AISHA HUMAIRA Part 1



   *Aisha humaira*
     *Aisha humaira*
!!wai kina ina ne yar nan ina kiran ki kina jina amma kika min shiru ko se na shigo dakin?
  Zaki fito ko sena shigo!
  Bakin ta kamar ya hade da bango tsabar tsiri dan masifa
   Ke da'ada wai kin fiya takurawa mutum wallahi Allah
  Ta jefe ta da cokalin hannun ta
 Kaucewa ta yi hade da kyal- kyalar dariya ta dau bokiti tayi hanyar bangaren baffa idi tana yan wake-wake.
   Baffa na alwala a tsakar gida ya daka mata tsawa ke wai aisha humaira yaushe zaki nutsu ne ki shigo gida ba sallama se wake.
      Yi hakuri baffa na tuba
Kullum a haka kike ai dama kin tuba.
Sum sum ta shige cikin gidan
Inono na kan sallaya tana lazimi haba ta rike cike da mamaki a ranta tace wannan yarinyar da shakinyanci take
   Inono ina wuni
Kai ta gyada mata saboda lazimi ne a bakin ta.
  Inono ina fatima bintu?
  Daki ta nuna mata bokitin ta ajiye a tsakar falo ta yi cikin dakin da gudu fatima bintu na bacci taji an fado mata a ka
Ihu ta zunduma tsabar tsoro tana mikewa kuwa aisha humaira tasa mata dariya harda tsugunawa kasa
  Fad'ima bintu ta tsuguna ta gartsa masa cizo a kunnen ta tsalle ta daka tana ihu
 Inono ta shigo da sauri da carbi a hannun ta wallahi se kun fita daga gidan nan wallahi yanzun nan na rantse da girman Allah.

   Suka yi waje da gudu.
  Aiko suka ci karo da hamma yusuf ya tsaya tsabar takaici yana kallon su kullum ku rayuwar ku a gudu kuke da tsalle kamar wasu yan biri ko to maza maza ku yi ciki kusa hannun ku a sama.

  Narai narai da ido fadimatu tayi ta kasa motsi a gun ita ko aisha humaira tsaki tayi ta zumburo baki ta juya keya, mamaki ya kama shi ya rasa ma mezai ce musu tsawa ya daka musu kun tsaya kuna kallona ko sena make ku mara sa kirki marasa mutumci.
  
    Ni ruwa zan debo ma da'ada,fa!
Mariya ya kwalawa kira ta fito da sauri tana gani hamma
Dauko bokitin da'ada a dakin inono ki debo mata ruwa ki kai mata kice aisha humaira na sata aiki.
    Tom hamma yusuf.
Tusa keyar su yayi dakin inono yasa suka sa hannun su a sama.
Shi kuma ya zauna kan kujera yana kallon su duk wadda ta sauke ya rakwashe ta a kanta
  Se la'asar inono ta lallaba shi ya kyale su.

Suna fita suka shiga bangaren adda mardiya (matar yayansu ce) tana tuka tuwon alkama dan hamma idirisa yana son tuwon alkama.
  Suka zazzauna aa yan gidana se yanzu
Kede bari adda ai yau mun shiga wani hali
Da me fa?
Hamma yusuf mana
Au ai kun saba se kuyi tayi ai kun ki girma ai zan sa shi ya sa a saku a lalle.

   Suka yi kwal da ido a waje


Lalle kuma suka kyalkyale da dariya gaba dayan su harda tafawa suka yi shewa ahayee yerhh!!.
  Mardiya ta kama baki yan banza kun rika ai dama hamma din naku yana nan a daka.
  Da gudu suka kuma yin waje .
   Dakin da'ada suka shiga kuma zaman su keda wuya da'ada ta kama aisha humaira tana duka daldaldal
Ai tuni fadimatu tayi waje tana dariya da kyar aisha humaira ta kwace ta fyalle a guje
  Tayi dakin adda rabi tana kuka adda na daka ta juyo da sauri yaya?
Ba da'ada bace ba ta dake ni
 Kai aisha humaira kin fiya rashin ji wallahi kin fiya kiriniya har se kin kure an miki duka kike jindadi.
  Ta kyabe fuska ta juyo a hasale.
Cikin fada da bacin rai kamar zata make addan
 Addan tace kai ni kike ma wannan kallon.
Wallahi na kara miki dukan.
Ba saiki dake ni ba din in gani.
Tabdi jan tayi kan ta da sauri ta gudu wallahi sena hadaki da isuhu ya min maganin ki ya zane min jikinki tukuna zan ji dadi.

