BINTU DIYAR BAYI CE PART 2



Cikin sauri ta tashi tsaye ta gaishe shi da harshen (French) faransanci wanda da dama da shi su ka fi amfani a makaranta. Gaba d’aya ta manta da wani kunyar sa da ta ke ji yanzun da ta gan shi tsaye gaban ta dan kwarjinin da ya mata.  Kan ta sunkuye tana wasa da ledar k’wilin ta ya amsa mata a takaice fuskar babu walwala ya ce ‘’me ki ke yi waje lokacin cin abunci?’’

 ‘’Gimbiya Binta na ke jira ta gama cin na ta sai ni ma na ci nawa’’  ta amsa zuciyar ta d’aya ba tare da ta d’aga kai ta kalle shi ba.

Cike da mamakin amsar ta ta ya ke duban ta, ita sam bata lura da kallan na ta da ya ke ba. Kana ya ce "wacece Gimbiya Binta?’’ jin tambayar na sa Bintu ta bud’e baki,cike da mamaki ta ce "laa ba ka san Gimbiya Binta ba? Yar sarkin Sa'ayrasa fa, wata fara tas kamar d’iyar larabawa, ta na da kwarjini matuk’a’’.

Badaban ran sa a  6ace ya ke ba, yanda ta ke kod’a Gimbiyar ta ta sai da ta kusa ba shi dariya. Amma sai dad’a tsuke fuska ya yi kafin ya k’ara da ‘’ban san wakike magana akai ba, amma abunda na ke so na sani shi ne shin dokar makarantar ce sai wata Gimbiya ta gama cin abunci kafin sauran d’aliban su ci ko kuwa?’’

Tuni Bintu ta fara shan jinin jikin ta dan kuwa tabbas idan hukumar makarantar ta ji wannan maganar matsala zai zame mata. Kana ta ce "iye! Na’am? Dama wai,dama ai..........’’.
"dama me?” ya katse ta ya na mai duban ta. Nan fa Bintu ta shiga cikwikwiya ledar hannun ta, ta rasa amsar da za ta ba shi.
"dokar makarantar ce sai wata Gimbiya ta gama cin abunci kafin sauran d’aliban su ci ko kuwa?’’ ya dad’a maimai ta mata tambayar cikin k’aguwa. Ganin ba ta da niyar amsawa rai 6ace ya furta "menene dangantakar ki da wannan da ki ke kira gimbiya ?ya sunan ki?’’

Cike da tsoro Bintu ta amsa ma sa "sunana Bintu, Bintu Bala Mahuta, ni d’iyar bayi ce, ni ce baiwar da ke kula da Gimbiya Binta ta masarautar Sa’ayrasa.....’’ 
‘’wannan ne ya bata damar hana ki abunci? Haka ake gudanar da lamarin wannan makarantar? Saboda zalinci? Toh daga yau ya k’are ni Aisar ba na san zalinci kuma ba zan juri ganin zalinci ba’’ ya na gama magana ya juya a fusace ya fara tafiya, ganin haka Bintu da tun da ya fara magana ta gama firgita, ba ta san sanda ta saki ledar k'wilin ta ba, ta bi shi da sauri tare da shan gaban sa, sai ga ta ta zube gwiwowi biyu a kasa. Da sauri ya ja ya tsaya ya na mai duban ta cike da mamaki ganin duk zafin ranar be hana ta saka tafukan hannayen ta biyu k’asa ba ta mai duk’ar da kai kamar wacce ta ke shirin shigewa k’ark’ashin k’asa.

Hankali tashe ta shiga jero masa magiya ta na mai fad’in "tuba na ke, ka gafarce ni, na tuba, ka yiwa Allah da manzon sa kar ka had’a ni da Gimbiya, aradu idan ta ji wannan maganar na kad’e har ganye na,ka min rai, na tuba....’’ ta k’arasa maganar na ta cikin kuka. Aisar kuwa kasa magana yayi ya na mai duban ta cike da tausayawa kana daga bisani ya ce ‘’tashi....."

maimakon ta tashi sai ta dad’a kask’antar da kai ta yi kasa ta na kuka, jin kukan na ta ya ke har ran sa. Idanun sa runtse ya ce ‘’ya salam wannan wata irin yarinya ce mai shegen taurin kai! ki-ta-shi-na-ce’’ a hankali yayi maganar kamar mai koyan magana. Sai a sannan ta tashi, amma har lokacin hawayen ta ke.

Kallan ta yayi na wasu dan dak’ikai, kafin ya mata nuni da inuwar da ya tadda  ta zaune ya ce koma can ki zauna ina zuwa. Baki ta bud’e da niyar yi masa musu, amma ko da su ka had’a ido sai ta tsinci kan ta ta na mai fad’in ‘’toh’’ ta yi sauri ta koma k’ark’ashin bishiyar in da ta jingina jikin ta, ta na mai mayar da ajiyar zuciya ganin Aisar shi ma ya juya ya tafi.

