BINTU DIYAR BAYI CE PART 3
Babu shiri Bintu ta tashi da sauri, jin Mary na maganar sauko da ita ta ka ta san muguntar Mary za ta aika. Hanyar fita ta nufa ta na jera adduoi iri-iri, ta kama wannan ta saki, wani ma ko k’arshen shi ma ba ta iya kai wa. Su Gimbiya ma ba su yi k’asa a gwiwa ba, biye su ke da ita, ita dai burin Gimbiya ta ji shin da wa Bintu ta ke6e, idan kuwa Aisar ne sai na lahira ya fita jin dad’i, dan kuwa a daren ranar kwanan Sa’ayrasa ne ya kama ta.
Ganin Bintu ba ta jira ta k’arasa gabanta ba, ta na haki kamar zakanya ta fizgo ta, ta hard’e kafar ta sai ga Bintu zube gabanta cikin ca6al6alin ruwan sama "Rage tsinannan tsayin naki dan ubanki, shiyasa ki ke tunanin kin balaga kin isa ke6ewa da malamai." Fad’in Mary ta na mai shararawa Bintu mari. Bintu durkushe bisa gwiwowinta, hannunta bisa kuncinta inda hawaye ke gangarowa daga idanunta, fad’i ta ke ‘’Ina tuba Anty Marry, ki gafarce ni, kimin rai’’
Fili ya cika maki’il da d’alibai, kowa na fad’in albarkacin bakinsa, da masu tausayawa Bintu musammam da su ka san ita ba ‘yar kowa ba ce ta shiga hannun Marry, da ma dai ita d’iyar masu mulki ko sarauta ce da duk jarabar Marry sai ta saurara mata gudun abun da zai je ya dawo. Sai kuma masu mata Allah shi k’ara. Wani wawan mari da Marry ta dad’a kaiwa Bintu, sai ga Bintu a k’asa, sunkuyawa Marry ta yi, hannu bisa kan Bintu ta kama gashinta, ta fisgo ta cikin zafin nama, sai da Bintu ta runtse ido tsabagen azaba. Cikin rad'a ta ce "Ke da wani Malami ki ka ke6e a sashen karatu?’’
Idanun Bintu runtse, da kyar ta iya furta ‘’Ina tuba Anty Marry’’ Cike da mugunta Marry ta fizgi gashin Bintu kamar mai shirin raba gashin da fatar kan Bintu, wani kuka Bintu ta saki, sai ga kallabin ta hannun Marry, inda gashin da dama nad’e shi ta yi cikin kallabi ya warware, sai gashi ya sauka har gadon bayan ta. Ba Marry da su shedigyal ba, hatta sauran d'alibai sai da su ka yi mamakin kyawun gashin Bintu, da ke kullum kanta d’aure ya ke da kallabi, idan ba tsautsayi ba, babu wanda ta ke bari ya gani.
Sikanti ba ta san sanda ta ce ‘’Car uban nan, gide akwai mai irin wannan gashin cikin makarantar nanniya?” Shedigyal da wani bakin kishi ya rufe ta ganin gashin Bintu cewa ta yi ‘’Wannan har wani gashin azo a gani ne?’’
Marry kuwa da tuni ta yi mutuwar tsaye, hannun ta rik’e da kallabin Bintu, murmushin mugunta ta saki, ta na mai jinjina kai ta ce ‘’Sikanti ba ni aran almakashina ki.’’ Gaban Bintu ne yayi mummunar fad’uwa, ta d’ago idanunta da su ka yi jajur ta na mai duban Marry. Marry na murmushi ta gyad’a mata kai ta ce "Gashinki zan yanke muddin ba ki fad'a min da wanda mu ka ganki ba, bayan kuma kin fad’amin na kai bayin k’asa ki lashe kashin yan aji d'aya da su ka yi da harshen ki.’’
Wani sabon kuka Bintu ta saki, musamman jin Sikanta ta tura wata yar aji d’aya ta d’auko mu su almakashi. ‘Dalibai ta bi da kallo cikin neman d’auki, amma sam ba ta ga mai niyar taimakon ta ba, kowa na tsoran sa baki kada gobe idan an je wajan matemakiyar shugaban makaranta wacce ta ke mace ce, a ce har da su, suna ji suna gani a had’a da su. Idanunta ya sauka kan Gimbiya, ta watsa mata harara dan ita ko a jikin ta, Ita so ta ke ma a zo a yanke gashin Bintu ko ta samu ta ji wani Malami ne aka gan shi da Bintu, dan kuwa ta san tun da Bintu ba ta musa ba ko shakka babu da gaske an gan ta d’in ne.
Hankalin Bintu be dad’a tashi ba sai da ta ga an mik’awa Marry almakashi, yayinda ta tsugunna, ta sa hannu ta tattare gashin Bintu cikin hannun ta, wanda rabi kad’ai ta iya kamawa tsabar cikar gashin Bintu, tsakiyar gashin ta sai ta almakashin na ta, ta na mai fad’in ‘’Gide da wani Malami mu ka gan ki?’’
Bintu da ta za6i masifar da hukuncin Marry akan na Gimbiya, ta kasa bud'ar baki ta furta sunan Aisar, sai ta tsinci kan ta ta na mai fad’in ‘’Ki yi hakuri, ina tuba, ba zan k’ara ba.....’’
