ARNE Part Five (5)

ARNE Part Five (5)
.
Haka rayuwa ta kasance tsakanin faryal da kamil sai dai su hadu a waje amma ba gidan ba    Domin kuwa run ranar haj mariya ta sa ido sosai akan kowanne daga cikin su            Inaso ka bincika min waye saurayin faryal a garin nan""" khalid ya  Fada ma guard din sa guda daya dake tsaye cikin office dinsa  Ogah me za amasa in angansa,?  just get his name da enda yake kabar min Sauran  Ok sir yafada ya fice " Sake daukan wayarsa yayi ya cigaba da jera  mata miss cols din da  taki kulawa tun tuni  Mikewa yayi ya ja tsuka   straight ya dosa hanyar makarantr su,      Bayan tsawon nemanta dayayi bai sameta  Dan gefe ya nema ya zauna ya jira ko zata fito don' an tabbatar masa da bata tafi gida ba Daga nesa ya ganota tana tsaye tana waving kamil da har ya kusa ficewa a haraban schl din  Minti daya bai kara a zaune ba ya mike ya Isa wajen, Cahkwamota taji anyi wanda yasata juya wa a firgice,.  Ke dan ubanki kifada min waye wannccan kazami waywan da kike kulawa?  Tas yaji an wanna masa mari  Kul nasake ji. Sunan ubana abakinka,mahaukaci kawae Ta bishi da wani mugun harara ta wuce abunta  Kamo hanneyenta yayi da karfi ya murdasu""" kika mare ni faryal yafada fuskan sa a damke "    Kicin kicin din kwace hannunta tafara yi ga tsoro da yagama lullube ta  Ka sakeni khalid you are hurting me   Anki a sake ki ,come with me yai zan koya miki hankali yafada Yana  janta har cikin motar sa ".  kulleta  yayi ya nufi hanyar fita shima  Kuka faryal take tana dukansa amma ko ajikinsa,  Har sanda sukayi nisa kafin ya tsaya,kashe ac yayi sannan ya dago fuskarta da ya gama jikewa da hawaye  Khalid dangirman Allah ka maida ni gida,  Wani murmushin mugunta yayi,not untill kin Fada min akan wani wawan ne zaki mare ni?  Idan ba haka ba zan koya miki hankali anan,  yafada yana kokarin kai fuskansa cikin nata  Da karfi ta turesa ,na Fada maka ka kyaleni nace bana sonka  Just shut up faryal,ya daka mata tsawa" duk wannan surutun ki is useless   mahifiyarki bata gaya miki an bani ke bane? Meyasa zaki na kula wani   Kin rainani ko? Yafada ranshi a bace kamar me shirin dukanta  A dan tsorace tace what,Allah ya kiyaye wallhy ba wanda ya baka ni  Mummy ai ba ita ke da iko akaina ba  Shakureta yayi yahada bayanta da sit din motar      
.
Hawaye ne kawae ke tsilala ba bakin magana wajen faryal  Kinaji na ,bazan dauki wulakani da iskancin ki ba ""yanzu ba da bane got it?  Kuma Tunda taurin Kaine dake namiki alkwari zan koya miki tarbiya da kaina nan gaba Naga alaman gidanku basu farsa miki baki ba  Wani mugun kallo faryal ke binsa da shi  And one last time yafada yana mata wani mugun kallon shima  Kifada ma duk wanda ma yake rudin Kansa akan ki,   haduwar mu dashi bazai yi kyw ba  Tari ta farayi sosai kafin ya hankara ya sake mata wuyan ta  Kuka kawae take yi batace uffan ba...domin kuwa ranta a hargitse yake da Bacin rai  Bai saurareta ba ya ja motar ya kaita kofar gidansu Da hanzari tafara Kokarin bude wa taji GAM an kullee,  Hannunshi taji a bayanta yana cewa baby am sorry kinji,kije gida ki huta  Bata sanblokacin da ta joyo ba tana watsa masa wni zazzafan harara " Azzalumi': mugu ,allah ya tsine maka,tafada cikin wani sabon Kukan  Bab...ka bude min Kofa khalid tafada a hatsale  Ai Da sauri ya bude mata tafice  Kallo ya bita da shi har ta mule gidan nasu   kaga fuskarsa a lokacin wane maraya "kamar ba shi yagama shaketa ba  .
.
