ARNE Part Four (4)

ARNE Part Four (4)
.
Da safe karfe 7.30 shiru faryal bata sauko ba  Hajiya mariya dakanta ta fito ta kama hangar dakin NATA don ta duba ta  Hangota tayi da karami. Coffee cup tana zaune da littafin Q/A na biology,  Mummy ena kwana,tafada fuskarta ba yabo ba fallasa  Ah,a rike gaisuwar ki,ena nice abokiyr gabarki a gidan nan faryal  Mummy kiyi hakuri,nifa ba haka bane kawae abubuwa ne kinsan fa muna final exams  Ke kinci gidanku, ki kalli tsakar ido na kimin karya? Ai ni nasan kina dawo wa dawuri fiye da ma normal school hours a da   Ki Fada min meye namiki kwana biyu kike kin sakewa a gidan nan dani  Wato salon ubanki ya dawo yace namiki wani abun ko?    Saukar da murynta tayi,tace mummy ba wani Abu bane...kawae banason kinasa baki a maganan mu da khalid ne  Khalid fa baida kunya,gashi baya girmama nagaba da shi Ke yi min shiru ,kaji maganan banza rike min tsuliya nayi kashi,  Eyeeee lallai faryal kin girma,..kece zaki Fada min halin mutum ko nice zAn Fada miki,yaushe kika girma kikayi hankali da zakisan mai kunya da marar kunya  Mummy wallhy bakisan halin khalid ba...nace kimin shiru faryal ta katseta  Look girl,yaron nan kusan dai dai yake da ubanki a arziki,ballantana babansa Alhaj garba  Nida nakeso soyyayarku ta daure ki huta nima na huta  Mummy nifa bana sonshi   Lahhh.  hai lahhh kaji min yarinya.me kika sani akan so? Faryal Ashe bakida tunani?lallai ma rashin hankalinki sai Dada bunkasa take  Toh ahir na sake jin bakin ki akan wannan magana   Kuma in kinason mu shaida juna agidan nan to kibani hadin kai,muddin nafada miki magana bakiji to zami samu matsala dake,INA fata ba da gunki nake magana ba?  
.
Cikin muryan kuka faryal tace naji mummy Tamike tafita....  Binta da kallo haj mariya tayi taja tsaki...wawiyan yarinya kawae zata jawo min tsiya inaganin arxiki  Waya ta dauka ta kira haj shafa ,bayan minti 30 sai gata ta iso gidan nan suka nufi ware house office na baban khalid  Yaune rana ta karshe a makaranta kowa na bakincikin rabuwa da juna anata faman Neman yafiya  Siyama CE ta dafa ta ,hey faryal   Dan yatsina fuska tayi sannan tace,wai meye ne  Dariya abun ya bata amma saidm ta dake,yayanki ne zaiyi magana dake tafada tana mika mata wayar  Da sauri karba ta koma gefe,hello faryal my sister,  Ko amsawa batayi ba saboda kukan dayaci karfin ta.... Faryal,faryal..yake Fada sannan ta samu tace Yaya zafar  Ohh my god waya taba ki haka faryal,kukan me kikeyi?  Fadan hakan dayayi ma yasata kara fashewa da kukan kamar ba jiya jiya sukayi waya ba  Cikin tashin hankali zafar ke tambayarta meya faru  Dan control ta yi dakyr cikin shesshekar kuka tace,Yaya zafar dan Allah ki dawo mana,I'm so tired nagaji da gidan   Dogon numfashi ya sauke ,yace haba faryal I called to congratulate you Yau ranar kammala schl amma kizauna kina kuka haka ?  Zamu dawo ai just stay put ok?   
.
A hankali tace ok ,nan ya dan dinga bata baki had ya mata alkwarin bata gift kafin dare  Dariya tayi tace nidai zanga ya gift zai taho daga England zuwa abuja  Toh zaki gani ai just be close by...  Haka suka yi sallama ya mika wa siyama wayrta tabar wajen  Zafar sis dinka har yanzu fushi take dani akan kamil,   Murmushi yayai yace kyaleta she wll soon forget that....   Bayan shigar mummy da haj shafa ware house said ga alhaji garba da khalid nan tafe suma   Da Sauri khalid ya taho wajensu,mummy har kin iso eh son  To muje ga dad dina Ku gaissah kafin ya wuce  Nan suka tashi suka isa Dad ga haj mariya mum din faryal ,she's one of the holders na company AbuZAYAL investment  Ohh nagane ,haj barkanku fa yagaya min yana zuwa gidanki ,matar alhaj abdallh koh? Eh ranka ya Dade suka Fada tare suna yake  Ahh bakomai ,em make them comfortable, ka kawo min takardun Nasu anjima  Wani farinciki ne ya lullube su gaba daya barin ma shafa da yanzu ne NATA business din zai samu wannan daman   Faryal ko ko bin ta kan mummy batayi ba dakinta ta wuni tana jiran surprise din da xAfar ya mata alkawari  Karfe 9 na dare taji ring alert na video call  Da kamar bazata dauka ba don' tunaninta bazai wuci khalid bane  Jin mai kiran yaki hakura da kira yasata juya a fisace zata danna  Chak ta tsaya ganin code din countryn daya nuna akan screen  
.