Jin sautin almakashi ya na ratsawa cikin gashin ta, da kuma sautin mamaki da ya fito daga bakin d’alibai ne ya katse amsar da ta ke bata, idanu runtse yayinda zafafan hawaye su ka zubo daga idanun ta, jin saukar jelar rabin gashin ta k’asa.
‘’Lah'ilaha'illallahu’’ Fad’in Iya Dije wacce dawowar ta kenan ta shigo dan ganin ko Bintu ta koma d’akin ta, ta tadda d’alibai sun yu da'ira, ta na kutsawa ciki Marry na yanke jelar rabin gashin Bintu. Da saurin ta k'arasa in da Bintu ke tsugunne gaban Marry, Shedigyal da Sikanti, ta yi saurin d’ago Bintu ta na mai fad’in ‘’Yo menene zan gani ni Dije?!! Gide wannan wani irin rashin hankali da zalinci ku ke yiwa yarinyar nan?!!! Gide akan wani dalili?!!! Gide wa ya ba ku wannan lasisin?!!’’ Ta shiga jera mu su tambayoyi kamar mai shirin taya Bintu kuka ta na mai duban gashin Bintu da su ka yanke.
Ba tare da nuna nadamar abun da ta yi ba Marry ta amsa mata da ‘’Kama ta mu ka yi ta ke6e da Malam Aisar....’’ Waje ya kaure da hayaniyar d'alibai, Gimbiya kuwa kukan kura ne kad’ai ba ta yi ba ta je ta shak’o wuyar Bintu.
Ran Iya Dije idan yayi dubu ya 6aci, kallabin Bintu ta fizge daga hannun Marry yayinda ta mik’awa Bintu ta na mai fad’in ‘’Gide daura ki koma d’aki, kar ki damu ni Dije sai na bi mi ki hakkin ki, aradu ma kuwa" A sanyaye Bintu ta karbi kallabin, har lokacin kuka ta ke, gaba d’aya kayan ta ya b’aci da ta6on ruwan sama da ta kwaso, kan ta sun kuye ta shige ciki. Bayan tafiyar ta Iya Dije ta mayar da kallan ta ga su Marry kana ta ce ‘’Ni Dije ni na ce Malam Aisar ya bar min sak’o wajan Bintu kasancewar ba zai same ni ba, kuma sak’on ba na kowa ba ne face sak’on Malam Hashim.’’
Wato daga Marry, har shedigyal da Sikanti babu wanda bai tsorata ba cikinsu, dan tabbas sun san matsayin Iya Dije gun Malam Hashim, da sun san da sa hannunta da ba su yiwa Bintu abun da su ka yi mata ba. Tuni idanunsu ya raina fata, cikin kame-kame Shedigyal ta ce ‘’Yetto Allah shi an sheda na hallau daliban nanniya su assheda na, yatsa ban kai ga jikin yarinyar ga ba, idan k’arya na kai aratta kashe ni."
Ko da jin haka Sikanti ma ta yi saurin d’age hannu sama ta na mai fa’d’in ‘’Balanta ni hallau Marry na rako’’ Marry kuwa da ta san k’iri-k’iri Iya Dije ta ganta tana yanke sumar Bintu, jikin ta ne ya hau b’ari, kana ta yi k’ok’arin jan Iya Dije gefe domin bata wani abu dan kuwa kowa ya san Iya Dije da san abun duniya. Amma Iya Dije ta yi kyememe ta k’i sauraronta, sai ma barin ta ta yi awajan ta yi tafiyar ta. Tuni makaranta ta d’auka gobe Marry za ta sha horo, har da masu shagali dan murna. Gimbiya kuwa duk da jin Iya Dije ce ta tura Bintu gun Aisar ba ta fasa mata bambamin wai akan me ya sa ba ta fad’a mata ba ita je a madadin ta tun da ta san ta na san shi, ko damuwa da abun da Marry ta yiwa Bintu ba ta yi ba bare ta saurara mata.
Da daddare Iya Dije ta kira Bintu ta na mai jaddada mata kar ta damu, ita za ta tsaya har sai an bi mata hakkin ta, ita dai duk abun da Iya Dije ta ce gaban Malam Hashim ta amsa mata da eh. Da ke Bintu mace ce mai yafiya sai cewa ta yi ‘’Dan Allah Iya Dije ki bar ta kawai ba sai kin wani bi min hakkina ba, Inna ta tace kowa yayi na gari dan kan sa’’
Iya Dije na mai girgiza kai ta ce ‘’Wagga gaskiya d’aita, amma wannan maganar ban barin ta ko dan rufin asirin kai na, aradu ma kuwa! Yo ki na tunanin idan shi Malam Aisar d’in ya ji bari zai yi? Abun da dai ya fi sauki ki yi yanda na ce kin ji ya?'’