Ta na mai addu’ar Allah ya sa ya hakura kar ya dawo har ta samu ta shiga d’akin cin abunci. Sai a sannan ta lura da ledar k’ulin ta a k’asa ta yi sauri ta d’auko ta  ka6e dattin da ya mak'ale jikin ledar kafin ta tura cikin aljihun ta dan kuwa shi ma ya fita ran ta. Jim kad’an Aisar ya dawo d’auke da wata yar bakar leda, ya mik’a mata ledar tare da fad’in "gashi maza ki je ki sami waje ki ci’’ ledar ta bi da kallo, wani irin kamshi ke ziyarta hancin ta daga cikin ledar, tuni ta mayar da mugun yawu, ta na mai girgiza kai ta ce "ah ah na gode ai ba na jin yunwa dama’’ "ba kya jin yunwa?’’ ya maimaita cikin sigar tambaya. Kai ta gyad’a masa alamar eh. Amma mai za su ji? ‘’kulululu’’ sautin da ya fito daga cikin ta kenan wanda ya ke gasgata zargin Aisar na Batun Bintu ba ta jin yunwa yasasshen zance ne.

Cike da jin kunya ta sunkuyar da kai k’asa, duk 6acin ran sa sai da ya tsinci kan sa ya na mai murmusawa. ‘’kar6a ki ci maza kafin a koma aji’’ sai da ta d’an yi jim, kafin daga bisani ta sa hannu biyu ta karb’a ta na mai godiya, fad’i ta ke ‘’Godiya na ke, madallah, Allah ya saka ma da alkairi’’ ba ta jira jin amsar shi ba tayi gaba, hannu na rawa ta ke k’ok’arin bud’e ledar dan ganin abun da ya ke, ganin lafiyayya abuncin da ke cikin ledar tuni ta fara k’ok’arin fara kaiwa baki dan ta ma manta da Malam Aysar da ya bi ta da kallo cike da tausayawa har ta k’ure masa. Kai ya jinjina ya na mai shan alwashin maganin wannan zalincin da Gimbiya ta ke yiwa Bintu na hana ta cin abunci cikin d’alibai yan uwan ta. Shin dama har yanzu ana irin wannan zalinci? wannnan wani irin sakaci ne daga hukumar makarantar, da ga alama dai ba banza ta kawo shi makarantar ba, babu mamaki watan rufe makarantar ce ta tashi muddin ana irin wannan zalincin da sanin hukumar makarantar. Da wannan tunanin ya nufi ofishin Malam Hamisu. Yayi rashin sa’a ba ya nan dan haka dole ya hakura ya koma ofishin zaman malamai da k’udirin cikin ran sa.

Yanda Bintu ke cin abunci kamar wacce ta shekara ba ta ci ba ya sa ta saurin gamawa kafin su koma aji. Suna komawa kuwa lokacin koyarwar Aisar ne. Da shigowar sa ba tare da 6ata lokaci ba ya fara abunda ya kawo shi, wato koyarwa. Darasin na sa yau akan "Gaba" ne. Aisar ya fara da tambayar misalan yankuna ko masarauta masu tarihin gaba tsakanin su, ba jamhuriyar Nijar kad’ai ba har mok’otan su. D'aya daga cikin d’aliban ce ta d’aga hannu, in da Aysar ya bata damar amsa tambayar, ta ce "kamar gabar da ke tsakanin masarautar Sa’ayrasa da masarautar Fabarusa’’ Aisar na mai jinjina kai ya ce "haka ne ku tafa mata’’ aji aka d’auki tafi "raf raf raf"

Bayan haka ya k’ara tambayar "su waye ‘yan masarautar Faburasa cikin ajin nan?’’ wajan mutum uku ne su ka d’aga hannu, bayan wani d'an sakanni ya ce su sauke, masarautar Sa’ayrasa ma su d’aga hannu. D’alibai shida ne su ka d’aga hannu, ciki har da Gimbiya. Bintu kuwa ta na can ta na tunanin duniya, gaba d’aya hankalin ta ba ya ajin. Hannun su d'age be ba su izinin saukewa ba dan shi hankalin sa kan Bintu ya ke, suma kuma ‘yan ajin sun lura da hakan dan su ma d’in Bintu da ta doka uban tagumi su ke kallo.

Kamar daga sama ta ji ya ce ‘’Bintu hankalin ki ba ya aji na!’’ ta yi firgit ta dawo cikin hankalin ta ta na mai cire hannun ta daga tagumin da ta yi. Ganin idanun kowa kan ta, ga hannun wasu daga cikin yan ajin har da Gimbiya d’age ya sa Bintu kai duban ta ga Aisar, in da shi kuma ya maimaita mata umarnin da ya ba su. Da saurin ta ta d’aga na ta hannun sama sannan ya ce su aje hannun na su. Wata har da fad’in "wash hanuna" a hankali yanda Aisar ba zai jiyo ta ba.