Abokantakar zafar da siyama da ta sauya ta dawo shakuwa da soyyaya kullum manne take dashi   Ranar jumuah da misalin karfe 6saura na yamma suka shigo gidan alhaj garba tare  Siya,hope u had a good day with me? yafada yana kallon cikin idon nata Murmusawa tayu ta kamo hannayensa  Zafar mu shi Shiga please, kullum Baka kaunar ka shiga ciki No cwety ba haka bane kinga is alrady late fa  Uhm ban yarda ba  amma ni ai ena Shiga gidnku ko ko yaushe ne   bahaka bane ,am just in a haste Amma musamman zanzo   Bai ma karasa zancen NASA ba " sukaji karar horn maigadi na kokarin bude kofar gidan  Yawwa my dad,dama ka Dade Baku gaisa ba tafada tana yake  Rusunawa zafar yadanyi ya gaishe sa   Zafar ne dady,my boyfriend tafada tana dan murmushi  Ohh""""  ayyah to shigo cikii mana yafada yana tallabo kafadan zafar  Yes sir zafar ya ce   nan suka jera zuwa ciki  A zauna tare a valour .yace ya babanka I hope kuna lpya Lpya lau dady,  Good " make your self comfortable, Yafada yana mikewa ciki  Bai jima ba aka fara masa formalities na abinci kala kala  Badin yaso ba don' dole ya zauna yaci abincin da aka jera masa shima  .soyyayr su da siyama ta samu asali ne tun lokacin dayake england, don kuwa siyama a duniya batada amini dayake dauke mata kewar rashin uwa kamar zafar   tun bayan rabuwarta da kamill Daga nan Abun ya zarce har aka furta ma juna kalman soyayya  Zaf,tafada tana maida kallonta kansa  Ya dai Hajiya enajinki,...zo muje kaga wani abu Dan zaro ido wajee yayi yace ae'na siyama" ko ena shiru agaidan nan  What tafada tan dan yatsina fuska  ;' CE maka akayi muna cin mutane,         c'mon durling" tasoo , tafada tana Jan hanneyan sa  Wani daki suka nufa tare wanda aka masa kwalliya tamkar kana gidan zinare ne  Ko ena an masa adon kyale kyalen gold wajen sai sheki yakeyi  Zauna mana "tafada ta mike zuwa wani wardrobe  Wani akwati tadaauko me shegen kyw ta bude masa a gabansa  A hankali yasa hannu ya dauko hotunan da yake ciki  Wata kywawiyar mata CE yagani rike da karamar yarinya da ba sai an gaya maka siyaman bane " da  kuma khalid a gefensu  Your mum? Ya tambaye ta idonsa akan hoton Yes ,she died plane crash on her way to Casablanca run ena 4yrs Allah sarki" Allah ya jikanta ya mata rahma,  Ameen zafar. Nan suka cigaba da fitar da pics kala kala Ciki kuwa harda hotonan alhaj garba lokacin yana yaro   Wow dady fa thug ne da can a zamanin su"" zafar dubi wani makeken tattoo a kirjinsa!! ,siyaman tafada tana dariya  Nan shima ya sa ido yace wow ,kinsan mutanen da bakamar yanzu ba   Our parent wil go crazy in mutum yace zaiyi tattoo yanzu  Said ace ka dawo dan iska Amma what does it stand for naga kamar zanen monkey?  Yeah dad yace shida friends dinsa ne sukayi duk iri daya Kagane irin peer group haka  Tabe baki yayi yace  Ohh that's nice , ..
,
Agogonsa ya duba yaga already six ya dau hanyar gaucewa  Baby let's get going,zanyi sallah na wuce gida . Dan hararsa tayi taje ta kulle kofar  sannan ta jefa key din A bra dinta yana kallo  Ufff siyama meye hakan ne wai?bani key din pls yafada yana mika mata hannu  Dan hararsa tayi ta Dada daga boobs dinta tace "sai kasa hanu ka dauka zafar   Haba siya na" kinsan bazan iya ba ai ko,to meye dalilinki na ajiye ni a gidankun enajinki  Tamke fuskanta tayi kamr ba eta ba,tace just sit kawae     Dan dolensa ya nemi waje ya zauna  
.
  Ya Dade yana lallaba ta ta cire tabasa haka taki fir har akayi maghrib  In kaga na baka key din nan" toh kacire ne da hannun ka and don't touch my boobs tafada fuskarta a shake ' Yau na Shiga uku siyama ",shikenan , I surrender Mi kikeso nayi miki toh,? Tell me kinga dare nayi" kuma Yau fa kinsan tun safe Muke tare koo  So? Ko banyi derseving time dinka  bane zafar? Sake daure fuskan tayi ta juya masa baya   baka gama cinye ranar ba ne " ai full day kace zaka min yau   Dan mirmushi yayi sannan yace  Toh naji madam,when zan tafi   Babu rana tafada tana tura baki  Dan shiru yayi sannan ya matso kusa da ita ya langwame fuska yana kallonta ,siyama what's is the problem?  Juyowa tayi jin sassayar murynsa na kokarin kashe mata jiki, Take idanun ta suka cike da kwalla tace masa,I'm so lonely zafar" I missed my family, my mummy, I want a family," Nagaji da rayuwa nikadai":;;       Dad hardly ka gansa a kasar nan" ko ya zo ma bai fi mu hadu few times ba sena Neme sa na rasa  Zafar tun ena karama "gashi yanzu har na saba da hakan ta fada tana taro hawayen ta daya fara sauka    Cikin sanyin murya ta sake cewa and Khalid is just like dad running from one place to another in search of fame       dan dago kanta tana kallon cikin idon sa,don't I derseve to be happy?  Kallonta shima ya keiyi a sanyaye "ga tausayin ta da ya keji na shigar sa   Kai kadai ne kake sanyaya min rai na"    just imagine yadda zan kasance ko yan zun nan in ka fice,  Nika dai ce,no one will be here with me Sosai ta fashe da kuka a gaban NASA,har ta Neman isa kasa   Shhhh yafada yana jingina ta a kirjinsa,     a hankali yake buga mata bayanta kadan kadan kodan ta sassauta kukan data keyi  Sosai tabashi tausayi,rashin uwa da family babban rashi ne komin arzikin mutum a rayuwa   Dada shigewa jikinsa takeyi ta na kakkame shi cikin yanayi mai tada hankali da kyr ya samu yayi controlling dinta tabar kukan  Siyama let's stop....zafar ya fada a raunane  Kallonsa tayi da jajeyen idanunta tace Baka so nane,?"u hate to touch me zafar"      da Sauri ya rufe matA baki da dan yatsan sa No siyama "ba haka bane,I love you so much more than anything else  To meyasa kullum kake avoiding dina,?not even a kiss da ka ta min_  Oh C'mon love'kinsan Don' ena sonki ne siyama,let's not defile our selves tun yanzu kinji?  I want to prove it to you that son da nake miki has nothing to do with your body kinji?  Mikewa tsaye tayi a fusace tace Nooo ni ban yarda ba" ,yanzu na gama nuna maka sirrin gidan mu baki daya ,na nuna maka maka waye ni ba wanda na taba kawo shi nan   Its a Secret room na family na .