Da wannan su ka yi sallama. Daren ranar Marry kuwa kasa bacci ta yi tsabagen fargaba, gashi ta cire wa d'iyar mutane suna, gashi duk abun nan da ta yi a banza tun da da sanin Iya Dije, babban tashin hankalin ta shi ne matakin da Malam Aisar zai d'auka idan ya ji abin da ta aikata. "Kar dai fa ace ita d’in sai an yanki rabin gashin kan ta!'’ Abin da zuciyar ta ke raya mata kenan, yayinda ta ke kwance bisa gadan ta, kowa yayi bacci ya bar ta. Sai shafa d’an gajeran gashin da be ma kai kamu d'aya ba ta ke, ta san lalle idan da za a cire shi duka ko kwatan wanda ta cirewa Bintu ba zai kai ba. Girman kai ya hana ta iya zuwa ta bawa Bintu hakuri ko ta sami rangwame, "Ni Marry gide tawa ta same ni kishiya tara rana d’aya’’ Ta fad’a a fili yayinda ta tashi zaune ta na mai d'aura han[truncated by
Tin da Iya Dije ta fara jawabi idanun Aisar da ya k’ada yayi jajur ke bisa fuskar Bintu, wacce ke zaune kusa da Iya Dije kan ta sunkuye. Zaune su ke offishin Malam Hashim, dan kuwa gari na wayewa ko taron d’alibai(Asembly) ba a yi ba Iya Dije ta ja Buntu zuwa ofishin, ta na cikin masa jawabi ne Aisar ya shigo sanye da wannan shigar na sa da ya saba, wato (suite) amma wannan karan ruwan k’asa ya saka.
Shigowar Aisar babu alamar da Malam Hashim be yiwa Iya Dije na ta yi shiru ba,
amma ina ta kasa d’aukan haske. Hankalin sa ba k’aramin tashi yayi ba ganin Asar ya tashi tsaye a fusace ya na mai maimata ‘’ta saka Ciseaux (Almakashi) ta yanke sumar Bintu!’’ shima Malam Hashim d’in tashi yayi, ya na yiwa Iya Dije alama da ido na ta rufa asiri ya ce "Ciseaux kuwa uwa Iya Diya?’’
Ita kuwa Iya Dije amsawa ta yi "kwankwatsi ma kuwa, ba mai bi na bashin rantsuwa, ai ga d’iyar nanniya(ai ga yarinyar nan), gani ya kori ji’’ kan Bintu ta ankara iya dije ta ja dan hijabin jikin ta, sai ga daga hijabin har kallabin na ta hannun Iya Dije, dan kunya kamar k’asa ta tsage ta rufe, musammam yanda rabin gashin na ta ya sauka har gadan baya, rabi ya tsaya iya wuya. Ta so yanke sauran dan ta daidai ta su amma sammakon da Iya Dije ta doka mata ya sa ba ta sami dama ba.
Cike da tausayi Aisar ya ke duban ta, ji yake kamar ya ruke ta ya kwashe mata gaba d’aya damuwar ya mayar zuwa kan shi. Gashi saboda shi an wulak’an ta ta, har aka mata cin zarafi ta hanyar yanke mata suma. Malam Hashim kuwa duban sa ga Aisar ya ke, in da zuciyar sa ke jaddada masa lalle watan rufe wannan makaran ta tasu ce ta tsaya...
"Bintu....’’ ya kira sunan ta cikin wani yanayi ya na mai sassauta kullin nakatayal (Neck-tie) din wuyar sa, dan ji yake kamar numfashi ba ya isar sa tsabagen 6acin rai. Hatta Iya Dije da Malam Hashim sai da su ka kai kallan su ga Aisar, ita kuwa Bintu kasa d’aga ido ta kalle shi ta yi. Malam Hashim ya gyara murya ganin yanayin 6acin ran da Aisar ya shiga ya ce "Ina Iya Dije, zai fi kyau ku d’an ba mu hili (fili) mu zanta da Malam Aisar’’ ta na mai mik’awa Bintu kallabi da hijabin ta, ta ce ‘’ye to ai sai mu fita rariya (sai mu fita waje), Bintu mu tahi ko?’’
Da saurin ta, ta karb’a ta d’aura kallabin kafin ta sanya hijabin na ta, Iya Dije a gaba ta na biye da ita, idanun Aisar kan Bintu har su ka fita. Shiru ne ya biyo baya na wani d’an mintina, kafin Malam Hashim ya d’aure ya ce ‘’na san abun da ke ran ka, amma ina mai tabbatar ma ka makamancin haka be ta6a faruwa a wanga École ba, wanga da ya faru ma tsautsayi ne Monsieur Aisar (Malam Aisar)’’
‘’ka na nufin baka san d’aliban ka su na aje makami a tare da su ba Monsieur (Malam)? Ai na zaci k’aida ne hukumar makaranta ta na bibiyan d’akin d’alibai lokaci lokaci dan binciken kayan su domin gudun irin haka? Me ke faruwa a wanga École ? (me ke faruwa a makarantar nan?) Shin me ku ke yi da har irin haka ka iya faru? Ya ilahi da ta kashe d’iyar mutane fa!!!’’ fad’in Aisar wanda tun da ya fara maganar kansa ke kallan silin. Malam Hashim kuwa zufa ne ya lullub’e shi kana ya ce ‘’lillahi warasulihi Monsieur (Malam) abin ga da ya faru tsautsayi nai, na kuma yi maka alkawarin duk matakin da za ka d’auka daidai ta (daidai ne), amma kar ya shafi wanga École(Makaranta) ’’
Sai a sannan Aisar ya mayar da kallan sa ga Malam Hashim, kana ya ce ‘’wannan laifi ne da ba zan iya d’auke ido akai ba, kasan k’asar mu ta Nijar k’asa ce da ke san jama’ar cikin ta, mai daraja dukkan abu mai numfashin da ke cikin ta, a matsayi na na d’an k’asa mai kishin k’asan ga, na ga irin haka na d’auke kai tabbas na ci amanar k’asa ta’’. Jin haka hankalin Malam Hashim ne ya tashi. Sai gashi ya taso ya zo gaban Aisar ya na mai ruk’o hannun sa ya ce "wanga École (makaranta) ta kunshi d’alibai daga kowani sassa da yankunan jamhuriyar Nijar, ruhe (rufe) ta ba k’aramin asara ba ce ga k’asar ga, kai ka sani k’asar mu na buk’atar makarantu ma su inganci irin Sovereign.......’’