Bintu ba ta tsorata ba sai da ta ga Gimbiya ta juyo ta watsa mata harara. Wani mugun yawu ta had’iya tuni hantar cikin ta ta kad’a. Malam Aisar kuwa be gushe ba ya cigaba da "shin wa zai fad’a min lokacin da gabar ta samo asali?’’ d’aya daga cikin su ta amsa da "gabar ta samo asali ne tun kaka da kakanni amma anfi dangan ta shi da lokacin mulkin sarki Abdulrahaman III na masarautar Faburusa’’ Malam Aisar ya ce a tafa mata sannan ya sake tambayar hanyoyin da ya dace a bi domin kawo karshen gaba tsakanin k’asa da k’asa ko masarauta da masarauta. Dalibai da yawa su ka d’aga hannu, amma ga mamakin kowa sai ji su ka yi ya ambaci sunan "Bintu’’

‘’Wayyo shi dai sai ya fad’awa kowa ya san sunana ko menene haka?’’ ihun da Bintu ta kurma cikin ran ta kenan. Gaba d’aya ajin idanu su ka zubo mata yayinda ta tashi a hankali murya kamar ba nata ta ba, ta furta abun da ya fara zuwa bakin ta "auratayya tsakanin masarautar’’ nan fa aji aka kwashe da dariya, Zahira ta ce "auratayya tsakanin bayi, d’iyar bayi ta auri dan bayi.....’’ aka dad’a sa dariya.

Kunya ta rufe Bintu kamar ta shige k’ark’ashin kujera ta 6uya. "shiru!’’ Aisar ya daka musu tsawa. Aji yayi shiru kamar wanda ruwa ya shanye, ran malam ya 6aci. ‘’wata mara tarbiya ce ta yi wannan maganar?’’ ya tambaya a fusace. Aka rasa mai bashi amsa, har sai da ya sake maimaitawa sannan Zahira ta tashi tsaye gwiwa a sanyaye. Bintu ya duba ya umarce ta da ta zauna kafin ya koma ga Zahira. Ya ce da yan aji kowa ya dube ta, shin ita yar wata yanki ce. Ta na zumb’ure zumb’ure ta amsa da ‘’Niamey’’ kai ya girgiza kan ya ce ‘’Niamey na alawadar da masu hali da kalimi irin na ki, kalamai ne irin na marasa tarbiya wanda su ka tashi a watse, lalle idan har Jamhuriyar Nijar na da yan k’asa irin gaba tsakanin yankuna ba zai tab’a yankewa ba, fitar min daga aji kuma kar ki sake shigowa in har ni ne cikin ajin’’ Zahira ta wuce fuuuu za ta fita ya ce ‘’dube ta k’azama kawai’’ kunya ya rufe ta ta fice da sauri.

Jikin kowa yayi sanyi, tin ba ma Bintu ba. Aisar kuwa be sake cikakken minti goma ba ya fice da ga ajin,dan kuwa tabbas d’aliban makarantar na fama da rashin tarbiya na gaske. Surutai kuwa ta sha wajan yan aji, daga mai fad’in "kun ji yanda ya ke kiran sunan ta kuwa?’’ sai mai fad’in ‘’ta yaya ya san sunan ta bayan be ta6a tambayar sunayen mu ba?’’ ita kuwa Bintu kai ta kifa bisa teburi dan Allah kad’ai ya san masifun da ke gudana cikin zuciyar Gimbiya, ta san yau kam sai yanda aka yi da ita wai d'an daudu a kabari.




Bayan an tashi daga makaranta, ko kallan ta Gimbiya Binta ba ta yi ba ta ta wuce gaba ita da Ruqayya, Bintu na rawar jiki rik’e da jakar Gimbiya ta bi bayan su. Ba su zame koina ba sai d’akin su in da su ka tadda Zahira na jiran su dan gasawa Bintu gurasa danya a hannu.

Zagaye Bintu su ka yi tsakiyar d’aki,   sai ta fad’a musu yanda aka yi Aisar ya san ta yasan sunanta da har ya ci mutuncin Zahira saboda ita. Bintu na raba idanu ta ce ‘’Dan Allah Gimbiya ki min afuwa, aradu shi da kan sa ya tambayi sunana........’’

Ji ka kake tas! Gimbiya ta kwashe ta da marin da sai da Bintu ta ga wuta a idonta, a gigice ta sa hannu bisa kuncin ta na mai fashewa da kuka. Gimbiya ba ta gushe ba ta ce " Yar iska! A shekarun ki har kin iya karuwanci?!!!’’ Ta sa k'afa ta shure Bintu. "Yo dama ana raba bayi da karuwanci ne Gimbiya?’’ Rukayya ce ta ara ta yafa. Zahira ta k’ara da,   "Wallahi tunda ki ka sa mutum kamar Aisar ya ci mutuncina sai kin yabawa aya zak’inta."

Ita dai Bintu ta kasa magana, kanta durk’ushe, sautin kuka kad’ai ke iya fita daga bakinta. Gimbiya ta ce ko dai ta fad’a mu su yanda aka yi ya san ta har ya tambayi sunan ta ko ta kira waya fada a zo a mayar da ita Sa’ayrasa. Jin haka haka nan da nan Bintu ta shaida musu komai. Duka da mari babu wanda ba ta sha ba. A fad’ar Gimbiya don tasan tana da k’udirin auren Aisar ya sa ta ke masa shisshigi dan ta 6ata ta wajan shi, toh wallahi ta yi kad’an, duk randa ta yarda wani abu ya k’ara shiga tsakanin su ta tabbatar ranar zaman ta a wannan makarantar ya k’are. "Godiya nake Gimbiya’’ a
Abinda ke fita daga bakin Bintu kenan har su ka k’araci masifar su, su ka tafi d’akin Zahira.

