BUTULCI Page 16-20
Tunda yayi sallar asuba bai koma asibitin ba dan duk ynxu asibitin ya fita a kansa, sam baya jin dadin irin kallon da Alia take mai gashi bai son takurata dan ya lura in yana dakin a takure take shiyasa yayi zamansa a masallacin sai da ya ga garin ya yi hske ya fito ya shige cikin asibitin, bai yi mamakin ganinsu umma ba dan ya san da zuwansu, gaishesu yayi sannan shima ya ja kujera ya zauna, Dr Zakir ne ya shigo yayi murnan ganinsu sosai bayan sun gaisa ya dubi Alia yace Mrs Sadiq ynxu kin samu full house sai dadi kike ji ko, murmushi kawai tayi a zuciyanta kuwa tana tunanin mehsa ake yawan hadata da sadiq dinnan, bayan ya dan dubata ya ce "kina iya tashi ko? Kai ta gyada mai, ya dubi su Abba yace toh i will luv to c u ol in ma office any moment from now wen u r ol ready u mt me in ma office Abba yace ynxu ma zamu iya tafia ai ko ya fada yana kallonsu Alia, Alia ce tace Abba i nid to use d toilet kuma ina so inyi wanka ta fada yayinda take kokarin tashi, wani jirine ya dibeta tayi baya kaman zata fadi Sadiq da ke kusa da ita yayi saurin rikota, Dr Zakir yace I dnt tink u r fit to b wlkn alone dole a na biye da ita duk inda zata, zame jikinta tayi daga jikin sadiq ta je ta ce toh umma kaini wlhy a matse nake ta fada kaman mai shirin kuka, Ummanta ne ta rikota ta zaunar da ita tace y not mijinki ya kaiki ta fada tana kallon sadiq,dagowa tayi ta kallesa sannan ta dubi ummanta, kai ta gyada mata yes Darling daughter yayanki sadiq is now ur husband n u shld fil proud n lucky to hv him as ur husband, gani tayi hawaye ya fara bin kuncinta, riko hannunta tayi tace " whats wrong DD? Cikin kuka tace "I dnt even knw him mum n evryone kips saying hs ma husbnd ta kareshe cikin kuka, dagowa umma tayi ta dubi sadiq sannan ta dubi Dr Zakir tace " Dr meh ya samu yata? Ajiyar zucia Dr Zakir yayi sannan yace "Dama abunda yasa nayi kiranku zuwa office ina kenan so i wl liv u now in kun gama dn we dscuss, yana fita Abba ya bi bayan Dr Sadiq ma ya juya zai fita ta tsaida shi, a hankali ya tako ya zauna kujeran da ke fuskantar Alia, Umma ta riko hannunta tace "DD u trust me dnt u? kai ta kada, ummarta ta cigaba da cewa toh in kin yarda da mu kin san cewa baza mu taba yin abunda zai cuceki ba, dis ta nuno Sadiq is ur husband I knw dia is alot of tins going on n alot of explanation dt nid to b made but for now u hv to trust us n trust him dtz y nake cewa ki tashi ynxu ya tayaki shiryawa ni znje wajen Abbanki in kun gama sai ku samemu.
Tunda umma ta bar dakin Alia bata bar zubar da hawaye ba towel sadiq ya dauko ya aje mata sannan ya wuce dan hada mata ruwan wanka,kafin ya fito har ya ta cire kayanta ta lullube cikin mayafinta batareda ya kalleta ba yace muje na aje miki ruwan yi tayi kaman bata jisa ba sannan ta tashi tana dafa bango,ji tayi ya dagata cak ya kaita bn dakin sannan ya fara kokarin cire mata mayafin da yake knta ganin hawaye na bin kuncinta ya sa shi juyawa yace in kin gama ki mun magana sannan ya fice.