"ka na nufin ita kad’ai ta École mai inganci a wanga k’asa ta mu? (ita kad’ai ce makaranta mai inganci a wanga k’asa ta mu?) Kada fa ka nemi ka zagi k’asa ta Monsieur Hashim!’’ Aisar ya katse shi cike da nuna 6acin rai. Cikin sauri Malam Hashim ya girgiza kai ya ce ‘’ba haka na ke nufi ba Monsieur Aisar, yo to na fad’i haka ban yi ma k’asa ta adalci ba, aradu ma kuwa, École (Makaranta) kuwa masu inganci mu ke da su a k’asar mu, amma ruheta kan iya jawo asarar d’aya daga cikin su, sabida Allahu da manzan sa wanga batu ka duba, duk hukunci da za yiwa wannan d’alibar ka mata ita ta jawa kan ta, yo mi zan ce zanin aro ya toye? amma kada laifin wani ya shafi wani’’
Bayan nazari na wani d’an lokaci Aisar ya ce "ko wani hukumci ka ce Monsieur Hashim?’’ Malam Hashim ya jinjina kai kafin ya ce ‘’ko wani hukunci muddin ba zai shafi wanga École ba, ba zai kuma shafi jarabawar gama sakandiri da d’iyar ta ke rubutawa ba....’’ wani irin kallo Aisar ya watsa masa jin maganar ta sa. Da sauri Malam Hashim ya ce ‘’ba dan d’yar ba Monsieur Aisar, dan cigban k’asar mu, ka ga idan ya shafi jarabawar hallau ya shafi cigaban k’asa ta fannin karatu, k’ak’a ka gani?’’
Tashi yayi ya na bai gyara nakatayal(neck-tie) d’in sa, sannan ya ce ‘’na fahimce ka, zan mata hukunci daidai da yanda ta aikatawa yar uwar ta’’ ya na gama magana ya fice in da ya bar Malam Hashim ya na mai zubewa bisa kujera yayinda ya ke goga zufan da shi kan sa be san ya tsefo masa haka da yawan gaske ba. A waje Aisar ya tadda Bintu da Iya Dije tsaye suna jiran tsammani, be iya kallan in da Bintu ta ke ba tsabagen haushin kan sa da ya ke ji akan abun da ya jawo mata. Kana ya dubi Iya Dije ya ce ‘’ko zan iya samin Ciseaux da sabuwar reza gun ki Iya Dije?’’ Cikin fad’uwar gaba Bintu ta d’ago kai ta na mai duban Malam Aisar, sai a sannan ta lura da yanayin shi da ya canza gaba d’aya, ya zama kamar ba shi ba tsabar 6acin rai. Murya a sanyaye ta ce ‘’dan mai sama Monsieur (Malam) ayi hakuri a bar maganar ga, yo to menene dan an aske gashin niya?(menene dan an aske gashi na), in dai dan niya ne arudu na gafarce ta’’
Kallan ta Aisar yayi ba tare da ya tanka mata ba ya sake maimaitawa Iya Dije tambayar, ganin haka Bintu ta sawa bakin ta sakata, in da Iya Dije ta amsa da ta na da su duka, ya ce to ta kawo masa filin taron d’alibai(assembly ground) yanzu ba tare da 6ata lokaci ba. Ya wuce ya bar Bintu da bin bayan sa da ido. Ita kuwa Iya Dije jiki na b’ari ta nufi 6angaran su dan d’auko sak’on Aisar.
A wajan taron d’alibai(assembly), d’alibai da malamai babu wanda be hallara wajan ba, filin ya cika mak’il. Bayan sun yi abin da su ka sabayi kullum, wato na daga al’adar makarantar ne aka bawa Aisar filin. Gannin shi gaban su d’alibai su ka yi tsit, ita kuwa Marry zawo ne kad’ai be zubo mata ba, musammam ganin Iya Dije tsaye kusa da Aisar hannun ta ruke da almakashi. Kamar saukar aradu haka ta ji sunan ta bakin Aisar, bayan ya kira Bintu. Nan da nan d’alibai su ka shiga bud’a mata hanya, da kyar ta ke iya d’aga k’afa ta na takawa saboda tsabagen nauyin da k’afar ta yi mata, har ta kai ga Aisar da tun fitowar ta ya ke mata kallan hadarin kaji.