Gidan su amira ta je ta sameta cikin kayan makarantar islamiya zata wuce makaranta tama makara mama na mata fada
  Taga aisha humaira kamar an jefo ta.

 Mama ta kama kai shi kenan Allah ya kawo min ke se kuyi tayi ai amma wallahi se kunje makaranta yanzu in ba haka ba zan sa a kira min yusuf ya zane mun ku wallahi kun fitini kowa gwara ma wannan yaran ya yi ya dawo ko na samu sa'ida a gidan nan
  Amira ta ce nifa mama na shirya to maza jeki dauko kayan ki ku wuce makaranta
  Sum sum suka shirya suka wuce
  A hanya tace ke amira yaushe hamma zai dawo?
Ke har so kike ya dawo?
Eh man kinsan ina matukar san sa
 Tab wannan mugun?
Ke kul kar ki soma ki kuma ce masa mugu
  Hmm kya ji dashi ke kika sani
  Amma ai mugu ne hamma.
  Mintsinin ta tayi tayi kara suka sa dariya.
  Suna gama daukar karatu suka yi hanyar gida suna hira.
A kofar gida suka ga hamma yusuf amira tayi sunkui da kai ta gaid shi
Ya amsa da yar fara'a
Aisha humaira ta sa dariya harda kyakyatawa yusuf ya harareta tayi cikin gida ita kuma
 Amira ta tsaya suka dan gaisa da shi sannan ta tafi gida.

Zaunawa tayi a tsakar dakin da'ada tana kallon ta tana tsinta,to mutniyar ayi hakuri a yi wa da'ada ahuwa kin ji?
Ta zumburo mata bakin ta.
Haba yar lele tawan ki yi hakuri kar a ji kan mu a sa mana dariya.
Sannan ta juyo sai suka kuma sa dariya suna hira ta bata abinci taci.

   Ke yar nan dazi gidan su mutumin ki aka kawo mun waya muka gaisa da wannan yaron
  Wa kuma?
Masdook mana
Ta zabura ta mike da sauri haba hamma ne ya bugo amma ba a ban wayar ba.
To ba kina makaranta ba ?
Kash banji dadi ba mama bata kyautan ba to ya tambaye ni ko ?
Ina fa ya dai bugo mu gaisa ne kan me zai tambaye ki?
Ta zumbura mata bakin ta kai da'ada yana sane ai
 Ta kyabe baki sha kurumin ki ina ji dazu ana maganar za a kai kudin auran sa
Ta mike da sauri wa?
Masdook mana
Na shiga uku
Da'ada da gaske ko da wasa
Ta mata dakuwa kaniyar ki kina ji ko se ki shiga uku saboda auran shi
Da'ada ya za ayi haka ni bazan yarda ba kam wallahi tallahi se an warware
  Ke ni na ga ta kaina yau ni bintu dan ubanki zaki hana ne
 Ta zauna dabas tana kuka da'ada ke ma fa kin san tun ba yau ba ina san hamma kuma shi ne zaki bari a masa aure?
Da'ada ta kama bakinta na ga ta kaina kar ki sake a ji ki ma a gidan nan zaki hana aure ne ke yaushe kuka yi da shi yana sonki zai aure ki?

 Kafin ya koma man da muka hadu dashi a gidan su hajojo da daurin auren hamma isyaku.

Yaushe kuke magana dashi har da zaku yi soyayya  ba a sani ba ?
Da'ada a tambayi amira tasan komai ai
 Shi ne ze ci amanata ya ce wata zai aura
  Da'ada ta ce tabas bazai yi haka ba tunda ya miki alkawari se ya cika alkawarin nsn bs wadda zai aura sai ke
 Dadi ya kama aisha humaira ta yi bacci mai dadi ranar za a bata hamma masdook
Tunda da'ada tasa baki mayafi ta ja tayi gidan su amira tana kallo kuwa ta ce ke zo kiji.
Me zaki zo ki dameni a daran nan?
Ke nayi kwaba fa kuma bana tsoro amma ina fargabar hamma masdook sede ki zame min sheda kawai nake so.
 Me kika aikata?
Fada mata tayi tsalle amira tayi ta dire tace keda wa?ni amira wallahi baki isa ba kar ki soma sa ni a cikin haukan ki hamma masdook din zaki sa ya min tijara ba ban san anyi ba
 Shi kenan ai kar ki taimake ni nima sena ki taimakon ki hamma yusuf ysce yana sonki da zan miki hanya amma na fasa
  Riko ta tayi tsaya kawata zan miki
Ko kefa tayi wani murnushi me kayatarwa na mugunta ta gyara tsayuwarta suka tafa