Ta nemi hawaye a fuskanta ta rasa a lokacin wani farinciki taji na ziyrtan xuciyanta  Da sauri ta danna ,masha Allah murmushin kawae taga yanayi inda ita kuma ta kafe shi da ido,kyw na musamman taga yayi gashi ya kara girma da kwarjini kamar badan 20yrs ba   Wani kishi ne ya tukareta ganin yadda yadawo dole mata zasuna binsa Nan hawaye suka fara silala a fuskrta  Angel.. .baki farincikin gani na ne?   Don't talk to me tafada cikin kuka   Murmushi yayi yace I know Angel,kimin duk abunda yadace nasan ban kywta ba da na kyale ta   Amma ai tasan da ita nake kwana nake tashi ko?  Bansani ba yay kamil,wannan wani irin rayuwace,u left me alone baka so na   a cikin fushi take ta masa masifa wanda shikaran kansa ya dena gane maanan abunda take Fada  Shiru yayi ya sa fuskan tausayi, sai hakuri yake bata  Da kyr faryal tadaina bori ta saurare shi Magana sukayi cikeda kauna da kewar juna  Ohh dama gift din yay zafar kenan,amma wallhy yaci nabashi kyawta  Dariya kamil yayi yace gaskiya kam... 
.
Ki kwanta faryal kinga past 12   Turo baki tayi zata sake sa kuka yace toh shikenan kinaso kar na sake kiranki ko faryal?  Ba nafada miki avunda abba yace ba  Da sauri ta gyda kai alaman Ah a....  Good girl,ki kula da kanki angel,for me?   Of cous yay kamil  and you too....   Haka har ta katse wayar badon son ranta ba ta sulale kan gado ta lumshe ido tana jiwo muryansa da fuskansa   Haka har bacci yayi a won gaba da ita   Washe gari kan dining suna cin abinci haj mariya mamaki ne ya rufeta ganin canjin yanayin faryal cikin dare zuwa safiya  Wayarta ne yafara ringing,ganin sauyin fuskarta yasa haj ta CE  Me haka faryal? Ki dauka mana Nan ta danna ta sa a kunne hello,  My baby,....I'm sorry jiya ba time ban Miki congrat ba  Angama schl saura akawo min ke ko? Batasan lokacin da tsaki ta kufce mata ba Nan ta katse wayar batare da tace komai ba  Waye wannan haj mariya ta tambaya Emm mummy khalid ne fa  Mtsw tashi kibani waje kar naci ubanki yr banzan yarinya  A fusace faryal ta wuce sama   Sallama Malm chief security yayi ya durkusa yagaida haj mariya, Yadai naganka da safen nan  Dama aika ne na kawo ma faryal daga Khalid Ohh ok to ajiye anan   Vudewa hj mariya tayi taga iv na graduation party musamman na faryal da cheque din 35million na kayan sawa da sauransu  Ware ido tayi tana danna ma faryal din kira  Ranar haka tasa ta agaba ita da haj shafa akayi shopping sharp sharp na designers aka gyra mata gashi aka mata make up   Bayan isha aka zo da motar gidan su khalid aka tafi da ita wajen party  Kamr zata fashe don'bakin ciki.wani zuciyan yace ta kira abba tafada masa komai amma wani yace tabari if not zata Shiga uku da haj mariya  Cikeda baki kala kala mata da maza harda yan uwan alhaji garba su uku  Iya tsaruwa wajen ya tsaru,siyama ma taci ado harta gaji da kyw,  Bayan an kammala yan ciye ciye da rawa da perfmance da akayi na shaharraen mawakin nan davido... 
.
Waje ya gauraya anata hidima  Nan MC ya bada fili ma khalid donjin abunda zai ce Wanda yayi dai dai da shigowar alhaj garba wajen   Nagode jamaa da kuka tayani farincikin wannan rana  tare da sister na siyama .muna gode muku da taya murnan kammala karatun su  Inaso nayi amfani da wannan dama na bayyana ma jama'ah  Sarauniya ta wacce nake so nake kuma muradin aure kwanan nan Bawata bace illah faryal abdallh ..yafada yana murmushin yake   Dum zuciyarta ya fara bugawa ga wani hasken da aka danna mata akai kowa  kallonta  Yau zaka gane kuranka khalid tafada cikin ranta tana mikewa zuwa Inda yake.....  Karban MiC din Tayi tace Nagode daka bani damar zuwa nan wajeen.domin kuwa nasanar da jama'a I'm not ur Queen in any way ni ba sonka nekeyi ba, na tsaneka,kuma har abada bazan taba dawowa matarka ba...   Ta wurga musu mic dinsu ta kama hanyar waje abunta  Da zafin nama ya mike zaibita wake  nan alhaji garba ya dakatar da shi ya ja shi zuwa ciki  Nan fa guri ya kaure da kace kace kowa na fadan albarkacin bakinsa  :
.