Jin umarnin da Aisar ya bata na da ta juya ta tsugunna bisa gwiwowin ta gaban d’alibai ya sa ta matsawa kusa da Aisar ta na magana a hankali dan kar a ji abun da za ta ce tace ‘’dan Allah Monsieur (malam) ka taimaka kada su raina ni’’ wani irin tsawa ya daka mata ya na mai fad’in ‘’matsa min daga nan in ba haka ba ina kishe ki a nanniya!(in ba haka ba ina dukan ki a nan)’’ da saurin ta ta ja baya, ba ta san sanda ta zube k’asa ba jiki na 6ari. Ba tare da wani dogon bayani ba, haka ma d’alibai ba sa buk’ata dan kuwa gaban su aka yi komai dan haka Ciseaux din hannun Iya Dije ya kar6a ya na mai mik’awa Bintu ya ce ‘’kyarbi ki mata abin da ta mi ki jiya!’’
Hannun Bintu na rawa amma ta kasa d’aga su ta kar6a, cikin magiya ba tare da ta iya furta wani abu ba ta ke kallan Aisar ta na mai girgiza masa kai. Ga mamakin kowa sai jin Aisar cikin rarrashi ya ce da Bintu ‘’kar6ar wanga Ciseaux tare da yiwa wanga azzalumar aski shi ne hukunci mahi(mafi) sauki a gare ta, idan ba haka ba barin wanga École nan har abada ba tare da ta gama jarabawar ta ba ya kamata, za6in na ki ne’’ jin haka tuni waje ya kaure da hayaniya d’alibai, masu tausayin Mary da masu Allah shi k’ara wanda su suka fi yawa, in da yan aji shida kuwa idan ran su yayi dubu ya 6aci, dama duk ajin Mary aka fi tsoro, ita ce mai kankaro mu su girman yau ga ta tsugunne gaban kowa kuma a wulk’ance, tsabagen d’ibar albarka ace yar aji uku ce za ta mata aski! Gaskiya sun zube ba nauyi. Sai ga hawaye sha6e sha6e a fuskar Mary.
Tuni zufa ya fara kyetowa wa Bintu, musammam da ta kai kallan ta ga Malam Hashim ya gyad’a mata kai dan kuwa dai ba kukan sa ba uwar kishiya ta mutu. Wata malama ce wacce dama ta dad’e da tsanar Mary ta k’araso kusa da su ta na mai fad’in ‘’ Monsieur ba ka san halin wanga d’ya ba ne (wannan yarinyar ba ne), in aka biya ta za mu shekara nanniya ba tare da an samu abun da ake so ba, bari kawai ni na taimaka mata da zab’in’’ ta na magana ne in da ta ke aikawa Marry da sako murmushin yayinda ta sa hannu ta cizge kallabin Mary, Mary ta yi saurin d’aura hannayen ta bisa kan ta domin 6oye cinyayyen gashin ta, ai ganin gashin sai ga d’alibai na darawa.
Muryar Mary na rawa ta ‘’in ki na yiwa Allahu ki yi hakuri Madame , kwankwatsi (rantsuwa) na tuba, dan Allah kada ki yanke min suma ta’’ cike da mamaki ta ce ‘’yo ba ki so a yanke na ki shine ki yanke na wata, aradu kwal kwabo zan mi ki ma kuwa, Iya Dije ruk’e min hannun ta’’ ganin Iya Dije ta yo kan ta, ta saurin sauke hannayen ta k’asa, ta na ji ta na gani Malama ta sai ta almakashi bisa d’an gunjin ta, ta daidaici rabin gashin cikin hikimar raba kan gida biyu, ta fara cire na sama sama. Dake Malamar ma ta na fama da mugun ta, sai da ta karb’i sabuwar rezar hannun Iya Dije, ta kwashe rabin gashin Mary tas sannan hankalin ta ya kwanta.
Fuskar Mary ba k’aramin muni ta yi ba da kai rabi kwakwaido rabi kwal kabo, ko da yake dama yaya bare sarki ya aiko. Dan kunya da takaici ta kasa ko da motsi bare ta iya d’aga idanun ta ta kalli jama’a, d’alibai ba su fasa ihu da sowa ba, musammam da malamar ta ce ayiwa Marry ihu, su ka d’auka ‘’ihu dube ta kwakwaido da kwal kabo’’ Malam Hashim ne ya matso gaba, in da ya kira Shedigyal da Sikanti, ya had’a har maryam ya kwace kallabin muk’amin su, ya kuma jaddada hukunci mai tsanani ga duk d’alibar da aka k’ara kamawa da makami ba tare da kwakkwaran daliliba, ko da kuwa reza ne.
Farin ciki gun d’alibai be musaltuwa, dan kuwa kurace ta mutu, sun huta. Gimbiya kuwa tuni ta sha jinin jikin ta ganin yanda Aisar yayi ruwa yayi tsaki bisa ga lamarin, batun akwai wani abu tsakanin Bintu d’iyar bayi da Malam Aisar tun daga wajan ya fara shawagi tsakanin d’alibai. Har aka sallame su Mary ba ta iya tashi daga tsugunnan da ta yi ba, sai da yan aji shida su tada ita, nan ta saki kukan da dama ya tsaya k’ark’ashin mak’oshin ta, ba ta ta6a jin ta tsani kan ta ba kamar ranar ba. Ko da ya ke ba ita kad’ai ba duka yan aji shidan ma hakan ta ke. Sauran d’aliban kuwa yau ta ke sallah, dan kuwa abin da aka yiwa Bintu gaba ta kai dan sun sami sakewa da wa tayawa, a ranar Bintu ta yi farin jini sai san barka ake yi mata, hatta Gimbiya a ranar sai da ta sarara mata.
