsu be ce komai ba illa kallon ta da yake yi kawai.

Suka gaba tsokanarta
Yace to nagode fa kun yi hirar da yawa kun dami matata
  Nas yace ohhhh *matarka*
Suka yi dariya gba daya hamma yusuf yace muje mu waje kafin yace mana *get out*
  (Hhhhhhhhhh)gaba dayan su suka yi

Dayan bayan daya suka dinga fita daga dakin aka barsu su kadai
   Inono ta leqo masdook zamsn me kake a ciki?
 Ganawa zan yi da matata kinsan an dade ba a hadu ba

Ta kama haba lallai masdook ka rika ta koma waje .


Harara ta sakar masa hade da mikewa zata fita ya yi maza ya kulle kofar ya hankadata kan gadon dake dakin
 Ta juyo idanunta masu kalar bacci ta zuba masa
 Yasa hannun shi a kirjinsa yana dan shafawa wow!ina son kallon nan
Ta juya ta gyara zaman ta tana me sirfa masa harare harare kala kala .

Ya kwanto kan cinyarta ya dan rankwafo da fuskarta kan nasa ya soma sumbatar bakin ta kamar wani zaki daga kwancen ya masa tsauri ya mike ya koma kqnta yqna aika matq da sakwannin love me wuyar dauka a gareta .
  Turesa take ammq a banzq kamar dada angiza shi take yi cikin kuka tace haba hamma me hakq wai da mutane fa a gidan ka manta taron biki ake yi wannsn ai rashin kunyq ce ba dabi'ar mu bace ka tashi ka tafi dan Allah.
Shhhh ya dora yatsan sa a bkin ta ki min shiru saina gama abunda nake yi tukuna zan tafi kome za a ce a ce a shirye nake.
 Na shiga uku wai me haka ka manta wacece ni a gunka?
Matata ce
 Hamma ka manta kace niban isa komai a gunka ba dan me kuma yanzu zaka rude a nan?
 
  Ya cikata yana kallon ta da sexy eyes na shi da suka koma ja dan jaraba tsoroma yake bata ita kam
   Jikinta sai rawa yake yi ya kalleta hade da nuna mata dan yatsa 👉🏻look humaira kar ki yaudari kan ki ki dauka cewa son ki nake babu shi a dictionary dina ba sonki nake ba
  Ya ja hannun shi kan jikinta yana zagayawa dashi jikin ki shi nake so ke kike sona masdook yake son jikin ki so kin sameni nima dole in sami abunda nake so.

Siraran hawaye suka zubo mata masu zafi da daci a zuciya ta kuma kallon sa ta mike da kysr dan jikin ta ya gama mutuwa da kalaman hamma masdook
  Hamma tabbas ka gama dani ka tuna yadda nake sonka haka zan iya daina sonka kuma na ji duniya ba wnda na tsana irin ka
*Get out daga dakina ta fada cikin tsawa so ba haukq bane na daina son naka mezan da kai marar imani mugu wanda besan darajar so ba ta juya a fusace kai wa ma zaka iya so ? Babu yadda ka min saika rasa me sonka zaka yi kuka a kan so*

Mari ya dauketa dasu kwarara guda biyu wanda seda taji kunnen ta ya dauke ji na yan sakwanni ta tsuguna a gurin tasa masa kuka .
 Tsugunawa yayi a kusa da ita yana devlish murmushi
*welcome to hell humaira*
  _Welcome_ _ina miki marhaba da zuwa gidana gidan da bazaji ji dadin sa ba gidan da kullum sekin zagi ksnki dalilin zuwan shi se kin yi danq sanin aurena ko sanina zaki san cewa ni din bana wasa bane stupid girl_

Nima na maka alkawari bazan hanaka komai ba a kaina amma zaka yi repenting lokacin ni kuma zan nuna maka ainihin aisha humaira.