.
Amma meyasa kai bazaka proving min ka yarda dani ba  Siyama I know,wai meyasa kike ganin kamar bana sonki ne?  Ba gashi ba tafada a zafafe ,Sauri kake ka tafi ka barni "'.       baka son kazauna tare dani ";I have to beg u to stay"  ta karasa cikin muryan kuka  Hannu tasa a boobs dinta ta fito da key din,ta mika masa gashi ka bude   Share kwallanta ta hau yi tace emmm thanks for keeping me busy today  ta juya masa baya  Jitayi an kamo waist dinta daga ta baya  a hankali   "juyota yayi tana fuskantar sa,numfashin su na gugar juna Sanyin labbansa taji akan nata sosai ya ke tsotsar bakin nata   Lumshe idonta tayi etama ta biye masa sanda sukayi mai isarsu " kafin da kyr ta bude ido ta kallesa,  I love you siyama,please trust me...kinji? Ya fada yana dada Jan ta kan kirjinsa Lamo tayi tana jin bugun zuciyarsa wani sabon kaunarsa ne ke ratsa jininta   Da kyr suka rabu hakan wajen 9.30 saura ya fice ya nufi gida   Kameel ne kwnace shima Tunanin mahaifiyarsa CE kawae a zuciyarsa   take wani hawaye ke Neman saukowa kan kuncinsa. Mikewa yayi ya dauro alwala yasa hannu  ya dauki qurani ya cigaba da karantawa  Har bacci tayi  awon gaba dashi   Washe gari da safe khalid ya fito cikikn shirin fita office.  A bakin mota guard dinsa ya tare sa "Ogah duk abunda kake so yana cikin nan guard ya Fada ma khalid tareda mika masa envelope  Budewa yayi ba jira,tuni ya dakata ransa yaji ya mummunan baci a take" ganin hoton daya fado a cikin envelope din  Wani busashen dariya yayi,I see Kammil ne dama?I knew it Yarinyar nan is so cheap da wannan shashashan zata na hada ni ? Amma bakomai tattara sauran information din ka ajiye bana bukatrsu yanzu  Ogah amma yakama ka duba fa" guard din yace a dan tsorace  Bari kawae Nasan shi ai gaba da baya,kake kawae     Mumushin keta yayi yana ciza baki....... A ransa yana cewa '  "kamil the battle is just about to begin      Tsakanina da kai zanga wa zai winning Muzuba 
.
Gabanta ne ya hau dukan uku uku ,ganin sunan alhaji garba kan screen  Hannu ta sa ta dauka hello alhaj,ranka Dade  Hajiya Mariya? An wuni lpya   Kalau,alhaji lpya kuwa naga ka kira da wannan lokaci   Eh toh,  kinsan dalilin da zai iya sa nakira ki ai                     "yaro Yazo min da korafi akan yarki tana wulaknta sa akan wani yaro.     Anya Hajiya kina aikin ki da kyw kuwa?  Da e"e na tace alhaji dan matsala aka samu amma insha Allahu ba za a sake ji ba ma   Dama kinsan da hakane?  Ah a wallhy alhaj, nima ban tabbar ba      saboda faryal da ba enda take zuwa inba makaranta ba ena zataga wani saurayi? Kawae dai bazaka Sha bakin uaro bane  Dan dariya yayi sannan yace  Hajiya kenan "ai yaran namu ka haifesu ne baka haifi halinsu ba  Kedai nabaki dama ta karshe kiyi bincike ki warware matsalan nan nan da wata daya   Inba haka ba to fah karkisha mamakin hukuncin da zan dauka akan Ku gaba daya da yarkin  Ayi hakuri alhaji,kafin nan zakaji kykkwan labari na maka alkawari   Toh Hajiya wannan ya rage naki nidai kywkkwan labarin kawae zan ji daga gare ki  Nan ya katse wayarsa  Sauke ajiyar zuciya Hajiya tayi ta nufi dakin faryal.      bata ganta ba yasa ta juyawa domin zuwa gidan Hajiya shafa   Kawata lpya naganki haka kuwa?  Ena lpya fa alhaji yaji labarin kamil da faryal?   Yanzu haka danake Fada miki wayarsa nagama ansawa yabani wata daya na kunce komai tsakaninsu  Tab,amma anyi tsinannen yaro wallhy,            faryal ma inbanda kyal kyal banza me zatayi da ShI?   yaron da ba yida asali ma Gane min fa shafa,ke bar wannan agefe anemi abun yi tun yanzu kar abun yazo ya kufce mana a kukrarraen lokaci  Dan shiru shafa tayi sannan tace,nikam mariya me zai hana muje gidan mallam zanah,ko rabasu yayi  kowa ya huta  Dafe kirji haj mariya tayi tana cewa A ah shafa ,banda malamai,           alhaj yaji labarin nan kinsan ranar zan bar masa gida ko,  ballantana Inda yasa yaron nan aransa "Idan nayi wani Abu ai na Shiga uku Gaskiya nemo wata shawarar  Kai mutumiya ta akwae tsoro, To gaskiya kibani lokaci ko gobe ne sai na San me zamuyi akan su  Yawwa ko kefa shafa, kinga  Barin ykoma gida kinsan baisan nafito ba Tafada tana mikewa Sai naji ki,  Saur i takeyi zata tafi schl Yau evening lectures ne da ita A bakin gate suka hadu da shi inda tayi kokarin komawa ciki da sauri amma ya damko ta sanda ya fitoda ita waje    Da Allah malam sakeni tafada tana ture hannunsa   Ke dan rainin wayo da kaamil zaki hada ni takara?  