Amma kin san akwai matsala ko idan hamma masdook ji wannan labarin
 Ke kin fiya tsoro ni wallahi akan shi ba abunda bazan yi ba kome ze mun sena aure shi wallahi sena aure shi.
Kallo ta bita dashi kawai tana jinjina karfin hali irin na aisha humaira .
  Komawarta gida keda wuya ta shiga dakin su amma bata samu da'ada ba sai ta zauna a kasan carpet tana jiran dawowar ta
 Bata wani jima ba ta dawo ta zauna kasan ita ma sannan cikin fara'a tace ke kwantar da hankalin ki a kan masdook baza kiyi kuka ba insha Allah kin same shi kin gama daga gun baffan ki nake yanzu nasa aka kira min shi baffan naki da abban masdook din na masu bayanin kudurina kuma ba wanda ya musa min a cikin su kamar yadda nayi tsammani tabbas muhammad ya cika dan halas me tarbiya ya maidani tamkar mahaifiyar sa ko dangin su na asali ban taba ce masa yi ba yaki yi ba tankar ni ce na kawo shi duniya.
  Komai aisha bata ce ba illa ranta fes take jin sa da wannan daddan labarin hamma masdook zai zamto nawa.
Da'ada waccan fa dazai aura?
Kwantar da hankalin ki ke kadai ce bai isa kawo wata ba .
 Dariya tayi na jindadin abunda ta fada ranar baccin dadi tayi.

Zaune yake kan kujera yana duba wasu takardu a kan tebur din sa tun kafin ya fara duba patients amma ran shi a bace yake ya rasa dalili kawai Allah Allah yake yi ya samu hutu ya koma gida.

Wayar shi ya dauka ganin tana ringing kuma sunan abban shi ya gani a kai an rubuta
*abbu* dauka yayi da sauri ya ce salamu alaikum,
 Wa'alaikum salam
Ina kwana *abbu* ina gajiya an tashi lafiya
  Lafiya lou ina son ganin ka masdook
Abbu yaushe zan zo
Ko gobe ma kazo
To abbu insha Allah zan ajiye komai nazo
To ina sauraron ka.
Ajiye wayar yayi amma fa gaban shi na faduwa abbu be taba masa irin wannan kiran gaggawar ba in ba yau ba wayar ya dauka ya kira yusuf
 Hello masdook
Yusuf fada min akwai abunda yake faruwa a nan gida ne?
Aa me ka gani?
Kawai naji a jikina akwai abunda yake faruwa nan gida
Aa feel free har yanzu banji wani abu ba kila sai ka zo din se muga
To ina fata hakan ne
Amin
Amma wai har yanzu bska dawo ba.
 Wallahi kuwa kila mu koma tare da wayanan yaran nake son maidawa boarding baffa nake lallabawa ina gamawa zan kaisu munjibir a huta kila su ma su nutsu.
 Haka ne amma wayan na yara ?
Da aisha da amira da fadima da mariya da kulthum
  Gaskiya kam da ka kyauta
 Anyway sai anjima gobe zan shigo insha Allah
Allah baka iko amin.


Baffa na zaune a falo shi da abbu suna tattaunawa da matan su kan batun da da'ada tazo musu dashi jiya da daddare
Mama tace to me kuke jira na yin shawara?ai bai kamata ta bada umarni ba ace se anyi shawara inji inono
 Ba wai shawara muke nema ba kawai ina ganin kamar masdook zai bamu matsala ban yarda da zancen aisha ba sam sam.