_I like promises yadda kika rabani da love of my heart haka kema bazaki ji dadin love dinki ba ill make sure hakan ta kasance_

Matukar son da nake maka na tsakani da Allah ne ill win over you ka bar ganin sonka we ll be my weekness ko kadan it will be my strength.

Kai ya gyada yana dariya shi kenan ai let the circle start caiculating love angle ya koma war angle
  A gunka love is bad a guna love is good kayi da yar halak wallahi masdook muhammad dikko seka soni so na hauka sona har abada so na ba mantawa so wanda kai da grate masdook seka yi *kukan so*i promise you that

_Well muje zuwa i ve d trupm card_
_And i ve the king in my hand_

Hannun shi yasa ya jawota jikinsa ya matse ta da hannun sa rike da kugunta jikin su na gogar na juna we shall see ya sa glass din sa a ido ya hankadata ta fada kasa
  Tun a nan kin farq faduwa? Nan gaba ya kenan ?
_hmm ko wa seda ya fadi yq tashi so falling and raising in love is normal yau nina fadi gobe kai zaka fadi principles da rules na love kenan ai_
So mr.masdook dikko get ready to fall in love
*Never*

 *you most dole ne ma ai u most fall in love*
Ya juya ya bude kofar ya fita abunsa
Tq baje a gun tana kuka kukan tausayawq kan ta daga bisani ta mike ta share hawayen ta bazan taba bari yayi winning ba sena ci galaba a kansa sena nuna masa cewa true love always wins
True lovers are always blessed by Allah.
Son da nake ma hamma na tsakani da Allah ne na har a zuciyq ne son da nake maka is limitless komai zanyi a kanka
Son da nake maka karfina ne ba ragwantq ba zan baka mamaki.


_happy birthday my dear sisi aisha muhammad lame its ur day sweethart Allah's khair and nur be with u Allah kawo bikin ki mu dance miji nagari fata amin_

_Wannan page din na kowacce aisha humaira ne_


   Wanka tayi ta kwanta tsabar gajiya ga takaicin da masdook ya guma mata ga shi kaunar shi ya mata katutu a zuciya ya hanata sakat ta rasa dalili a kan sa duk wani tsiwa da wulakanci nata bacewa yake yi bat kamar ba ita ba sometimes ma tana zargin kanta anya ita ce kuwa *aisha humaira*?
Mtsw
  Bacci be wani dade ba yayi awon gaba da ita ya dauketa dan ta gajin daman.

***
Dakinsa ya koma ya shiga toilet ya sakarwa kansa 🚿 shower yayi wanka dake ma ma'abocin ruwan sanyi ne shi
In dai yayi wanka da ruwan zafi se 'kuraje sun fito masa a jiki .

Siglet da short ya saka ya kwanta kan gadon sa gaba daya artabun sa da humaira yake tunawa wai wannsn wacce iriyar yarinya ce me kaifin kai da tsaurin ido ni ta kalla ta fadawa waddanan maganganun kuma i just left her she's daring gaskiya kam yarinyar
Wasan namu zeyi kyau kam amma ya zama dole na koya mata hankali i wont let her win
Mtsw kawai a hada mutun da jaraba yoh ai humaira jaraba ce dan ta maidani jarababbeb karfi da yaji na zama mayan mata da kunnena shiru hayyan
 Mtsw alakakai.


Wanka ta sake aka yi wuni aka gama da daddare kuwa dakin inono ta kwanta dan ta gaji da yawa a dakin dada yan biki ba barinta zasu yi ba ta huta kila ma wannan mr.arrogant din yazo dan abunda zata dibga kiransa kenan mr.arrogant dan shi ne he deserves the name.


Bata wani jima ba bacci yayi gaba da ita a dakin.

  Inono ta shigo ajiye kaya tayi a kan gado ta ga mutum ta ksma salati au kina nsn ana ta neman ki a can ?
 Inono wallahi sossai na gaji shi yasa na yo nan
 Dan Allah karki fada musu ina dakin.
  Inono bakin kofa take a tsaye ta ce *mindili*
(Tazo kenan)
Da kyar ta karsa gunta
 Jikinta ta taba taji garau
 Dariya tayi kai inono lahiyata kalau wallahi kar ki damu kawai gajiya ce bsn san damu
To.