Wani dariya ta fashe dashi,taja tsaki zata wuce Janyota yayi ya jillata gefe saura kadan ta zube kasa  Nasan baka da hankali khalid basai ka dada bayyanawa anan ba   kaje can gidanku na rash in tarbiya na azzalumai kayi ba anan ba  Kai hanu yayi zai sake janyota zafar ya tare, Wani huci yakeyi kamr zai hade ransa  Khalid me haka ka kyaleta ta tafi schl,  Kai kuma asuwa?da Allah malam stay out of this . 
.
A zuciye zafar yace masa innaki fa,akwae abunda zakayi ne?  Wani mugun kallo ya bisu da shi kawae ya juya ya fita,            don kuwa khalid a baki ne kawae ba'a yar hanu da shi..lol  Are you OK? Zafar ya tambayeta da dan damuwa a fuskan sa       Am ok yay  zafar,karka damu.    Toh shikennan  Zo ki wuce   
.
Haka khalid ya cigaba da sa bin cike akansu kamil da faryal  Sannan  Yasa ana bibiyansu duk yadda suke haduwa ya sani  Ranar tun misalin karfe 4 na yamma aka fara ruwa  Ruwa sosai akeyi kamil ma har bayan isha  ko gida baisamu ya koma ba  yana office yana ta aiki abunsa  Karar waya CE ta hankarar da shi.   Dan Murmushi ya sake kafin  ya sa hanu ya danna yace  Ruhi is missing me right?  twinsoul kana ena ne,I'm stucked, motar driver  yayi blocking akan titi . Gashi wai yaje neman mai gyara tun tuni ina kan titi. Kuma kaga tun dazu  ana ruwa bai dawo ba  am scared twinsoul dan Allah kazo tafada a shagwabe  Wani kan titi kike?nan ta masa kwatance enda take din  Ciki Minti 35 ya taho wajen  Hangen motar yayi da kyar sabida iska da ruwan tazo da shi   Ga duhu dare ya farayi    Ta cikki ta bude masa ya shig yasa meta Am sorry ruhi,ruwan ya tsananta bana gani sosai,banzo da wuri ba ko?  Are you ok? Yafada  da fuskar damuwa  I am fine,baga ka nan ba ta fada tana kallon sa da baby face.  Dan lakace mata hanci Yayi yace  Mutafi toh na kai ki gida  nasan shima maybe ya rabe ne a wajen mechanics din kinga ruwan yayi yawa  Toh muje ,ta fada itama tana kokarin bude motar  Rigar suit dinsa ya cire duk da jikar ya mata lema da shi suka nufi bakin nashi motar Ganin yadda wuri. Yayi duhu ga ruwa na sauka kamar da bakin kwarya yasata kan kame shi sosai don' tsoro  Dolensa ya tsaya ya dauke ta i chak ya wuce da ita motarsan ya rufe   Gaba dayansu sun jika sosai ,harta bra dinta sanda ya nuna boro boro ta cikin rigarta  A hankali yake tafiya dasu ,Barin ma faryaal data kan kame shi sosai, taki Barin jikin sa  . Gaba daya hankalinsa baya jikinsa soboda dumin jikin ta dayake gogar nasa   Twin soul mutsaya mana is dark,tafada kamar xatayi kuka  Ok Barin nemi waje,dan wani fili ya samu yayi parking sannan ya jingina kansa kan sit shima  Sanyi tafara ji sosai tana nemar fara karkrwa  ruhi yadai ya fada yana tallabo fuskarta Narkewa ta farayi ajkin nasa da wani salo mai kashe jiki .   gashi a yanayin  da take kusan komai na jikinta a bayyane ne  Balle button din jikkaken rigarsa ta Shiga yi ahankali  shiko  bai hanata ba har ta kammala,.wani dumi ta jiyo a jikin NASa tuni ta shiga goga fuskanta Akan faffadan kirjinsa  Lumshe idanunsa yayi yanajin abubuwa na masa yawo har tsakan kansa a take . Lura da shiru yasa ta fahimci abunda takeyi ne yasa shi jikin wannan yananyi . dakata wa tayi sannan ta Kai kallonta tayi dai dai fuskarsa tana kare ma kyykwan halittarsa kallo  A hankali ya soma bude idanunsa da suka rine sukayi ja  Tallafo ta yayi ya hada goshinsa da nata .ruhi zaki kasheni ko?  Kar ki sake min irin wannan kinji yafada yana murmushi  Kokarin turo baki tayi tsam taji ta daura akan nasa Batayi wata wata ba ta fara aika masa sakonni kala kala na kisses  Da kyr ya controlling kansa,ya daga ta  Ruhi please_ yafada yana rungumota jikinsa  cikin sanyin murya tace Twin soul toh ni xan kwanta tafada tana dada mikewa kan kirjinsa  Daura Kansa yayi kan kafadan ta sukayi shiru bawan da yace uffan Kowannen su yana tunani kala kala aransa  Basu hankara ba kuwa bacci ne mai nauyi yayi awun GabA dasu awajen basu da farkawa ba sai 6 na safe  
.