  Ajiyar zuciya inono tayi tace nima dai kawai naji ne amma masdook yaushe zai tsaya soyayya da aisha fitinaniya kunsan yadda basa shiri da ita
 Amma ita aisha tana matukar son sa kuma kunsan aisha humaira ita ce da'ada kuma da'ada ita ce humaira tun bayan mutuwar adda aisha(babar aisha) ta dauko ta ta maidata ta tamkar ita ta haifeta
  Ni bana jin masdook zai ketare maganar mu ya ki ba an riga an zama daya amma gaskiya sai aisha tayi karatu in yaso yanzu a daura auran kamar yadda ta bukata tunda sun ci jarabawar shiga ajin gaba dama yusuf ya zo da maganar boarding meze hana su tafi can ta kara girma da wayo tunda da akwai wadda yake so baza a cuce shi ba sai ya aureta
  Hmm kai ma dai abbu baka ji me da'ada tace ba bata son a mata kishiya.
  Zan lallabata na mata magana har ta sauko amma ai aisha humaira bazata iya daukar nauyin masdook ba.
Haka ne.
Sallamar masdook suka ji a bakin kofar dakin amsawa suka yi ya shigo ya tsuguna suka gaisa gaba daya abbu da baffa suka tambaye shi aiki yace alhamdulilahi.
Abbu yace masdook waye ni a gun ka?
Abbu meya kawo wannan tambayar kuma
Ka bsni amsa
Kai mahaifina ne.
Alhamdulilah da'ada fa?
Bayan ku sai ita
Yayi kyau
To ni a matsayina na mahaifin ka na yanke shawarar daura auren ka da aisha humaira
Da sauri ya dago kan sa gaban shi ya buga ya dinga kallon abbu da sauran mutanen gurin gumi ya tafaso masa.
  Umarni nake baka ba shawarar ka nake nema ba ko amincewar ka ba.
  Abbu ban isa na ki bin umarnin ka ba kuma zan bi ko da banda komai amma abbu nayi wa zainab alkawarin aure kuma yanzu ys za ayi aisha yarinya ce bata da wayan daxata iya dani
   Baffa yace mun sani kuma mun yanke shawarar za a hada da auran ka da wadda kake so kuma aisha zata koma makaranta daga baya ta kuma wayo se ku tare amma za a baka wadda kake so.
   Mama tace wannan hukuncij da'ada ne ba namu ba kuma dole a bi maganarta
  Insha Allah mama bazan ki ba amma aisha humairan ta yarda?
  Kaje kuyi magana da da'ada zuwa jibi zamu san yarda zamu yi
Amsawa yayi ya fita jikin shi ba laka lakwas ba dadi
  Dakin da'ada ya shiga jikin sa a sanyaye ya tarar da aisha da fadima da amira suna yar carafke a tsakar gidan wani irin abu ya tokare masa makogwaro tsabar takaici ya wuce cikun dakin suna gaida shi ba wadda ya amsa aisha murna ya cikata ta mike ta yi waje debo ruwa tayi wanka da kwalliya hamma masdook yazo.
A zaune ya samu da'ada tana jan carbi tana ganin shi ta washe baki tsabar dadin ganin shi zaunawa yayi ya kskalo murmushin jindadi ya gaida ta cikin filanci dan yawance haka suke magana shi da ita.


Masdook na waje na ka gama min komai tunda kake son abar da nake matukar so kaf duniyar nan ina godewa Allah da ya nuna min wannsn ranar masdook dame zan saka maka ?
Bafan ma ita aishan ta fada min gaskiys cewa kuna soyayya ba ai da ka manta da ita ka auri wata can bare
  Ya dago da kan sa yana kallon ta cikin msmaki ya nanata *soyayya*ni da aisha humaira yaushe?
Da'ada waya fada miki muna soyayya da ita?
Ita man ta fada min kayi mata alkawarin aure tun bikin isyaka ko ka msnta saboda wadda kake so?
Shiru yayi tsabar takaici koda yaji tayaya da'ada zata hada shi da yar yarinyar da ya bsma shekaru wadda bayan gaisuwa ba abunda yake hada shi  da ita ace zasu yi aure.
  Tabbas badan ysna ganin girma da darajar da'ada ba da tuni ya karya wannan shirin
 Amma humaira zata gane kurenta badai shi zsta aura ba harta yi girman dazata hada masa tugu tabdi jam.
Da'ada Allah kara girma ya sanya alheri ni zan je gun su yusuf
To Allah maka albarka amin.

 Ai ko wata atanpa ta saka yello da ratsin pink a jiki ta daura zanin ta da riga yar firit ta caba uwar hoda da janbaki a fuska ta tsaya jirsn sa ya fito ai yana ganin ta wani malolo ya tsaya masa a makogwaro ya dalla mata harara a fuska sannan ya shiga dakin su ta bishi duk da a tsorace take dashi
  Wani kallo daya buga mata seda hantsr cikin ta ya kada ta soma kyarma
 Ni kika je kika ma sharri ko nida ke muke soyayya ko?
Dan uban ki ina wasa dake ni zaki ma karya ai ni kike son aura ko zaki aure ni amma zaki yi dana sanin aurena zaki san cewa ni ba saanki bane ba zaki dandanani zan baki mamaki zaki yi danasanin sanin *Masdook Muhammad dikko*
Shiru tayi ya nunata da yatsa
 Ta zumburo bski oho dai nidai ina sonka kuma sena aureka sede ka kashe ni na yarda in na matu a ce matsr masdook ce da ace aisha humaira kawai kums ksima dole ka soni yadda nake son ka
Mamaki ya ksma shi haka kika ce ko?
To mu zuba nida ke ya fice waje abunsa yana mamakin karfin hali irin na aisha humaira.
Ta soma hararar hanyar da ya bi ya fita.

