AISHA HUMAIRA Part 2




Hutun mako na karewa suka wuce makaranta amma gaba daya aisha humaira hanklin ta na kan masdook tun bayan daurin auran be kuma zuwa ba kullum in sun yi waya da baffa ko abbi ko su mama yace aiki zai zo ko da makarantar ne amma kasan ranta tasan ya fada ne kawai karya yake yi ita ce baya son gani kawai.

Masdook,yusuf,nas,ni'imatullah,hanif zaune a tsakar falon masdook suna hirar bayan rabuwa
   Kai ango haka ake yi sai ka bace daga murna?
  Hmm kai ne kake ganin abun murna a cikin wannan auran
Auran alakakai.
   Kai mutumina baka da kunya da kirki muna nan kake ci ma yar'uwar mu mutunci ko
   To ace ban da hadi da ita man
  Aa meye zafi?
To ai karshen cin muntunci kenan
 Ni'imatullahi yace dana san da haka dana shiga na fita da fadanci na karbi auran aisha humaira
  Kallon shi kawai masdook yayi ya kyabe fuska ya dau lemo me sanyi ya sha ya ajiye ka makara kuma ba .
  Me aibun humaira masdook kai ko.
 Tana da kyau
diri
Ido hanci zukeke
Ga gashi ga haske irin matqn nan ne masu kyan jiki da tsari tana da fara'a in ma yarinta ce ai zata daina lokaci ne kaima fa kayi nagani
   Yusuf yace amma hanif kai dan iska ne kai kuma ka tsaya ana tanka ma zubi da tsarin matar ka ko kayi shiru ai da ni ne da tuni na make masa baki yayi jini
 Aka sa darya ban da ogan ya sha mur yana wani nazari na daban shi kadai yasan me yake tunani se wanda yayi shi (Allah).

Ku kuna ta ma humaira campaign inji yusif ku barshi man ai ido ke gani shi be hango ba amma ina tabbatar muku da cewa zai dawo yana a masa sulhu in ya fada tarkon yar mitsilar yarinyar da ya raina.

Fatan ka kenan yusuf?
Sossai ma.
To xamu gani ai inda rai da lafiya ba
 Yes we shall see.

   *BAYAN SHEKARA UKU*

Wasu siraran hawaye ke yawo kan kuncin kyakyawar fuska me dauke da murmushi kullum a yau kuma hawaye ke zuba kamar bazai kare ba
   Ta gefenta ta riko hannun ta tana rarashin ta haba kawata haba ban san ki da haka ba ni kawata jaruma ce wadda tasan jaramunta da dauke kai kin hakura har shekaru uku balle yanzu kuma?
  Hmm bazaki gane ba so dafi ne me wuyar warkewa so in ya kama ka baya cika ka so wuya ne dashi so nauyu gare shi a zuciya musam irin wanda nake yi *son maso wani* amira only my Allah knows yadda nake son hamma amma na rasa mesa baya sona har bakin jini na ya ksi haka amira da za a kini?
Me aibuna na gyara?
Me nake yi mara kyau fada min na gysra?
Ta fada tana jijjiga ta tana kuks fada min amira fada min.
 Na gaji wallahi Allah na gaji na kasa sukuni
Duk sanda na runtse idanuna shi kadai nake kallo shi kadai nake gani a ko ina na kasa cire shi daga raina am getting mad amira zan zauce
  Rungumeta tayi haba kawata ki daina damun ksn ki insha Allah komai zai zo karshe komai yayi farko ai zai yi karshe ki daina damun kan ki focus in ur education ki bar hamma besan me yake loosing ba
 Kiyayar tayi yawa amura good three years ace ban sa shi a idona ba
   Na sani amma ki kara hakuri shi ne ribar zama na duniya ki kara hakuri kin ji
 Kema ur tym will come zaki ce na fada miki .

 Allah sa amma zan koya wa kaina share alamuran sa a zuciyata.
  Ko kefa ki daina kuka kawai ki min murmushin nan naki dake nunan cewa yes wannan ce *Aisha humaira* ta
  Murmushi ta mata me kayatsrwa
Point dinta ya loma ya koma ciki sossai karamin bakin ta ya kuma tsukewa ta share hawayen ta sannan tace so ba karya bane ill make it
yes zaki iya.


Aiki ya gama kacame masa a office bashi da hutu sam sam
 Ga wani gumi da yaji yana zubo masa har rawar jiki yake yi saboda ciwo
  Drower ya bude ya dau maganin sa yaga wayam alamun babu kenan tsaki yayi ya juya dan dauko wayarsa da kyar ya iya dauko wayar ya danna number abokin sa nas
 Hello nas
 Ya akai masdook
Nas dan Allah kazo office ko da lemun tsami ne
Ni ina zan ga wani lemun tsami ?
Ban sani ba kawai i need it.
Yq kashe wayar ba tare da ya kuma jin meze ce ba
 Nas dake kwance a quters ya mike ya duduba ko da akwai a fridge din sa yaga bsbu tsaki yayi ya dau mukuli yayi waje
  Masdook ko ciwon ciki sossai ya ksma shi ga fanka ga ac amma duk da haka gumi yake yi ya kasa sarrafa kan sa.