Calm down khalid,me haka ?   Kyaleshi dad I told him yarinyar batada class,sai wani huci yake kamar zaki  Da Allah malama kimin shiru karna FASA miki baki  Harara siyama ta visa dashi. .of cous khalid ba baki ba ma kill me if u want  Ena akan yarinyar da bata San kanayi bane  Don't talk to me like that siyama raina a bace yake yanzunann can't u see  Enough alhaji garba ya dakatar da musun nasu  Son ka kwantar da hankalinka no one dares me and win...duk abunda kake so a duniyan nan zaka samu I promise   Tare suka kalle uban nasu da ba alamar wasa a fuskan sa  Dad me kake nufi yarinyar da ta yarfa ni agaban kowa da kowa.   this girl has dissed me  in front of everyone dad tace bataso na after all I have been tru saboda ita  Kallonsa Alhj garba yayi yace khalid tell me kanasonta ko baka sonta  Enasonta mana dad,but I mean to teach her a lesson   Just live dat to me wannan tsakanina da iyayenta ne Daga Yau kadauka ka aureta an gama  Daka tsalle khalid yayi ya damke baban NASA dad are you serious  Tsaki siyama taja tafice abunta Yes my son .but ......  But what dad kafadi komai zan maka yanzun nan   Are you sure? Yes enajinka dad  Khalid i want you to live this country  Zan tura ka las Vegas   Kafin ka dawo I give you my words aurenka da wannan yarinya ba fashi  Come on go and think about it gobe zanji amsa  Dan shiru yayi kafin yace Yes dad,bakomai zan sameka goben  Good jeka ka huta have fun  Itako ko ajikinta kwnciya ma tayi tayi baccinta, ko bin ta kan haj mariya batayi ba  karfe 2na rana alhaj garba da khalid suna tsaye yace Son u have made the right decision nikuma zancika maka alkwarinka kafin kadawo Sannan kuma  Duk abunda na gindaya maka shi zakayi a Vegas kaji banason kuskure?   Yes dad Barin wuce kar nayi late zan kira ka in na isa  Nan sukayi sallama ya nufi sit dinsa dayake private jet ce  Daukar waya yayi kira mint 5  saiga wani bakin karkarfan mutun ya shigo enda yake  Mika masa envelope yayi yace masa ka nemo min komai gameda su  Angama ogah.....family photon Alhj abdallh aciki da cheque na rabin kudin aikinsa   Bayan wata daya,ba khalid ba labarinsa ko ajikinta don' itakam ma dadi takeji jin shi shiru  Kallon post din sa a Twitter yasa ta Jan tsaki...maye kawai Ai nayi maganinka  Ke,dawa kike magana ?
.
Mummy ,ba kowa tafada a dan tsorace Kwace wayar tayi taga suna khalid ne akan tweet din  Wani mugun harara ta watsa mata  Tashi ki fice min nikam ubanki na kira shasha   Da Sauri ta sauka abunta don'tta matsu ita ma ta tafi makaranta tabar mummyn data sata agaba tun data ji labarin abunda yafaru tsakaninta da khalid ranar  My princess baki Fada min Schl din dakike so ba  Charab haj mariya ta karbe magana  Alhaj ba enda faryal zataje,asata kusa da gida kawae ena kallonta  Karamar yarinya kamar faryal har sai ka tambayeta ena zataje karatu  salon tahadu da miyagun kawaye a dagula min tarbiyan ya....gaskiya alhj  ban isaba bazan iya daukawa ba in wani Abu ya faru da faryal Ta Fada tana fashewa da kukan karya  Sake baki faryal tayi tana kallon mummy Data dage tana share kwallan ban mamaki  Haba mariya wannan ai bakomai bane,muna da hakkin yin hakan ma Amma yanada kyw Dama aji zabin NATA  Ah a nidai banyarda ba yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi halayensu ba  Kawae tayi Turkish university ya isa tana zuwa tana dawo wa  Me kikace princess,shiru faryal tayi ji take kamar ta rusa ihu awajen amma wani mugun idon da haj ta kalleta da shi  Ya sata amsawa ba shiri,eh abba na amince  nan ta shige ci‬:
Ogah Hajiya mariya ta iso, CE mata ta shigo  nan aka kaita har Inda yake zaune shikadai  Alhj an wuni lpya? Zauna mana Hajiya ai nan kamr gida ne  Itadai gaba daya tsorone fam cikin ranta haka dai ta dake ta zauna  Nan aka fara jera ma Hajiya mariya kayan alatu na abinci da shaye shaye wanda akayi musamman dan ita Bismllah Hajiya  Cikin mamaki ta zauna tare dashi akan dinning  Alhaji ena fatan lpya dai ko? Ahh ,dan gyran murya yayi yace bakomai hajiya  Wata alfarma ne nake nema awjnki Kiyi hakuri ban nemi mijinki  saboda naji yanada tsaurin ra'ayi sosai kuma banason na takura   Koba haka bane haj?   Dan shiru tayi tace ,hakane Alhj abdalla baida saukin kai sosai amma ba halinsa bane na asali  Amma Alhj bangane alfarman dakake nema wanda baishafe Alhj ba ya shafe ni  Kwantar da hankalinki akan mariya maganar yarki CE faryal Inaso kibani tabbacin Dana Khalid zai aureta shikenan   Ena miki maganan nan a mtsayin business deal ne  Ba inaso na baki doka bane   Ku mata kunsan yadda kukeyi  da yaran Ku Kin fahimceni?  