Bintu na zaune inda suka bar ta, ta had’e kai da gwiwa in ban da ajiyar zuciya babu abun da ta ke, sai ga Iya Dije ta shigo da sallamar ta. Ganinta Bintu ta yi saurin gyara zama ta na mai k’ok’arin goge hawayen da ke fuskar ta gudan kar Iye Dije ta gani. Cike da mamaki Iye Dije ta ce "Bintu lafiya? Me ya sa ki kuka haka? Ya na ga idonki d’aya ya kumbura?’’  "Ba na jin dad’i ne Iya Dije, ciwon kai da ido na ke’’ Bintu ta yiwa Iya Dije k’arya gudun abun da zai je ya dawo. Cikin nuna tausayawa Iya Dije ta ce " Ayya Allah ya sauwake, na ce dai kin je kilinik (clinique, karamin asibitin makarantar) an duba ki ko?’’ Kai Bintu ta girgiza alamar ah ah, sannan ta k’ara da ‘’Ba sai na je ba, ina da magani, idan na sha shikenan."

Kallan ta Iya Dije ta ke kamar mai nazarin wani abu, kafin daga bisani ta ce ‘’Toh Allah ya sauke.’’ Ta ja wata yar kujera ta zauna sai a sannan Bintu ta lura da ledar hannunta, a gaban Bintu ta aje ledar kan ta tambaya "Shin al’adar ta ki ta d’auke ne?’’ Cikin nuna jin kunya Bintu ta girgiza kai alamar ah ah. Iya Dije ta ce "Ai bakomai, dama daga kwana d’aya har zuwa kwanaki goma sha biyar yakan iya kai wa. Dama batun turaren ne, Malam Aisar ya ba ni kud’i, sanin ba a bari dalibai su fita daga makaranta yasa na yi karambani na siyo miki’’ Ta sa hannu cikin ledar sai gashi ta fito da kwalaban turare har guda uku, ta aje gaban Bintu ta na fad’in ‘’Kinga wannan Danduwala ne, ga kuma Kafin-kafin, ga Binta Sudan duka na ki ne." Ta k’arasa maganar tana mai washe hak'ora don tasan ba k'aramin gwanin ta ta yiwa Bintu ba, duk da dai rabin kud’in da Aisar ya bata a aljihun ta ya k'are.

Bud’ar bakin Bintu sai cewa ta yi "Iye Dije na gode amma dan Allah ki mayar masa, aradu ba zan iya karb'a ba, ba na so’’ ‘’La'ilaha illallahu!" Fad’in Iye Dije ta na mai tafa hannu "Ku ga yarinya za ta watsan k'asa a ido! Ba kya so a na wani dalili? Iyye?!!!’’ Ta yi tambayar ta na mai fidda idanu ganin Bintu na shirin kwance mata zani a kasuwa, don kuwa karya da gaskiya ta had’a ta fad’awa Aisar kan buk’atun Bintu, haka ya bata kud’i CFA na gugan CFA har (10000 CFA), fiye da rabin kud’in ta kashe. Bintu ta rasa amsar da za ta bata, ta tsinci kanta tana mai fad’in ‘’Na ga ba na buk’ata ne Iya Dije.’’

Ba ta ankara ba sai ganin Iya Dije ta yi ta d’aga hannunta tana mai k’ok’arin cusa hancin ta k’ark’ashin hammatar Bintu. Da sauri Bintu ta ja da baya ta na k’ok’arin kwatar kanta, fad’i ta ke ‘’Iye Dije ya haka?” Iya Dije kuwa duk da babu abinda ta shak’a na wari daga jikin Bintu don kuwa Bintu irin mutanen nan ne wanda sam ba su da warin jiki, sai ga ta ta yi baya da sauri ta na mai toshe hanci ‘’Kin ji yanda ki ke bugawa ki na hamami kuwa? Har ki ce ba kya buk’ata? Shi kan shi Malam Aisar d’in wannan hamamin na ki ya ji shi ya sa ya ce na tambaya ko ki na da buk’atar turaren.’’

Jin haka kunya ta rufe Bintu, kamar k’asa ta bud’e ta shige. Ta na mai yin k’asa da ido ta ce ‘’Ai idan Gimbiya ta gani ko ta ji ina kamshin turare ma su k’amshi haka Iya Dije kashi na ya bushe’’ Sai a sannan hankalin Iya Dije ya fara kwanciya, ta ce ‘’Yo ba sai ki 6oye yanda ba za ta gani ba, sai ki na sawa kad’an haka, ni dai ba zan mayar da wanga turare ba’’ Ajiyar zuci Bintu ta saki ganin babu yanda za ta yi dole ta hakura ta kar6a ta na mai godiya. Ita kuwa Iya Dije ko da ta samu ta cusawa Bintu turare sai ta sami kwanciyar hankali, dan da ba ta san yanda za ta yi ta biya da kud’in Aisar da ta ci ba.