  Hasbi nallahu wa neemal wakeel faryal"  ,tashi its 6clk ..  Idonta ta bude kamr a mafarki take jin maganan sa  Da sauri ta mike ta CE twinsoul safiya CE fa? Bai tsaya sauraren ta ba ya kunna mota a guje suka nufi gida  Sallan safiyai tayi kafin ta fara kokarin shafa cream dinta  Ban kado kofar taji anyi da karfi   a tsorace  ta juya,har cream din ta ya fada kasa ta maida kallon ta bakin kofar  Tsayawa haj mariya tayi tana kare mata kallo inda ita kuwa sai bari take faman yi a tsaye Cikin sanyin murya tace mummy ena kwana    Faryal INA kika kwana jiya? Tafada da normal muryanta  Mummmyyy......ruwa ak...e...yi  Faryal """hajiya ta kira ta cikin tsawa  Ki Fada min ko naci ubanki. Yau kashe ki zanyi a gidan nan idan baki Fada min Inda kika kwana ba    tafada tana jan hannayen ta gaba  Kuka faryal ta fashe dashi sosai.  Mummmy wallhy a mota na kwana  Mota? Motar wa ? Wani ubankin ne ya baki mota da zaki kwana aciki ," Bayan na sa a dauko ki a enda driver ya ajiyeki ba a sameki ba  Mumy wallhy har bayan isha ena wajen shiyasa........ Yi min shiru ai idan Karya zaki mun,ai bazaki ma ubanki ba ko Nan hajiy tafara yunkurin fita  zuwa site din abba  Da Sauri faryal ta kamo hannun ta  mummy wallhy dagaske ne a mota na kwana na rantse miki mummy tafada tana kuka  Fincike hannun ta tayi tace faryal motar waye?  Ehm ummm emmmm.....  Ke,kifada min kar na taka ki anan wajen motar wani shegen kika kwana  Da kyr faryal ta sassauta kukan tace motar yay kamil ne mummy  Wani wawan mari taji a fuskarta  Na Shiga uku faryal? Me ya miki "me kuka yi?  Mummy wallhy ba abunda mukayi na rantse....janta Hajiya mariya tayi ta hau jibgarta   Ashe asiri na KiKE so ki tona a garin nan,me kika SANI da zaki bada kanki wa namiji  Gardin banza,  kwana da wanda ba muharraminki ba faryal?  Mummy dan Allah kiyi hkiri wallhy ba abunda mukayi  Ki min shiru dan ubanki, Yau sai na hadaki da ubanki   Ihu faryal ta sake awajen tana rokon mummy data ke faman masifa tana bori  Munafuka Niki sake min kafa ai Kin girma yanzu tunda kika san ki kwana da da namiji  Karar wayanta ne ya dakatar da ita  Shafa na gode allah da kika kira  Meya faru mariya kukan waye haka nakeji kamar faryal An sameta ne?   Bar shegiyar yarinya bayana take son gani? Wai ace faryal ta kwana a motar kamil,kiji min wannan badala fa   Sallamewa haj shafa tafara sannn tace ,ke mariya ki nutsu kiji abunda zan Fada miki kije gefe  Bayan minti 5 tasake shigowa hango faryal tayi ta takure a gefe ta hade kai da gwiwa tana faman kuka   Wallhy ban gama dake ba faryal,.... Saura shi kuma munafiki azzalumi ma cucin yaron   Yau zai gane kuransa,tana kaiwa nan ta fice  Kuka faryal ta sake fashewa dashi,tana kokarin daukar wayanta da ke faman ringing  Ruhi,ya dai inata kiranki shiru ? Wani matsanancin Kuka ta  sake fashewa da shi,  A daburce ya ke jero mata tambayoyi kala kala   Da kyr ya samu ta bashi labarin abunda ya faru  Innalihhi wa inna ilaihi rajiun,am soo sorry ruhi kiyi hakuri, Ni na jawo miki,ki yafe min kinji?  Noo twinsoul..... ...shhhhhh ruhi kinsan ya zaayi? Ki kimtsa kanki ki je kiba mummy hakuri kafin nadawo  muntafi bauchi da zafar Amma Gobe zan dawo ok?  Ok tafada da disashhen muryanta, Kisha magani ruhi,take care for me kinji? I love you  Love you too twin soul,bye tafada ta mike ta fara suturta jikinta   Har bayan isha ranar bata leko waje ba Saboda  Tsoro ne tam cikin ranta haka ta mike ta fita don' kamill ya takura akan taje din  Da sallamrta ta Shiga har cikin bedrum din mummy  galla mata harara tun daga kofa tayi tace  Meya kawo ki? Tsugunawa faryal tayi jikinta na rawa tace mummy dan Allah kiyi hakuri bazan sake ba wllhy ...nayi kuskure  Murmushi haj mariya tayi sannan tace,toh ni INA ruwa na na Riga na Fada ma ubanki kijira shi yadawo Ku karata chan  Ihu ta fasa ta fara birgima awajen,mummy dan Allah..... "ke kimin shiru karki sake ki Tara min jamaa'h  Nan Hajiya ta kalleta a nitse tace faryal? 