Ranar da su ka gama jarabawa da yammaci, ana gobe za su tafi gida, Gimbiya Binta ta ce da Bintu ta raka ta wajan Aisar, dan ta ga idan su na tare ne kad’ai ya ke d’an sakar mata fuska. Sanye ta ke cikin doguwar riga ta alfarma kalar ja, dake Gimbiyar fara ce ba karamin kar6ar ta kalar ta yi ba, ita kan ta Bintu sai da ta yaba da kyawun Gimbiya cikin ran ta. Bintu kuwa kayan su na bayi ne jikin ta, kan ta tufke da kallabi, jin Gimbiya ta ce za su gun Aisar ya ta ware kallabin dan ya dan rufe mata jiki, amma duk da haka iya ka wuyar ta ya ya tsaya, gashi ita ba mayafi gare ta ba.
Gimbiya tafe Bintu na biye da ita ba su zame koina ba sai ofishin malamai. Malaman duka ba sa nan, daga Aisar sai wani malami da su ke kira Malam Sunusi, shi ma d’in su na shiga ya na fita. Malam Aisar da ke zaune bisa kujera ga teburi gaban sa ya na rubuce rubuce, sanye cikin wannan shigar ta sa dai, ko da ya d’aga ido ya ga su Bintu sai ya dakatar da rubutun da ya ke ya na mai aikawa Bintu murmushi. Ita kuwa ta kau da kai karda Gimbiya ta gani ta shiga uku.
‘’assalama’alaikum warahamatullah’’ sallamar Gimbiya kenan gare shi, ya amsa da ‘’wa’alaikum salam’’ Bintu kamar munafuka sai 6uya ta ke bayan Gimbiya ma sallamar ta masa a tak’aice, ya amsa ya na mai k’arawa da ‘’Bintun Sa’ayrasa, ya ki ke 6uya ne, fito sarari mana’’ Gimbiya ta juyo ta watsa mata harara. Jiki a sanyaye, kan ta sunkuye Bintu ta fito sarari. A sannan Malam Aisar ya lura da shigar da ta yi, sai dai duk sanda ya ke ganin ta da irin shigar be tab’a ganin ta sa riga k’arama wacce ta kama ta kamar ta yau ba, gashi zani ne d’aure jikin ta kuma ya fi fitar da surar mace, dad’in dad’awa kuma gashi Bintu ba kad’an ba duk da dai yarinya ce.
Nan da nan su ka nemi fara’ar da ke fuskar Aisar su ka rasa, har sai da Bintu ta tsargu ta d’an ja da baya, Aisar na mai d’auke kai da barin kallan ta ya ce ‘’dole ki 6uya mana, tin da kin hito(fito) yawo ba mayafi da irin wanga shigar!’’ Bintu ta sunkuyar da kai ta na mai tunanin ko dai ya manta da tsayuwar Gimbiya a wajan ne ko me? Allah ya sa kar ya ja mata jaraba. Gimbiya na kallan ikon Allah cikin ran ta fad’i ta ke ‘’aikin banza kyaramuwa tsaftar yaye!’’, Aisar be gushe ba ya k’ara da ‘’kul kar ki k’ara hita(fita) haka ko da a masarautar ku ne!’’ Bintu ta amsa da ‘’toh’’
Gimbiya ya ce ta ce "Monsieur Ina wuni’’ ba tare da ya kalle ta ba ya ce ‘’lafiya’’ ganin haka ta ce da Bintu ‘’Gide hita (fita) waje ki yi jira na....’’ be jira amsar Bintu ba yayi saurin katse Gimbiya ta hanyar fad’in ‘’idan kin hita ki wuce d’aki kar ki tsaya waje da wanga shiga ta ki, idan kin gama kya same ta ca’’
Cikin sauri Bintu ta bar wajan ta na mai hamdalar ceton ta da Allah yayi. Bayan fitar Bintu maimakon ya tsaya ya saurari Gimbiya sai ya cigaba da rubuce rubucen sa, kamar be ma san ta na wajan ba. Kamar za ta juya sai dai ta d’aure ta ce ‘’Malam gobe za mu koma gida’’ ba tare da ya d’ago ya kalle ta ba amsa mata ‘’sai aka yi yaya?’’ Gimbiya ta d’an cije le6e kafin ta ce ‘’dama zuwa na yi na maka sallama, na kuma gayyace ka zuwa masarautar mu idan da hali’
‘’na gode da sallamar, sai dai masarautar ta ku ce ban da lokaci’’ amsar da ya bata kenan. Kana Gimbiya ta dad’a gwada sa’ar ta ta hanyar fad’in ‘’dama wai ina nufin in ka sami lokaci.....’’