Aisar kuwa sai da ya tabbatar ya kaiwa Malam Hamisu k’orafinsa kan rashin tarbiyar d’alibai da kuma zaman wata d’aliba a waje lokacin cin abinci ba tare da ya ambaci sunan Bintu ba. Malam Hamisu ya nuna rashin saninshi kan maganar yanayin cin abincin d’aliban, kuma ya yi masa alk’awarin d’aukar mataki. Saidai batun rashin tarbiyar d’aliban ya ce su ma hakuri su ke da su kasancewar kowani tsuntsu kukan gidansu ya ke, amma In sha Allahu za su k’ara tsauri kan lamarin.

Washagari da safe wajan taron d’alibai (Assembly), Mallam Hamisu ya ja kunnan d’alibai akan bin duka, musammam wanda ba sa halartar wajan cin abinci idan lokacin yayi, ya kuma tsawatar da hukunci mai tsanani muddin aka ga d’aya daga cikin d’aliban na aikata hakan. Da wannan Bintu ta sami saukin samin cin abinci tare da yan uwan ta d’alibai duk da kuwa sai da ta sha tuhuma gun Gimbiya akan zargin ko ita ta kai k’arar ta.

Kwanci tashi haka rayuwa ta kasancewa Bintu cikin makaranta. Gaba d’aya gudun Aisar ta ke, tun shi ma bai gane ba har ya zo ya gane ya daina nemanta. Ita kuwa Zahira hakuri ta je ta bashi tare da sa bakin Malam Hamisu ya hak’ura ya bari ta koma ajin na shi. Gimbiya Binta babu irin cusa kai da ba ta yiwa Aisar, amma sam ba ta gabansa bare ya san ta na yi, manyanta ma yan aji biyar da shida fama su ke bare ita karan kad’a miya acikin jerin ‘yan mata.

Da yammacin ranar lahadi, ana saura sati biyu su Bintu su fara jarabawa. Yanda garin yayi wasai, gajimare yayi lub-lub, ciyawa da bishin da ke cikin lambun sun yi kore shar, ga wani ni’imatacciyar iskar da ked’awa wanda sanya rassa da ganyayyakin bishiyun da ke cikin lambun rausayawa suna mai fuzar da feshin ruwa sanadiyar ruwan sama da ya sauka ya kuma tsaya mintina talatin da su  ka wuce ne ya sanya Aisar da ke kwance kan kujerar hutun da ke k'ark’ashin d’aya daga cikin rumfunan lambun, in banda kukan tsuntsaye da kuma k’arar saukar sauran ruwan sama da yayi ragowa bisa kwanan rumfar lambun babu abun da ke tashi.

Sanye ya ke cikin bakar riga mai k’aramin hannu, da wando wanda ya ke shi ba gajere ba bai kuma kai masa har k’asa ba. Idanunsa lumshe tamkar mai bacci, ko da yake da zai sami bacci da hakan zai fi so dan kuwa tunanin da ya dad’e ya na damun sa yanzun ma shi ya sa shi gaba. Ba kuma tunanin kowa bane, face na Bintu, musammam yanzu da aikin binciken su ya k’are, Bintun ce ta zaunar da shi a makarantar da tuni ma ya dakatar da koyarwa, dan kuwa dai hakin su ya riga ya cimma ruwa a game da aikin su. Abin takaicin shi ne tsakanin sa da Bintu sai dai a aji, duk yanda zai yi ya ganta bayan aji ya gwada amma abu ya faskara, don kuwa dai Bintu gudun sa ta ke k’iri k’iri. Shi kan shi bai san meyasa ya kasa cire yarinyar daga ransa ba, amma dai yau idan har bai sa ta a idanunsa ba zai iya shiga damuwa. Gashi kuma yau lahadi  ko makarantar bai shiga ba bare ya ganta a aji. Nan fa wata dabara ta fad’o masa, ya tsinci kansa ya na mai murmusawa.

Ajiyar zuci ya saki yayin da ya bud’e idanu a hankali jin d’igar ruwa bisa fuskarsa sanadiyar iska da ta kad’o wani reshe zuwa cikin rumfar. Tashi ya yi zaune ya na mai duba lokaci, k’arfe biyar daidai, ya aje hannu inda ya tashi cikin azama ya na mai k’ok’arin zura takalmi cikin k’afafunsa. Kai tsaye ya  fice daga cikin lambun, ya bi ta farfajiyar gidan ya shige falonsa wanda zai sada sa da d’akin baccinsa. Cikin k’ank’anin lokaci ya sauya kaya izuwa farar jamfa da hula tare da farin takalmi. Ya gama fesa turaren sa mai kamshin gaske ya wuce cikin motarsa. Hankali kwance ya fito daga gidansa, sai gashi kan titin francophonie, kai tsaye ya nufi makarantar Soverign.