Kasuwa ya je ya samu lemun tsami ya yi asibitin.
  A yadda ya same shi ba karamin kaduwa yayi ba ya yi saurin tallafo shi aa masdook jikin ne har haka?
  Ina lemun ?
Ungo ya bashi ya dan lasa a bakinsa ya kuma zuqa ya kwankwadi ruwa ya kwanta a kan kujera.

Yayi ajiyar zuciya.
Masdook wai kana son kan ka kuwa?
Ban gane ba nas
Masdook kasan cewa halin da kake ciki ya kamata ka samu partner a kusa.

Hararar sa yayi ya juya masa baya kar ka soma nas kasan bazan iya kiran wannsn yarinyar ba dan ba abunda zata iya min bata kai ba kuma ba zata kai ba.

Ok naji amma zaks iya samo wata matar ko ka aura wadda kake so.
  Ina zan samu kawai nas na fawalawa Allah komai

To Allah kiyaye amin.
Nagode na taimakon da kayi kuma kar ka fadawa ko da yusuf ne
  Ok naji ta wuce.

Amma in fadama wani abu?
Uhm kawai ya fada.
Ka yi reconsidring din dangantakar ka da aisha humaira aure ba fa wasan yara bane kuma kana bukatar ta tunda an daura auran ka daure kayi kokarin ganin kun zama daya kaga tana sonka kar Allah ya ksma ka da hakkin ta.

Hmm nas nagode sossai .

     *makaranta*

Sun shiga ss1 yanzu a science class amira da aisha suke.
  Komai ya sauya musu domin nutsuwa taxo musu sun rage wannsn shirman na yarinta musamman ma aisha humaira da ta kara girma.
 
  Kullum da son shi take kwana take tashi a ranta amma hakan besa ta daina karatu ba illa ma da ys bata kwarin gwiwar yin karatun a ganin ta dan bata da ilimi da wayewa yasa baya son ta shi sa take ganin idan tayi karatun zai so ta.

   *****************

*a gurguje kuyi hakuri ina dan yin labsrin da sauri ne hakan ya kasance ne saboda wasu dalilai da dama*
Tafiya take yi kamar tana tsoron taka kasa hannun ta rike da wata iriyar jaka ta gayu rataye a tsintsiyar hannun ta
  Tayi irin daurin nan na zamani me hawa hawa ta ci ado tasa irin takalmin nan me tudu ta saka
 Gefenta amira ce wadda na dinga kallon su yadda suka yi kyau suka canja gaba daya kamar ba jikokin da'ada ba tsabar nutsuwa.

   Fadima ta riko hannun *aisha humaira* kinga sis mutumin ki ya iso fa
  Dagowa daya tayi ta masa kallo daya ta maida kan ta kan wayarta gaban ta bugawa yake yi amma ta basar zuwa ysnzu ta san cewa hamma masdook bazai sota ba ta koys wa kanta kokarin share shi ita ma kila nauyin zuciyarta ya ragu.
  Hamma yusuf ya yafito ta da hannu bata gani ba fadima ta tabota hamma yusuf na magana
  Tsaki tayi tana taunar cingum kamsr a kan ta a ka fara cin cingum.

  A hankali ta karasa gurin da suke inda kamshin turaren ta ya musu sallama
  Gani hamma
Ungo ya mika mata leda gashi soveniers ne kuyi amfani dashi a gun dinnar din ku bawa mutanen ku.
 Tom hamma angode
Amma kina ji ?
Eh
Ki fadawa amira ta dan koma daga ciki mana kafin anjiman ban son ana kalle min ita
  Murmushi tayi to hamma angama a mana afuwa mun yi laifi
 Ta juya kenan yace baki gs masdook bsne?
Na gan shi ta kara gaba dan inta kara tsayawa zata kasa daurewa.
  Masdook besan inda zai sa yanayin da ya shiga ba amma yasan cewa lallai yaji wani abu a tare dashi.

Mutuniyar fa ta koyi halin naka
Ni ina ruwana da ita?
Kai ko kake da ruwa
 Hmn kai ka jiyo
Hhh kai kam ka ksms ka rike ta ka kyaleta mana masu so su aura
  Wani kallo ya masa yana gyara tsayuwar sa
  Ni na rasa tsayuwar me suke yi ma a waje gaba dayan su .
Ni'imatullahi dallah kora yaran can cikin gida
Wane yara?
Gasu can man
Ya kalli yan'matan yayi dariya a ransa ysce wannan masdook da manyance yake wallahi.


Wai ya zaka hana yanmata sha'anin biki ina aka taba kora daga harkokin biki in ba a gunka ba masdook
  Hararsa yayi sannan yace ni da ma...
Se kuma yayi shiru
Karasa mana masdook matar ka ko?
Ban ce ba kar ka kaini inda ban je ba
  To ma gani dai masdook .