Dan dariya tayi,tace haba alhaji harka tsoratar dani   Wannan maganan ai mai sauki CE Kabarmin komai a hannu na faryal batada mijin da ya wuce khalid  Naji dadin zancenki Hajiya mariya,nikuma namiki alkwari zaki ji dadin wannan harkan muddin burin Dana ya cika  Washe baki haj mariya tayi aranta tana hamdalan  Business da alhaj Garba ainko wani iri ne zanyi ballanta wannan Riba biyu,tab  Kafin Hajiya mariya ta fice a gidan sanda aka mata jaka daya na dollars acikin booth din ta hade da wasu pleasantries  Faryal kuwa ana faman jigilar makaranta ta sami fannin medical physiotherapy  Tsaye yake a bakin titi ya rufe fuskarsa da bakin sun glasses Dafa shi akayi Adan asirce, ya juya ya biyo shi suka Shiga ta baya Inda ba jama a sosai  Mr kamil I'm glad this is the last piece of information  I will be giving you...look man this shit is crazy and deadly.  The police...... Shhhhhhh    I know thanks Jordan,heere is your pay up Nan ya mika ma baturen nan envelope ya juya ya nufi gida  Alhamdulihh dukannin vayani danake nema naga ma samu ,saura na fara binsu daya bayan daya don nayi alkwari  Sai na ruguza alamarin duk wanda ya ke da hannun aciki ruguza rayuwta Dana iyaye na   Nan ya dukufa aikin bincike  da kyau yakaranta file din kowannensu  Baisha wani wahalan sarrafa binciken NASA saboda kamil ya gabata fannin ilmin sarrafa computer  kota wani hanya  Bayan hour 4 ya fito daga sallah ishai_ nan ya cigaba da bin file din dayake downloading Ai kuwa yana tabawa yaga download completed.... Da hanzari ya zauna ya fara karanta wa  Acikin su barayi shidan mutane hudu sun Riga sun mutu wanda duk ta hanyar kisan haya (assassination) ne  Daya shine shaharraren dan siyasa ta kasar burtania da jamian tsaro suka kai shi prison sakamakon daukar fansa da wata yarinya  tayi akansa bayan ya raping dinta ya kuma kashe mata iyaye  Case din da yafara gani a news  Dan jingina kansa yayi yace dayan yana las Vegas amma dan Nigeria ne  Shaharren dan cacar casino ne....wanda kudi ma daya gansa sai da ya Sara masa...iya dukiya ya mallaka a rayuwarsa baisan ma adadin su ba   Sai dai tsoron tsananta bincike yasa yake harkokinsa a asirce  Babban matsalar shine bani da cikaken sunansa ...amma na tabbata shine gunner wanda ya so ya kashe ni da abba...  Yana cikin nazarin  ne alert ya shigo computers a Inda yayi hanzarin dubawa  Tracker daya sa ne  ta gwada masa present location na gunner is abuja...Nigeria Address ya fara kokarin dubawa amma yaga access denied   Ohh what now,ya zanyi na gano sa? Gashi hotunar su na da ne a net ko yanzu ya kammanin su Yake oho Dan tunani yayi can yace Yes akwae tattoo but ya zanyi na ga tatto bayan a gefen kirjin su yake  Haka ya hakura yA kwanta da tunanin abun a ransa....
.
Haka kamil ya cigaba da binciken sa batare da ya sanarda kowa ba,  Sai dai haryanzu bai samu cikakken vayani akan wanda ya rage yake kuma nema ba  Bayan shekara biyar gidan alhaji abdallah ba masaka tsinke yau kusan sati aka dauka ana tsare tsaren gidan domin dawowar su zafar da kamil   Musamman Hajiya ta shirya abinci kala kala tasa kuma aka zanxa tsarin dakunan  su  komai da komai sabbi aka musu barin ma zafar datake ganin yanzu ya zama cikakken namiji zai hau kan harkokin dukiyar mahaifinsa  Da yamma karfe biyar  faryal dake neman cika shekaru 20 da haihuwa ta sauko cikin wata Riga da skirt na material baby pink mai ratsin silver stones ,ta parking dogon gashinta  sai dai wannan karon sake shi tayi jelar ya Fada har gadon bayanta  duk da Light make up ne a fiskarta amma tayi kyw sosai sannan ta rataye mayafinta putchia pink da takalmi da jakar vine a hankali take takowa zUciyanta fal da farinciki    Ke wallhy zaki sa muyi latti, nafiso Dana yafara sauka a idon mummynsa  haj mariya tafada tana kokarin turata gaba zuwa mota  Kamr baza akai airport ba haka kowannen su yakeji,  5pm aka sanar da saukan jirgin Dubai, kasa zama faryal da haj sukayi sai hange hange suke  Abba kuma hamdala kawae yake  yarana sun iso insha Allah  Kusan Rabin mutane jirgin sun sauko amma shiru ba zafar,da kamil   Jitayi an damke ta ta gefe da Sauri haj mariya ta juya ido hudu sukayi da zafar wanda ya sauya ya dawo tamkar balabe suits ne ajikinsa farii da bakin Riga ta ciki mai dogon hannu  Mummy yafada da karfi, wani farinciki ne ya lullube hj mariya tuni ta rungomu sa tana dariya aida gudu faryal ta karaso ta kankame shi itama dukansu uku kamar bazasu sake juna ba  Abba tsaywa yayi yana kallonsu cikin sanyin rai da hamdaln ubangiji  Karasawa yayi wajen nan zafar ya fashe da kuka yayinda yafada jikin abban nashi  Shima alhaji. Daurewa yayi amma yayi kewarsa sosai musamman ma da tunda suka fara shi baije Inda suke ba  Ina kaamil abba ya tambayeshi,yana........
.