Minti goma kacal ya kai shi makarantar, Allah ya taimake shi ya had’u da Iya Dije a bakin gate ta na shirin fita kenan. Tsaida Ita ya yi, ya  nemi alfarmar ganin Bintu. Iya Dije da tun da ta ga Aisar da yamma haka, gashi ranar lahadi ta san banza ba ta kawo zomo kasuwa, ta yi kud’irin samun wani abu daga aljihun sa. Jin buk’atar ta sa sai ta yi hamdala cikin ran ta, ta na mai  gyara tsayuwa ta ce ‘’ai kasan yanayin dokar makarantar ne Malam, an hana d’alibai kebewa da Malamai musammam irin wannan lokacin da ba na d’aukar darasi ba’’

Duk da maganar ta Iya Dije  ta yiwa Aisar wani iri, jin ta yi amfani da kalmar ‘’ke6ewa’’ amma sai ya basar, ya na mai murmusawa ya ce ‘’ba ki fahimce ni ba Iya Dije, ba wai tsayar da ita zan yi ba, kawai dai sak'o zan bata, na ga fita ma za ki yi ko?’’ nan fa Iya Dije ta samu mafaka, ta amsa da ‘’eh wlh kasuwa zani, zan saro kaya duk da dai ba wani jarin arziki gare ni ba’’ ganin Aisar ya sanya hannu cikin aljihu jikin ta har rawa ya ke. Ilai kuwa sai gashi ya fito da kud’i CFA na gugan CFA, ba tare da ya k'irga ba ya mik’awa Iya dije ya na mai fad’in ‘’gashi ki k’ara kan jarin na ki’’

nan Iya Dije ta cafe kud’i saura kiris ta had’a da hannun Aisar, fad’i ta ke ‘’kai dai ba ka gajiya, madallah, yo ai in da yarda ai na yarda da kai, bara na kira maka Bintu Bala Mahuta, amma dan Allah kar ta dad’e ka ga dai ni fita zan yi’’

Aisar na murmushin nuna jin dad’i ya amsa da ‘’toh, ina nan kusa da ofishin malamai ina jira.’’ da azar6a6in jiki Iya Dije ta koma ciki ta na k'irga kud’in da aka ba ta.

Bintu na zaune cikin d’aki, kasancewar Gimbiya Binta ba ta nan ta je karatu,  itama  ta sami damar yin na ta karatun. Sanye ta ke cikin shigar su na bayin Sa’ayrasa dan ba ta isa ta sa kayan gida ba duk da dai yau d’in kowa ado ya ke yi. Sai ga Iya Dije ta shigo, kallo d’aya za ka mata ka tabbatar da farin cikin da ke tattare da ita. Ta na mai washe baki ta ce

 ‘’Bintu tashi maza ki biyo ni, Malamin ku ne ya ke neman ki, eh! Malam Aisar’’

jin sunan Aisar Bintu ta fidda Ido tare da fad’in ‘’Iye?’’

 Iya Dije ba ta damu da yanayin tsoron da ya bayya na fuskar Bintu ba, ita dai burin ta  shi ne ta kai ta ga Aisar ta samu ita ma ta fita,

ta ce; ‘’ke tashi mana, ni kasuwa zani kin ga dai yamma ta yi sosai, shida na yi ba lalle na samu shiga ba, kuma kayan abincin ku na sati zan kar6o’’

‘’Iya Dije dan Allah ki ce ba ki ganni ba’’ ta fad’a ta na yin rau-rau da idanu kamar mai shirin yin kuka.
Baki bud’e Iya Dije ta ce ‘’kun ji ni da yarinya, yo me zai mi ki da za ki sa ni yin k’arya da tsufa ta, na k’i na ce ban gan ki ba d’in’’

Bintu ta ce ‘’Iya Dije aradun Allah Gimbiya ta ce idan ta ganni da shi sai na lahira ya fi ni jin dad’i, ki min afuwa ki taimake ni’’

‘’wannan kuma ke ki ka sani, idan dai ba ke ki fad’a ma ta ba ina za ta san ma kin gan shi? Ko ta na nan ne?’’ Bintu ta girgiza kai alamar aha ah. ‘’toh maza yafa mayafin ki mu je’’ Bintu ta ce ai ba ta da mayafi. ‘’ai kuwa dai ba na tafi da ke ti6i ti6i da ke haka ba, budurwa kamar ki ki ce ba ki da mayafi? A garin na ku haka ki ke yawo?’’ Iya Dije ta tambaya ta na mai duban ta.

 Kana Bintu ta amsa mata da ‘’ina da su, su na gida ne Gimbiya ta hana ni zuwa da kayan gida’’

Cike da nuna Allah wadai da halin Gimbiya Binta, Iya Dudu ta ce "wannan shi ne  zancen 6ir in ji tusa,  menene amfanin hana ki ado ko rufe jikin ki ? Ke tashi mu je ko aran zani ne na baki ki yafa ko ma d'auko wannan d’an hijabin nan da ku ke sawa ki yafa, ai yafi babu kaka ta wajan uba’’ .
 Hakan ko Bintu ta yi, ta na magiya amma Iya Dije ba ta fasa jan ta ba su ka fito daga 6angaran d’akin kwanan d’alibai, tun suna wuce d’alibai wanda ke zaune farfajiyar wajan har ya zama tsilla tsilla kad’ai ake gani, musammam da ka baro sashin kwanan d'alibai su ka shigo farfajiyar makarantar. Ganin sun nufi ofishin malamai gaban Bintu ya fara fad’uwa.