  A waje yaga su nas da yusuf ran shi duk a bace yake ya zauna kawai dirshan ya rasa meke masa dadi
 Aa likitan birni daga ina kuma waya taba ka?
Nas kaidai bari kaina ya dau caji
Aa likita da kan sa ai se a sha panadol
 Mtsw dadina da kai kennan ka fiya shiririta.
  Ni'imatullahi ya katse su danuwa meke faruwa?
Wai ni yarinyar nan zata ma planning?
Wacca yarinya?
Aisha humaira mana
Meta yi inji yusif ya fada cikin xakuwa shi sa nace zan kaisu boarding
  Mtsw ai in wannsn ne da sauki
Wai zuwa tayi ta fadawa da'ada cewa ni da ita muna soyayya na mata alkawsrin aure
  Ita aisha humaira din
Ita man
Kiran da abbu ya min kenan sun yanke shawarar aura min ita saboda maganar da'ada dole a bita
Tabdi lallai humaira ta hsda ma zafi zainab din fa?
Sai sun duba sun yi shawara.
Lallai an kassara ka an gama da kai me wata aishs humaira zata ms bands tsiwa da rashin kunya da kinji da jawo magana inji yusuf
 Ai wai makaranta zaka kaisu ksn nsn ta kuma wayo da hankali
  To Allah sa haksn shi yafi alkairi
Amin suka fada banda uban gayyar.

   Wallahi sai hamma masdook ya aureni ko kallon shi xan dings yi kullum yana dukana ko namsn jikina zai dinga yanka yana ci sai ya aureni
  Harda hawayen ta
(Son maso wani)
Ta share kukan ta ita knta ta rasa yadda take mugun son sa bayan tasan ita dashi akwai banbamci

_ummi_ _hambali_ _ina_ _mika_ _gaisuwata_ _gareki_ _da_ _fatan_ _kina_ _lafiya_.


*zaunawa tayi jugum yau duk hayaniyar aisha humaira shiru kake ji har da'ada da kawayen ta na jajen ta a waje
  Da'ada ta shiga dakin da aisha take ta dafata yar nan yau ya na ganki shiru?. Ana ta cigiyar ki cikin gida.
  Hmm ba komai da'ada kawai dai na gaji ne yau din to ko lafiya?
Ta fara tatabata ko bata da lafiya kuma taji jikin ta ba komai alamar rashin jindadi kawai dai garin ne.
Fita tayi ta barta a dakin.
  Amira ta shigo ita da fadima aminan ta suka zauna gefen ta sannan ta saki ajiyar zuciya kuma hawaye suka zubo mata a fuska daya na bin daya zur zur.
Fadima bintu ta rungumeta a kirji ke menene?
Fadima baya sona baya kaunata
Waye baya sonki?
Cikin sarkewar murya da shassheka ta ce hamma masdook mana
  Amira ta ce aa fa aisha yana son ki man
Aa ta fada tana jijjiga kan ta cikin kuka ni ina son sa wallahi shi ma kuma seya soni
  Anji din amma kema sai kin dage munyi karatu mun fara zuwa makaranta ke ba kya so ki waye tayaya dan birni dashi yasan duniya yaga wayayyu zaki ce wai ya soki a haka muna wasan yara har yanzu?
Hmm ta kyabe fuska inko dan wayewa ce baya sona zan je makaranta kuma zan waye nima sannan na ja masa ajina.
  Fadima ta gyara zaman ta tana dauke kan ta kenan yanzu a fasa auran ko ?
Ta harareta hade da rankwashin ta muguwa bakin yi ya saei danyan kashi kuma se anyi sede ki mutu.
  Aa meye zafi yi hakuri mutuniyar ni na isa in shiga tsakani?
Kin ma isa ?
Suka sa dariya.
 Dazu hamma yusuf yace gobe zashi makarantar yaga abunda zamu bukata a can

Hmm wai da gaske boarding din zamu je?
Eh wacce su husnan gidan baba kabiru suke zuwa munjibir.