  Baiko karasa naganar NASA ba .....nan ta hangesa yana tahowa jaka ne a hannunsa yar karama kamar brief case  Zaro ido waje haj mariya tayi tana mamakin da kokwanto anya wannan kamil ne?   Sam ya sauya mata daga kamannin da ta sani saboda inka gansa ma zaka dauka dan gidan wani sarkin larabawa ne,farar designer jallabiya CE fara kat a jikinsa ya nade bakin sumansa da ja da bakin hularsu haraami...bakaramin kwarjini ne ya bayyana tattaree da shi ba  Suman tsaye faryal tayi don' harga Allah son shi da tsoron shi Taji ya kamata a take   Da murmushinsa ya tinkaro abba kamr bakomai aransa..abba na kai hannunsa don' ya tarbosa nan ya Fada jikin abba ya fara kuka kamr yaro karami Har cikin zuciyar sa yakejin son kamill din  Kamilu Ashe baza a girma ba yafada yana dagosa   Abba ,nayi missing dinku sosai,. Dan murmushi abban yayi yace,muma haka son I'm proud of you guys  Naji dadin sakamakon Ku dukka,   Mun gode abbah yafada yana juyawa  Murmushi yayi ya dan rusna gaban hj mariya ena wuni hj,   Hajiya mariya kam tsaywa chak tayi tana  kallonsu itade har yanzu bata yarda shidin bane   Wani bakinciki taji ya tokareta a lokacin, da kyr ta furta lpya tana yake   Haka nan dai aka hakura aka tattara aka koma ta gida   Isarsu keda wuya kowa yanufi dakinsa yayi refreshing ya sauya kayan jikinsa  Wani sabon wankan faryal tayi itama .tubarkallah kowa yafito Ra's  Ranar tamkar kwae haka ake tarairaya su a gidan abinci kam sanda suka gaji dan kansu suka bari  Allah Allah take tasamu dama ta gana da kamil domin gani take kamr baza su hadu ba      
.
   Wayarta take ta nema bata gani ba,gashi kusan karfe 11.30 na dare   duk hankalinta ya tashi saboda taso tayi amfani dashi ,musamman ma da ba abata dama sun gana da kamil dinta sosai ba  Toh ni waya dauka min phone tafada ranta a dan bace  Kodai na manta a palour ne,barinje dai na duba Tsaki ta danja ta bude kofar dakinta ta nufo waje  Kan stairs tagansa zaune a bayan coriidor na  fannin  gurin haurawa sama  Kansa akasa alaman waya yake latsawa  Murmushi tasake aranta tana cewa wow ga abunda na ke nema anan ashe   Nan ta cire takalmnta tafara saukowa a hankali  zuwa wajensa  Bai lura ba Hannun yaji a kan idanunsa an kullesu gam,sai dai kamshin turaren ta da laushin hannun yasa shi fahimtar muradin ransa a wajen  Kamu daya yama dan hannayenta ya zare su duka ya jawota gabansa tana fuskrtan sa  Zaro ido waje tayi tace what! Dama kaine ka daukemin waya koh?  Wayace ka sacemun wayata ,ai baka damu dani ba, bayan ko kira na baka sonyii da katafi,ena kaaje chan ne ka sa mu wasu ka mance da ni ? tafada fuskarta ba alaman wasa sai wani murmurdaa vaki takeyi tana hararsa   Dariya sosai ta basa yadda ta Dage tana masa Fada kamar dagasken satar yayi  Mikewa tsaye yayi yazo dap Da ita ,tsit tayi don' ita har yanzu kwarjinin dake tattare da shi na sata taji kamar bazata iya kykwan tsayuwa agabansa   ,murmushi ne mai dauke da sakonni kala kala na kewa da kauna  A tare zuciyarsu ke bugawa yayin da gaba daya sun lume cikin kallon idanun junansu....
.
A hankali takai hannunta kan fuskrsa mai haske da laushin tabawa....  Shima a hankali ya kai bakinsa kan hannun nata hancinsa na gogan fatar hannun nata a lokaci daya  Kamar kar ta bude ido takeji ,aranta cewa take in mafarki take bazata farka ba  Iska taji ana hura mata a fuska , a hankali ta bude idanunta da suka fara sauyawa   chak ta ci karo da narkakkun nashi idanun sa daya kasa daukewa akan ta  Zuciyarta ne ke tsananta bugu,numfashin ta na nemar canza salo, Dan girar sa ya daga ya tabe baki yana murmusawa  Hmmm Ta biyoni ne ko ? Marar kunya harda cewa na sace mata waya   Turo baki tayi tace ni wayata zaka bani    Ga wayarki hajiya ,kar asake karo min laifi Gwalo masa ido tayi sannan tace Waya kunna maka abunda na rife da password  Ohh kin manta ba abunda za'a iya kullemin Yanzu? Nida abuna ma wazai hana ni budewa Cikin tsokana yake cemata   Na duba ne Dama naga rivals dina da akamin bana nan yafada yana dan satar kallonta   Dariya tadanyi tace,ina ka gansu? Ai sai kabani wayarka nima naga yan matar naka na chan masu hanaka kira ta  Kuma dama da ka dawo ko oyoyo baka Min ba tafada a dan shagwabance  Dariya yayi sosai kafin yace oyoyo? angel katuwa dake?da CE miki akayi ke baby CE da zan miki oyoyo?  Daure fuskanta tayi tana kananun magan ciki ciki  Nice ma zaace ma katotuwa koh  Mekike cewa ne katuwa,zoki karbi wayar toh tunda zagi na kike a zuciya Yafada yana kallonta yana murmushi   A fusace ta juyo zata nifi hanyar steps wai a dole taji haushi   I'm sorry ruhi na yi hakuri  Sassanyar dadaddar muryansan ne ya dakatar da eta  Nan ta ja ta tsaya tana kallon karasuwarsa Inda take  Jitayi ya rungumeta tsam ajikinsa i missed you ruhi, bakisan yadda nakeji ba ne kawae  Some words are better left unsaid   Dan dagota yayi ya nuna mata screen din wayarsa Hoton tane tsaye ta dafa glass door na airport dazu da suka fita  Dazun Dana ganki a airport naso ace ke zan fara  sacewa ba wayarki ba kin kara kyw angel, Hope dai ba a dama mun ke a schl din kun nan  Dan turesa tayi ta jingina kanta akan stairs Ai nikam ba cewa nayi naga ma fushi dakai ba.5years fa tafada kamar zatayi kuka  Shhhhh haba ruhi na nasan nayi laifi amma kinsan i need to fulfil abba s promise ko   Kema kinsan kina tareda ni kowani lokaci, in har zan manta dake Ashe zan iya manta dakaina kenan   Hannu ta mika masa ya karaso kusa da ita Kara kankame shi tayi tanajin yanda ya sanyaya muryansa yana cigaba da magana a kunnenta    Shiru tayi ta kasa magana sai lumewa takeyi ajikin nasa Shikuma ya Daura kansa a kafadanta  Ehm uhmm sukaji abayansu da Sauri ta sake shi duka suka maida kallon su bakin stairs   .