   ***
   Da safe tun asuba data tashi bata koma baccin ba
Wanka tayi da ruwan zafi sossai sannan ta koma ta kwanta cikin doguwar riga slik pink gaba daya ta kwanta jikin ta luf

Karfe goma daidai ta fito tsakar gida ta gaida ysn tsaksr gidan dan ko gidsn ya ragu da mutane da yawa kuwa dan an ragu tunda an daura auren jikinta duk ciwo yake a corridon dada mi'ka ta kamata

Daga sama taji ana mata magana gwara kiyi ladab na hutar dake kin gaji da yawa tunda kinsan masana sun ce idan mace tana mi'ka tana da bukatar namiji a kusa da ita kizo kawai tunda ke da mijinki a kusa

Hararar sa tayi sannsn tayi tsaki Allah sauwake kai din me
Tayi ciki da sauri
Dariya ta bashi sossai.
Cikin gidan ya bita tana kwance jikin dada
  Nesa dasu ya zsuna ki daga mana dada ksr ki karya ta dan ta tsufa bamu gaji da ita bafa
Harar dai shi ta kuma masa dan ta lura ya maidata abun wasar sa.

Kosai da kunu ta ke ci ta hada da kunun ta har ta gyatse.
 
Tea ya sha da kwai soyayye da bread
Dada dake fa zamu tafi
Allah sauwaka !
In biki barni agidan mijina yadda aka kawoni haka za a dau gawata ehe
Suka yi dariya gaba dayansu
 Fadimatu dake gefe tace dada kyale su ina zaki bisu su kashe miki ragowar idanuwan ki da soyayya ta zamani
Unbola ta mata ungo nan wane soyayya zaku yi ku kam ai soyayya se a zamanin mu ku me kuke yi bsnda shirme.

Hah  dada kina nufin ku kuka iya so?
Fadi ki kara hajiya ku ai sababbin shiga ne me kuka sani?

Mu q lokacin mu mazajen mu ji suke damu muna mutuntq juna ke se ayi aure baku san juna ba se an kqi ki ku ga juna kuma ku zauna lafiya ko yaji bama yi balle aji kan mu
.ku fa abu kadan ayi yaji a koma gida saboda tsiya ina soyyar da bayan aure se fada da hayaniya ba zaman lafiya
Ai abun kunya ne banda yaudara da karyq da fada ba abunda kuka sani.

Ho su dada an tuno da za a sauke mana wahayin soyayya

Kai dada kin zama love guru
Me kuma wani lac gura
Aka kwashe da dariya gaba daya dada ban iyawa da caftar ki yanzu cikina yayi ciwo .
Ke in kin gama ki shirya yau zamu wuce ayyuka sun mun yawq ana ta kirana a can gun aikin

Kamar ya ku wuce masdook ai se anjima an zo se a kai maka ita da kai zata tafi da

Dada kin san ban san wannan abun kawai zan tafi da ita daga baya kwa zo kuga gidan amma yau kam
Yau naji dan banzan yaro an taba haka?
Dada dan Allah kar muyi haka dake ki barni na wuce da ita in kin min haka ai se aji kanmu  a mana dariya dada.

To me kake nufi yanzu?
Ki bari ta kimtsa mu wuce kawai daga nan se kano zan yi report gun aiki

Masdook gaskiya
Dan Allah dada kinji dadata ki yi hakuri na miki alkawari da kaina zan dawo na tafi da ke da mama da inono da sauran yan matan

Hmm amma banso haka ba yanzu ku biyu kawai zaku tafi?
Eh dada
Aa kuje da fadima.
Dada in naje da fadima wa zai dawo da ita yau dan ni kam aiki ya min yawq kamin na samu hutu se na jima kuma ita ba zama zata yi ta yi ba har sena dawo da ita.