Tabdi kice zamu hadu da su ko
Dama ina binta bashin duka goma na wannan wasan da muka yi a soron gidan su mudi ihu suka saka shegeyia haka nake so ai
  *(Kuji fa yanzu take zancen wayewa se zancan ramuwa)*

✨✨✨✨✨✨✨
Yusuf wallahi Allah ina matukar bakin cikin wannan alamarin ni ina zan iya da aisha humaira ta fiya fitina da neman magana dazu fa yar carabke na tarar suna yi kamar ni ni wai ni masdook in auri yarinya yar karama
To ya zaka yi masdook haka Allah ya rubuta so ne kuma Allah na dorawa kowa a kan sa.
Kayi hakuri kaida ka samu ma za a baka wadda kake so


Mtsw guy barni dan Allah ku taku me kyau ce kaga wannan aishan se a hankali ai ina jinjina zamana da ita kuma sarai nasan halin ta
  Hmm masdook kenan zaman duniya se hakuri rayuwa tayi tsada ka samu mai son ka ma ai ka godewa Allah wanda ba a son sa fa yayi yaya? Kawai kaja ta a jiki ka koya wa kan ka how to...
Hmm kai yusuf haka ma zaka ce min dawa zan yi rayuwar?wallahi da zuciya1 nake fada maka bana son yarinyar.
 Shiru yusuf ya masa to meze kuma ce masa?
Babu inji khairat.

Wasa wasa kwanan shi hudu a dikko ya koma bakin aiki sa domin baffa da abbu sun sa wata hudu zaa daura auran kuma satin sama zasu fara makaranta ta sakandari a kano munjibir.

   Amina zaune kan kujera tana kallon masdook wanda gaba daya hankalin ta na kan shi hankalin ta a tashe yake da jin labarin da ya kawo mata tsabar takaici kuma kukan yaki zuwa dan bakin hali.
  Ta kalle shi ya yi gum da bakin shi tun bayan fada mata sakon da yayi kuma a gunta sabo wai zai auri wata watan ma karamar yarinya kafin ita itan ma se an yi shawara da danginsa saboda ga me bakin jini mara gata da dangi ita bata ce seta duba ba sai su zasu ce se sun duba
Masdook kayi shiru kuma .
 Zainab mezan kuma ce miki magana na gunki ai
Haka ma zaka ce?
Seda komai yazo mana karshe za ka zo min da wannan labarin marar dadin ji da sauraro a kunne ni bazan iya hada zaman aure da wata ba dan mahaifiyata ma ita kadai ce se ni a kaina za a fara?
To zainab ya kike so nayi ne da rayuwata can ba dadi nan ba dadi kinsan dai ina matukar kaunar ki...
Ya isa ta daga masa hannun ta ya isa kana kaunata ko
Lah shakka
To ka bijire ma iyayen ka ni kawai ka aureni.
Ya mike a fusace in bijire musu saboda ke ?
Ai ina tunanin mun zama daya
 Seya zama me?
Se ya xama na fisu yanzu kamar ya wanke ta da mari haka yaji takaici ya ishe shi.
 Zainab yau kin nuna min cewa ba kya sona
Bana son ka fa kace?
Tabbas duk wanda zai hadani da iyayena makiyina ne
Makiyin ka kenan ni makiyar ka ce?
Sossai ma tunda ba kya son iyayena
Masdook gwara da Allah yanuna min halinka haka zan shiga dangin ka kana nuna sun fini
 Look zainab ya isa is over kiyi naki waje gwara da kika nunan naki rashin tarbiyar tun kafin muyi nisa.
Yq kada kai yayi waje daga gidan
Msmaki ya cika zainab soyayyar shekar biyar ta tashi a mintuna kalilan saboda banzar muhawara marar tushe tayaya iyayen sa zasu fini a wajan sa?
*(Khairi nace tayaya zaki raba da da mahaifi kice budurwa tafi su)*


Zuciyar sa kamar ta fito waje haka ya ke ji Allah ne kadai yasan irin wahalr da zuciyar sa take yi da kyar ya karasa gidan shi zaunawa yayi da kyar ya zauna a kan kujera yana jin jikin sa na rawa kamar mazari
Daga bisani ya dauko ruwan sanyi ya kwara a kansa sannan yaji dadi.

 Wanka yayi ya sauya kaya zuwa marasa nauyi ya kwanta kan gado yana jin wayar sa na ringing amma yayi biris da ita ya dada gyara kwanciyarsa ma daga karshe yasa ta a flight mode .