   Bayan magrib suka nufi gurin kwalliya su hudu harda amaryar
   Inda sun sha ado da kwalliya se walkiya suke yi
  Kayan jikin su iri daya sun sha dinki ya kama jikin su dake fitet gwon suka sa hill da roses 
 Ba karamin haskawa humaira tayi tadan dosana mayafi kan kafadar ta
  Da karamar purse a hannun tq kalar sarkarta da takakmi

  Angwayen sun sha ado suma suna jiran amaren cikin mota da aka faka guda uku .

Masdook ni'imatullahi da nas sune ke jan motar jiran su kawai suke yi su fito su tafi hall din dan su ake jira a gurin.

   Fitowar su keda wuya masdook ya maida hankalin sa gaba  daya kan humaira gsba daya ta tafi da imanin shi amma a fuska baxaka gane ba ya ci kunu ya sha mur ya bata rai
 Bude motar yayi ya shiga a tunanin sa zata shiga motar sa ne sede abun mamaki motar ni'imatullahi ta shiga gidan gaba fadima ta shiga motar da amaryar da angon suna motar masdook.

Haka aka yi tafiyar.
   Isar su keda wuya kowa da wani a gefen ta suka shiga cikin tsari suna xama ya samu gu ya zauns har kan sa ya fara juyawq ma shi saboda hayaniya banda matsayin yusuf a gurin sa ai ba abunda zai kawo shi gun nan.

Can aka saka wakar kujerar tsakar gida ta ado gwanja kar kusu kuga yanmata da maza yadda suka hade suna cashewa.
   A xaune take amma kidan ya tafi da ita bata ma san sanda ta shiga filin rawar tana cashewa wani hadaddan guy ya mike cikin isa da salo yana mata liki a jikin ta ganin ya nace mata yasa ta gyara tayi waje ta koma gurin inono ta zauna
 Inono tace ke kam anyi ysr kaniya kin shiga rawa kamar wata budurwa kuma mijin ki na nan
  Inono ayi hakuri .
 Kiranta fadima tayi mikewa tayi ta isa gareta aka sha gabsn ta dagowa tayi da sauri dan ganin waye wannan guy din ne ya sakar mata murmushi tsadadde
  Kai tsaye yace ina son ki sunana *ADNAN MUBARAK CIROMA*
Ina fata zaki ban hadin kai mu sasanta ksn mu waya sani ko mune next za ayi...
  Yi hakuri bawan Allah ina da aure
  Haba dai ki bsri mana ai baxan yarda ba cewa kina da aure dan ki yafice ksn ki daga gareni ni kuma na gani ina so.

 Wallahi ina da aure ga mijina ma can ta nuna masa masdook wands tun daxu yake kalllon su ya sha mur ya dauke kai kamar baya gurin amma basarwa yake kawai ya rasa dalilin da ya sa ran shi ke baci kan yarinyar da baya so kawai abu daya ya ke masa yawo a kwanysr sa
*ina sonka kuma dole ka so ni*
Ya girgixa kan sa yana cewa *no* bazai yuwu ba.

Kinga zo dan Allah zo mu zauna kinji mu fuskanci juna in ba haka ba zan biki duk.inda kika shiga Allah.

Jin haka ta tsorata sannan ta zauna kan kujera ya zauna shima
Ko kefa sunan ki fa?
*Aisha humaira*
Nyc
Dan Allah kice kina sona zaki aureni kinji wallahi ban taba haduwa da macen data sacen zuciya cikin yan lokuta ba kamar ki (love at first sight)
Nagode adnan amma ka makaro ni zuciysta mutum daya keda ita daga shi babu wani har abada ka fahimce ni ka yarda kuma duk wsnda zaka tambaya a nan matsayina zai fada maka cewa matar aure ce
  Oh God nima mijin aure ni naga alama sona ne ba kya yi.
  Murmushi tayi hmm aisha humaira mutum daya zuciyarta tske so take kauna kamar yadda uwa ke san danta haka nake son sa ba me maye gurbin sa a raina ina fata ka fahimta.

  Nayi rashi hummy nayi rashi amma ...kawai mutum suka gani a kan su ya tsaya yadan rankwafo ya ce bawan Allah ko zaka iya bani aron matata?in kun gama gaisawa ?
  Am sorry fa kayi hakuri
 Hannun ta ya kama ya yi waje da ita inda ba hayaniya. 
  Cikin mota ya turata ys kulle da key yayi gaba abunsa.
  Ta dunga bugawa hamma ka bude min kofa zaka rufe ni ksmar wata fursuna ka bude open the door.

Komawar shi keda wuya gun adnan ya koma ya nuna sa da yatsa kayi na farko kayi na karshe ksr ka kums ko a hanys ne ka nuna kasan matata ya kada ksn sa ys shiga cikin hall din sossai wajsn su nas ya zauna





Nas ya dafa shi ya dai man
Ba komai.
Da kyar ya tsaya aka gama kammala partyn
  Humaira yake nema gaba daya idan shi na neman ta amma be ganta ba
Nadiya ina humaira?
Sun tafi a motar hamma ishaq .
 Yyi jim ya gyada kai ya fice ba wacca ya dauka a cikin yanmatan harsu inono din be bi ta kan su ba.