To ai shi kenan Allah ya sa hakan shi ne daidai
Amin.
Ki shirya yanzu fa kar na leqo kiran ki
Uhn kawai ta fada amma badan taso ba.

**
Zaune suke gaban baffa da su abbi suna musu nasiha
Kai masdook ga humaira nan amana ce a gurin ka yadda take amana a gurin mu gashi yau mun baka amanar mu ka cigaba da rikewa in ka cuce ta mu ka cuta kome ka mata kamar damu kake wallahi masdook kar ka bari inji wani mugun ji a zaman ku
 Insha Allah baffa baza a samu matsala ba.
Ke kuma masdook mijinki ne ,abokin ki ne,kuma ya zame miki tamkar uwa da uba ysnzu ki masa biyayya iya iyawar ki in yace yi ki yi bari ki bari banda rashin kunya humaira ki zamto mace tagari wadda za a ke kwatance da ita ki.kasance  me bin umarnin mijinki seki ga kun zauna lafiya.

Sannan farkon abunda zaku lura ku kula dshi a zamsn auren ku shi ne *hakuri* hakuri shi ne farkon abun luran ku in baku yi hakuri da juna ba akwai matsala ko wanne gidan aure da haka yake tafe wannan *hakurin* shi zama na aure zama ne na zo mu zauna zo mu saba ,zama ne na amana da yarda to fa ku rike wannan amanar ku yarda da juna
Humaira kar a kawo min karar ki ksima masdook kar a kawo min karar ka
Insha Allah abbi zamu kiyaye mungode
To kuje ku Allah ya kiyaye hanys ya bada zaman lafiys da zuri'a d'ayyaba.
Amin suka amsa kasa kasa.

***
Motar shiru kake ji tsakanin mutanen biyu tamkar ma ba kowa a cikin motar
Gefen ta kswai take kallon hanya shi kuma gogan yana ta satar kallon ta yadda yaga tayi wani fayau tayi kyau kamar ba ita ba
Kawai ji yayi wani feeling na tashin masa ina ma ace ina gida ne ina ma zan iya nuna miki yadda nake da tsananin bukatar ki
Ina ma ina son ki da komai yazo msna da sauki sede kash wannan zuciyar tasa ni cikin damuwa.

Ina ma hamma masdook ze gane irin son da nake mishi nima ya soni mu zauna lafiys ksmar kowa ina ma hamma masdook zai canja ra'ayinsa a kaina da bamu fi haka  ba zuciysta baki min adalci bs kina son wanda baya sonki baya kaunar ki burinshi ya bakan ta miki ina ma ace zan iya cire wannsn zuciyar na cire son masdook daga cikin ta kawai hawaye ya zubo mata tasa hannun ta ta share
Baki fara kuka ba mrs.masdook
Hmm kar kayi tunanin na karaya ne ina kukan bakin cikin rashin yadda zan cire ka daga raina na yarda kai a bola kamar wani datti dan ka zamo dauda me illata takurawa mutum a guna.

Ohh mrs.masdook ai kisani ni kadai masdook nike da ikon zama sanadin zubar kwallar ki ni kadai na isa nayi hurting dinki ba wani ba ke kan ki baki da ikon hurting ksn ki sede ni ya nuna kansa ni masdook muhammad nike da wannsn ikon na takurawa rayuwar *aisha humaira*
Ki dinga tunawa da wannan duk sanda kike bukatsr yin kuka ki tuns cewa masdook ne sila.

Mr.arrogant ko kadan ban jin haushin ka illa haushin kaina dana kasa yakice kadaga rayuwata na watsa ka daga cikin rayuwata
Na rasa ina zan sa ka na kasa tantance me ya kamata na kira ka dashi
Masoyina ko makikina
I hate u ko i love u
Wallahi hamma masdook i just dispite you honestly i dispite you duk sanda na tuna da kalamanka i feel disgust

K then get ready to be dispite always my slave

Kallo ta bishi dashi kawai shi kuma ya cigaba da tukin sa yana wani taunar cingum kamar wata mace .