                       ***
Wata baranda gaban ofshin malamai su ka hangi Aisar zaune kan kujera, ganin Bintu tuni wani farin ciki ya lullu6e shi har cikin ran sa. Da kyar ya iya jira su ka k’araso in da Iya Dije ta bar shi ta na mai yiwa Aisar kashedin kar fa Bintu ta dad'e. Ba tare da wata damuwa ba tun da ita dai ta cika jakarta da kud’i ta yi gaba ta bar Bintu da Aisar. Ganin yanda Bintu ta bi bayan Iya Dudu da ido, Aisar ya ce Bintu ko bin ta za ki yi ne?”

Da sauri ta mayar da hankalin ta gare shi, ta gaishe shi cike da girmamawa. Ya amsa a takaice tare da mata nuni da wata kujera da ke gaban ta sa ya ce ta zauna dan kar ta b’ata k’afar ta cikin ca6in ruwan sama. Ba musu ta ja kujerar can nesa da tashi sannan ta zauna, kan ta sunkuye ta na wasa da yan yatsun hannun ta, ita dai Allah Allah ta ke Aisar ya sallame ta ko ba dan Gimbiya da sauran d’alibai ba, ko dan sanyin iskar damina da ke kad’awa.

 Jin shiru be tanka ba ya sa ta yanke hukuncin tambayar dalilin kiran na ta, amma ko da ta d’aga kai, sai tsintar idanun ta tayi cikin na sa, ashe duk zaman nan kallo yake k’are mata. Da sauri ta k’ara yin k’asa da ido, ganin haka ya murmusa ya ce "Bintu gudu na ki ke ko?’’

Shiru ba ta amsa masa ba, ya k’ara da ‘’ya karatu? Ki na dai yi sosai ko? Ko da ya ke na ga kin ci gwajin da na mu ku sosai’’ kamar ya na magana da dutse Bintu ta k’i amsa masa. Be gushe ba ya ce ‘’daga wannan zangon zan dena koyarwa a makarantar ku, ban san me ya sa na ke fad’a mi ki ba, amma ina jin ya dace ki sani ne’’

Jin haka Bintu ta tsinci kan ta da fad’uwar gaba, ba ta san sanda ta ce "saboda me? Ba dai laifi mu ka maka ba ko?’’

kai ya girgiza mata sannan ya ce "yanayin aiki ya sa, amma inshaAllahu zan sa a maido da k'anwata makarantar nan kin ga sai ki sami k’awa ko?’’ murmushi Bintu ta yi wanda ke k’ara bayyana kyan ta, hakan ya sa Aisar fad’in

"dama haka ki ka iya murmushi?’’

sai kuma Bintu ta tsuke fuska, ta na shirin tambayar dalilin kiran na ta, wayar shi da ta hau k’ararrawa ta tsaida ita. Da ke wayar tafi da gidan ka(handset) be gama cika gari ba, hannun wane da wane kad’ai ake gani, waya ce kirar (Nokia 3310), dan haka baki bud’e ta tsaya ta na kallan wayar har ya d’aga ya kara bisa kunan sa, ji take da zai bata ta d’an kara kunan ta da ba haka ba.

Bintu ba ta dad’a shagala ba sai da ta ji ya ambaci sunan Barde, nan da nan ta manta da wani nauyin Aisar da ta ke ji, ta fara Allah Allah ya gama wayar.

Ta gani ya kashe ta ce "Malam dama kasan Yaremi Barde na Fabarusa?’’

‘’ Na san Barde, amma yanzu ba da shi na yi magana ba’’ sai da ya ba ta amsa sannan kuma mamakin yanda aka yi ta san Barde ya kama shi, be san sanda ya ce ‘’Yerima Barde ke? Ina ki ka san Barde ke kuma ki na yar masarautar Sa’ayrasa?’’ ya tambaya cike da mamaki.

Nan fa Bintu ta fara jero bayani cike da nuna gwanintar yan ajin su ma ba a barsu baya ba ta ce "ai rannan a aji aka yi hirar shi, ance shi ne mai kyawun duniya kuma k'asar nan kaf babu wanda zai gwada masa k'asaita, rabin yan ajin sun ta6a ganin shi, ni ma ina so na gan shi ko da sau d’aya ne a rayuwa ta’’

Jin kalaman Bintu tuni Aisar ya had’e rai, yayi k’icin k’icin ya fara fad’a "wato a shekarun ku har kun san ku zauna ku yi hirar samari ko? Ba ku san komai ba sai kula samari da karanta littafin soyayya ko?’’