‘’ban da wannan lokacin’’ ya katseta ya na mai kafe ta ido. Ganin haka Gimbiya ta cije le6e ta na mai hamdalar korar Bintu da ta yi da yanzu gaban ta Aisar zai mata wannan cin fuskar. Fuuu ta juya ta fice ba tare da ta sake tankawa ba. Sai da ya ga ta fita ya aja rubutun ya na mai jan tsaki, takaicin sa na ganin ta na masa yawo da Bintu haka babu mayafi, ko wani kare da biri ya kalla! ‘’ba dan karancin shekarun wangad’iya ba, wallahi ba d’iyar bayi, ko d’iyar bola ce sai na aure ta! Amma ba komai lokaci ne ni Aisar mai hakurin jira ne’’ furicin Aisar kenan azahiri ya na mai jadda batun kawo kanwar sa Maryam makarantar ko ba komai ta ke saka Bintu a hanya. Tsaki ya sake ja ya na mai tura rubutun da ya ke gefe dan kuwa lamari in dai akan Bintu ne ya na jagula masa lissafi.
Komawar Gimbiya Binta d’aki kan Bintu ta sauke takaicin ta, laifukan na Bintu da yawa ciki har da ta na sane ta bita gun Aisar babu mayafi tsabagen ta na so ta yi masa tallar jikin ta, an fad’a mata shi d’an iska ne? Ta ji dad’in yanda ya yiwa Bintu kurar kare, da kuma ta ce ta jira ta waje shi ne ta bi umarnin uban ta ta koma d’aki.
Aiki tuk’uru ta saka ta wanda tun da Bintu ta zo duniya ba ta tab’a yin irin shi ba, hatta kayan ta da ke wanke a goge sai da ta sa Bintu dad’a wankewa da guga, dare yayi kuma ta tura ta lungu cikin sauro, nan Bintu ta kwana ta na mai adduar Allah ya sa iya haka hukuncin Gimbiya ya tsaya, ba za ta aiwatar da alkawarin sakawa a cire ta daga makarantar ba.
Washagari da ruwan sama aka tashi, motocin Sa’ayrasa na d’aya daga cikin motocin da su fara isowa. Sai da ruwa ya d’an tsaya sannan bayi da fadawa su ka taimakawa Bintu wajan kwasar kayan Gimbiya, har ya rage akwaitin karfen Bintu kad’ai ya rage a d’akin. Ita kuwa Gimbiya yar sarki mai dole kuma ta na jira a take mata baya zuwa mota, haka Bintu ta na ji ta na gani ta bar akwatin na ta su ka takawa Gimbiya.
Ta na shiga mota ta juya da niyar komawa ta d’auk akwaitin na ta, Gimbiya ta tsiyar da ita ta hanyar daka mata tsawa ‘’gide ina kuma za ki?’’ dan a zatan ta wajan Aisar Bintu za ta. Ko da Bintu ta fad’a mata cewar akwatin ta za ta d’auko, minti gama kacal Gimbiya ta bata idan ba haka ba za ta taka zuwa Sa’ayrasa da k’afar ta. Hanyar da za ta kai ta ga d’akin na su Bintu ta kalla, ko zuwa bakin kofar b’angarn sai ya fi minti goma bare kuma ga hawa bene ga nauyin kaya. ‘’ki nan tsaye ne? idan kin fasa ma iya tafiya’’ furucin Gimbiya cike da tak’ama.
Cikin hanzari Bintu ta ce ‘ tuba na ke ran Gimbiya shi dad’e’’ kafin ta tafi da sauri, sai da ta tabbata ta wuce ganin su Gimbiya sannan ta arta a na kare. Ta na ji wasu na ‘’fad’in ku kauce ta fara gudun na ta na masifa’’ har dariya ake mata ita kuwa ba ta san suna yi ba. Haurawa ta yi ta d’auki akwaitin ta bisa kan ta. Ta fito daga sashin kwanan na su kenan kamar daga sama ta ji an d’auke ma ta akwatin daga kayin ta.
A tsorace ta juya sai ga Aisar sanye dai da shigar nan nasa, amma yau fara ya sa, idanun sa rufe da gilashi, hannun sa ruk’e da wata leda mai d’an girma cikin nuna damuwa ya ce ‘’wanga ya yiwa d’iya mace nauyi’’ cikin kokawa Bintu ta ce ‘’dan Allah ka yi min rai ka bani na tafi, aradun Allah minti goma kacal Gimbiya ta ba ni’’ maimakon ya bata, sai ma dad’a ruk’e akwaitin yayi kafin ya ce ‘’idan kuma ki ka k’ara fa? K’ak’a za ta yi?’
Idanun Bintu na mai kawo ruwa ta ce ‘’aradu tahiyar su za su yi su bar ni a nanniya (wallahi tafiya za su yi su bar ni a nan)’’ Aisar na mai murmushi ya ce ‘’idan su ka tahi shikenan sai na tahi da ke gidan mu hankali kwance’’ ganin za ta sa masa kuka ya ce ‘’shhh..wasa na ke mi ki’’ akwatin ya aje k’asa sannan ya ciro zoben hannun sa ya mik’a mata ya na mai fad’in ‘’kan ki tafi ga ajiya ta Bintu, ina so ki aje min duk sanda mu ka sake had’uwa zan kar6a’’
Cikin saurin ya bar ta tafi, ba tare da ta kawo komai cikin ran ta ba ta sa hannu ta karb’a ta na mai k’ok’arin cusa zuben cikin zanin ta,ya ce ‘’ah ah a yatsar ki na ke so ki saka, nan ya na iya fad’uwa’’ ba musu ta fara k’ok’arin zira zuben, duk da ya so ya mata yawa ta samu ya shiga yatsar tsakiyar hannun ta na dama. Ta yunk’ura za ta d’au akwatin kenan Aisar ya riga ta cikin zafin nama, ya wuce gaba abun sa, da sauri ta bi bayan sa ta na mai fad’in ‘’ Monsieur ka bani akwatin dan Allah’’ shiru ya mata, dake Aisar mutum ne mai kuzari, nan da nan su ka isa ga motocin Sa’ayrasa. Bintu sai karanto adduoin da ta koyo makarantar allo ta ke dan neman tsari daga masifar Gimbiya, dan ba ita kad’ai ba ma kallo da zund’e da ta sha wajan sauran d’alibai ma sai Allah, musammam yan aji shida da dama sun gama tsanar ta, yau ga Aisar Gaddafi Nur yayi dakon akwaitin d’yar bayi. Shi kuwa gogan na ta ko a jikin sa wai an mintsli kakkausa.
