SAKACI Part 21
© *Fatima A Garba*. Wanna karan Baba ne yayi magana. "Jiya bayan sallar isha'i, mun fito daga masallaci nida Alhaji, muka had'u da kawun shi Ahmad, bayan mungaisa, ya ce ya zo ne akan batun aurenku, mukace muna saurarensa, yace dama suna so a d'aga d'aurin auren" "Nidai ban iya magana ba, ga Alhaji nan shi ne yace toh mai yasa basu fad'a da wuri ba sai da aka gama gayyatan jama'a, sai shi kawun nashi yace shi dai d'an aike ne" "Alhaji ya sake cewa toh idan an d'aga har zuwa yaushe ne, sai kawun nashi yace zuwa lokacin da suka kammala shirye-shirye amma idan kin samu miji kafin nan toh fa kar a jirasu a aurar da ke" "Tabbas alokacin da zan fad'i na tabbata zan rasa wani 6ari na jikina, ni nasan na yi *SAKACI* tun farko amma ance danasani k'eya ce" "Waya na d'auko da zummar yin kira amma Alhaji ya ce wa zan kira nace zan fara sanar da jama'a anfasa ne, Alhaji yace min waya ce anfasa, t...