(Tafiyar da nisa )

********      *******

Kaji me na jiyo kuwa?
Aa hajiya
Auren diyar ka ba tare da sanin ka ba anya ana ma adalci kuwa?
Hmm hajiya nima naji wannan abun amma yazan yi ?
Yazaka yi yarka tilo a duniya kace min ya zaka yi
To hajiya ki fada min ya zanyi me zanyi a lokacin da diyata bata san ni ba bata taba tuna ni ba bata taba yin tunanin dawowa ko zuwa gareni ba

Innalilahi wa'inna illahir raju'un
Dole nayi kuka dan wannan abun takaici ne a gareni ban ji dadin wannan al'amarin ba sam sam ina mugun bakin cikin shigowar wannan matsr cikin dangin mu ina wannsn takaicin Allah ya isa gashi ta zamo mana sila bani da ikon ganin jikata baka da ikon ganin diyarka.
 Hajiya se addu'a
Ka min alkawari koda bayan raina ne ina nemn alfarma ka kawo min yarinyar nsn taga koda gawata ne hawaye suka zubo mata
Subahanalahi hajiya kiyi hakuri dan Allah insha Allah zanje ni can garin zan kawo miki jikar ki ki gsnta amma insha Allah hajiya zaki ga jikar ki

To nagode maka nagode.


*****

Wajan la'asar suka shiga kano ya yi dasu sultan road inda gidan sa yake kawai kallon titi take yi.

Haka suka karasa gida yana parking ys fice kawai tana ganin hska ita ma ta fito ys hude but ya sauko da akwatin ta wanda ya rage ba a kawo mata ba
 Ki dauka ki shigo dashi
Kallon akwatin tayi yadda yake da uban nauyi da girma ta kalli hannun ta kai hamma masdook ko mugu akwatin ma bazai iya taimska min ba har ya shige ciki abinsa ya bsrta gaskiya bsn iya daukar wannsn akwatin harga Allah.

Waje takoma ko zata ga ysro da kysr ta samu wani dan saurayi tace ys taimaka mata haka ko aka yi ya shigar mata dashi palo ta ce masa ta gode ta bashi alheri yace yagode.

Masdook na kallon su ta saman bene kawai ya gyada kan sa .

Nima kairi na gyda kai ina cewa zaka zo hannu ne masdook au me.arrogant

Kan kujera ta zauna tana kawai tana bin gidan da kallo tabbas yayi mata kyau gidan da dakuna guda biyu a kasa da kitchen da kuma toilet a kasan benen.

 Mikewa tayi zumbur dan ta fi son dakin sama dama hawa saman tayi ta dinga kallon shi dakuna samsn guda biyar ne ta dinga leqawa har ta bude wani dakin kamshi ya doki hancin ta
  Leqawa tayi ba kowa amma taji karar ruwa kamar ana wanka
Wayat shi na neman agaji tayi kasadar dauka
 Sunan taga an rubuta
*zainab*

Haka kawai ta dauki wayar ta dau kiran
Hello masdook dan Allah kar ka kashe wayar kaji
Uhm
Kawai ta fada
Masdook ina son ganin ka dan Allah meet me ina son muyi magana nida kai
Wai ke mayya ce ko me na rabaki da mijina kinki ji kp to wallahi zan hada ki da 'yan'sanda su rabaku mayya kawai
Ke kuma wacece?
Matar sa.

Tsaki tayi gaki nan mayyar kin shiga tsakanina da masoyina kin kanainaye baya son ki dole ne

Haushi ys cika aisha ta kashe wayar ta goge call din ta sa num a blacklist
Komawa dakin tayi yayi daidai da fitowar shi daga toilet din

Rigar wanka ce a jikin sa ya na tsane gashin kan sa ya ganta dakinsa bakin shi ya bude
Dawayo da dabara ta ajiye wayar kan gadon
Ke me kike min a daki?
Ina da ikon shigowa ta fada tana harar sa
Kallon ta ya tsaya yi kawai
Ban baki izinin shigowa ba ai ni
Ni na bawa kaina
Kinga a gajiye nske bana son takura da damu zan kwanta na huta ban san damuwa.