.
Zan baki dama daya tak, ki ceci kanki da shi munafukin saurayin naki daga sharinn Dana ke shirin kulla muku wajen ubanki  Mummmy sharri kuma   Eh,ai in na fada masa gaskiyar naki bazata kama hanakali ba ne  enba sharrin zan fada ba wazai yarda baliga da valigi sun kwana waje daya ba abunda yafaru??  Bayan a ido na ranar kike rirrike sa  Sunkuyar da kai faryal tayi ,mummy wallhy .."".ke ni banson jin wani rantsuwarki  Inkin yarda da abunda na nzo miki dashi to in baki yarda ba  Ga hanya out,,,sai ki jira hukuncin ubanki dake da shi din  Ah a mummy koma meye ne zanyi dan Allah kar ki min sharrin  Dariya abun ya ba ta amma tadake tace ban yarda ba ki wuce kawae kifita min na FASA baki damar ma  Kuka faryal ta sake fashewa dashi tana rokonta  Toh ya isa,zoki zauna nan  a sanyaye faryal ta zauna kan kujera a gefen mirror   Kimin alkwari zaki na kula khalid sosai .sannan zaki rabu da kamil shikenan  Na miki alkwari Dake da shi kun kubuta har abada.  Zaro ido faryal tayi Ta mike tsaye hawaye nabin kuncinta  muryan ta na rawa tace mummy Na rabu da kamil?  Wani harara Hajiya mariya ta galla mata, ah Ah faryal kije kuci gaba da shashancin ku  Laifi nane da na baki Dama  Kafin na rufe ido na  bude kin bace min a daki "get out tafada cikin tsawa   Faryal din ma bata San lokacin da tayi waje ba dan tsoro  
.
  Kallonta mummy ta tsaya yi ,...   Sannan ta kau da kanta ta daure fuska  Shiru faryal tayi ta rasa abunda ke mata dadi, Bude bakin ta tayi tace mummmy....  Ki fice nace miki kar na faffasa miki jiki anan   Mummmy dan Allah ki zanca min zanyi kowanne amma wallhy bana son khalid mummy   Karki so shi mana, shima kamil din naki daga yau mahaifinki bazai kara amincewa da shi ba  A idonki za a masa koran kare Yau din nan ba jira  Haba mummy don' Allah kiyi hakuri,   kar ki rabani da shi ta fada cikin kuka   Toh shikenan ai, ni dai na gama baki daman da zan baki ta shi ki tafi ki bani waje kawae Sha shashar banza  toh wallhhy kisani   faryal duk abunda ya faru daku kiyi kuka da kanki  Da kyr faryal ta dafa zuwa cikin dakinta,  ranar ko runtswa ko ena  ba tayi ba duk ta kulla nan ta kunce can  haka har Kiran sallah ya shigo  Raka 'a biyu tayi   Kafin tayi sallan ta Adduoe sosai tayi . .    sannan ta mike zuwa dakin mummyn   Kallo mummyn ta bita da shi dan har cikin ranta ta tausaya ma yanayin faryal din duk fuskar ta sun haura,jikinta sam ba kwari  Me ya kawoki kuma? Ena wuni mummy  ta fada a hankali Lpya lau enajinki_  Mummy Dama.....Dama Ehn dama me? Faryal  Na amince zanyi abunda kike so,amma mummy dan Allah ki kyale yay kamil " ba laifin sa bane ,nice dama nace yazo ya dauko ni a schl din Ta fada tana share hawayen ta.  Alhamdulilhhi,yawwa auta ta ko ke fa,ai in cewa kikayi kar na sake kula sa mai sauki ne awajena Muddin kin amince da komai  Shiru faryal tayi,tana kan goge hawayen da suka ki tsaya mata a idanun taa  Toh tashi kije ki kwanta ki huta my princess, Yau kika dawo cikkaken yarinya mai tunani da sanin ya kamata  Itadai faryal bata CE uffan baa haka ta mike ta nufi dakinta a daddafe  Daga wayar ta tayi taga misdcols dinsa har guda 3 da TeX mssg guda daya Sa hannu tayi ta kashe wayar gaba daya ta jefa sa kan cushion   Wani Sabon kuka ta fara A hankali take furta am sorry twin soul, dole zan bi ta wannan hanyar na ceci mutuncin ka a idon abbah Sulalewa tayi kasa ta cigaba da rera kukan ta  Karfe Tara na dare,ya fito kofar gidan hankalinsa a tashe tun safe  Baiji muryn ta ba kuma bai ganta va  Hasken mota ne daya doke sa a ido ya sashi tsayawa yaga waye ne da Daren nan  Wani zafi yakeji a zuciyarsa wacce take nuna masa faryal dake fitowa daga motar khalid.,..  