Komawarta gida keda wuya ta yi wanka tayi sallar isha'i ta sa wasu rikitatun kayan bacci dake mutuniyar bata son zafi ko takura musamman manyan kaya ta baje kan gado ana hira amma hankalin ta na wani tunanin na daban dadi take ji hamma masdook ya fara kula da lamarints amma haushi daya take ji da beyi ba sai yanzu daya ga ta girma ta sauya kama mtsw dan rainin wayo kawai
 Kedawa ke kuma hajjaju?
Ban sani ba magulmata
Maida wukar sis bani na kar zomon ba rataya akw bani
Suka sa dariya gsba dayan su.
   Har bacci ya fara dauketa
 
  Shigowa yayi cikin kananun ksya ya canja kaysn sa ya shiga dakin da'ada ya zauna suka gaisa da'ada ina humaira?
Humaira tayi bacci yanzu ai dan tun daxu ta shirya ta kwanta kasan gajiyar biki.
 To dama zan fada mata wata magana ne
  Amma tunda ta kwanta bara na fada miki ki sanar mata kar na ganta gobe ba mayafi gun bikin nan kuma kar ta kuma tsayawa da wani kato

To ayi hakuri insha Allah zata kiyaye
  To seda safe
Allah tashe mu lafiya amin.

 Dakin ta leqa taga tayi bacci amma sauran na hira ku bazaku kwanta ba ku huta ga wani taron gobe zaku yi.

To yanzu zamu kwanta.

***************
 Da asuba ta tashi da matsanancin ciwon ciki da kai ta dinga kwarara amai gashi ta galabaits hankalin da'ada ya tashi ta kasa sukuni yar lele ba lafiya.
  Mutsumutsu ta dinga yi a kasan bandakin jini ko ya bata  mata jiki rabia ta kira wo inono aka taron mata a kai.
   Gaskiya tana wahala yarinysr nsn duk wata ace se mutum yayi kamar ya mutu
  Masdook na dakin sa yaji ana hayaniya fitowa yayi dan jin ba'asi 
  Meya faru kuma?
Humaira za a kai asibiti 
 Humaira kuma ?
Meya sameta
nima ban sani ba gashi dai zasu shiga mota da ita
  Key ya zara yayi waje da sauri amsarta yayi ya sa cikin mota ta gama galabaita bata gane kowa a gun
Numfashi sama sama take kawai idanta ys lumshe ta suma a gurin.

Rudewa mama hajja tayi shi kuma ya kara gudu har suka isa asibitin aka shiga da ita emargency
   Sai zarya yake yi a waje ya kasa zama gu daya mama hajja da inono sun zauna jigum.

Jin kadan likitan ya fito ya ce wani ya biyo shi office din sa ya zauna yana kallonshi
  Gaskiya tana fama da ciwo a cikin ta wnda shi yasa take shan wuya wajan aladar ta duk wata
  To dr.me za ayi yanzu ?
Ina tunanin better case ayi mata surgry a cire mata abun insha Allah komai zai dawo normal
 To dr yaushe za ayi aikin?
Anytime from now in kun shirya
Ok
  Amma waye zai yi siging na yardar op din?
Ni
Wa kake a gunta
Mijin ta ne
Ok to anjima ka dawo munyi admiting nata
ai kasan proccess din komai dan se yanzu na gane ka dr.masdook muhammad diko
  Murmushi yayi kawai ya fita.

Kai ya akai me likitan ya fada.
Cewa yayi za a mata aiki kar ku damu muje na sauke ku a gida zan dawo anjima
  Aiki kuma masdook meya sameta hska
Bayani ya musu a nutse yadda hankalin su baxai tashi ba
  Ya kai su gida ya yi wanka again ya debi kayan ta biki dai ya tashi a alhinin yar so yar lele aisha humaira ta da'ada matar manya masdook
   Haka aka daura auren ba wani jindadi dan dai ya zama dole ne da dagawa za ayi ma

 Yana kimtsawa ya koma asibitin bata farka ba har zuwa wannan lokacin
Kan kujera ya zauna inda ze dinga ganin movement nata
 Kusan after minti uku seya duba plus din ta sanan ya zauna
   Wajan magrib bayan anyi sallah dr.isa ya fara shirya aikin da zasu yi
  Hannu masdook ya sa aka shiga dakin op din da humaira shi ma bin su yayi dan is allowed .

   Banda baffa da abbi da baffa kabir ba kowa a asibitin.

Masdook ne ya fito yana cire gloves nurse na amsa ya dan sha mur
 Baffa ya ce ya dai?
Alhamdulilahi an samu nasara hutawa take yi an maidata dakin hutu.

To masha Allah alhamdulilahi har naji dadi a raina bara na kira su da'ada na sanar musu ko hankalin ta ya kwanta dan ta fi kowa damuwa dan humaira komai ce ta da'ada.