 Ni ka zo ka sama min abunda zan ci yunwa nake ji ta na murguda masa baki

Ki nemi bawan ki
 Ya fada yana jan bargo ya kwanta ksn gadon bargon ta janye daga jikin sa wallahi Allah bazaka kwanta ba seka bani abunda zan ci.tukuna zaka kwanta

Ba inda zanje baki isa ba
Ok haka kace ko ?
Eh na fada
Wayar sa ta dauka ta kira num abbi

Salamu alaikum abbi an wuni lfy
Lafiya lou kun isa lafiya
Wallahi alhamdulilahi
Abbi dama hamma ne
Ta fada tans kallon sa
Masdook me ysyi miki?
Dama wai nace ya.....kwace wayar yayi ya sa hannun sa ya kulle ke bski da tunani dama
Kafadarta ta dage masa alamar i don't care.

Hello ! Abbi ina wuni
Lafiya lou
Meya faru ?
Abbi ba komai shakiyancin ta ne kawai.
Ksi aisha bazsta girma ba.
Se anjima.

Kar ki kuma daukar min waya
Ka kawo min abinci yunwa nake ji.

Key ya dauka fice a fusace yana bala'i a ransa

Wanka tayi ta sake kaya kafin ya dawo ta shirya cikin atampa skirt da riga fitet ta daura dankwali simple ta dauko turare ta fesa

A falo ta koma ta zauna tana jiran sa bata jima da zama ba ya shigo gidsn ds take away ajiye mata yayi a kan center table ya wuce dakin sa.

Dariya ta kyalkyale da dariya kasa kasa yanzu zan fara uzzurawa rayuwarka
Bakin dakin sa ta koma ta kwankwasa yana ji ya dora pillow kan kunnen sa shigewa tayi kawai direct abunta.

Yana daga kwance ta masa tsaye a ka
Me kuma?
Icecream nake so
Icecream?
Eh icecream!
Bazan kuma fita ba
Ai kana sane kk siyowa kasan ina so saboda haka sai ka koma ka siyo min icecream din
In naki fa?
Ta nuna masa wayarta alhamdulilahi ina da num abbi ill just dail d num
Ya mike a fusace ya nunata da dan yatsa ki...
Ta ce ooo dont even start(karma kafara)
Kawai ka je ka kawo min mu zauna lfy.

Wallahi zan dau action akan ki
Ni kuma zan dau direct action akan ka

Hankadata yayi kan gadon ya fuce daga dakin dariya sossea ta kauce da shi tana masa dariyar mugunta zaka sani ai.


Icecream ya siyo roba biyu ys kawo mata tana ganin sa ta amsa tayi waje sannan tace wallahi an yi 1-0
Biyota yayi tayi waje da gudu tana dariya
Kwantawa yayi yace women are *(emotional blackmailers)*
Amma zaki san anyi 1-0 sanda zai koma uncountable zeros dazan baki.

Da wuri ya tashi ya shirya dan zuwa gun aikin sa ya gama shirin sa cikin kanun kaya
Ya fesa turare ya daura agogon sa sannan ya dau key da jakar sa ya fita daga dakin.

A dinning ya tsaya ya saboda saurin da yake ya bude cornflask ya zuba a bakin sa ya sa madara spoon daya da ruwa ya tauna sauri sauri

Dariya yaji ana masa daga baya juyowa yayi yana kallon ta
Sleeping dress ne ajikin ta nylon blue light wayaga gauro mutum da matarsa amma kamar bashi da mata kawai kayi ladab a maka komai irin name iyali ka tsaya girman head 

Ni a principle dina ban san na bawa mace hakuri ko na mata godiya ba to ke a suwa ban iya roka ba sede na kwata

Ta zauna kan kujera tana kallon sa ta rike haba ta ce ah! Da gaske ? Ai ban san cewa haka kake da principles ba amma nagode daka sanar min sena zama addicted ko ?