Sai da ta tabbatar ya fice sannan tayi wankanta,kasa fitowa tayi dan ta kasa koda daga kafanta daga inda take,tafi mintu uku a tsaye ji tayi an bude kofan tayi saurin gyara mayafin jikinta,kallo daya kawai sadiq ya mata sannan ya karaso toilet in ya dagata cak,akan gadonta ya ajeta ya dauko kayanta ya aje mata sannan ya koma toilet in dan gyarawa, cikin sauri ta sa gown da ya aje mata tana daure kanta ya fito batareda ya kalleta ba yace mujeko, mayafinta ta yafa sannan suka fice tana biye da shi a baya
Gaban Dr Zakir suka tarar da su umma alama hr ya fara musu bayani,suma suka nemi waje suka zauna, a hankali Dr ya fara bayani kamar haka " sir from d luk of tins ur daughter is suffering from memory loss though not ol bcs she was able to remember who u r so we cnt say she've lost ol her memory but i wil like to knw d cause of her accident,shiru sukayi suna kallon juna sannan Abba ya dubi umman Alia yace dauketa ku dan fita,sai da suka fita sannan Abba yace da sadiq ya bawa Dr zakir labarin abunda ya faru,jinjina wa al'amarin Dr Zakir yayi tareda tausayawa Alia ya dubi Sadiq yace Zan iya samun pic nasu a waje daya su uku,wayanta da ke wajensa ya ciro ya duba pic da sukayi ran attestation nasu,wanda suka dauka tareda Hamida da Dr Grema ya miko wa Dr bayan ya duba pic in ya ce sadiq ya shigo da su, gaban Dr suka sake zama ya miko wa Alia wayarta yace duba kiga ko kin sansu, ta jima tana kallon hoton sannan ta dago tace i dnt knw dem shiru sukayi gaba daya sannan Dr yace ki sake dubawa,sake kallon pic in tayi sannan tace i dnt knw dem, umma ne ta ce Alia ki duba da kyau dis is ur bstfrnd n ur fiance u have to remember them,dole ma ki tunasu ko dan.............ganin hawaye na bin kuncinta ya sa umma yin shiru itama ta juya tana sharan kwalla.
A hankali Dr ya fara musu bayani " ur excellency ur daughter is suffering from wat we call Emotional Trauma memory loss which is a natural
survival skill and defense mechanism humans
develop to protect themselves from
psychological damage. Violence, sexual abuse
and other emotionally traumatic events can lead
to dissociative amnesia, which helps a person
cope by allowing them to temporarily forget
details of the event. A person will often suppress
memories of a traumatic event until they are
ready to handle them, which may never occur, bt we hope zata yi regaining dt prt of her memory but ryt now am nt sure she is ready to handle it, abunda ya sameta ya jijjigata sosai shiyasa ta zabi boye wannan incident kuma ta mnta da duk wnda yake wajen lokacin da abun ya faru but she myt remember but dia is also high chances na cewa bazata tuna ba but fatan mu ta tuna kodan mijinta but let it occur naturally kr kuyi forcing nata akan sai ta tuna,in due tym zn sallameku but zata na zuwa follow up.
godia sukayi wa Dr zakir sannan suka fice dan komawa dakin da aka rike Alia, Bayan Sati daya Dr Zakir ya sallamesu, hotel Abba ya kama musu dan su kwana kafin su wuce zuwa Gida Nigeria. Washe gari duk suka dunguma zuwa airport inda suke jiran flight nasu ,can gefe na hango hajia na'eema da anty fiddy suna zaune alamun suma jira suke,hannu ta sa a jakanta ta ciro papern da nurse ta bata lst zuwansu asibitin ta bude ta jima tana nazarin papern sannan ta mikowa fiddy tace " fiddy duba kiga wannan da ya dan bugeni ne ya bar sako na bn hakuri, amma naga rubutunsa na mun kama da na...... Sadiq fiddy ta karasa tace sosai rubutun yayi kama da nasa amma umma meh zai kawo shi har nan mutumin da yau kusan shekara nawa ba'a san ko yana raye ko a'a ba kawai dai rubutun ne yazo daya amma wannan ba rubutun sadiq bane, krbe takaddan hajia na'eema tayi ta linke ta mayar purse nata sannan tace sadiq ina na raye fiddy ina ji a jikina yana raye kuma kullum ina ji yana zuwa kusa dani, mu dai mu dage da addu'a.