.
   Kaga  blue moon lovers "dare yayi aje dai akwanta  Wani kunya ne ya lullube ta da Sauri ta rabe jikin stairs da yayi hayar cikin gidan  Wurga masa hankerchif kamil yay yace Kaifa wallhy kasamin ido zafar,   Da Allah dakata malam "kace zaka zo lovey dubey dinka kabarni enata jiranka a dakin ka ,  Ba bacci kakeyi ba,na dauka tare zamu kwana ai,shyasa na barka  I missed you fa bro,meyasa kataso? yafada yana kwale masa baki   Yimin shiru da Allah"' kasan ma wadda kake fadan wannan ai .... endai bai isheka ba ne ai sai kajira gobe ka karasa fada mata Kar ka rude ni  Dariya suka kyal Kayle dashi suka nufi da kin Kamil din tare  Bayan sallahr asubahi abba ya umurcesu da su koma bacci su huta ,gaba daya satin ya basu Hutu su rabi gida kowa ya sake kafin aje next plan  Yan uwa da abokan arziki haka suka dinga Turin shigowa ana musu maraba su enna salima da su kawu kabiru da matansa  Mariya haka yaron nan yadawo? Ni na dauka balarabe ai kuka samu tacan kasashen  Kedai bari shafa,Kudi wasa ne? Kudi kuma me kike nufi kamil din yayi kudi ne    Hmmm ai sawa nayi adinga samin idon  Akansa.  Kinsan ba bazan sake alh ya dinga barnatar da dukiya ba  Nan ne naga achievement din sa kala kala da awards kuma wallhy kudi yake caska a hannun turawan nan bana wasa ba Kinsan fa ya mugun kwarancewa a ilimin sanin computer  Ni abunda ya tsaya min awuya ma shine,yanzu akwae companyn Samsung galaxies dasuka bashi contract zaiyi musu designing phone tracker na sabon tsarin zamani .....  Eyeeeeeee toohhhhh Me kuma wannan din toh mariya  Kee shafa wallhy in sukayo signing dinsa to fa ya tsalleke wallhy Kamfanin wayace fa?
.
Kikasan adadin mutanen da zasu saya wayar   kinsan bakaramin riba bane fa sai dai kiji ana kirga shi cikin billionairs nakasan nan kwanan nan  Dafe kirji shafa tayi tace dan Allah?  Shikuma dan namu fa?     Ehh kinsan yanzu shi zaina lura da harkokin mahaifinsa   amma ba nan ta tsaya ba shafa,so make nima na Daura zafar kan kamfanin da alhaji garba ya mayar karkashi na "GG investment'  Bani mu kashe kawata gaskiya kanji na ja mariya  Ai na dauka zaki sa ido ne Karen jeji ya wuce ma gida gata  Toh alhamdulihhi ai ko naji zance......nifa tsoro ma yaron yafara bani sai kace dan aljanu  anya alhaji ba gamo yayi ba da xuriyan aljanu?  Ke da Allah ,shafa ni ba wannan bane yanzu ya za ayi da Maganin khalid dan gidan Alhaji garba?   kinsan fa muna kan cin rabashe har mun fara giniga  da dukiyar Alhj garba   Uhmmmm hakane  Kawata,toh me make ciki yanzu   Gashi shima ance sati mai zuwa zai dawo kankat ya gama karatunsa a waje  Dan shiru shafa tayi kafin tace  Ai bakomai bane wannan mariya,ko eta faryal din tana da wani ne?   Haba haba wani,, nida na dau alkwari zanba khalid ena zancen barinta da wani   Uhm uhm mariya Ina fatan dai kina aikata abinda nake gaya miki akan ma nemartan dai  Eh shafa duk sun tafi na koresu bakowa yanzu  Amma kinsan meye Sam nakasa gane me tsakanin faryal da kamil tunda ya dawo fa  Eyeeee kaamil kuma? Oh Allah ana wata ga  wata  Kamr ya mariya Ban fahimce ki ba  Kawae naga yadda take shishige masa ne abun yana daure min kai wani lokaci   anya yaran nan ba soyyaya suke a boye ba  Ke zaki tsaya tamabya ne,ai bincikowa zaki yi        kinsan bamuda mafita a hannun Alhaji garba muddin wani matsala ya kawo khalid ya rasa faryal    Bayan sati biyu da dawowarsu kowa alhaj ya Daura shi kan companyn daya kamata ya kama aiki  Duk da rashin samin lokacin da kamil da zafar suke fama dashi "faryal Sam ta dena bin driver inzata schl  haka take jiran  kamil yakaita sannan su dawo tare  Ranan jumua da yamma Siyama CE zaune a falon ita da haji mariya suna gaisawa         kicinkicin taji alaman Shigowar su faryal  da kamil yasa ta mike ta CE ma siyaman toh bari na dubo miki shi zafar din ko   Don kuwa har aranta dadin juyin mulkin nan taji  zata hada zuriya da alhj garba ta da, ta ya... Toh mummy siyama tace tana duban kofa dake akejin motsin tafiyar Kamil ne yafara kutso kai ciki  Ai ko batasan lokacin da ta mike tsaye ba zuciyarta na Neman zaucewa ganin yadda ya sauya kamanni  Arrrmour Kaine wannan? Tafada tana nuna sa da hannu    Shiko murmushi ya jefe ta dashi yace,      siyama kenan u look great girma kenan Yafada cikin tsokana  Mutsininsa yaji anyi da karfi sanda yayi ouchchh ....angel  Ni mu wuce na gaji fa tafada tana narkewa ajikinsa  Tabe baki siyama tayi aranta tana cewa,,,,,   hmm yarinya da ba don ba don' ba wallhy saina dawo da tsohon zuma inga tafadin ki  Ana cikin hakan zafar ya tinkaro zuwa wajen   Bye siya talk later " OK kawae tace tana maida hararan da faryal ke fa man binta dashi  Hey yan mata na zafar ya Fada yana murmushi ,da gudu ta zo ta rungume shi dama itakam gwana  CE.  