Gaba daya a rikice suke ba suyi tunanin cewa haka zata kasance ba kuma sai kuka musamman ma da'ada da aisha da kyar aka lallabasu suka rabu ita kuka ita kuka .
  Haka suka tafi makarantar
 Nace da alheri Allah sa suyi karatun.
 **************
Mama ce ta kira numbar din dan nata tilo guda daya yana aiki yaga kiran ya dauka da sauri ys rusuna kamar tsna gurin saboda girmsmata da yake yi
 Babana wai se yaushe zaka taho ne?
Ya sosa kan sa yana muzurai mama zan zo.
Yaushe bana son abbin ka ya fara tunkarar ka tun fa da aka sanar da kai maganar baka kuma leqowa ba fa kuma lokaci ya gabata jibi zaa je masu visiting ya kamata mu sameka a can ko kuwa.
Mama ayi hakuri zan duba kin san aikin namu
Babana gobe fa lahadi
Ai sai yayi shiru mama zata daure shi
Kaga kafi kusa dasu ka daure ka leqa .
Insha Allah mama
Allah bada iko
Amin.

   Sumar kansa ya shafa ya runtse idanun sa.
     Kofar aka bude aka shigo
Ya juyo da sauri yaga waye
Aa nas sannu da isowa
Yauwa man
Nagan ka wani iri lafiya dai ko?
   Alhamdulilahi gajiya kawai.
Ai dole naje gidan ai a kulle nasan nsn kayo
   Wallahi kam nan suka fara hira a tsakanin su ta abokai ta yan'uwa.

Komai an riga da an kimtsa gaba daya sun kagu suma suga yan'matan nasu da aka kwana biyu ba a hadu ba
Yusuf ys ma motar shi full tank
Da'ada,baffa,mardiya,abbi,mama,inono dasu za ayi tafiyar.
Nas,da ni'imatullahi da adda munnaya da adda munawara suna mota daya lallai yan gata ne yan matan.

Ke kike wani zumudi nameye ne da zaki damu kan ki
Dallsh can da'ada ta fa zasu zo yau ya bazan ji dadi ba mun kwan biyu bamu hadu bafa in ga yadda ta koma ko waye yake debo mata ruwa yanzu kuma oho
  Yar banza kin girma fa suka sa dariya
Fadima tace to Allah sa mutumin naki yazo
  Ke muguwa kar ki damu xai zo dan naji a jikina surely zai zo kuma he  ve to
Suka kalli juna su uku suka sa dariya gaba dayan su
ita kuma ta kulle ta yi musu harara.

Bayan tafiya me dan nisa da gajiya suka iso garin na munjibir tunda ta ungogo suka bi suka kauyuka guda hudu hska yan kanana sannan suka isa garin na munjibir sannan suka shiga harabar makarantar.

Idanun aisha humaira kawai neman abunda take so take amma bata gan shi ba karasawa suka yi ta rungume da'ada da karfi tasa kuka kuma aka tsaya kallon su adda mardiya tace ja'ira ya makarantar ina fata an ladabtar min daku?
Hararta tayi ta wutsiyar idan ta 
Ta ce ina ba a fara ladabtar dake ba tukun
adda ni zamu yi fada fa.

Amira taja ta gefe mrs.overconfidence ina mutmin naki ?
   Ban sani ba ki kwantar da hankalin ki zai zo kuma zaki fada.
  Hmm maji ma gani ai
Tana tsaye kawai taji gabanta ya fadi dum wani murmushi tayi me kyatarwa
Wallahi yaxo
Ai na fada miki se yaxo
Naji a jikina zai zo juyawa suka yi lokacin ya danno kan sa cikin makarantar ya fito daga cikin motar sa parado ya ajiye kafafun sa da takalmin sa me tsada shaddar jikin sa har maiko take yi ga hular nan ta zauna ta amshe shi abun se wanda ya gani fuskar nsn ba walwala amma kamar yana murmushi haka ake gani tsugunawa yayi ya gaida su baffa sannn ya koma gefe ya tsaya yayi gum da bakin sa ya sa hannu a habar sa yana kallon farfajiyar makarantar.
   Tsaye tayi a kan sa tana masa kallo ta masa kuri da idonta.
  Be ma ankare ba har wani lilo take yi na shaukin son da take masa.
  Jikin sa ya basa cewa ana kallonsa.
Ya dago sexy eyes din sa yana kallon ta wani abu ya tsaya masa ya hasala kamar ya doke ta
  Ke me haka zaki min tsaye kina kallo na kamar mayya.
  Hararsa tayi eh din mayyar kace man kuma ai kyau ka mun Allah hamma kayi kyau ka daina kwalliya haka da yawa ana kallon ka.
  Kan sa ya dafa na shiga uku ya fada a ransa wannan yarinyar ko mara kunya
Baki da kunya zaki min tsaye gasu baffa a gun
Ta yamutsa fuska ta matso daf dashi
Keee aisha
Wani dadi taji ya kira sunan ta
Me haka kike yi ?
Soyayya man
Wai dan ina son ka kake min rashin arxuki ko hamma
Ya hade gida kinga mama tasa nazo kuma nazo kin ganni ni zan koma se wata rana ki daina expecting cewa ni masdook zan soki
Ya juya daga gurin ya barta siraran hawaye suka zubo mata a ranta tace
*SO*