Karfe takwas na yamma su Alia suka shiga gida kowa yayi side nasa, ba wanda ya san da zuwansu dan Abbanta baison taro, bayan duk sun kimtsa cook ya gabatar musu abinci suka ci sukayi nak sannan suka koma falo, Abbane yayi gyaran murya yace " nasan duk kun gaji sabida haka duk muje mu kwanta zuwa gobe sai in gana da dukkanku, umma ne ta raka Alia hr dakinta Sadiq ma ya tashi tareda ma Abba sallama,tsaida shi abba yayi tareda miko masa wani envelope yace wannan takaddun gidanku ne da mukallinsa da na motocinku sai ka rike a wajenka zuwa randa zaku koma ciki godia yayi wa abba sannan ya sake masa sai da safe sannan ya fice, wanka yayi da ya koma dakinsa sannan ya haye gado yana tunanin ynda zai rayu da wanda zuciyarsa ke matukar so yayinda ita kuwa kwakwalwarta ta mnta da shi, kwarai Allah ya amshi addu'arsa da ya tashi kafadunta amma baijin rayuwarsu zai tafi ynda ya jima yana tsarawa amma duk da haka yana farin cikin kasancewa da ita a matsayin mijinta da wannan tunani bacci ya daukesa inda hr yayi mafarki suna rayuwarsu cikin jin dadi da son juna kuma ta haifa mai yara kyawawa masu kama da ita.
Can bangaren su Hajia na'eema ma yamma lis suka shigo gida,bata ma shaidawa sarki zuwansu ba,yana zaune kawai ya ganta ta shigo side nasa hannunta rikeda plate na apple, gyara zamansa yayi yana kallonta hr tazo ta zube gabansa sannan ta gaishesa ya amsa fuskarsa cike da murnan ganinta yace "Ranki shi dade irin wannan zuwa ba ko sanarwa kuma hr kin kama aiki, murmushi kawai tayi irin tasu ta mnyan mata sannan tace Ranka shi dade zuwan ne yazo mana wani iri kuma nasan da na fada ma zaka ce zaka br jama'a kaje jiranmu kaga in anyi haka kuma an shiga hakkinsu,kada kai yayi yana jinjina maganarta yayinda yake jin sonta na dada ratsa shi, shi yasa a kullum yafi jinta a ransa dan iya tsara magana nata da sanin yakamata da kuma kare hakkin wayanda ke kasa da ita ga uwa uba iya kula da shi, hannunta ya riko yace " da fatan wannan karon chk up ba matsala, ba matsala ranka shi dade ta basa ansa sai dai ya samun lokaci mai tsawo kafun in koma kuma insha Allah daga shi ba sai na sake zuwa ba,toh Alhamdulillah cewar mijin nata sannan ta dauki apple ta fara yanka mai yana ci suna yar hiransu yana gaya mata yanda yayi kewarta, Hajia Maryam ce ta shigo, ba karamin faduwar gaba taji ba ganin Hajia na'eema zaune gaban sarki da kyar ta iya karasawa tace "yaya sannu da zuwa, saukar yaushe, sarki ne ya tayata amsa mata tace ai yar taki zuwan bazata ta mana sai ganinsu kawai mukayi, hajia mryam tace ai yaya da kin kira kin gaya mana ko dan wani abu nasa a hada muku, hajia na'eema tace wlhy bakomai bnson wahalar da kowane tunda mun sameku lafia ma Alhamdulillah, sarki ya dubi hajia maryam yace ya su Ramatun dan ta shirga mai karyan zata duba yarta alhalin kuwa inda taje daban, cikin i'i'na tace lafiansu lau suna ma gaisuwa, cikin yanayi na nuna gajia ta ce ranka shi dade amun izini znje in kwanta dan a gaje nake, zaki iya tafia ya bata amsa sannan ta dubi hajia na'eema ta ce yaya ni zan shiga ciki a huta gajia.
Tana shiga dakinta ta sa key ta zauna bakin gadonta ta hau rusa kuka, ita kadai ta san wahalan da ta sha a tafiyan da tayi yau dan wannan karon da knta taje amso maganin da take tunanin sawa sarki a apple,sake duba kafarta tayi tana ganin ciwon da taji wajen haye dutsen da tayi ga uwa uba kudin da ta kashe wajen anso maganin gashi ko ina ba a je ba Hajia na'eema ta zo, ita kam bata da sa'a duk lokacin da ta gama shiri sai ta zo ta rusa mata shiri, tsanar hajia na'eema taji ya dada darsuwa a ranta gashi muddin tana gidan baya yadda kowa ya kawo mai komai sai ita tun lokacin da akayi attempting poisoning nasa ya daina yadda da kowa, tashi tayi ta debi maganin ta zuba a toilet tayi flushing tun kan wani ya gani, ranan hajia mryam kwanan bakin ciki tayi