Zama sukayi tare suka cigaba da hirar suu   Itako farya tunda suka haura sama take kana nan magan ganu  Nikam wai fushin na meye ne haryanzu faryal?  Bakai bane? Tafada kamar zatayi kuka  Ni? Mena miki ohh Allah yanzu fa muka shigo  Ok baka SANI bako Tafada tana ware idonta waje,,,,, Yeah tell me ko na tafi na barki dodo ya cinye ki  Da Sauri tace Ai gwara dodon ma akan wanda kake wani CE ma ""siya u look great, girma kenan c yh ltr " tafada tana kwaikwayon maganansa   Dariya sosai tabashi abun ya matukar birgesa yadda take shake muryanta    Ita kuwa kuluwa ma ta dada yi ta juya zAta haura sama   Jawo ta yayi tsam tafada jikinsa   A hankali ya sauke murynsa yace ......angel am sorry banace miki ke kadai bace a duniyan ya mace a ido na Koba kiyarda bane?  Danja tayi daga jikinsa ta Dago kanta tace naji amma ni wallhy ban son tanace maka amour ka Fada mata   hannunta sarke a cikin nashi tana wasa dashi  Faryal.? Taji ankirata da wani murya " gaba dayan su sanda suka razana  Me zan gani haka?  Kinada hankali kuwa   Ki wuce ki barnan kafin naci ubanki tafada a fusace   Enda itama faryal din ta haura sama da sauri ta nufi dakinta  Wani harara ta watsa masa ta bi bayan faryal din 
.
   Banko kofar haj mariya tayi" Cikin hanzari faryal ta juya tace,, Mummy ... .ki min shiru dan uvanki,wani uban kike masa harda wani rirrike masa hannaye  Ohhh lallai fa,,,, wato shiyasa  kika nace yadinga kai ki makranta don' kusami filin kuna shagalin Ku ko?  A'ah mummy tafada cikin rawar murya  To Fada min meye a tsakaninki da shi ........    kinsan Hali na sarai zan gaya ma babanki komai daga ke harshi Ku gane kuranku agidan nan  Mummy dan Allah kiyi hakuri,wallhy ba wani Abu bane  Bazaki Fada ba kenan? Kuka faryal ta fashe dashi  Mummy INA son shi ne,shima yana so na  Tas taji mari a fuskanta  Kalleni nan faryal,    Yau yazamo miki rana ta farko kuma ta karshe da zaki furta kalman so tsakaninki da wannan yaron  kinji ko bakiji ba? Gyda kanta tayi alaman eh tana khannunta dafe da kuncinta  Ficewa haj mariya tayi tabar ta tsaye a wajen Sulalewa kan gado faryal tayo sai kuka kawae takeyi ba kaukawtawa  Da safe alarm din sallahn asubahi ne ya daga ta    mikewa tayi ta janyo wayarta hade da ware idn ganin miss call da texes da kamill ya jera mata     Murmushi tadanyi kafin ta sauko ta Shiga bayi  Wanna tayi hade da alwala ,kafin ta tura msa sakon gaisuwa  kamar yadda ta saba  Baifi Minti 2 ba sai ga shigowar kirarsa  Sallama tayi cikin sanyin murya ,shiru yadanyi jin yadda muryntar yake ratsa shi  Haba Ruhi na kinsa har nabi nakasa bacci"mai ya hanaki daga wayata jiya ?  Langwame fuska tayi kamar wacce take gabansa tace Twin soul bacci ne ya sace ni fa  Oh alhamdullhi,na dauka ko akwai matsala ne naga kamar mummy na fishi da mu  Uhm bakomai twin sou l Barin shirya na fito mu tafi ko  OK ki shirya din..  yafada yana katse wayar  Mikewa tayi tsaye a ranta tana cewa' mummy sai dai kiyi hakuri bazan iya rabuwa da twin soul ba nikam   Yanzu nake jinsa,   Karfe 5.na yammacin asabar. Laraba mai aiki ta shigo , Faryal ana Neman ki a falourn mummy  Batayi wata wata ba ta fice  ta nifi  hanyar site din haj mariya   da sallamarta ta shiga  Zoki zauna faryal khalid ne     haji mariya tace tana kmaida kallonta kan faryal din  A take ta murtuke fuskan nan kamar taga mutuwarta     Sannan ta zauna a takure batace uffan ba  Toh my son bari naje ciki ko?  haj ta mike ta nifi kasa  Wanda yayi dai dai da lokacin Yana kokarin saukowa shima tagansa        kai zo nan tafada da kakkauran murya tare da hade rai dan risinawa kamil yayi ya CE haj ena wuni?   