Kamar ya kwade ta haka yaji ga takaici ya kama shi gaba daya ya rasa meze mata jakar sa ya dauka ya kara gaba har yana tuntube ma
Kaje a hankali fa ni bazan iya daukar kato ba
Juyowa yayi ya harareta ya na mata kallon zaki sani !

***

Sun dade suna waya ita da amira;da fadima da rabia suna confrence call
Amarya ya garin?
Lafiya lou
Ya first night din?
Kiyi aure ki sani kema
Au Allah abin gori ne ns miji?
To ai miji ba karya bane
In kinji haushi kiyi auren kema
To aisha humaira tsiwa matar hamma miskili.
  Ke rashin kirkin ki ya tsaya a tsakanin mu banda hamma
To naji.
Haka suka gama tayi wanka ta  sa kaya ta shiga kitchen ta dafa masu abinci ta ajiiye a kan dinning din.

Ta kunns turaren wuta gidan ya dau kamshi ta kunna kallo kuma tana kallon wani flim din india me suna *prem rathan daan payo*
Na salman khan da sonam kawai flim din burgeta yake yi.

Wajan la'asar ya dawo yayi sallama ta amsa
Sannu da zuwa
Youwa kawai ya fada ya sha mur dan yaga alama in yana mata dariya zata cigaba da raina shi ne.

Dakin sa ya koma yaga yadda ta gyara masa shi ta saita komai duk da shi din ma me tsafta ne yaji dadij hakan ga kamshi na tashi wanks yayi yasa jallabiya yunwa yake ji dan rabon shi da abincin kirki tun jiya
Hamma kazo kaci abinci kaji
Ina wasa dake
Uhm uhm amma pls
 Kar ka yi wa kanka horon yunwa a kan fadan mu
Kai ya gyada ya raba ta gabsn ta ya wuce ya debi abincin da  kan sa yaci.
Yaji dadin abincin sossai ya sha lemo ya tafi palo
Duk abunda yske yi kallon sa kawai take yi burgeta yake yi.

Kawai jefa masa tambaya tayi hamma in tambayeka?
Uhm
Hamma kasan waye mahaifina?
Kallon ta yayi me yasa kike tambaya ta?
Kawai ji nayi ina sha'awar sanin ko da sunan sa ne

Kallon ta yayi cike da mamaki
Hamma ka fada min koda sunsn shi ne nima ina sha'awar sanin mahaifina ksmar kowa i feel lonely without him

Mikewa ysyi nima bsn san shi ba dan bani da imformation ksn mutanen duniya i just care for my self ya hau steps.

Hawaye suka zubo mata a fuskarta tana kuka biyu ne kuksn rashin uba da kuksn rashin miji ko da tana da mijin bashi da amfani a gunts tunda baya son ta baya kulata kuma be damu da damuwarta ba me son ka ai yana kula da kai da abunda ya shafeta ta hada kai da gwiwa tana kuka

Yana labe jikn kofa yana kallon ta zuciyar sa tayi sanyi tausayin ta ya kama shi amma bazai iya rarrashin ta ba.

 A nan bacci ya dauketa seda za ayi magrib yaxo ya tasheta tayi sallah.

***
Yusuf ya
Lafiya lou ya kake ya matsr taka
Lafiya kalou ya aisha humaira?
Tana lafiya
Dazu fa mutuniyar tamin wata tambaya wadda ta dan sa na tausaya mata
Tambayan me?
Cikin shekarun nan da dama bata taba tambayar mahaifin ts ba se yau
Subahanalahi
Me ka ce mata ksi ?
Kawai na kawar da zancen ne dan bsn san mezan ce mata ba.

Good ka shareta kaji
To dama in ban shareta ba ya zan yi da ita
 To se anjima