"wallahi malam ba na kula samari ni ba yar iska ba ce’’ furucin Bintu kenan yayinda idanun Bintu su ka fara kawo ruwa, sai a sannan ta ankare da 6aran6aramar da ta yi na tambayar Barde, duk da dai ita ba da wata manufa ta yi. Ganin Bintu na shirin masa kuka har da batun ita ba yar iska bace ya sa hankalin sa kwanciya, wato kenan ba ta kula samarin tun da har ta masa wata fassara na da ban, hakan ya masa daidai har ya na mai murmusawa. Ita ko Bintu ta shi ta yi da sauri ganin wasu d’alibai sun fito daga d’akin karatu, ta ce malam dama karatu na ke Iya Dije ta ce za ka bani sak’o’’
Sai a sannan ya tuna fa ashe ba ranar makaran ta ba ne, gashi shi babu wani sak’o da ya kawo mata dama ganin ta kawai ya ke san yi. Amma gudun kar ta d’auke shi sakarai fakewa yayi da dama ya zo wucewa ne ta makarantar ya ce bara ya tsaya ya ji ta na karatu kuwa,  maza ta koma ta cigaba da karatun. Da wannan ta masa sallama, har ta na fad’awa cikin ca6i dan saurin kar wannan d’aliban da ta hango su gan ta tare da Aisar. Shi kuwa gogan na ta ko ganin su be yi da ke su ma d’in lab’ewa su ka yi domin su tabbatar da abun da su ke gani.

                           ***
Sai da Bintu ta k'urewa ganin sa sannan ya tashi ya nufi motar sa, ya gifta ta gaban wannan d’alibai da ke leb’e bayan wata yar katanga sam be lura da su ba har ya kai ga motar shi ya shige ya fice daga makarantar.

"kut yau kuwa za yi bantan uwa a makarantar’’ fad’in d’aya daga cikin d’aliban kenan wacce su ke Marry yayinda su ke fitowa daga wajan 6uyan su ganin Aisar ya fice. Su uku ne, kuma dukan su yan aji shida ne ma su mik’amin. Marry ita ce mai ruk’e da muk’amin horo, sai shedigyal da kuma mai kula da tsafta da lafiyar d’alibai, wacce su ke kira da Sikanti.
Marry ba ta gushe ba jiki na rawa tsabagen masifa ta k’ara da "wai ido na ne ke zagi ko kuwa Malam Aisar na gani da wata kwaila a makarantar nan?’’ Cikin Jimami Shedigyal ta ce ‘’ni ma dai abun nan ya ban mamaki, ki ga yanda mu ke bin sa ya na mana wulakanci amma ya rasa wacce zai bi sai Bintu d’iyar bayi’’ sikanta dan mamaki ta ma kasa magana. Marry ta d’aga k’afa ta doka k’asa cikin ca6ali, nan da nan zanin ta ya 6aci amma ko aji kin ta, idanun ta ya rufe, kana ta ce ‘’ba d’iyar bayi, ko d’iyar saraki ce yau sai ta ci Uban ta, za ta min bayanin dalilin da ya sa ta kyebewa d Malami, kut Malamin ma wanda na ke so dan uban ta? Yau sai ta lashi kashin b’and’akin k’asa dan uban ta Bintu ta ke kowa? Ta yanki tsiya!" ta wuce fuu, dama ga ta jibgegiya tabarakallah. Su shedigyal su ka rufa mata baya, kai tsaye sashin kwanan d’alibai su ka nufa.

                          ***
Bintu kuwa komawar ta d’aki ta tadda Gimbiya ta dawo tare da k'awayen ta, ko da ta tambaye ta daga in da ta ke sai ta mata k’aryar Iya Dije ce ta aike ta. Ta ci sa’a yan masifar Gimbiya ba sa kusa, hankalin ta na kan labarin da Zahira ta ke ba su. Can gefe Bintu ta zauna ta na mai mamakin dalilin da Aisar ya fad’a mata na zuwa ganin ta. Zaman ta ke da wuya ta ji ana kwala mata kira "Bintu Bala Mahuta dan uban ki sauko!’’

Ba Bintu ba hatta su Gimbiya sai da su ka kasa kunne su na jiran tsammani. ita kuwa Bintu jikin ta ne ya hau b’ari jin muryar Marry da gaba d’aya ya 6angaran d'akin kwanan d'alibai. Gimbiya ce ta kai kallan ta ga Bintu ta na mai tambayar ‘’yar nema me kuma ki ka yiwa wannan mai fasalin mazan?’’ Bintu ta kasa magana tsabar tsoro, nan fa su ka k’ara jiyo har gowar Marry ta na mai fad’an ‘’dan uban ki na ce ki sauko kimin bayanin wani malami ki ka kyebe a bayan aji!’’

Nan fa Bunti ta kware saboda firgici da tsoran maganar da Marry ta furta, inda Gimbiya, Zahira da Ruqayya su ka tashi tsaye a a tare, Gimbiya na fad’in ‘’ki tabbatar wannan malamin da ake magana akai ba Malam Aisar ba ne!’’

Can waje kuwa tuni d’alibai kowa ya fito jin shela da tonan siririn Marry, wasu ma babu cikakken sitiran arziki jikin su haka su ka fito bawa idanun su abinci dan kuwa sun san koma wacece wannan ta shiga hannun Marry ta kad’e har ganyen ta, musammam jin ance "ta kyebe da Malami."

"BINTU BALA MAHUTA! Ko ki sauko ko na zo na sauko da ke ta!’’ fad’in Marry ta na mai kumfar baki.