Hmm a ransa yace baka ji tawa zuciyar ba abbi da ka tausaya min fiye da kowa.
    *

Washa gari ta farka lokacin fadimatu ce a dakin su msma na waje a zaune kan kujera masdook kuwa ya komq gida ya dan kimtsa jikin sa ya huta sai ya dawo
  A hankali tw kira sunan Allah tana kokarin mikewa fadimatu ta yi wuf ta mike ta yi wajebdan kiran mutan gidan.

Da sauri suka shiga dakin gaba daya dan ganin ta
  Tayi fayau ta rame cikin kwana daya cuta da wuya (wayanda basu da lafiya Allah yw basu lafiya masu shi kuma Allah ya kara musu).

Ya gama shiryawq kenan ya dau mukuli ya fita yaji alamar sako a wayar shi dubawa yayi da kyau kuma fuskar sa dauke da mamakin ganin sakon da number din
   *ya kake habibi na ina ka shiga ka manta dani masoyina ka manta da baya ka dawo mu fara sabuwar rayuwa nasan ni kake so ba wannan yarinyar ba*
  Tsaki yayi ya cigaba da tuki abun sa

    Haka ya tsaya a supermakert ya yi yar siyayya su yougurt da abubuwan kwadayi dan yasan humaira amma be siya za'ki ba dan yasan larurar ta.

    *ya zaka min biris duk yadda nake son ka ka manta baya nasan nayi kuskure amma ka yafe min ina kewar ka*

  Sitiyarin ya buga yayi tsaki
  *ban san ciwon kai kar ki kuma damuna ina wuce guri na wuce har abada baki isa komai ba yanzu a gurina ki fara koyo daraja iyayen wasu tukuna sannan na ga ko zan iya kara ki rayuwata*

Tana kwance a kan gadon ta taga sakon ya shigo dubawa tayi cike da mamaki tabdi jan lallai masdook ni xaka  wulakanta?
  Dani kske zancan.

**
 Hankalin ta kawai masdook take son kalla shi take son gani ko taji sanyi a ranta
  Soup inono ta bata a baki ta amsa tana sha ta shagwabe mata fuska inono ni bani son wannan abun
  Ki bani abinci me kyau naci
Uwariyo ki sha soup kiji dadi a jikin ki abinci me nauyi ba yanzu ba zuwa gobe ko jibi
  Kai ni wallahi bani son wannan gwara yougort da dan chips
  Bakin kwadayi ysr banza ki sha kina jina ko
   Ana haka masdook dikko ya shigo
 Lumshe idanun ta tayi dan kanshin turaren sa da ya ratsa dakin 
  Gaisawa suka yi da ysn dakin sannsn ya ajiye ledae hannun shi .  Ya me jiki kuma?
Jiki alhamdulilhi da sauki gashi zata fara aikin za a dora daga inda aka tsaya.
  Me take so kuma?
Zaqi man
 Nifa inono yought nace ba zaqi ba ki barni na sha ko suger free ne
 Ke kika san wani sugerr me oho miki
 Ta zumburo bakinta hamma pls ka sa su bani ban san soup

Fadima!
  Na'am hamma!
Bani ledar nan
Dauko masa tayi ta bashi ya dauko yought din zaunawa yayi kusa da ita ya dinga batq a baki
 Fadima ta kalli amira suka kanne ido daya a tare suna murmushi kasa kasa.
   Ya dan xubo mata gefen baki ya sa hanki nasa ya goge matq bakin
  Inono da mama suka fita daga dakin haka ma amira da fadimatu suka bar dakin suma.

  Hannun sa ta rike alamar ta koshi
  Ido ya bude mata ya kuma sa mata a baki
  Ta karba da kyar tana gyada masa kai alamar aa ta koshi.

Kinga bayan zama a nan ina da wasu ayukan fa ki karba kawai ki koshi ina da uzuririka da yawa dazan yi.

Hmm ta fada masa kawai tace ni na koshi nima ban ce ma ka zauna ba a nan kana iya tafiya ba rike ka nayi ba.

Kallo ya bita dashi na mamakin humaira sossea ta canja masa ko dama can haksn take garin ya mike ya zubar a kan rigarsa tsaki yayi ya shige toilet
  Dama ya bar wayar sa a kan gadon
 Sako ya shigo kamar karta dauks se ta dauka ta duba
  *pls masdook nace ka yafe min wallahi na tuba ina son ka zan iya zama da kowa ma a ksn ka zan iya zama da iyayen ka da so called matar ka*
  So called?
Ni kenan lallai ma wannan koma wace zata san cewa hamma masdook nawa ne ni kadai ba wadda ta isa shiga tsakanina da ita
Num tayi copying a brain din ta tayi sauri ta qjiye masa ta kwanta abunta
 Haka ya fito ya karqci kallonta sannan ya fita.


Juyowa tayi a kufule tana kumbure kumbure abunta tsaki tayi yafi a kirga ta riga tasan matakin da zata dauka kan wannan mayyar dazata ruguza mata rayuwa tun kafin ayi zaman auren ma.