ganin yadda kamil din ya tsura musu ido yan binsu da kallo  Khalid  yayi amfani da hakan yafara Kokarin rike hannunta   Gashi ya ci saa Sai ta mika masa hannun  A lokacin ba gardama   Duk da ma yasha mamakin rashin hanashi da batayi ba  Wani murmushin ya sake" a ransa ya na farin cikin sauyawar al'amarin  Faryal? Kamil ya kirata dab zata wuce shi ita da khalid   KASA daurewa tayi ta  sake hannun khalid din ta juyo   Kasa kallon sa tayi saboda irin sauyawar da ta gani a cikin kwayar idanunsa Ena kika fito?.  Na fita da khalid ne Ta fada tare da dauke kanta    duk abunda takeji alokaci. Kokarin dannesa takeyi Tace yaya kamil gudnite   Har ya bude baki zai yi magana...yaga tayi sauri ta wuce abunta   Kallon mamaki yabi ta dashi,  Kafi.n Ma ya lura da khalid dake gabnsa a tsaye  Mr kamil yafada hade da fashewa da wani mugun dariya  Look khalid just leave kamil ya fada ransa a bace   ,a gidan namu? Haba kamil" Yanzu tsakani na dakai ai Kaine zancewa leave a gidan nan  In karya ne ka tambayi faryal_   Tsaki kamil ya ja ya dauke kansa akan Khalid da ke faman masa dariya  Har yar juya xAi baar wajen yaji ance  And one last favour kamil"  kaga ka bata mata rai kasa ta tafi baka bari munyi gudnite ba  Pls tel her I have a great day today,_and I'm missing her already  Blowing masa kiss yayi yace  Hey not for you, for her  Ya juya ya fice yana dariya ciki ciki   Bari kawae kamil yake yi,gaba daya zafi yake ji a kirjin sa kansa na wani bugawa  A fusace ya shige ciki ya nufi dakin ta   Murdawa yayi yaji GAM an kulle ta ciki  Dakin sa ya koma ya zauna Still layin ta ma ya dinga kira akashe   Haka dai yayi tayi shika dai ba response hr bacci ta dauke sa shima 
.
   Da kyar ta tashi ta shirya zuwa makaranta ranar  Duk yadda kamil ya so ya ganta haka taki Ranar har lati yayi zuwa wajen aiki son jiran ta ta fito   Haka faryal ta dinga  Share kamil,karshe ma wasan boya ta fara mishi  Bayan  wata daya da hakan ranar Musamman alhaji garba ya kira haj mriya ya yaba da sauyawar faryal akan khalid  Sosai haj mariya taji dadi din kuwa har wani contract din yasa aka mata signing daga Abu Dhabi,a Dubai  Domin a duniya yaran sa ne am na farko a muhimmaci kafin kowa,Alhj garba yakan iya komai akan khalid da siyama  Riketa taji anyo da karfi sanda tadan yi kara ouucchhh   Ruhi mena miki ya fada yana kokarin juyota ta fusknce shi  Ka kyale ni yay kamil, stop it ta fada tana kokarin kwace hannunta,  Bazan kyleki ba not until Kin Fada min komai what's happening? Dan Allah me namiki ke ki azabtar dani haka  Kifi kifi da ido tayi tace bakomai ,look I'm not in the mood  What ? Saboda me faryal?  Rau rau da idonta tayi tace saboda yanzu........  yanzu khalid ne bani ba ko? Tell me angel why? Meyasa zaki na kona ni haka " kinki kibari ma mu hadu  a month kenan yau haba faryal? Kifada min mana why are you hurting me angel? yafada kamar mai shirin yin kuka  Duk maganan daya keyi idonta a kasa yake,saboda ita kadai tasan abunda take ji a ranta a lokacin  Girgiza ta ya sakeyi,yace kifa da min mana   Cijewa tayi ta dago kanta idanun nan a bushe tace Yay kamil nifa ba abunda ya faru... Imma akan tarayyar mu ne Its over between us please forget about me  Ka daina Shiga hrkata pls .saboda bana...  .shhhhh ya fada Yasa dan ytsansa a bakinta  Faryal kar kice min baki sona please, Stop hurting me .....I know akwai dalilin dayasa kike haka meyasa bazaki Fada min ba  I swear to you I will do anything to fight for us,I can't live without you faryal Kiyi hakuri pls,ya fada har jikinsa na rawa  Kuka ne yaso yci karfin ta  amma haka ta sake dannewa  Da karfinta ta turesa daga jikinta, Nafada maka its over, ni khlid nake so yanzu Meyasa bazaka kyaleni ba tafada cikin masifa da zafin rai  Faryal khalid kike so?   