Rike gaisuwar kamil,bana bukatar gaisuwan munafuki mai neman lalata yara kanana,,,,,  Dan shiru yayi baice komai ba  Nidai INA maka last warning,    kar na sake ganin ka kusa da yata faryal idan ba haka ba kaida wallhy kai da alhaj......   Ayi hakuri Hajiya   Ko kallonsa bata sakeyi ba tafice abunta  Wani shuumin kallo Khalid Kevin faryal din dashi  Baby I'm speechless..... kinga yadda kika kara kyw kuwa   Shine bazaki zo tarbana ba    I know kinsan zan dawo jiya.    not even a call or TeX tunda natafi  Dariya ma ya bata,khalid am not sure Inda ni kake magana. Tafada fusknta a mirtuke  Ena ruwana dakai dazan maka wadannan abubuwan pls?  Hhhh baby kenan,kina nan yadda kike har yanzu   I tot kin girma yanzu zaki bar yaranta and face reality Nidin nan fa mijinki ne kwanan nan "meyasa bazaki fara biyayya ba uhm baby    Hehehe wani shewa faryal tayi " kace me? Su mijii manya  Lallai tab.... Amma bada ni ba ,        and not even in your wildest dream khalid     Mikewa tsaye faryal tayi tana kallonsa tace    I belong to someone else shi ka dai , and u knw what? Ka kwantar da hankalin ka khalid he's better than you  Ke Faryal ,,,,,ya kirata da kakkauran muryansa   ,ke har a tunaninki akwae wani namiji better than me ne?     Kinuma min shi go ahead girl uafada yana kokarin nufota  Niko zan miki alkwarin. tabbatar miki that khalid GARBa is the only MAn for you  Mtsw sai kayi kuma,all you can brag abt is riches, you disgust me khalid....tafada cki ciki        Ni zan tafi tafada tan kallon waje    I'm stucked here khalid sai anjima tafice  Faryal,faryal ......
.
Yake kira ko  ta juya abunta    Dun kule hannunsa yayi yana furzar da iska a baki "  ya fice     Ko sallama baiyi ma kowa ba ya nufi hanyar waje,  Karo suka yi da kamil dake kokarin shigowa cikin gidan    Dada daure fuska Khalid din yayi    Haka suka wuce tamkar basu San juna ba      domin shi khalid Sam yaki jinin ganin kamil a fuska       Har cikin ransa yakejin ena ma ace Yau kamil ya mutu yabar duniya  Wajajen karfe 8 na daren ranar A hankali take tafiya harta kai bakin garden na back yard,              zaune yake yana danna dannensa shikadai  Farar riga CE  sanye ajikinsa da farar three quarter sosai yayi kyw " Sai da ta tsaya ta gama kallonsa kafin ta karaso  Twinsoul,ta fada tana kokarin zama tagaban sa,      Just in time Angel,I'm so happy to c you" kamar kinsan kece araina yanzun   Murmushi tadan yi tana kallonsa Riko hannunta yayi yace ruhi," meyafaru jiya? mummy tamiki Fada bazaki Fada min ba  ko?  Dan ja da baya tayi tace What ? No kawae ta CE min .....uhmm emmm" tace.....  Girgiza mata kai yayi yace uhm uhm ,kar kimin karya ruhi,just tell me   Kokarin kwakulo hawaye takeyi,tace twinsoul,idan nafada maka zaka dena bari na INA zuwa nan kullum  Gashi kaga tahana ni binka schl yanzu ...I don't want us to be apart"  nikam bazan iya ba  Ok Dama ita ta hanaki bina yanzu?   Ehhh tafada a hankali Amma kamil.... Shhhhh faryal kinsan bazamu saba dokan mummy bako,  Aiko fashewa da kuka tayi,tanacewa Dan nafada maka ko ?  Nooo angel c'mmon,     look idan baki bar kukan nan ba ba abunda zan Fada miki yanzu  Hannunshi yasa yana share mata hawayen yana cewa'.   stop you're wasting your precious tears ruhi,    ure too special to shed a tears ""na tsani kukan nan naki  Dan tura baki tayi tace toh ni kafadamin ya zakayi dani,u know I can live witot seeing you  OK fine,ZAmu na haduwa a schl  kafin a tashi ko     Uhm said wanne kuma tafada tana kallonsa     Shikenan ruhi ,for now  Yarfa hannunta takeyi tana cewa No,baza mu na haduwa a gida ba kenan ko me?  Yes ruhi,bana son kisami problem da mummy  Amma insha Allah na miki alkwari I will fight for us,zan tabbatar mata I love you and I wanna spend the rest of my life with you  Com"on smile ruhi.... Murmushi tai tana kallonsa ,a hankali ta furta me too twin soul,  Toh come let's get to bed kije ki kwanta kar mummy ta ga baki nan  Ok tafada tamasa peg a kuncinsa, Shima mayar mata yayi a goshinta sannan ta wuce ciki