Kwananta biyu a asibiti aka bata sallama taso taje kai amaryar amira amma dada ta hanata zuwa cikin yan kwanaki ta murmure tayi fes da ita ta dada cikowa
Ranar da yamma suna zaune a kan tabarma ita da fadima da ummu jamila suna hira
 Ta dau wayar ta wannan number ta danna tq kirawota harda shigewa uwar daka inda ba hayaniya.
  Hello!
Ba rokon ki nike son yi balle tambaya ina miki warning ne cewa ki tabbata kin rabu da mijina ki daina shiga harkar sa babu ke babu shi kina shiga min rayuwa kar ki kuskura ki kuma kiransa ko da a waya na mun gode da gaisuwar ma
  Ke dakata waye mijin naki?
*Masdook*!
Ohh kece dama banzar yarinyar data yi sanadin *(a sanadin ki littafina na gaba insha Allah)*

Ke kikayi sanadin rabuwata da masdook amma ki sani sena shiga rayuwar ki ta yadda bazaki iya fita ba sena ruguza farin cikin ki ta yadda zaki daina dariya ki manta yadda ake yinta masdook nawa ne nawa ne kawai ni kadai.
   Shi kenan ni ina da wani karfi guda daya kinsan me wannsn karfin nawa?
  Shiru ya biyo baya ok barq ma kawai na amsa miki
   Karfin Aisha humaira masdook shi ne karfina kuma matukar ina tare dashi matukar ina numfashi to da son masdook nake numfashi ko wanne dakika da second duk wani jini dake yawo jikin aisha humaira da son masdook yake diga tun bansan so ba nake son hamma masdook shekaru goma sha daya ina *dakon son sa*
A raina amma bsn bari yq kubuta min ba to ta yaya zan bari keda kika shigo rana tsaka na bari ki amshe shi a bagas?
  Na fada miki ki nisanta kan ki daga mijina snatcher kawai.
Ki nemo naki mijin masdook ya mijin aisha humaira ne.
Tq kashe wayar tana masifa kawai mutane su dinga bin mazan wasu suna damun rayuwar su ni da na zaunadashi ne ma yace yana sona ai da da sauki
  Kuka kuma ya zo mata ta juye hawayen ta idan abun ya cita wata ran tayi ta kuks ita kadai tq rasa wanne irin so take ma hamma masdook wanda shi ba haka take a gunsa ba.
  Hannayenta ta daga sama ta kai kukan ta ga ubangijin kowa da komai dsn shi zai yaye mata shi kadai zata dogara dashi ba mutum ba ya Allah ka dora masa sona yadda ka dora min nasa
Wallahi ina son hamma masdok
  *(so me wuyar sha'ani)*



Wayar ta yarda a kasa ta tarwatse a gun kan buuu ni wannan yarinyar zata karqntawa karatun rashin kunya da wulakanci lallai ta nunan ita din meson masdook ce amma nima nayi alkawri guda daya sena shiga rayuwar su sena tarwatsa su sena yi kace kaca da wannan soyayyar .
   Ta zauna tana saka abunda zata aikata mata ta huta a rayuwarta taji dadi ko bata auri masdook ba seta raba ta da masdook .

    ****

Kowa ya watse gidan ya yo tsit cikin wasu kananan kaya ya fito se kamshin turaren sa ke tashi ta ko ina ga tsadaddan takalmi ya saka ya dauko jakar laptop nasa ya shiga dakin dada dan ya mata sallama wucewa zai yi kano.
 Dada zan tafi !
   Aa tun yau masdook?
Wallahi na bar aiki fa da yawa kin san aikin namu
 To Allah kiyaye hanya
Amin.
Dada ina humaira?
Ina ga tana dakin ta
  To bara naje mu gaisa na wuce
To to
Ya shiga dakin humaira tana bandski lokacin daya shigo seya ji dakin ya masa dan shi meson kamshi ne dakin ko banda kamshi ba abunda yake tashi kums kal dakin ba kazanta .
    Tana waka ta fito daga toilet din
   *yanzu ni da kai ba shamaki bari ja da baya kar mi haka*
Tsayawq cak tayi tana mamakin ganin mutum a gurin
   Zata koma ya daure fuska
Ke ban san hauka mezan gani a jikin ki dazaki gudu a banza in kin koma ma zan fada miki ne zan tafi yanzu in akwai abunda yake damunki ki fada min ba sena tafi ba jarabar taki ta motsa miki bana nan kuma
   Kallo ta bishi dashi kallon me kake nufi ?
Kallon wacca jaraba kuma?
   Kin sa min ido kamar mayya kina kallo ina jiran ki ina da ayyuka masu muhimmanci da suka fiki fa
  Ta hararesa ba abunda nike so Allah kiyaye hanya ya kiyayeka daga sharrin masharata kawai ta fada
 Ya bita da kallo kawai yadda yaga jikinta me matukar daukar hankali
   In ka gama kana iya fita zan sa kaya ne ban san ana tsaya min a ka ko a takure ni da kallo.
  Kunya ta kama shi yayi waje da sauri abunsa.
  Ta window ta leqa har ya fice daga harabar gidan gaba daya.
  Zan yi kewar handsome look naka.