Yes ta fada cikin tsawa  ,kuma yau ya zamo na karshe da zaka na damu na....ai yanzu na warware maka it's over Ta wuce ta barshi tsaye awajen  In banda its over da ta fada ba abunda yake maimaituwa a kwakwlwan sa, tsaye yake ko motsi ba ya iyayi  Gefen wani empty lecture hall ta koma da gudu ta zube gwiwarta akasa tana rusa kuka sosai   Im soryy twin soul,I know I'm hurting you Ba yadda na iya ne.... take fada eta kai awajen   Da kyr  ya tattara hankalin sa ya koma gida, Wani zazAbi ne ta rufe shi a take   Haka rayuwarsu ta cigaba,har tsawon wata hudu ba abunda ya sauya Sai dai ma Karin rashin mutunci da khalid yake masa karara duk lokacin da yagan sa da faryal din  Tun abun na damunsa har ya fara amincewa da shawarar jabir  akan ya kyaleta tunda decision din ta ne  Sanye da bakar wando yake Jordan hade da cool bright yellow polo shirt hadaden agogon wayar sa ya daura a hannun sa na hagu da Paris hand band masu kyw a dama  Kallo daya kawae bazai isheka ganin kwalliyar tasa ba,domin kuwaa ya fito sosai  duk da dan Raman da yayi kwana biyu amma kwarjini. Na nan a Tattare dashi  Ba faryal ba har shi Khalid maida hankalinsa yayi yana kallon sa da yake tahowa  ko kallonsu baiyi ba ya wuce  Motarsa kirar Mercedes benz c class ya nufa ya yi hanyarr waje abunsa  Sosai ranta ya sosu don' har cikin zuciyrta ta tsani taga ya fito zai je wani wajen  gani take kawae wata zata gansa awaje ta kyasa  Baby yadai,naga kin wani bata rai kamar mai shirin fashewa  Niko? Tafada muryanta na dan rawa  Yeah,kodai kishin tsohon Zuma ne ya taso  naga kallonsa kike tun dazu  Khalid just stay out of this...bani kake so ba and here I am....bana son wani surutu tafada tana dauke kanta  Afuwan baby,yafada yana hada hannuwansa duka biyu   Gobe zamu je shopping tare da su siyama is best ace we are all there koh,all couples out   Ya fada yana kashe mata ido  Ok Allah ya kaimu,  Da rana misalin karfe 2.30 Zafar yA dai ,mummy tafada tana kallonsa da ya tsura mata ido  Nemar waje yayai ya zauna kafin yce mum meyake faruwa?  Aena zafar? 
,
Faryal mana mummy I hope bakida hannu acikkn sabon salon soyyayr da ta keyi da wannan marar kunyan yaron  Tohhhhh Ubana yazo kashe min warning  Mummy ba haka bane,  Yimin shiru malam,toh faryal din ne tayi rra'ayin haka  Bata karasa maganr tata  ba ma sai ga faryal ta shigo  Yawwa baby na Fada masa da bakin ki Ni nace ki shirya da khalid? Kallonta yayi da niyyan Jin amsarta  Dan shiru tayi sannan tace Eh  yay zafar ra'ayi na ne   Alhamdullhi to kaji ,  tashi kabar min Daki na  Kallo kawai ya bisu da shi sannan ya mike ya FIta baice komai ba  5 pm  da yamna siyama da zafar khalid da faryal suka shiga city mall ,babban super market ne wanda ba abunda babu aciki  Shidai zafar sosai sauyawar faryal ya daure masa kai  amma dai baida tacewa tunda mummy tace ra'ayinta ne kuma itama ta amsa da bakin ta  Haka kawae take jinta wani iri ranar Baby yadai Khalid ya fada yan kallon ta  Nagaji ne kahlid mu zauna please   Nan suma su siyama suka jona su kan table a cikin wajen fannin ice creams   Siyama ce tayi oda Aka ba kowa zabin sa   Zafar da siyama da hirarsu kawae sukeyi duk da ma ba sosai yake amsa wa ba  Don zafar ba ya yin khalid kwata kwata a rayuwrsa  Haka itama faryal da duk hankalin ta a tashe yake kuma bata San dalilin ba  Baby,baby Khalid ya kira sau biyu kafin ya lura da Inda take kallo  Kamil ne rike da hannun wata yarinya da bata wuce 12yrs ba Tamkar jinin sa CE tsabar kaman da suka so suyi  Da Sauri zafar ya mike ya nufi enda suke  Tare suka jera da kamil da yarinyar  suka nufo su siyama   enda faryal ta daure fuska sosai kadan take jira ta fashe  Sama sama suka gaisa da siyama  ko binta gansu baiyi ba ya juya abunsa suka fice da yarinyar  A fusace faryal tayi wurgi da ice cream din hannunta ba tare da ta San ta aikata hakan ba  Baby are u ok? Khalid ya fada a zafafe  Kallonsa tayi idonta cike da hawaye tace I'm ok nikan mutafi  Ta fada tana mikewa  Tabe baki siyama tayi tana jinjina ma kishin faryal din   Zafar ko kansa Dada daurewa yayi Aransa yace toh kishin me faryal xata yi da kanwar jabir.  Ba ta CE khalid take so ba?