Matsa min mara kunya kawai banda tsaurin ido da rainin hankali ki kalle ni kice min wai ni kike so saboda baki da wayo.
         To so karya ne?
Yayi kamar ya mare ta ni kike fadama haka?
Ta zumburo masa bakin ta tayi tsaki ta juya zaka sani ai in dai nice ban daina son ka har abada kai har gaban abada.
 Tsabar takaici ma magana ya kasa yi ya bita da kallo tayi gaba abunta .

Haka suka gama hirar su sannan suka juya
Masdook yace su bishi gidan shi gobe sa koma dan yamma tayi da kyar baffa ya yarda.
Suka koma.

A gida mama ta kira masdook ta zaunar dashi a kasa
  Kana jina masdook dan Allah kar ka bawa abbi kunya a cikin mutane kasan yadda yake son da'ada ita kuma da'ada humaira ita ce ita yadda take mutukar son ta kuma abbin ka baya son bacin ran da'ada tankar uwar sa haka ya dauketa.

Insha Allah mama zan bi dukkan abunda abbi ke so nima ai ina son da'ada sossai ko bana son abu zan so shi saboda ita
  Jeka Allah maka albarka.
_amin_

Dakin sa ya koma ya kwanta kan gado yana nazari in ba dole ba ta ya zai hada kan sa da humaira?
Basu hadu ta ko ina ba bata da girman da zai rude shi bata da class shi in ba rashin class ba taya mace zata zubda ajin ta tace tana son sa ?
Mtse an gama dani wallahi ita kuma waccan zainab ni zata gayawa magana ta ina zata fi iyayena?
Babu wadda ta isa a doron kasa ya bata mahimmanci fiye da iyayen sa babu ita mata matsala ne a ko ina kullum da tsarabar da suke zuwa dashi.

  Ranar baccin farin ciki tayi aisha humaira taga abun kaunarta taga sahibinta masdook the handsome zan yi karatu saboda shi zan yi komai sabod shi xan nuna masa nima macece me aji me wayewa
  Hamma masdook ina son ka ina sonka ta fada tana rungume fillo din ta.

Tun daga kan nan ta kama karatu ba kakautawa duk wani rawar kai ta rage ta rage yin duk wani wasan banza
    Har suka kare zangon wannan karatun suna shirin komawa gida daidai lokacin daurin auren su ya gabato se doki take amma a wani irin tsari.

Komawar su gida keda wuya aka fara nan nan dasu a gidan
Kowa yayi murnar ganin su a gida yadda suka samu nutsuwa a tare dasu ba karamin mamaki ya bawa su inono ba.

  Kwana uku a tsakani da dawowar su aka fara maganar auran masdook da humaira inda baffa ya tara jama'a maza kawai bayab sallar juma'a karfe biyu da rabi aka daura auran
Masdook da aisha humaira kan sadaki dubu ashirin sabida albarkar ake nema .

 Aisha humaira da jin wannan dadadan albishir ta shige uwar daka ta kwanta daga bisani tayi alwala tayi sallah raka'a biyu dan godewa Allah daya cika mata burin ta bazata taba manta wannan rana ba ranar juma'a a watan janairu aka daura auran ta da habibin ta abin alfaharin ta
  Ta ys zata manta wannan rana?
Babu kam inji aminiya ummu arif.

Masdook dama ana daura auran befi hour daya a garin ba ya koma ksno da abbi ya tambayi dalili yace saboda aiki ba a wani bashi hutu ba ya fada ne kawai dan ya nesanta kansa kar a ga rashin farin cikin sa da wannan auran.

Hajiya da'ada ta dinga raba alawa da goron biki na murnar auran jikokin ta guda biyu.