****
Wai ni baffa wannan yaran su yaushe zasu tare lokaci yayi fa da ya kamata masdook yace wani abun
   Haka ne amma tunda banga ya motsa ba shi yasa bsn yi magana ba
Amma nags yarinyar zata fara makaranta a can buk idan lokacin yazo ba sai kawai su karata su biyu ba.

Haka ne Allah ya taimaka yasa ayi a sa'a
Amin.

   Ni fa dada yau gidan amira zanje
Ni bsn hanaki ba amma ki tambayi mijin ki
 Wai kice in tambsyi mijina yana ina dazan tambaye shi?
Kawai ki bani kudin mota ko na je gun baffa da abbi ya bani.
  Ni ba ruwana kinsan halin masdook yana jin kin fita zai min wannan aikin nasa
To ina ruwan sa da fitata?
Ban sani ba
Wallahi dada sena fita kawai ki ban kudin mota kinsan banda kudi
Nima banda shi mara mutunci
Dada dan Allah ki ban wallahi na riga nayi niysr zuwa kuma na fada mata naga da fitar nake ba tambaye shi ba sede in tambaye ki kuma ki barni se yau.

   *so ba shi ne se mutum yana son ka ba ya kasance so so yana faruwa ga kowa ko ka shirya ko baka shirya ba idan Allah ya riga ya shirys maka ba yadda zaka yi one has to be self content with what he have*

Ba wani jimawa suka yi ba suka sauka a katsina gouruba road
   Wayarta ta zaro ta kira num aminiyarta
  Hello amira
Hello sis kina lafiya?
Wallahi alhamdulilahi ina kalau ya mijin naki da gidan ?
Wallahi komai alhamdulilahi
  Kizo waje man ki bude min kofa
  Kee sis ban san tsokana fa
Shi kenan bari mu koma tunda baki son ganin mu
Aa ina zuwa mayafinta ta zara tayo waje tana budewa taga sis dinta ai da gudu ta rungumeta tana ihun dadi
Wayyo Allah na yar'uwa shigo daga ciki
 Hamma kamal sannu da zuwan ku naji dadi sossai yau kune a gidan
  Dama ina ts zaman kadaici kai amma naji dadi
  Suna xama ta tara musu abun makulashe a gaban su
  Ya karfin jiki kuma?
Da sauki wallahi
To masha Allah.
 Hamma sannu da zuwa kune na farkon zuwa gidana
  Uhm lallai kam ina hamma yusuf din
Ya dan fita amma nasan yanzu ya kusa yana hanyar dawowa
 To ai shi kenan.
Amira ta kasa zama yi wannan hada wancan ta gama hada musu abu mai dadi sannan ta zauna
   Jim kadan hamma yusuf ya dawo suka zauna suka gaisa ya yi cikin daya falon da hamma kamal suk barsu a anan.

Kee sis haka kika kara fresh cikin kwana biyu kawai me hamma ya baki haka?
Hmm krdai bari kema zaki je gurin
  Wallahi sis u look take away sossai kika yi kyau kamar ba ke ba hamma ya iya kiwo
  Hhh kai aisha humaira
Wallahi da gaske nake miki fa to shi kenan godiya dubu.

Kin ban sha'awa sis kin yi kysu hamma na son ki kina son sa kuna soyewar ku kamar ba ku ba amma ni da aure a kaina kusan how many years wanda da me sona ne da tuni mun dan tara
  Hmm aisha humaira kenan bari cewa haka wallahi yana sonki tsabar tsantsar miskilanci ne
Menene alamar so ne?
*Kulawa*
Naga kulawa a tare da ke a idan hamma masdoo.
*damuwa*
Naga damuwa a idansa lokacin da baki da lafiya.
*kishi*
Naga kishin ki zallah a tare da shi lokacin bikina.
  Sossai hamma na son ki
 Ki daina kare yayan ki dan Allah ni na san baya sona
 Wallahi baxan yi kaffarq ba hamma yana mugun son ki kuma kema kin san da hakan nagani a idan sa
  Ki daina bin zancan idanuwan nan ki daina sauraran su in ba haka ba zasu yi decieving naki a barki a ruwa.

  Kinga mu canja topic banda lokacin wannan zancan yanzu.


**
Kwance yake a kan gado ya kasa katabus kawai daya kulle idanuwan sa surar matarsa yake gani
 Idanuwanta ke masa yawo a idan sa
 Yadda take tsiwa,murguda baki,masa rashin kunya burge shi yake yi.
  Ya mike ys jingina da bangon gadon nasa ya Allah meke faruwa?
So wata zuciyar ta bashi amsa
 Ya juya da kyar no bani son ta mesa zam dinga tunanin ta haka kawai
  *Ni wacce ita a guna*?
Matar ka,halalin ka,masoyiyarka.
Duk duniya ba wanda zai nuna maka so kamar ta *aisha humaira*
Tana son ka mugun so tun kafin ta san ma'anar so take son ka.