Suna isa ya sakar mata murmushin da ita kan ta Bintu ba ta san na menene ba, ita dai ta na ganin sabon salo kiran sallah da husir, kana ya ce ‘’wata motar Gimbiya za ta shiga’’ Bintu ta amsa da ‘’ai Gimbiya ta na cikin waccar motar’’ ta masa nuni ga motar da Gimbiya ke ce. Aisar ya kai kallan sa ga motar, ko da yayi ido hud’u da Gimbiya, duk da 6acin ran da ta shiga ganin Aisar d’auke da akwatin Bintu, sai da ta tsinci kan ta ta na mai sakarwa Aisar sakon murmushi. Yayi saurin maido da kallan sa ga Bintu ya na mai fad’in ‘’ba Gimbiyar ki na ke magana akai ba, Gimbiyar Aisar na ke nufi, wata motar za ki shiga?’’
Cike da mamaki Bintu ta amsa masa da ‘’iyye? Na’am? Ni Bintu?’’ kai ya girgiza mata, jiki a sanyaye ta masa nuni dai ga motar da Gimbiya ke ciki, kana ya ce da direba(driver) ya ce ‘’Aboki na bud’e min bayan motar na aje kayan ko’’ jin haka Bintu ta yi saurin fad’in ‘’waccar motar ta baya za a aje kayan’’
Aisar ya ce ‘’toh gidan gaba ko baya ina ki ke zama?’’ ta na hango Gimbiya ta na girgiza kai har da kwafa, ta na mai duban Bintu ta ce ‘’a juri kai zuga gabas, wataran ta zo da ruwa’’ maimakon Bintu ta bashi amsar sai kawai ta kai hannun ta ga murfin motar da niyar bud’ewa, yayi saurin tsaiyar da ita, ya b’ud’e da kan sa, Bintu ta shiga, ita kan ta ta san ta wuce gona da iri. Ledar ya aje bisa cinyar ta, ba tare da ya rufe motar ba ya ce da direban ya fito kai akwaitin Bintu cikin motar da ake ajewa. Direban ya so yi masa musu, amma ko da suka had’a ido da Aisar ya ga waye gaban shi tini ya fito yayi yanda aka saka shi.
Aisar ya ce ‘’ki gaida gida ki gaida yan gidan Bintu, sai kin ji daga gare ni’’ kai kawai Bintu ta iya gyad’a masa, yayin da ya mayar da murfin mota ya rufe. Direba ya dawo ya tada mota har su ka fita be dena kallan motar da Bintu ke ciki ba, ji ya ke kamar ya bi bayan su.
Da fitar su, ta baya ta ji Gimbiya ta kifa mata mari, ta na mai fad’in ‘’shegiyar kaya!dama wajan shi ki ke san zuwa sai da jiki na ya ban!’’ kuka Bintu ta saka, fad’i ta ke ‘’ki yi min rai Gimbiya, tuba na ke, ba wajen shi na je ba a hanya mu ka had’u, idan karya na kai arratta kashe ni’’
Tas! Ta dad’a kwashe ta da mari ‘’shi ne har da d’aukar d’an akurkin ki ko? Kai direba tsayar motan nan! Direba ya ja ya tsaya, sauran motocin ma tuni suka faka gefe guda ganin na Gimbiya ma ya faka. Ledar hannu Bintu ta fizge ta na bud’e, mayafai ne manya masu kyan gaske har guda goma. Tsaki Gimbiya Binta ta ja yayinda ta sauke gilashin motar ta na ji ta na gani ta wulga mayafan waje, kan idanun Bintu haka su ka sauka cikin ruwan sama da ya kwanta a gefen titi, sannan ta ce ‘’Direba mayar da d’iyar bayin nan cikin bayi sa’annin iyayen ta’’ Direba ya dubi Bintu da ke faman kuka ya ce ‘’yo to ai sai ki hito ko?’’
Bintu na k’ok’arin fitowa ta ji Gimbiya ta ce ‘’ke da wanga ecole har abada! aradu ma kuwa!’’ da ma dai ko ba ta fad’a ba Bintu ta san ta faru ta k’are ramamme ya zagi maye. Haka ta na mai fad’in ‘’ina tuba’’ amma Gimbiya ta mata kunne uwar shegu, yayinda direba ya raka Bintu izuwa motar bayi a wulak’ance. Nan su ka d’auki hanyar masarauta Bintu na mai bakin ciki da fad’uwar gaba.