Wayar shi ya dauka ya kunna dan tun safe a kashe take
   Data ya kunna ya leqa watsap family grp nasu ya shiga an tutura hotunan bikin yusuf da amira
  Suka gama budewa gaba daya humaira tayi kyau wani hoto ne ya dau hankalin sa sossai wanda humaira tayi ita kadai ta yi mugun kyau
  Ga killar smile data yi
Shi ma besan sanda yayi murmushi ba a cikin grp din ya dau nuj ta.
   Da niyar zai kirata a waya.

Wanka ya fara yi yaci ado yayi kyau ya sha turarw yadda kasan shi ne ma turaren ya dau tsadaddan takalmin sa ya saka ya dau key da wayar sa ya kulle gidan nasa.

Mota yq shige abunsa ya juya mata kai yayi gaba
  



   Cikin nutsuwa yake tukin tamkar bashi da wata damuwa kwata kwata a tattare dashi
  Hankali kwance yake tafiya yana dan murnusawa.

Cikin hour biyu da rabi ya isa inda yake shirin zuwa ya karasa layin su ya parker motar shi cikin yan dakika kadan ya parker motar ya fito abunsa.

Bangaren su ya fara isa ya samu mama kwance kan kujera tana hutawa
 Salamu alaikum
Amin wa'alaikum sallam wa nake ji kamar masdook?
  Mama ni ne
To amma nayi mamaki shekaran jiya fa ka tafi
 Wallahi mama kawai na dan dawo ne
 To sannu da hanya tashi tayi ta dauko masa ruwa me sanyi ta zuba mishi ya kurba
Kaje ksyi wanka tukuna se kazo ka ci abinci ka huta
Ai mama yau zan koma fa

Hba dai kamar ana korar ka tashi kaje kayi yadda nace maka yaushe zan bari ka koma yau tsaka da yamma sossai.
Mikewa yayi yana dan murmusawa.

Da ya gama kimtsawa ya shirya yayi.cikin gida gurin su baffa ya je suna zaune kan tabarba a tsakar gidan suna cin tuwon dawa miyar busasshiyar ku'bewa.

Ya tsuguna ya gaida su dukka suka amsa faram faram
Aa masdook sannu da hanya ka sha hanys ko
Wallahi baffa ya aiki
Alhamdulilahi!to masha Allah
  Baffa dama gun ku nazo
To lafiya dai ko?
Baffa lafiys lou dama akan maganar aisha humaira ne
To bismillah
Baffa ina so cikin sati biyu daza su zo a yi kokari a yi bikin nan ta tare a can ina da bukatar ta q can.

Eh to muma munyi wannan tunanin amma se muka ce mu bari tukuna ta samu makaranta a can garin seta koma .
  Baffa ,abbi duk bazai zama wahala ba a gareni da ita yafi sauki a can in ta samu ai tana garin
  To shi kensn masdook zan yi wa da'ada da iyayen naku magana
To baffa Allah kara girma da arxiki
Amin amin!

**
Tsohuwa me ran karfe kin ci zamanin ki kina kuma cin na wasu!
Ta murmusa kawai.
Kin wani kashingada kin yi wani fresh me sirrin ne tsohuwa.
   Unbula ta masa
Yayi murmushi yana gyara zaman sa a kasan kilishin dakin
Da'ada ya kike ya gdan ?
Lafiya lou masdook ya aikin naga shekaran jiya muka rabu har ka dawo ?
Kawai hutawa nake da yau zan koma amma mama ta hsna wai se gobe ni ku nazo gani dama
  Tayi murmushin manya ta ce masdook lallai ka girma ko dai gun matar ka kazo ?
 Ya sosa keyar sa yana murmushin jindadi
Kai tsohuwar nsn da fassara kike
 Yoh ai abun ne yazo dani da kai zamanin mu daban bar gani na da hurhura a ka ina da sani tun farko
  Uhm lallai ins matar tawa?
Ai wannan ja'irar ban gants ba tunda tace min zata shiga gari gun amira nace ta tambayeka a waya taki ban kuma ganin ta ba ko tayi fushin ne tana dakin inono ko kuma tayi gun matar ismail.
To bara na duba ta.
Dakin inono din yaje suka gaisa rimi rimi ya tambayeta matarsa itama ta fada masa.

Gida ya koma gun mama tana jan carbi a hannun ta zaunawa yayi kan kujera dan ta karasa amma iya kaduwa ta gama ya gama kaduwa .
Tana gamawa ya tsuguno a gabsnta
 Mama kin san inda aisha take?
  Uhm tana kastina man.
 Mama mesa kika bsrta ta tafi
  Da kamal na hadasu ya kamata a ce yanzu sun dawo ma ko me ya tsaida su oho?.
Mama ni ban san fita wallahi
  Yau naji ikon Allah masdook me zan yi to?.
Mutum za a rike shi ne kamar marar yanci?
Mama ba hakq bane ban san fitar ta ne.
 To masdook yi hakuri ba za a kuma ba nayi laifi nayi iko da matar ka na daina.
Allah huci zuciyar ki mama kiyi hakuri ba haka nake nufi ba
Ya fice waje abunsa.